← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 152

Sashe 4

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki kunna fitilar yanzu, Ni kuma zan shiga ɗaki In ɗauko Akwatin kayan mu da backpack ɗin" ta amsa da toh, Batul na kunna fitilar Haske Ya gauraye ko'ina na ɗakin tsohuwa Tamira, Zazzaro ido su ka yi ita da Gabriel da mamaki akan fuskokinsu suke bin Bedroom ɗin da kallo, basu ta6a sanin haka ya ke ba, Yau ne rana ta farko da batul ta fara shigowa ɗakin tsohuwa tamira. Kallon Juna su ka yi ita da Gabriel Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu ba tare da sun yiwa juna magana ba.

Turo ƙofar ɗakin akayi da sauri suka kalli mai shigowa, Angel ce janye da akwati ɗaya na kayansu, Ta goyo back pack ɗin Unaiza saman bayanta sai ta yi tamkar Ɗalibar makaranta, A tsakiyar ɗakin tsohuwa tamira ta ajiye akwatin saman floor, ta kwanto jakar bayanta ta ɗaura ta saman table.

"Angel Har yanzu ba ki yi mana bayanin ta ya ya akai kika gane inda ƙofar nan ta ke? Waye ya faɗa maki kiyi amfani da ruwan zafi don shafen wurin ya tsage? after that Mun yi mamakin yadda akai kika buɗe ɗakin tsohuwa Tamira ko dai itace duk ta faɗa maki hakan"? Batul ce tayi mata tambayar a ƙagare da son jin amsarta.

"Zan baki amsar tambayarki amma kafin nan inaso ki kira mini su Haris su shigo ayi komai agabansu" har ta juya zata fuce da fitilar hannunta da sauri Gabriel Ya cafko damtsen hannunta tare da janyo ta baya yana fadin"So kike asirin mu ya tonu? Ina zaki da fitila"? Murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Na shafa'a ne" kar6ar fitilar yayi ita kuma ta fuce Jim kaɗan Su kaji an turo ƙofar Haris Ne agaba Deeja na abayan shi dasu Hibba a jere suka shigo Hada azeeza Hannah ce ta ruƙo hannunta.

"Wa ya ce ku zo da Azeeza? Ba a kwance ta ke ba"? Gabriel ne yai maganar Yana kallonta, Naufal yace"kasan halinta da rigima tafi son komai za'ayi ayi agabanta mutun na fama da makantar dare,"

Ranta ne ya 6aci sosai jin abunda suke cewa, fusge hannunta ta yi daga ruƙon da Hanna tayi mata, A ƙasa ta zuƙunna tana rera masu kuka.

Angel tace"Dan Allah ku rarrashe ta idan ba so ku ke ta tona mana asiri ba" Gabriel ne ya nufi wurin da ta ke a zuƙunne ya kai hannu ɗaya ya ɗago da ita kamar jira ta ke yi ta faɗa saman laps ɗinshi tana cigaba da kuka, Murmushi ya saki yana kallonta har mamakin Ƙarantarta ya ke yi,
"Its ok Share hawayen ki My Azeeza, kinsan bana son zubar hawayenki, Ko so ki ke Ajiyo sautin kukan ki asirin mu ya tonu"? Muryarta da shessheƙar kuka tace"A'a" yace"okey wipe ur tears, zan Goya ki abayana don bana son kisha wahalar neman ɗan jagora," yai maganar tare da miƙa ma Batul fitilar hannun shi, bayan ta kar6a ya zuƙunna Azeeza ta haye bayan shi ta ƙanƙameshi sosai, Ya miƙe ɗauke da ita"

Angel na ƙoƙarin fara yi masu bayani muryar jemimah da suka bari ita kaɗai acikin ɗaki ya karaɗe kunnuwansu ta kware baki Tana ƙwala mata kira"Genie! Genie! " da sauri Angel ta nufi ƙopar ta buɗe ta fuce, Bayan fitarta Hankalinsu Ya koma kan ɗakin da su ke a ciki na tsohuwa Tamira Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu su ke yi, Parveen Acici Tana Hango Wannan Tea pot ɗin da ƴan kofuna biyu jiki na rawa ta nufi table ɗin dake ɗauke dasu, ta zauna saman kujera tare da ɗaukar pot ɗin tana jijjigata don taji idan akwai ruwan shayi aciki,

"Kada ki kuskura ki ce zaki sha, Kawai daga ganin abu bakisan tsawon lokacin daya ɗauka a ajiye ba kin ɗauka zaki sha da ya ke ba ki da linzami indai akan abinci ne" Deeja ce ke yi mata magana, Saboda kafiya irin ta parveen ko kallo bata isheta ba hada cewa"dama kin daina wahalar da kanki wurin yi mini magana don wlh saina sha tea ɗin nan" Tsawa haris ya daka mata"Zaki tashi ko saina 6ata maki rai"? Murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi"Wai ku ina ruwan ku dani ne? Cikina ne ko naku"? dafe kai Hannah ta yi tare da cewa"ku ukun nan kunfi kowa jaraba dake da Azeeza sai waccan ƴar jemimah, Ni inaga Idan mun tashi tafiya mu bar su a kurkukun domin kuwa nan yafi da cewa dasu, in ba haka ba zasu ja mana ne" Jin maganar Hannah yasa azeeza dake kwance bayan gabriel ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, saboda ance za'a barsu a kurkuku

"Pls Hannah stop saying that, na samu na rarrasheta gashi yanzu kinsa ta kuma fashewa da wani kukan" acewar Gabriel, ta6e baki hannah ta yi ba tare da ta tanka mashi ba.

Daƙyar ya samu yashawo kan Azeeza ta daina yi mashi kuka, Parveen kuwa harta Tsiyaya Shayin A cikin Cup hada lashe baki zata fara sha, Kamar daga sama taji an damƙi wuyan rigarta daga baya, da sauri ta ɗago don taga wanene, dama saida ranta ya bata cewar shi ne

Harara ta shiga jefa mashi tare da murguɗa mashi baki, Ya ɗaure fuskarshi sosai babu annuri

"Tashi ki bar wurin" kaitsaye ya bata umarni, tasan halin shi sarai miƙewa ta yi ranta a6ace, bata so ya hana ta shan tea din ba, ta ƙwallafa rai.

Acikin hannunshi ya ruƙe nata sosai don kada ta kufce mashi ta koma shan shayin, Naufal kenan.

"Angel shiru bata dawowa ba, Tabar mu atsaitsaye cirko cirko, Ni bari ma in haye saman gadon tsohuwa in kwanta"

Rubina ce ta yi maganar, bata kai ga zuwa ta hau gadon ba, Angel ta turo ƙofar hannayenta biyu rungume da uniform dinsu, Jemimah na kwance saman bayanta, Ta ƙanƙameta da hannayenta, abunda ya jawo har suka daɗe Jemimah ce ta buƙaci ta rakata toilet zata zazzage cikinta, Shiyasa basu dawo da wuri ba, Sai da Angel ta jira ta gama tukunna ta kamota suka dawo ɗakin.

Ataƙaice Cikin daren suka jera uniform ɗinsu acikin akwatin kayan, Hada barguna Deeja ta ɗauko masu guda takwas daƙyar akwatin ya iya ɗauke su, Har saida suka rage uniform din dake a ciki suka turasu cikin backpack ɗin Unaiza tukunna ya ishe su, Bayan sun kammala sanya kayan suka datse shi, daga cikin abubuwan da suka dauka bayan uniform da barguna hada cotton scarves dinsu da Hulunansu sai rigunan sanyi da takalmansu, A cikin jakar unaiza suka saka Madubin da tsohuwa Tamira ta basu kyauta, ba su bar cikin ɗakin ba saida Angel ta fayyace masu komai dangane da tattaunawarsu da Salsabeel.Abu ɗayane bata fada masu ba komawar Danish Giant bata so su sani gudun kada su tayar da hankulansu. Haƙiƙa tsohuwa tamira ta kafa tarihi acikin zukatansu, A yau ta amsa sunanta na mahaifiyar su wadda ta raine su, basu ta6a yarda cewa tana sonsu ba sai yau da Angel ta labarta masu komai dangane da taimakon da ta yi masu, sun ji ƙaunarta sosai har suna fatan Allah ya haɗa su da ita kafin subar kurkukun, sai da su ka kammala shirya komai tsaf na kayansu, Angel ta kalle su ɗaya bayan ɗaya Azeeza tuni bacci ya ɗauke ta abayan Gabriel, hankalinta kwance sai sharar bacci ta ke Yi, Jemimah kuwa Idonta biyu Sai faman baza ido ta ke yi Hannunta na a ruƙe dana Angel.

"Me yakamata Mu yi yanzu don ganin An dawo mana da ɗan uwan mu Danish"! Haris ne yai maganar

"I'll go and get him back tonight!" da ƙwarin gwiwa Angel ta yi maganar.

"Ta yaya hakan zai yiwu? Angel muna jin tsoron wani abu ya same ki, Me zai hana mu tafi gaba ɗayan mu"! batul ce ta yi mata maganar fuskarta da alamun damuwa

"Zan bi ki Angel Mu tafi atare"! Gabriel ne Ya yi maganar" girgiza kai ta yi"Bana so wani abu ya samu ɗaya daga Cikin ku, Bazan bari ka bini ba Gabriel ni kaɗa nake so na jefa kaina cikin hatsari Zan roƙi Allah ya tsare ni....." muryarta na ɗan rawa ta ambaci hakan kamar akwai rauni atattare dani, tabbas tana matuƙar fargabar abu biyu, Na farko tafiyar da zata Yi tabar su da jimamin Awani hali take a ciki, Na biyu Haɗuwarta da garkuwar kurkuku, Wani irin azababben tsoron shi ta ke ji tun kafin ta yi tozali da shi.

"Genie Pls don't leave me Ki tafi dani..." cikin shessheƙar kuka Jemimah ta yi maganar tana ƙara damƙe hannun Angel dake ruƙe da nata.

"Wlh Angel hankalin mu ba'a kwance ya ke ba, Gani mu ke kamar wani abu zai faru da ke idan kika tafi kika barmu" Deeja ce ta yi maganar, ta fahimci kowannan su atsorace ya ke da tafiyarta.

"Angel bazamu ta6a yafewa kan mu ba idan har wani abu ya faru dake ta silar taimakon mu da ki ke ƙoƙarin Yi,"

Javed ne yai maganar, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin kowannan su, La66anta sai kerma su ke yi sam ta kasa buɗe baki ta yi masu magana sai binsu ta ke yi da ido, Zuciyarta ba ƙaramin karaya ta yi ba, Ita kanta tana ji a jikinta cewa wannan karan zaiyi wuya ta dawo cikin su ba tare da wani mummunan abu ya faru da ita ba.

"Idan har muka ji kin daɗe baki dawo ba, Zamu biyo ki ne"! Hibba ce tai maganar hawaye kwance saman kuncinta

Daƙyar Angel Ta iya tattara natsuwarta tare da cewa"Ku daina sanyawa ranku cewa wani abu zai faru dani, idan ma ya faru dani to ku sani ƙaddarata ce wadda ban isa in sauyata ba, Ni da Allah na dogara wani mutun ko Aljan ɗaya daga cikinsu bai isa ya cutar dani ba face da izninsa, ƴan uwana addu'arku kawai nake buƙata akan Allah ya bani Sa'a akan abunda zan je nema......." Sautin shessheƙar kukansu ne ya gauraye Ɗakin tsohuwa.

Muryarta adisashe tace"Tunkafin ma na tafi kun fara kuka? Meyasa? Dan Allah ku daina kamar fa kuna discouraging ɗina ne, Nafi so inga kuna ƙarfafa mini gwiwa, ganin hawayenku da nake yi ba ƙaramin raunata mini zuciya ya ke yi ba.
Chapter 4 · 0% Book details