← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 152

Sashe 26

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kinga tun da ke kika ɗaga Kiran nan Ki lalla6a ki je kawai ki kai masu awuce wajen” Acewar Abla, Yamutsa fuska marwa ta yi, Ba yadda ta Iya don dole ta haɗa masu coffee acikin mugs guda biyu ta ɗaura saman Plate ta fuce daga cikin kitchen ɗin.

Tun lokacin da Able ta fita hannunta ɗauke da tray Na breakfast ɗin Hajiya Saratu, Kai tsaye ta nufi Part ɗinsu, Tun kan ta ƙara sa gaban ƙofar ɗakin ta daddaɗan ƙamshin turarenta Ya daki hancinta, macace mai son ƙamshi ga iya ɗaukar Wanka, A bakin door ɗin Ta tsaya tare da Yi mata sallama, daga cikin ɗakin tajiyo muryar Hajiya saratu

“U can come in” A hankali ta tura ƙofar ta shiga, Hajiya saratu tana azaune tsakiyar Katafaren gadonta, jikinta na asanye da jallabiya, Kanta babu Kallabi Kitson zanene all back Wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗarta, fararen idanuwanta suna a manne da farin glass medicated, tana da duhun fata mai kyan gaske, Hutu ya zauna mata, Hankalinta gaba ɗaya yana akan tsadaddar Apple Laptop ɗin da ta ke yin operating, ga dukkan alamu aiki ta ke yi.

“Once you’re done looking at me, please put the food on the table and leave my room.” Muryarta ce ta fargar da Safa daga kallon ƙurullan da ta ke bin ta da shi, Adabarbace ta gaishe da ita”Ina kwana Hajiya,” Guntun tsoki taja ba tare da ta amsa mata ba, ko kallo ba ta ishe ta ba, asaman front table din bakin gadon, Safa ta ɗaura mata tray din

“ko akwai wani abu da ki ke buƙata “? cikin Jin shakkarta Safa ta yi mata tambayar don tasan halinta, in har bata ba mutun iznin tafiya ba, yai yunƙurin Juyawa zai tafi atsawace zata ce mashi da Iznin wa!

Safa har ta gaji da tsayuwa shiru bata tanka mata ba, tamkar bata san da mutun awurin ba, Halinta ne share mutane, sai da ta mula ta sha iska tukunna ta ba ta zinin tafiya, bayan fitar Safa daga ɗakin, Ta dakata da yin aikin laptop ɗin, Yunƙurawa tayi tare da kai hannu ta damƙo Burger Ta soma turata abakinta tana ci, Bata wasa da Cikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta handameta, ta kuma janyo Chicken wings tana ci, baya tagama ta ɗauki bowl ɗin dake shaƙe da plaintain chips hannu baka hannu ƙurya kamar mai fama da cutar yunwa, Saida ta lamushe komai, a ƙarshe ta kora da ruwan lemu mai sanyi.

“Daɗina dake bakya wasa da Cikin ki,” Jin muryar Mijin nata yasa ta ɗago da eye balls ɗinta akan fuskar shi, Daga cikin toilet ya fito waist ɗinshi ɗaure da towel, Ƙirarshi tamkar ɗan wrestling, Kakkarfan mutunne Jibgegen ƙato, Kyakkyawan ba’indiye Sumar kanshi akwance luf saman kanshi, Ga wani kwantaccen saje gefe da gefen doguwar fuskarshi, ‘ ta6e mashi baki Tayi”meye haka? Bana hanaka yawo da towel a qugunka ba? Yanzu da ace mai aikin nan tana acikin ɗaki ka fito fa? Fuskarta aɗaure tayi mashi maganar, Matsawa yai kusa da ita yaɗan ranƙwafa saitin fuskarta”yaushe zaki daina kishina? Murga mashi baki tayi”Bansani ba, Ni dai na faɗa maka, Karka kuskura ka ƙara fitowa ɗaure da guntun abu a qugunka bana son ta6ara” Ido cikin ido suke kallon Juna.

“Ƴa’ƴan mu Uku, kowan nan su Ya mallaki hankalin shi, Na yi tsammanin zaki rage kishi na da kike Yi” harara ta watsa mashi”pls Ka wuce ka je ka sanya suturarka, bana son ganin ka ahaka” Hannu ya kai yana ƙoƙarin warware towel ɗin gabanshi da sauri ta damƙi hannayenshi aɗan fadace tace”Pravin meye haka? Yarinta ce fa wannan”? Kashe mata ido ɗaya yayi fuskarshi ɗauke da murmushi yace”indai ina atare dake bazan ta6a girma ba, saboda tsantsar ƙaunar da kike nuna min” ta6e baki Saratu Tayi”naji yanzu kaje ka sanya suturarka, Sannan me kake son Ci insa akawo maka” Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”abunda kika ci shi nake sonci abar ƙaunata, naga ma har kin kammala naki breakfast ɗin why ba ki bari na fito munci atare ba?” Ɗaure mashi fuska tayi “Pravin mu fa ba ƙananun yara bane da zaka tsaya kana gayamin kalaman Soyayya, ko da ya ke nafa tuna kufa indiyawan nan bautawa soyayya kuke yi har ku tsufa kuna abu ɗaya” cikin Zolaya ta ƙarasa maganar, gyaɗa kanshi yai”komi zaki ce bazanji haushin kalamanki ba, Amaryata kuma uwargidana, sannan uwar ƴa’ƴana abun alfaharina,” lumshe ido ta ɗanyi idan zata biyewa pravin ba zai barta taci gaba da yin aikinta ba, gwanine a fagen Iya soyayya da daɗin baki, Ya ƙware wurin Iya jan hankalin mace.

“Romeo, now your Juliet is at work, I’m almost done, zansa a kawo maka breakfast ɗin ka, Ni da kaina ma zan baka abincin abaki” Amsa mata yai da Okey, Daƙyar ta lalla6a shi Ya miƙe ya nufi Cikin ɗakin Yana tafiya tana satar kallon Bayanshi, a gaban closet ɗin kayanshi Ya tsaya tare da kai hannu ya buɗe

“My Juliet ba ki faɗa min kayan da ki ke so In sanya ma”! Murmushi ta saki”Yau babu aiki, ka samu hutu don haka Nafi sha’awar ganinka Cikin shigarku ta al’ada, Ya gane me take nufi, riga da wando Ya curo kalar na mazan Indiya ya sanya su ajikinshi, sun bi shape din jikinshi yadda kasan matashin saurayi saboda haɗuwarshi.

Bayan ya kammala Shirya kanshi, Hajiya saratu tasa aka kawo mashi breakfast, Da kanta take bashi abaki Yana ci, mugun son shi ta ke yi, ta mutu akan pravin, kamar yadda shima yake ƙaunarta, Allah Ya hada jininsu. Babu mai cin moriyarta irin Mijinta, komai nata mallakin shi ne.

Lokacin Da Sophia ta ƙarasa Bedroom ɗin twins dake acan Upstairs Second floor, Jikinta na kakarwa ta yi knocking ƙofar, almost 3 times kafin tajiyo muryar ɗaya daga Cikinsu “you can come in” Numfashi taja kafin ta tura ƙofar Haɗaɗɗen bedroom ɗinsu, Sanyin A.c da ƙamshin Turarensu ne Ya daki hancinta har sai da ta lumshe idanuwanta saboda tsabar yadda ƙamshin Ya kurɗaɗa ta ƙofofin Hancinta, tunkan ta shiga ciki Ta hango Ɗaya daga Cikinsu A tsaye Gaban tanƙameman dressing mirror Daga shi Sai short a jikinsa launin ja, Yayin da twin brother ɗin shi yake a kwance saman gado rabin jikin shi lullu6e da duvet. Kyawun surarsu sak irin na mahaifinsu Pravin, tamkar yayi kakinsu.

Muryarta na ɗan rawa tace”Barka da safiya yalla6ai, Ga coffee ɗin Ina zan aje’ ba tare da ya juya ya kalle ta ba yace “On my head” tuni tasha jinin jikinta, Batasan Ya zatayi ba, Zaid dake a kwance saman gadon Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya saman front table ɗin gaban gadon.

“Is that how your parent taught you to enter a room without saying ‘Assalamu Alaikum ? Ɗakin kafurai kika shigo”?

Muryarshi tamkar ta mashayin giya

“Afwan yalla6ai, kafin in shigo saida na fara yin sallama, wata’ƙil baka jini ba ne” A sukwane Ya juya yana binta ɗan iskan kallo

“Am I deaf?” girgiza mashi kai tayi muryarta na kakarwa tace “That’s not what I meant, sir...” bai bari takai ƙar ƙarshen maganarta ba, ya nuna mata ƙofar fita
Aɗan tsawace ya furta “Oya Go back ki sake yin wata sallamar”
fuskarshi a murtuke yayi maganar, Idanuwan sophia tuni sun ciko tab da ƙwalla, Jiki asanyaye ta juya ta koma waje.

Kware Murya tayi”Assalamu alaikum” shiru bai amsa mata ba, shiga ciki tayi”Sir nayi sallamar in shigo? Coffee ɗin Yana hucewa”

Kafin Ya bata amsa Zayn dake kwance saman gado ya furta “I didn’t hear it. Go back and make another greeting”

Tayi mamakin Jin muryarshi duk a tunaninta bacci yake yi, ashe idonshi biyu, “ Maƙoshinta tamkar zai 6allo ta ƙara kware murya wurin Yi masu Sallama, Tun tana yi da marmari har ta fara gajiya, idanuwanta sunyi luhu luhu, A ƙalla tayi masu sallama kusan sau Goma sha biyar ba tare da sun bata iznin shiga ɗakin ba, Har saida Coffeen hannunta Ya salafce, sai da suka tabbatar Ta jigata sosai tukunna Zaid yace da ita ta shigo ciki, hawaye nabin kuncinta ta shigo.

Kishingiɗe ta samu zayn ya ɗaura kanshi saman pillow, Ko kallon arziƙi bata ishe shi ba, jiki na 6ari ta nufi Table zata ɗaura plate ɗin, Kakkausar Murayar zayn ce ta dakatar da ita

“Don’t you dare put that on the table! Ki koma ki canza wani coffee ɗin, wa zai sha abu ya salafce” juyawa marwa tayi tana kuka ta fuce daga Cikin ɗakin, ko a jikinsu, sun Iya rashin mutunci da mugunta idan suka so, duk rana ta Allah sai sun sanya ɗaya daga cikin masu aikin gidansu zubar da hawaye.

“Bro, when are we going back to America?” Zaid ne yai maganar while sitting on the dressing table chair.

Yatsina fuska Zayn yai “we have no way out, Zaid, seriously, naji takaicin tursasa mana dawowa Nigeria da obie yai, Ya hana rayuwarmu sakat, mu kaɗai mu ka tsone mashi ido, ga Owais can kamar tsuntsu Yana shawagi a ƙasashen waje sai mu da muka tsone mashi ido, nifa na gaji da halin dattijon nan, na rasa zaman me yake yi acikin duniyar nan, duk shekara sai na sayi sabon likafi da miski na mutuwarshi but yaƙi tafiya” Ranshi a6ace yake magana

Zaid dake kallon ɗan uwan nashi yana murmushi yace” I know what you’re mad about” Yatsina fuska yai”Kai ma ɗin itace damuwarka, Ummin america ce silar komai, “ Yana magana a harzuƙe ga dukkan alamu an fama mashi raunin dake acikin zuciyarshi.

“Everything about her is different. From the first day I saw her, I knew she was a classy woman with a magnetic personality that could captivate any man.” lumshe ido zayn yayi, bakomai yake tariyowa ba face farkon haɗuwarsu da ita.

“Naso ace ta amince min, ba abunda zai hana in aureta, zan tattara dukiyata gaba ɗaya data mahaifiyata, da ta Dattijon can duka In bada a matsayin sadakinta, sai dai kash ta nuna bata buƙatar aure arayuwarta, Zaid ya zanyi da raina? Ta sanya min jarabar da bazan Iya gogeta ba” cikin jin shauƙi yake magana.
Chapter 26 · 0% Book details