← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 152

Sashe 30

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Parveen sun ƙi sakin jikin shi tun da su ka rungume shi ba su ɗago ba, faffaɗan tafin hannun shi ya ɗaura asaman kawunan su a hankali ya ke shafa sumarsu kan su, sai ƙara ƙanƙame shi suke Yi, a hankali ya furta masu”Ya Jikin naku”? Jemimah da Azeeza suka haɗa baki”Ai mun warke, Gidan daddyn Genie zamu je yau”
Ganin sunƙi sakin shi yasa Angel yi masu magana”ku sake shi mana, Ko mun samu muyi sauri muci mu tafi, idan har ba barin Dajin nan mukayi ba Hankalina ba zai kwanta ba” Jin maganarta yasa suka sake shi, Ya ruƙo hannun Azeeza dana Jemimah suka jera atare suna tafiya, Cikin Kogon dutsen su ka koma gaba ɗayansu, suna shiga suka tarar da Haris zaune shi kaɗai, bai jima da farkawa daga bacci ba, A ƙasa kowanansu ya zauna, Angel ta curo kayan marmarin ta rarrabamasu, A tsanake suke sha suna kallon Juna, bayan sun kammala sha, Suka fara shirin tafiya, Ba tare da 6ata lokaci ba, Angel Ta goya jemimah abayanta da mayafi ta ɗaureta, Gabriel Ya goya Azeeza abayanshi, sai daɗi suke ji an goyasu har gwalo suke Yima Parveen, Batul kuma ta Goya Back pack ɗin Unaiza abayanta, Javed Ya ruƙe masu akwatin kayansu, basu bar komai acikin kogon ba, Hatta Gorar ruwansu acikin kwandon kayan marmarinsu su ka sanyata, Parveen ce ta ruƙe kwandon a hannun ta.

Matafiya sun shirya tsaf saura tafiya ta rage masu, kafin fitarsu daga kogon dutsen saida Angel ta yi masu addu’o’i tabi kowan nan su ta tofe shi tun daga ƙasa har sama ko da ta zo kan Danish sai ce wa yai me take yi haka? ta daina watsa mashi yawu baiso, dariya tayi batare da tace mashi komai ba, Danish ne ke ruƙe da Haris saboda rashin ƙwarin Jikin shi.
Suna tafiya suna fira a dokar dajin, Su parveen sunga abubuwan da suka ɗaure masu kai, Komai suka gani sai sun tambayi Angel menene shi? Lokacin da rana ta ƙwalo Kowannansu Ya zazzare idanuwanshi suna kallon Sararin samaniya inda rana ta hudo, Angel sai ƙoƙarin hanasu takeyi akan su daina kallonta, gudun kada hasken ranar ya kashe masu idanuwan su.

Bakomai yasa su yin hakan ba face tsantsar mamaki da al’ajabi, su fa duk ɗaukarsu Fitila ce aka ajiye sama, kamar dai yadda ceiling ɗin ɗakin su na kurkuku Yake, Parveen sarki kwa6a magana da ta gaza jurewa tace da Angel ta faɗa mata tayaya akai har aka ɗaura fitilar sama? Ita bata ta6a ganin fitila mai hasken ta ba,” Dariya Angel tasaki tare da cewa”Kai parveen Nafa ta6a faɗa maku saboda gudun haka, Rana ce wannan da kuke Gani, Babu wanda ya ɗaurata Yana daga cikin halittar ubangijin mu Allah, bayan ita akwai Wata da taurari suma duk Allah ne ya halicce su, Idan Dare yayi zan nuna maku su, taci wahala wurin wayar masu da kai daƙyar ta samu suka fahimce ta, kusan saida ta maimaita masu karatun data koya masu tukunna suka Iya tunawa, A ƙalla sun shafe awanni suna kutsawa cikin Dajin babu alamun zasu shigo cikin Garin, Wani irin kurman Dajine ta ko’ina acunkushe yake da tsirrai.
Gaba ɗaya sun gaji da tafiya, Dama jikinsu bai saba da wahala ba, Ga6o6in jikinsu duk sun raunata, Mutun Biyune basu jikata ba, Jemimah da Azeezah, hankalinsu kwance Har bacci ya ɗauke su a goye sai daga bisani suka farka,
“Wlh mun gaji Angel, Wai haka zamu dinga tafiya ba tsayawa? Ƙafafuwana duk sun rurruƙe, Ga yunwa inaji” Parveen ce tayi maganar,
“Ya ki ke so muyi parveen dole muyi tafiya da da halima hada gudu, in ba haka ba zamu ƙare acikin Dajin nan ne,” fuskar Angel ayamutse ta yi maganar,
Danish duk yana sauraronsu, hankalin shi na akan Haris daya ruƙe.
Parveen ta hanasu sakat, don dole Naufal Ya goyata abayanshi, Jemimah hada tsokanarta”ƙatuwa dake dole sai an maki goya irin namu” Harara parveen ta watsa mata. Ba tare da tace komai ba.
Zogin da ƙafafuwansu suka fara yi masu ne yasa suka yada zango agaban wata ƙatuwar bishiya suka zazzauna suna faman yin haki, Gorar ruwa parveen ta curo masu, Bayan tasha ta miƙa ma Naufal yasha ya miƙa ma Hannah, sai dakowa yasha ruwan, Sun natsu suna faman lumshe idanuwansu,
“karfa kuyi mana bacci anan, bamu gama tafiya ba, naga kuna rufe ido,” Angel ce tayi masu magana, Fuskar Parveen atur6une tace”kaɗan zamuyi, “ batul Ta natsu tana kallon Bishiyoyin dake a kewaye dasu,

“Angel Su waɗannan basu gajiya da tsayuwa ne”!? Fuskar ta aɗaure tayi maganar babu alamun wasa
“Su wa kike nufi” Angel ta tambaya tana kallon fuskar Batul, Da hannu ta nuna mata Bishiyoyin dake fuskantarsu, Ɗan zaro ido Angel tayi tare da kallon Danish dake kallon fuskarta, kiris ya rage ya saki murmushi jin wautar Batul. hankalinta a kwance taci gaba da cewa”tun da muka taho suke ta tsayuwa babu motsawa, Itama rana sai binmu takeyi da gudu duk inda mukayi sai na ganta, to wai su basu gajiya ne”? Kalamanta sun rufe ma Angel baki ta kasa bata amsa, daƙyar ta iya cewa”Haka Allah ya Halicce su Batul”

Gabriel da ya ƙumshe dariya abakin shi yace da ita”ke yanzu idan waɗannan bishiyoyin suka motsa zaki tsaya? Har kina da bakin cewa Basu gajiya da tsayuwa”? Sai lokacin ta ɗan saki murmushi ba tare data kalle shi, shiru su ka ɗanyi na wani lokaci, Har bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukar su Jemimah ta fara ambaton fitsari take ji, Ɗaukarta Angel tayi tare da miƙewa ta kalli Danish”Zanje nakaita tayi fitsari,”lumshe mata ido yai tare da cewa”No, basai kunje nesa ba, Zata iya yi ko abayan bishiya ne” Amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi bayan bishiyar da ita, bayan sun dawone tace dasu su tashi suci gaba da tafiya kada dare yayi masu anan, Miƙewa su kayi jiki duk ba ƙwari, Ta maida goyan Jemimah gabriel ma ya goya azeezarshi suka dasa da tafiya.

Allah ya tsare su tunda suke tafiya babu wata muguwar dabbar da suka ci karo da ita, Sai dai sautin koke kokensu da suke ji acan wani sashe na Dajin, Sunyi nisa da tafiya kwatsam Ba zato ba tsammani Akuya ta faɗo wurinsu kamar an jehota, a matuƙar figirce suka watsa da gudu cikin dajin duk su ka tarwatse saboda tsabar firgitar da su ka yi.

Hankalinsu Danish ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda suke jima tsoro kada wata dabbar ta handamesu, Mutun biyar ne suka watse waɗanda suka rage Danish ne sai haris shima saboda Ya ruƙe shi ne ya kasa guduwa, Gabriel dake goye da azeeza sai Jemimah da Angel, Basu ta6a ganin akuya ba sai yau, shiyasa Suka watse, mun shigo uku Danish! Ya zamuyi? Angel ce ta ambaci hakan, Bai amsa mata ba ya kwantar da Haris jikin bishiya da gudun gaske ya faɗa Cikin Dajin don Ya tattarosu.
Jemimah ta ƙanƙame angel sai satar kallon akuyar take Yi, ta yi tsaye tana Lasar baki, Ciyawar dake awurin take Ci,
Ran Angel ya 6aci, Duwatsu ta tsinta a kasa ta dinga jifar akuyar, Da gudu Ta watsa tana kuka, Sautin dariyar Jemimah ne ya karaɗe kunnuwansu
“Genie ashe ma matsorayaci ce, wai wannan abun su Batul suke ma gudu, ni sun bani dariya, Ko kunya ma bata ji tana yawo zindir babu kaya a jikinta, ƴan nonuwanta azube kamar na tsohuwa, Genie itama mutunce kamar mu ko”? shiru Angel bata tanka mata, Damuwace ƙarara akan fuskarta, Hankalinta ba zai ta6a kwanciya ba idan har ba adawo dasu Batul ba.
Azeeza tana a la6e saman bayan Gabriel, Muguwar matsoraciya tun da akuyar nan ta faɗo wurinsu Ko yatsanta tagaza motsawa, Numfashinta ma a dabarbarce yake fita, Jikinta sai kakarwa yake yi, ba dan Allah yasa tana a goye a bayan Gabriel ba kuma ya ɗaureta da mayafi da kuwa Silar 6acewar azeeza kenan acikin Daji, Allah kaɗai yasan inda zata kutsa kanta saboda tsoro.
“Shiru basu dawo ba Angel, Ni inaga zan bi bayan Danish ne” Gabriel yai maganar, da sauri tace”A’a, Kada kaje ko’ina, Inaji araina zasu dawo atare, nasan duk inda suka shiga Danish zai nemo su”

Haris dai Yana a langwa6e jikin bishiya, suna cikin jimamin rashin ƴan uwansu, suka soma Jin takun tafiyarsu da sauri suka Juya baya suna kallon su, a jere su ke tafiya suna tunkaro su, abun da zai baka mamaki Hada naufal da javed su da suke maza, Batul na aruƙe da hannun Hannah, dana Parveen Sai haki sukeyi sun hada uban gumi, Danish na abiye da bayansu, Tunkan su ƙaraso Angel ta fashe da dariya hada dafe cikinta, Hatta Gabriel dariyar yake yi masu, hakan ba ƙaramin ƙona ransu yai ba.
Chapter 30 · 0% Book details