← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 152

Sashe 60

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Uwargidan shugaban ƙasar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa! Sarauniya ɗaya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ƙari mun kulle ƙofa” sautin ƙayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya karaɗe kunnuwan saratu, da alama taji daɗin yabon da saratu ke yi mata.

bayan ta gama yi mata kirarin ta ɗaura da cewa”Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem ɗin baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke” (idan kaga hajiya saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba ƙaramin mutun bane, babban gorone magogin ƙarfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da kalar yadin🤣)

Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice ɗinta zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arziƙi waɗanda suka gaji abun, da izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata.

“Ba abun da ki ke tunani bane ƙanwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma na kira don mu gaisa” itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa.

“Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka ƙasarmu” fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana.

“Naji daɗin kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ƙara godewa Allah daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, haƙika ban ta6a danasanin auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ƙarƙashin inuwa ɗaya har Allah ya azurtamu da samun zuri’a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna nuna min ƙauna sosai nima Ina sonku”

Hajiya saratu baki yaƙi rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta ƙarasa haɗiye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya.

“Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu ƙanwata baki daina ciye ciye ba ko”? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta sai ƙara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara neman izni ba to bata ɗaga kiran nashi.

*A GIDAN ƊAN IYA*

Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su ɗan ƙara kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu cewa Ai sun samu gidan da zasu zauna a abuja ya 6oye ne bai sanar dasu, harma ya samu aiki a companyn sharufuddeen, ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba sun tayashi murna sosai, musamman da suka ji cewa bazasu raba Aneelerh da junaid ba ko da yakai shekarun da zasu Iya kar6ar shi ne, Zasu haƙura ne har Allah ya bayyanar masu da su Uzair, dama rashin ɗan nasu ne yaja har suke son kar6ar shi, Aneelerh hada kukan farin Ciki, Ta ƙara jin son surukan nata, ba ita kaɗai ba hatta su mami sun ji dadin ziyarar da suka kawo masu sun kuma jinjina ma ƙoƙarinsu na barma Aneelerh ɗanta, su kansu sun fahimci ba ƙarami so suke yima yaron ba tun da gashi ta dalilinsa sun dawo abuja da zama, ba su kai ga barin gidan ba, abie ne ya dakatar da su yace su ɗan jira akwai malaman da zai sanya su yi masu safkar alƙur’ani a sabon gidan su, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, don su basuyi tunanin yin hakan ba.

Hankalin Mahboob yaƙi kwanciya tun da yayi tozali da hoton Angel, a daren ranar daƙyar Ya iya runtsawa, saboda fuskarta da ke yi mashi gizo, ya kwana da mamakin baiwar Kyan da Allah Yayi ma yarinyar, bai ta6a ganinta ido da ido ba sai dai ahoto yasanta tun tana ƴar ƙaramarta, Aneelerh take ɗaukar ta hoto da video tana sanyawa a status dinta to anan yasanta, a ƙarshe daya gaza haƙara bayan sun dawo daga sallar asubahi, ya lalla6a yaje ɗakin aneelerh, tsabar Iya fadanci hada Kiranta da aunty, bai ta6a kiranta hakan ba sai yau da Allah ya jarabe shi da son sanin komai dangane da Angel.

Tambayoyi ya tsare Aneelerh da su akan ta fada mashi dagaske yarinyar mutunce bata haɗa jinsi da aljanu ba? Don shi gaskiya bai yarda da kyanta ba, Ya zarce na jinsin mutane, tun da yake kallon indian film, da korean drama bai ta6a ganin jarumar da ta kama ƙafar Yarinyar a kyau ba.

Aneelerh taci dariyar wautar Mahboob, har tambayar shi ta yi ko dai sonta ka ke yi ne? Naji kanata zuzuta kyawunta, “ da sauri ya dafe ƙirjinshi da hannu Yana faɗin”Sai kace dai bani da hankali aunty Aneelerh? Ae rijiya ba wurin gaɗar makaho bane, Nasan ciwon kaina ban shirya yin jinya a gadon asibiti ba, ni kawai kyanta ne ya ruɗe ni ba wani abu ba, tsakani da Allah yarinyar ba matar yaku bayi bace, ko makaho ya shafa fuskarta zai shaida hakan tafi dacewa da Manyan ƴa’ƴan masu kuɗi waɗanda suka jiƙe da naira, ni yanzu idan nace zanso ta, ko zan aureta, Aunty Aneelerh ina zan samu kuɗin ɗaukar ɗawainiyarta? Kuɗin man shafawarta dana zuwa saloon kaɗai sun isa su takaita jarin mutun balle ni da ba kuɗi gare ni ba”

tsabar dariya Aneelerh hada hawaye, shiko fuskarshi a daure yayi mata maganar bada wasa ba, ya ƙara da cewa”ƙwara na auri ƴar talaka wadda ba ta da tsayin gashi, sai yafi min sauki, in manna mata ƴar naira ɗari biyar taje gidan kitso ayi mata, man shafawa a jiki kuma Ko vaseline na siya mata ya wadatar, Iya kuɗin ka iya shagalin ka, Amma wannan Ifritun yarinyar wlh aunty Aneelerh duk talakan da ya aureta ya cuci rayuwarta, yasin ni har kotu zan Iya kai ƙarar shi, ita kanta idan ta auri talaka batayiwa kanta adalci ba fisabilillahi.

Lamarin mahboob sai addu’a, Haka ya dinga santin kyan Angel, Har faɗi yake shi ya kosa A gano su, in sha Allah zai tayasu da addu’a akan Allah ya bayyanar dasu, burinshi idan Allah yasa ta dawo gidansu da zama zai zama na hannun damanta saboda idan ta auri basarake ko wani mai ji da naira, ya dinga samun ƴan canjin kashewa.

Saboda Angel Ya manta da zancen neman zoben shi, gaba ɗaya ya ɗaura burin duniya akan Angel, harya fara ƙiyasta kuɗin da zai tatsa wurin Mijin da zata aura.

Daƙyar Aneeleerh ta samu mahboob Ya fita daga ɗakinta, ya addabeta da zancan kyawun Angel.

Alhamdulillah, a yau labarin 6acewarsu Angel ya dawo tamkar sabo a shafukan sada zumunta, ta ko’ina buga labaransu Akeyi tare da hotunansu, tun da Ont suka fara yaɗa labarin nan take sauran gidajen jaridu suka bubbuga labaran da gidan radio. Ta ko’ina zancen su akeyi kamar yau abun ya faru, labari ya dawo sabo, Yanzu shine Top story dake trending a social media, mafi yawan mutane Kyawun Angel ke ruɗarsu har su kaiga ɗaukar labarin su karanta sannan suyi share ɗinshi don ataimaka a gano su.

Fuskar Aneelerh tun safe da annuri akanta, Mutane sai kiranta sukeyi awaya sunayi mata jaje haɗi da tambayarta wasu bayanai da suka danganci Angel, a ƙarshe sunayi mata fatan Alkhairi, Numbobinsu ne akan labaran da akayi share nasu shiyasa mutane ke ta kiransu suna yi masu jaje.

Ta natsu saman mirror chair, turkish gown ce a jikinta launin maroon tayi bala’en yi mata kyau, babu mayafi akanta zallar sumar kantace
Hannunta na aruke da wayarta, tun ɗazu take maimaita karanta labarin su Angel da akayi posting ɗinsa a shafin Ont na insta

“Mommy” muryar junaid ce ta janyo hankalinta ga kallonshi, ta cikin mirror, Hajiya adama tayi mashi gayu don yau ma a ɗakinta Ya wuni, ita tayi mashi wanka, tasa Aneelerh ta kawo mata kayan shi ta santa mashi jeans da shirt fara, sumar kanshi tasha gyara.

Ƙarasawa yai gaban kujerar da take a zaune, ya daura kanshi saman laps ɗinta, ƙamshin turaren jikinsa na Hajiya adama ne da ta shafa masa
‘Wow my baby boy, kayi min kyau sosai, lallai granny ɗin nan taka tana matuƙar sonka irin wannan gayu haka da tayi maka”

Ɗaura wayar tayi gaban mirror, ta sanya hannu biyu ta ɗago da junaid ta ɗaura shi saman laps ɗinta, langwa6ar da kanshi yai saman kirjinta

“Mommy namanta ban faɗa maki ba, jiya wani mutun ya kira awaya har yace wai in faɗa maki....” katse shi tayi”yaushe aka kirani? Bana son ƙarya fa”
Muryarshi da shagwa6a ya ce “mai ƙarya fa ɗan wuta mommy, ni dai Allah ba ƙarya nake maki ba” miƙa hannu Aneelerh tayi ta ɗauki wayar, tana shiga call logs tayi arba da New number da aka kira kuma an ɗaga kiran.
“Junaid bana hanaka ɗaga min kira ba”?
Zumbura mata maki yai’to ai nayi tunanin Angel ce ke kira, kuma baki a ɗakin shine na ɗaga, kuma yace in kai maki wayar ku yi magana ni kuma naƙiya nace sai dai ya faɗamin in gaya maki” tun da ya fara magana ta ƙura mashi ido tana kallon shi, komai nashi burgeta yake yi, musamman in yasanya shagwa6a a maganar shi.

“Meyasa baka kawomin wayar ba”?
Ƙura mata ido yai ba tare daya furta kalma ba
Sam hankalinta bai kwanta da baƙuwar number da ake yawan kiranta da ita, tuntuni take ganin missed calls daga Number taƙi yarda ta ɗaga kiran don har yanzu bata daina fargabar mutanan nan da suka ɗauketa da sunan jami’an sirri.
Chapter 60 · 0% Book details