← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 152

Sashe 12

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yunƙurin caka mata wuƙar ta yi ba zato ba tsammani taji an buge kanta da wani abu mai nauyin gaske tamkar dutse kafin ta yi yunƙurin juyawa don taga wanene taji an ƙara buga mata shi akanta, nan ta ke kanta ya juye Ta kife ƙasa,.

Batul ce a tsaye Tana haki, Hannunta ruƙe da sandar Zafreen da ta jefar ƙasa, ƙarfin sihirin da ke a jikin sandar ne yasa har ta yi nasarar kwaɗeta da ita, daddagewa tayi da ƙarfi taci gaba da buga mata sandar, Jijiyoyin wuyan ta duk sun furfuto waje saboda tsabar 6acin rai, babu sassauci atattare da ita tun tsohuwa zafreen na motsi har ta kai ga idanuwanta sun Juye, Jefar da sandar Batul ta yi ƙasa tare da ɗaukar wuƙar da zafreen ɗin ta jefar, Saman ruwan cikinta ta haye ta daddage ta dinga luma mata wuƙar Jini yadin ga ambaliya kamar an kunna fanfo harta saman fuskarta, Kacaca tayi mata sai da ta farketa, A ƙarshe dai Baful ta yi nasarar kashe tsohuwa Zafreen ko shura wa ba ta yi ba nan ta ke rai yai halin shi, harta mutu batul bata daina farke jikinta da wuƙar ba, saboda bata acikin hayyacinta, kuka ta ke yi tamkar ana zare ranta.

Farfaɗowa tsohuwa Tamira ta yi a hankali ta buɗe idanuwanta da suka ruƙida su ka yi jawur dasu, ta wurga su kan Batul da ke a zaune saman Zafreen tana aikin fiɗa.

Muryarta na rawa ta ambaci sunanta”Ba..tul..” Sai lokacin ta jefar da wuƙar hannunta, jiki na rawa ta sauko daga saman jikin zafreen ta rarrafo Zuwa gaban tsohuwa Tamira.

Fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, taci gaba da yin kuka tana faɗin”Ta zalunce mu ba mu yi mata laifin komai ba, ta kashe mana ƴan uwan mu ta gama da rayuwar mu.....”

Hannun tsohuwa na kerma ta ɗaura shi saman sumar kan Batul da ke a tarwatse daƙyar take iya yi mata magana”Batul babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin baku haƙuri akan irin jarabtar rayuwar da kuka fuskanta, Ku yi haƙuri kuyi haƙuri Allah yana atare da ku.......” Da numfashinta na ƙarshe ta ƙarasa maganar nan ta ke rai yai halin shi, A matuƙar kiɗime Batul ke Fuskarta.........

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E4🔥💫_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu kamar zasu fasa fatarta, hatta saman fore head ɗinta jijiyoyin ne....

A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin ɗaki, tun suna kuka har sun fidda rai da ƴan uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shessheƙar kukansu har ta kai ga yanzu basu Iya jin komai, A bakin ƙofar ɗakin tsohuwa Tamira suka zuzzuƙuna, Zuciyoyin na tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun ƙafe, Haka zalika Naufal da javed babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba ƙoshin lafiya ce da shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi, Daƙyar ne yai tsawaicin kwana.

A firgice su ka ɗago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin ɗakin su, jiki na kerma suka miƙe suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba ƙaramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin murya ya soma yi masu magana.

“Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima ɗan uwan ku ne nasan ba ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira”! Duk da basa acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi.

Cikin shessheƙar kuka Haris yace”ƴan..uwan mu suna a cikin ɗakin tsohuwa Tamira, Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su saboda ta datse ƙofar.....” tun kan ya kai ƙarshen maganar, Salsabeel Ya wuce da wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ƙofar Nan ta ke ƙofar Ta buɗe.

A fujajen Ya faɗa Cikin Ɗakin Hankalin shi a matuƙar tashe Ya ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira har izuwa kan su Parveen da ke a sume ƙasa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform ɗin su yashe a kasa da ta Cire masu, Da ƙarfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa’inna ilaihirraji”un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya dunƙule, Tsabar ƙunar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa ƙirjin shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka ya ke Ji.

“Ya Allah ka ɗauki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne” Muryar Batul ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa’iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar tsohuwa Zafreen A can gefe ɗaya, tangal tangal yai kamar zai kife ƙasa Da sauri ya tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai ɗumin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba wlh da ɗaya daga cikinsu baƙin ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel ɗin har su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka fuskanta a wannan baƙar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta zama mahaukaciyar ƙarfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya zuƙunna cikin rauni na murya ya furta”ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni kaɗai a cikin wannan Duniyar mai cike da ruɗani”? Daƙyar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma magana Batul ta ɗago da runannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu ta ƙura su akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi.

“Hada kai Aka kashe min Ƴan uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine”! ɗago wa yai tare da kallonta, Kafin yai yunƙurin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman jikinshi tare da dunƙule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko’ina tana faɗin Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe mana ƴan uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne....? bata ƙarasa maganar ba kuka Yaci ƙarfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka ɗaukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ƙai, Maganar su ta ƙarshe ya soma tariyo acikin kanshi.
Chapter 12 · 0% Book details