Sashe 146
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan tafiyarta, sheikh imam Ya mayar da dubanshi kansu Sajeed da suke a tsaye cirko cirko suna kallon shi.
“Allah ya yi maku albarka, ubangiji Allah ya kareku daga sharrin duk wani abun cutarwa, Allah ya daukaka rayuwarku......” addu’o’i ya dinga karanto masu suna amsa mashi da ameen ameen
Bayan ya kammala yi masu addu’o’i, yace dasu”Ku faɗamin sunayenku ina son ji” hatta maganarshi da ƙarfin hali yake yinta duk ya rasa kuzarinsa.
Sajeed ne ya fara cewa”Ni sunana sajeed, wannan kuma Azeeza’ ya faɗa yana nuna Azeeza, kafin Ya ɗaura yatsan shi kan Naufal”Sunanshi naufal ta gefenshi Parvin, ga kuma Jemimah da Hanna, sai Javid and Haris, da Batool, ƴar uwarmu data tafi kaima aunty ummi waya sunanta Unaisah”
duk wanda ya nuna sai ya fadi sunanshi bayan ya kammala sheikh imam yace”sannu da ƙoƙari Sajeed, nagode daka faɗamin sunayen ku” murmushi Sajeed yayi ba tare da ya ce komai ba.
A hankali Sheikh Imam Ya dubi boss man da big guy, bai yi mamakin ganin kallon da su ke yi mashi ba, yasan dole suyi tunanin wani abun daban, launin idanuwanshi har sun canza zuwa ja, kau da idonshi yayi daga kansu ya kalli su Haris muryarshi asanyaye yace”ku zauna muyi fira ƴan jikokina” zazzaunawa su ka yi kan carpet shi kuma ya zauna kan sofa, su boss ma suka zauna suna fuskantar shi.
*UNAISAH❤*
Koda Unaisah ta ƙarasa ƙofar ɗakin ummi dafe glass door din ƙofar tayi a hankali ta zugeta, bata sameta a adakin ba, sai dai ta jiyo shessheƙar kukanta acikin toilet.
Ɗaga murya tayi tare da cewa”Aunty Ummi, ga wayarki na kawo maki” shiru ummi bata tanka mata ba, kusan sau biyar tana maimaita maganar babu alamun za’a amsa mata.
Saman gado ta ajiye mata wayar, kafin ta nufi ƙofar toilet din ta sanya hannu tayi mata knocking,
“Aunty Ummi dan Allah ki daina yin kuka, bamu jin daɗi, idan wani ne ya 6ata maki rai, ki yi haƙuri” lallashinta Unaisah taci gaba da yi tun tana jin shessheƙar kukan ummi, har tadaina jiyo sautin kukanta, hankalinta ya ɗan kwanta juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, maimakon ta sauka down ta koma falo sai ta kalla6a ta nufi ɗakin Danish, dama abun take yima zumuɗi kenan shiyasa ta kar6i wayar ummi da sunan zata kai mata.
Idan muka koma 6angaren Danish tsawon mintuna da suka shiga da shi bathroom, kafin su fara yi mashi wankan saida prime minister ya tofe ruwan da addu’o’i kamar yadda sheikh imam yace adinga yi mashi, batare daya cire mashi short din jikinshi ba yayi mashi wanka da ruwa mai ɗumi, tamkar ya samu jinjirin yaro, saƙo da lungu na jikinshi sai da prime minister ya cuccuɗa shi, bayan ya kammala ya ɗauko farin towel cikin jerin waɗanda ke sagale jikin hanger, ya ɗaure mashi a waist dinshi da dabara ya zame short din daya jiƙe duk don kada yaga tsiraicin shi, shanya short din yayi kafin salsabeel Ya taimaka mashi suka fiddo da shi daga cikin kwamin wankan.
Kafin fitowarsu Chief Owais kadai ya rage a ɗakin, Cikin takun sauri ya nufi faskekiyar closet din Danish ya buɗe yana bin jerin tsadaddun suturunsa da kallo A hankali ya tsayar da idanuwanshi wurin jerin jallabiyoyi yana da tabbacin zaifi samun walwala acikin jallabiya, launin fara ya ɗauko mashi, ya dawo ya ɗaura kan gado.
Jin motsin buɗe toilet door ne yaja hankalinshi ga kallon su
A daddafe suka fito da danish hannayensu tallabe da shi, da sauri chief Ya ƙarasa gabansu Ya tallabo masu shi a saman shimfiɗeɗan gadonshi suka kwantar da shi.
“Sannu da ƙoƙari Uncle,” acewar chief
Prime minister yace”yawwa my son, kaima sannunka da ƙoƙari, tun jiya mun hana ka runtsa”
“Bakomai uncle kada hakan ya dame ka aikina ne”
Murmushi prime minister yasaki haɗi da bubbuga kafaɗar chief owais alamar jinjina.
“Uncle yakamata ka koma gida, za’a iya nemanka, ni zan cigaba da kula maka shi”
Girgiza kai Prime minister yayi”No, ba yanzu zan koma gida ba, sai zuwa anjima” Chief bai musa mashi ba don ya fahimci baison tafiya yabar Danish.
“Sabeel, bring me some body lotion and perfume” cikin girmamawa salsabeel ya amsa mashi da toh sir.
Ya juya da sauri ya nufi dressing mirror ya ɗauko body lotion tare da turare yazo ya ajiye su kan gadon.
prime minster ne ya soma bin ko’ina na jikin danish yana shafe shi da mai haɗi da yi mashi tausa don yaji dadin jikin shi, chief ne ya taimaka mashi wurin burkito mashi da danish Ya juya mashi bayanshi, Ya shafa mashi man kafin yabi da turare ya feshe shi.
da taimakon chief suka sanya mashi jallabiyar, masha Allah, tayi bala’en yi mashi kyau, a karo na farko kenan don bai ta6a sanya jallabiyaba, tabi shape jikinshi ta bayyana kyakkyawar surar jikin shi, musamman broad chest dinsa da strong arms nasa sun fito ruɗu ruɗu ta jikin jallabiyar.
Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, ganin sunci nasarar gyara mashi jikin shi, hatta sumar kanshi saida prime minister ya sharceta ya shafe mashi ita da mayukan gyaran gashi, ƙamshin turaren danish ya cika ɗakin kamar wanda akayi ma wanka da ruwan turare.
“Yanzu me ya rage mana”? Acewar chief, prime minister yace”nasan yana jin yunwa, Yana buƙatar abincin da zai ci”
Salsabeel yace “Yayi bacci yanzu, naga lokacin sallah yakusa cika, may be kafin mu kammala yin sallah ya farka sai mu bashi abincin”
“Kana nufin har muka yi mashi wanka bacci yake yi”? Prime minister ne ya faɗa yana duban salsabeel.
“A’a yalla6ai, idonshi biyu, tun lokacin da muka shiga dashi bathroom, Yanzu nan yayi bacci”
“Taya akai ka gane yayi bacci” da mamaki yayi mashi tambayar, chief dai yana atsaye yana sauraronsu.
“Yatsun hannun shi dana ƙafarshi, suna kerma yanzu kuma sun daina gaba ɗaya sun tsaya yadda su ke”
Fuskar prime minister dauke da murmushi yace”ka karanci ɗan uwan nan naka sosai, naji dadin jin hakan, may be wankan da mu ka yi mashi ne yasa shi jin daɗi har yayi bacci”
Saldabeel yace”ƙwarai kuwa yalla6ai, ay kayi ƙoƙari, Allah yasaka maka da mafificin alkhairinsa kamar yadda ka faranta mashi rai ka gatanta shi kaima inayi maka fatan Allah ya faranta maka ya ƙara ɗaukaka ka” Har cikin ranshi yaji daɗin kalaman salsabeel,
“Yalla6ai kaima ban barka abayaba, domin kuwa kayi namijin ƙoƙari wurin ganin ɗan uwana ya samu lafiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka” ya faɗa yana duban chief owais.
Jinjina mashi kai yayi batare daya furta komai ba.
Kiraye kirayen sallar Azhar da aka farayi ne Yaja hankalinsu
da sauri chief ya zaro agogon azurfar hateem tare da Zobensa daga aljihu Ya miƙa mashi.
Bayan ya saka a hannun shi, ɗaya bayan ɗaya su kayo alwala, kafin fitarsu daga dakin saida prime minister yaje har gaban gadon danish ya ɗan duka tare da kai small lips dinsa saman forehead din danish Ya manna mashi peck, ji yake kamar karya tafi yabar shi, ganin abun nashi bamai ƙarewa bane ga time ɗin salla na tafiya ya kafe danish da ido babu ƙyaftawa da sauri chief yaje ya ruƙo hannun shi ya janyo shi a hankali suka nufi ƙofar fita ɗakin.
Adai dai lokacin Unaisah dake la6e bakin ƙofar ɗakin tana sauraron su, jin motsin tafiyarsune yasa tayi saurin watsawa da gudu ta la6e a wata ƴar corner.
Akan Idonta, Chief Owais Ya fito hannun shi ruƙe dana prime minister, still bata samu damar ganin fuskokinsu ba, sai dai salsabeel daya biyo bayansu shi tagani da kyau, tunani ta somayi aranta ko wanene wannan babban mutumin, taso ace taga fuskarshi shida chief, Allah bai bata sa’a ba, Har saida suka 6ace ma ganinta tukunna cikin sanɗa take bin bango tana nifar ɗakin danish cikin sa’a ta buɗe ƙofar ta shige, daddaɗan ƙamshin turarenshi ne ya daki hancinta har saida ta lumshe idanuwanta tana shaƙar shi ......
Cikin takun sanɗa ta nufi gadon, yayin da idanuwanta suke hango mata Man dinta, hayewa saman gadon tayi daga gefenshi ta dakata tana bin body dinsa da kallo, from head to toe, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin shi cikin shiga ta farar jallabiya yayi mata kyau, aranta ta ayyana nasan waɗannan mutanan ne suka taimaka mashi wurin gyara jikinshi saboda boss ya faɗamin cewa ko yatsanshi bai iya ɗagawa, idan kuwa hasashena gaskiya ne naji daɗi ubangiji Allah ya saka masu da gidan Aljanna, ta ƙare zancen zucin fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki.
Ta rasa gane bacci yake yi ko idonshi biyu, amma dai tayi missing dinshi na tsawon awannin daya ɗauka tun jiya a halittar maciji, ashe dai da rabon zata sake ganinshi da ainihin suffarshi, yayin da take kallonshi karaf idanuwanta suka sauka akan jan tabonnin dake akan farar fatar dogon wuyansa, harzuwa saman fatar hannunsa.
Ras taji gabanta ya faɗi, ta zazzaro idanuwanta waje tana fadin”My man meke damunka? Jan tabon menene nake gani a jikinka”? Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa, hawaye tuni sun jiƙe gashin idonta.
Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura saman wuyanshi ta soma shafa tabonnin slowly ta zame fingers din daga neck dinsa zuwa kan broad chest dinsa, a hankali take 6alle links din gaban jallabiyar don ta samu damar ganin sauran tabonnin da ke akan fatarshi, da ta buɗe faffadan kirjin nashi, hankalinta yayi matuƙar tashi da ganin tabonnin ta ko’ina, ji tayi tamkar zuciyarshi bata bugawa da sauri ta kanga Kunnanta na dama saitin zuciyarshi, natsuwa tayi tana sauraran yadda take harbawa cikin kwanciyar hankali, tsawon mintuna bata ɗago da kanta ba saboda dadin sauraran heart beat dinsa da take ji, A hankali ta ɗago da kanta karaf idanuwanta suka sauka akan soft lips dinsa batasan ya akai ta tsinci kanta dayi masu kallon ƙurulla ba sun ɗan kumbura, zuciya ce ta soma tunzurata akansu, unaisah da kasada ta ɗaura yatsun hannunta na dama kan la66ansa tayi squeezing ɗin su, ba zato ba tsammani taji yaja dogon numfashi da ƙarfin gaske, tsabar kiɗima jiki na rawa ta rarrafa ta ta wulkita can ƙasan gadon ta faɗo ta labe zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi jikinta ya hauyin kerma duk tabi ta ruɗe gani take yi kamar ta fama mashi ciwon shi...