← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 152

Sashe 101

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Gabriel na dawo gareka, tunda kana so ka musulunta, babu buƙatar 6ata lokaci, Zan biya maka kalmar shahada saika maimaita da kyakkyawar niya” murmushi gabriel yasaki bashi ba hatta sauran ƴan uwanshi sunji daɗi, ba tare da 6ata lokaci ba, Ya biya mashi kalamar shahada, wani irin daɗine ya lullu6e su Angel, shima Gabriel din daɗin yake ji sai faman washe baki yake yi.

“Ina taya ka murnar shiga addininmu, ko kana buƙatar na canza maka suna? tun kafin gabriel ya bashi amsa su Batul su ka yi saurin cewa”Eh wallahi acanza mashi, sunan shi wahalar faɗi yake yi mana,” dariya boss man yasaki jin abunda suka ce.
“Okey, daga yau zamu dinga kiranshi da.....”bai ƙarasa sunan ba yai shiru yana kallon fuskar Gabriel duk sun ƙagara da suji wani suna za’a sanya mashi.

“SAJEED” wani irin ihun farin ciki suka saki, Sunan yayi bala’en yi masu daɗi musamman Azeeza.

“Ina fata sunan yayi maka”? Jinjina mashi kai Gabriel yai”eh, nagode sosai”
Boss man yace”okey, daga yanzu sunan da zaku dinga kiran shi da shi kenan wato Sajeed, Kefa Angel meye asalin sunanki” farfari tayi mashi da ido kafin ta bashi amsa da cewa”Unaisah”
Tamkar baisan sunan ba yace”wow suna mai daɗi, mai zai hana kema mu dinga kiranki da asalin sunanki” zumbura mashi baki tayi ba tare data furta komai ba, tana son asalin sunanta sai dai tafi son sunan Angel saboda daddynta ne ya za6a mata shi.

“Dan Allah Angel ki amince mu dinga kiranki da Unaisah Yafi daɗi Allah” Batul ce tayi maganar, Hannah tace”nima nafison Unaisah din yana da daɗi”
Haris ma yace”nima shine za6ina, Unaisah”
Ta6e baki Angel tayi tare da kallon fuskar Danish don taji me zaice, batasan boss man na kallon ta ba, Ya fahimci tafi ƙaunar Danish akan sauran ƴan uwanta, saboda yadda take bashi muhimmanci.

Da ido tayi mashi alamar ta amince da sunan ko kuwa”? Ɗaga mata gira yai alamar eh.
Dawo da dubanta tayi akan fuskar Boss man”shikenan na amince, adinga kirana da Unaisah”
Murmushi ya saki ba tare da sun gani ba saboda mask din fuskarshi.
Javed ne yace “um sallah ma Angel ta koya mana amma bamu taba yi ba dama tace in muka zo zamu rinqa sallah da karatu”

Jinjina kai yayi tare da fadin “karku damu zamu rinƙa karatu tare in sha Allah komai zaku iya wanda ya shafi addinin muslunci” Da alama sunji dadin maganar
Jemimahh tace”wai kai ba zaka cire abun fuskarka ba”?
Girgiza mata kai yai”a’a” tace “to meyasa baka son mu ganka? Ko dai mummuna ne kai baka da kyau”? Dariya ce ta kubce mashi.

Azeeza tace”bakya jin magana jemimah ina ruwanki da shi? Ke komai sai kin nuna zaƙewa” harara jemimah ta watsa mata”Ni ki ƙyale ni,” ta faɗa tana duban shi”dan Allah ka cire muga fuskarka”
Javed yace”nima inason naganka, tun da kace atare zamu rayu agidan nan, please ka cire mu ga fuskar ka.

Girga mashi kai yai”Ku yi haƙuri ba yanzu ba, tunda muna atare wata rana zaku ganni”
Angel tace”babu komai, Allah ya nuna mana lokacin, Ni sai na ke jima kamar nasan muryarka don dai kace ba yanzu zaka buɗe fuskarka ba ni kuma da saina gane wanene kai” hakanan ta faɗa bada wata manufa ba, tasan batasan shi ba.

Murmushi yai ba tare daya tanka mata ba, kallon Ummi yai, tun da ta zauna tana sauraron su bata ce komai ba
“Ba abunda zaki faɗa masu ne”?
Yamutsa fuska tayi kamar bata son furta magana tace”naso yau in taimaka masu su gyara kansu, amma nabari sai zuwa gobe ko jibi, idan na ƙara hutawa”

Yace”okey, ku tashi mu tafi inaso zan nuna maku ko’ina na cikin part dinku, duk abunda kuka gani wanda kuke neman ƙarin bayani akanshi Ni zaku tambaya” suka amsa mashi da toh.
Miƙewa sukayi Ummi ma ta miƙe don tana son itama ta ƙarema ko’ina na part din kallo, cikinsa da wajensa.
Yinin Ranar sunsha yawo, Sunga abubuwan ban mamaki dana Al’ajabi, ido ya samu abinci, kamar karsu dawo cikin gidan, Boss man yasha tambayoyi kamar ƴan jarida, duk abunda basu gane ba sai sun tambayeshi ba ƙaramar wahala yasha ba, itama ummi tana taimaka mashi wurin amsa masu tambayarsu, duk yawon da suka sha basu leƙa wajen gidan ba, kuma basu shiga sauran part din ba.

*JOS CITY*

Idan muka koma 6angaren Alhaji ubaid, tunda garin Allah Ya waye da sassafe Benazir ta farka tana sambatu akan mijinta da ƴarta, Alhaji ubaid Ya jira kiran Dr.shureim sai dai shiru, har kiran layin wayarshi yai amma bai ɗaga ba, ya kira Alhaji musa akaci sa’a kiran ya shiga kusan sau goma tana ringing ba’ayi picking ba, gashi lokaci yana ta tafiya babu alamun zuwan Shureim, daga bisani suka kira likita domin duba lafiyar benazir, bayan ya duddubata ya faɗa masu cewa lafiyarta ƙalau, sai dai akwai abun da ta ƙwallafa rai akanshi yaji tana fadin mijinta da ƴarta yace to kada su kuskura suce zasu faɗa mata zancen babu su, don a halin da take aciki yanzu bazata Iya jurewa ba, zata Iya samun ta6in hankali, zaifi suja baki suyi shiru, sannan suci gaba da kwantar mata da hankali har zuwa lokacin da zata samu natsuwa sosai, tukunna su faɗa mata, sunji dadin shawarwarin da likitan ya basu, bayan tafiyarshi cikin ikon Allah, Benazir ta dawo hayyacinta a lokacin da basu yi tsammani ba, ganin Iyayenta a gefe da gefen gadon da take akwance yasa ta rushe da kukan farin ciki tana ambaton sunayensu haɗi da roƙon yafiyarsu akan babban laifin da ta aikata na guduwar da tayi ba tare da sanin su ba, tayi mamakin jin suna kwantar mata da hankalinta, sukace su basu ruƙeta aransu ba, sun yafe mata, ta daina kuka komai ya riga daya wuce, tuna baya baida amfani tun da ya riga da ya faru, ƙaddarace da babu wanda ya isa ya canza ta, haƙiƙa taji daɗin kyakkyawar tarbar da ta samu awurinsu tayi tsammanin zasu koreta ne idan sun ganta, saima suka koma suna lallashinta haɗi da tarairayarta, abinci ma abaki hajiya layla ta bata shi, duk bayan ƴan mintuna sai ta tambayesu ina mijinta da jinjirar data bari a cikin kwamin wanka? tana son tagansu, idan suna agida dan Allah su taimaka su kaita wurin su, hajiya layla ta bata haƙuri da cewa sunyi tafiya basa a ƙasar amma tana da tabbacin sun kusa dawowa, sai lokacin tace toh ita yarinyar ta rayu? Waye ya rene ta harta girma? Kuma ya sunanta”?
Hajiya layla tace”ta rayu mana, kyakkyawar budurwa ta ɗauko hasken fatarki, kamannin fuskarta ne dai ta ɗauko na daddynta, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, tana ta faman sauke ajiyar zuciya tace”baki faɗa min sunanta ba? Kuma tasan ni? An faɗa mata sunan mahaifiyarta? Kuma Kuna nuna mata hotona”? Shiru hajiya layla tayi don batasan amsar da zata bata ba, ita kanta ba zumunci take yi da tajuddeen ba, saboda bada son ranta ya auri Benazir ba, shiyasa ko zuwa gidan bata ta6a yi ba, tun lokacin da suka koma dubai da zama, a hotone ma ta ta6a ganin Angel din, taji nauyin amsar da zata ba benazir, daƙyar ta Iya furta mata sunanta Angel, tana faman murmushin yaƙe tace ai tasanki ya za’ai mu ƙi nuna mata hotonki, duk in tajudden ya kawota gidan nan sai mun nuna mata hotunanki, Yarinyar tana sonki sosai, kullum maganarta ina mamanta take? Yaushe zata dawo? Meyasa kika tafi baki waiwaye ta ba’ jin hakan yasa benazir ta fashe da kuka, Hajiya layla duk tasha jinin jikinta, fargabarta ranar da Allah zai haɗa benazir da ƴarta idan har tana araye tabbas zaiyi wuya yarinyar ta amince da ita, ga kuma ƙaryar data faɗa mata.

Cikin shessheƙar kuka benazir tace”amma dai baku fada mata a yanayin da na tafi nabarta ba ko”? Hajiya layla tace eh bamu faɗa mata ba, mun dai ce mata kin 6ace ne ba’asan inda kika tafi ba, to dayake yarinyar tana da tawakkali kuma tana samun kulawar tajo da kuma kulawar da muke bata hakan bai dameta sosai ba”
baiwar Allah benazir jikinta duk yai sanyi, tace Ina aneelerh da mijinta”?
Hajiya layla tace ai mijin aneelerh baya nan shima tare suka yi tafiyar, ta matsa lamba akan tana son akaita gidansu Aneelerh don taganta, Alhaji ubaid ya sanar da ita cewa ai basa garin jos sun koma abuja da zama, badan taso ba ta haƙura, damuwar hajiyar laila ɗaya kada tace su nuna mata hoton ƴarta saboda babu maishi acikinsu, har ƙwara Alhaji ubaid wata’ƙil asamu hutunanta na yarinyata saboda yana son yarinyar, cikin ikon Allah benazir bata tambayesu game da hoton Angel ba, saboda halin damuwar data shiga gani take kamar bazata ta6a ganin mijinta da ƴarta ba, duk da mommynta ta kwantar mata da hankalinta.
Masu gadin gidan kusan sau uku suna shigowa cikin gidan domin duba lafiyar benazir, duk sun damu da ita, haka zalika zainab takasa samun sukuni duk bayan ƴan mintuna saita leƙo ta dubata, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba ganin yadda kowa ya damu da ita.
Tana akwance saman gadonta, hajiya layla tana a gefenta, a lokacin Alhaji ubaid Ya koma dakinshi, damuwar duniya ta ishe shi, tun da ya jaraba kiran layin shureim dana Alhaji ubaid basu ɗaga ba, ya rasa sukuni, sai faman yin zarya yake yi acikin ɗakin shi, kaf family dinsu babu wanda yasan da dawowar benazir, saboda bai sanar da su ba, hatta mutanan da suke zumunci da su bai faɗamawa ba, saboda mai gemu ya basu shawarar su dan jinkirta tunda ba’asan wanene yai silar yi mata asirin ba, zasu Iya ƙara cutar da ita idan suka ji cewa tana araye kuma ta dawo gida, da ace Iyayensu na araye da kuwa sune mutun na farko da zai fara sanarmawa donsu taya shi murna sai dai babu su, mutum biyu ne yafi yarda dasu ƙanin shi Alhaji musa sai ƙanwarsu autar gidansu Hajiya Laurat, second wife din mai girma sharafuddeen obinna, itama ya jaraba kiran layin wayarta bata yi picking ba, abun duniya duk ya ishe shi.
Chapter 101 · 0% Book details