← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 152

Sashe 119

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Umarni yaba big guy akan ya dauki Unaisah ya maidata gida, jin ya furta hakan yasa ta watsa da gudu cikin falon bata nufi ko’ina ba sai saman benan da zai sadata da macijin, da gudu big guy yabi bayanta, cikin shessheƙar kuka take fadin”dan Allah kada ku kashe shi, wallahi ba maciji bane, ɗan uwanane danish”

damƙo hannunta big guy yai, tadinga kiciniyar ƙwace kanta ranta amtuƙar 6ace ta soma zazzaga masu masifa tana fadin”wallahi babu inda zanje, nace maku dan uwanane, ku ƙyale shi ku daina harbinshi tunda bai cutar da kowaba, wayyo Allah na danish ɗina”

Sautin koke kokenta Ya cika gidan, hatta sauran mazauna gidan baba obie saida suka jiyota, ɗaya bayan ɗaya masu aikin gidan suke fitowa daga makwancinsu, Pravin bai jima da shiga ɗakin hajjaty ba ya jiyo sautin Kukan mutun agidan, sai gashi ya fito hajjaty na abiye dashi, Hajiya saratu kuwa jin sautin kukan Yasa ta fito daga ɗaki ta shigo falon, koda tayi arba da unaisa ga jami’ae da kuma shirgegen macijin dake bin bango, hannayenta biyu ta ɗaura akai tana ambaton Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un! Maciji acikin gidan nan? Wacece wancan Yarinyar? Ya akai ya shigo? Aruɗe ta furta hakan
Kowa Ya shiga ruɗani, Jami’an sun dage sai antaya mashi Harsashi suke Yi, Ganin suna ƙoƙarin yi mashi illa yasa Unaisa tayi wani irin kukan kura, ta bangaje big guy da iya ƙarfinta na ƙarshe, ta haura sama da gudun gaske, duk yadda suka so su kawar da ita sun gaza yin hakan har saida tayi nasarar ƙarasawa inda yake, tsawa suka dinga dakata mata suna korarta daga gabanshi amma taƙi matsawa, macijin yabi ya nannaɗe kanshi Ya dunƙule waje guda saman floor, lullu6e shi tayi da bazar rigarta, tana kuka tana fadin”danish dan Allah ka saurareni, ka taimaki rayuwata, bana so na rasa ka, ka canza halittarka ka tabbatar masu da cewa kai mutunne ba maciji ba, idan ba haka ba zasu Iya kashe mun kai” cikin jin ƙunar rai take Furta maganar, ta ƙanƙameshi kamar zata maida shi jikinta, jami’an sun natsu suna kallon ikon Allah, Hajiya saratu sarkin tsoro sai faman baza idanuwanta take Yi, baba obie Yana la6e bayan Mai girma sharafuddeen, Senate Ya ruƙo hannunshi dake tayin kerma, A hankali Hateem Ya zare farin glass din dake asaman fuskarshi Ya ruƙe ahannunshi, komai ke faruwa akan idanuwanshi, tamkar amafarki suke kallon lamarin, an rasa wanda zai janyeta daga jikinshi. Abunda ya ɗaure masu kai babu alamun macijin zai cutar da ita.

Duk da baya iya furta mata magana, ranta yana bata cewar yana son ya rikiɗa ya koma mutun sai dai ya kasa yin hakan, jikinshi ya ɗau zafi sosai, cikin sanyin murya ta soma yin magana, hawaye naci gaba da wanke fuskarta
“Ɗan uwana rabin raina, dan Allah ka canza halittarka, idan ba haka ba babu wanda zai yarda cewa kai mutunne zasu ci gaba da cutar min dakai” ta faɗa tana ƙara kankameshi a Jikinta.
umarni Owais Ya ba jami’an akan su daina yunƙurin harbinshi, amsa mashi sukayi datoh, ya fadi hakanne saboda ya fara kokwanton mutunne kamar yarda ta faɗi, a faɗace hajiya saratu tace”akan me zaka basu umarnin su daina harbinshi? idan ya cutar da wani fa”? Ko kallo bata ishe shi ba, muryar baba obie Na rawa ya furta”Ku kashe macijin nan, bana son ganinshi, ku kawar mana da shi”

“Baba ka kwantar da hankalinka, Ni na yarda da maganar yarinyar ba maciji bane mutunne” mai girma sharafudden ne yai maganar.

A harzuƙe Obie Yace”tayaya mutun zai zama maciji? hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Ni bazan ta6a yarda ba, ku kawar mana dashi kawai, idan baso kuke zuciyata ta buga ba, Ita kuma waccan Yarintar mai kasada ƴar wacece? Ku ɗauke ta mana daga Jikinshi kada ya sare ta”yai maganar yana nuna Unaisah da sandar hannunshi.

Duk yabi ya furgice masu, big guy ne ya kutsa ta cikin jami’an Ya nufeta, muryarshi ƙasa ƙasa tamkar tame Yin raɗa ya furta”Unaisah, ki tashi mu tafi gida, za’a dawo maki dashi” maƙe mashi kafaɗa tayi, la66anta duk sun bushe sun faffashe.

“Babu inda zanje, Ina atare dashi, Idan nayi nesa dashi, ba zaku Iya sarrafashi ba, zai Iya guduwa ya nufi wani wajen” magiya ya dinga yi mata akan ta miƙe amma taƙi tashi, hakan Yasa Chief owais motsawa ya haura saman benan Ya nufe su, Darewa jami’an suka dinga yi suna bashi hanya har ya kaiga ƙarasawa inda suke, faffaɗan tafukan hannaye shi ya ɗaura saman unaisa ya ɗaɗɗagota tare da ɗaurata saman broad shoulder dinshi, juyawar da zaiyi da niyar ya tafi da ita, giant snake din Yai wata irin girgiza da gudun gaske yabi bayan owais daya ɗauketa.

Jami’an suka saita shi da bindiga owais Ya hana su harbeshi yace masu su barshi akwai dalilin dayasa yayi hakan, Yana tafiya macijin Yana bin bayanshi, kasancewar ya ɗaurata saman kafadarshi tana Iya kallon giant snake din daketa ta faman jan ciki Yana nufosu, hawayenta tamkar zasu ƙare muryarta shaƙe take ambaton sunan Danish.

Ganin macijin zai sauko down yasa Hajiya saratu ta watsa da gudu zaninta har yana kwancewa ta ruƙo shi ta nufi hanyar part dinsu aguje ta shiga ɗaki ta datse kofa, tabi tagogi duk ta rufesu, a karshe cikin toilet ta shige tayi locking kanta.

Hankalin baba obie yai matuƙar tashi sai ƙara ƙankame jallabiyar mai girma sharafuddeen yake yi, Hateem kuwa ko kadan baiji tsoron macijin ba, tsabar mamakine Ya hana su furta magana, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah, duk inda owais yai da ita sai macijin yabisu, fucewa yai daga falon Ya nufi motarsu da su ka yi parking dinta abakin entry hall, Ya buɗeta Ya shigar da unaisah aback seat na motar, ya buɗe front seat a mazaunin driver Ya zauna yai mata key, da gudun gaske Ya fusgi motar, ta cikin glass din motar take kallon macijin daketa binsu da ƙarfi Ya daka uban tsalle Ya haura saman motar Yai kwanciyarshi.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin yana atare dasu, bai nufi ko’ina ba sai sashen da gidansu yake, ta gate din Baya ya shigar dasu a bakin entry hall chief Yai parking din motar, Ya fito Ya buɗe back seat din Ya cuccu6i unaisah Ya ɗaurata saman kafaɗarshi Ya nufi Babban falo da ita, hankalin shi kwance tamkar baisan da zaman macijin ba, saukowa yai daga saman motar yabi bayansu da gudun gaske yake jan jiki.

Cikin takun sauri Owais Ya haura upstairs da ita, kafin Ya ƙarasa second floor, macijin Ya riga shi isa, wani wawan tsalle ya daka Yabi ta jikin bene Ya faɗo tagabansu, ƙoƙari yake ya nannaɗe ƙafafuwan owais sai dai yakasa yin hakan saboda owais bai bashi damar ruƙe mashi ƙafa ba, sai kakkauce mashi yake Yi, a haka ya ƙarasa bedroom din Danish Ya shiga daga ciki, Ya kwantar da ita saman gado, Shigowa ɗakin macijin Yai yana faman huci kamar zai kai mashi hari, saman gadon Ya haye Yana faman bin mattress din. Owais dake a tsaye ya goya hannayenshi saman wide chest dinsa, Ya natsu yana kallonsu.

Giant snake din Ya nannaɗe jikinshi agaban unaisah ya ɗago da kanshi Yana kallon owais, duk a tunaninshi wani abu zaiyima unaisah shiyasa Yabiyosu, shi kuma owais daya fahinci Baya iya cutar da ita shiyasa yai dabarar daukota sai gashi yaci nasara akanshi”

Fitowa yai daga ɗakin Yaja ƙofar Yai locking dinta, Yabarsu su biyu adakin Ya nufi down.

Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi, tsananin tsorone Ya kamata, amma saboda ƙaunar da take yi mashi takasa motsawa, duk tasha jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta sunan shi”danish ɗina” juyowa macijin yai da kanshi Yana dubanta, jikinta na kerma saboda ƙarfin hali ahaka ta miƙa mashi hannunta, jan jiki ya somayi yana nufarta, saman kirjinta ya nannaɗe kanshi, wani irin sanyi taji ya ratsata, lokaci ɗaya tadaina jin bugun da ƙirjinta keyi mata, asaman fatar shi ta ɗaura hannunta, a hankali take shafashi duk don ta kwantar mashi da hankalinshi, ita kaɗaice zata Iya fahimtarshi a halin da yake ciki.

Walking quickly chief Ya nufi Ƙofar fita daga part din, Kafin Ya ƙarasa Muryar Boss man ta katse mashi hanzarinshi”yalla6ai” cak Ya tsaya da tafiya ya waiwayo yana dubansu, su biyune suka fara shigowa shida big guy, daga bayansu sauran jami’an isod ne da suka Biyosu, hankalinsu duk ba a kwance yake ba, musamman Boss man da yaji labarin abakin big guy shigowar shi kenan gidan duk wannan budurin da akeyi baida masaniya yana a part dinsa.

Fuskar chief owais ta canza zuwa yanayi na damuwa.
“Yalla6ai Ina macijin yake”? Big guy ne ya jefa mashi tambayar.
Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta”yana adakin shi, tare da yarinyar na kullesu” waro ido waje sukayi suna kallon shi
Muryar boss man na rawa ya furta”kana nufin tare da Angel ka rufe su aɗaki? Idan ya cutar da ita fa”? Gaba ɗaya yabi ya ruɗe.

Big guy yace”ka kwantar da hankalinka, Ni na fahimci hikimar yin hakan, da ace bai daukota ba macijin bazai dawo gidan ba, bamusan inda zai shiga ba, amma yanzu kaga mun kulleshi aɗaki ta dalilinta”
Chapter 119 · 0% Book details