← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 152

Sashe 46

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Angel ina ne nan? Wanene Ya kawo mu? Wlh tsoro muke ji, munga wasu mutane da bamu saba gani ba, kada su cutar damu Angel, sai kallon mu suke yi kamar zasu lashe mu” Su parveen ne ke kora mata jawabi
“Ko dai mafarki muke Yi ne? Mu dake acikin Daji Ya akai muka tsinci kanmu a wannan wurin tare da wasu mutane masu fararen Kaya, Angel ko dai Aljannace da kike bamu labari? Idan mun mutu zamu shiga” Maganar Batul tayi matuƙar bata dariya, Daƙyar ta samu suka saketa, Ga jemimah ta ƙanƙameta Jikinta sai kerma Yake yi.

Azeeza tana maƙale da Gabriel Sarkin tsoro, Ta kasa ɗauke idanuwanta daga kan faces ɗin Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirko suna kallonsu.

“Angel mun shiga ku, Sai kallon mu suke yi,” Hanna ce ta yi maganar
Muryar dr. Laura ce ta katse masu Hanzarinsu cikin harshen turanci ta ke yin maganar

“Ku kwantar da hankalinku, babu wanda zai cutar daku, Anan inda kuke Asibiti ne, mu kuma da kuke gani likitoci ne da nurses haƙƙinmu ne kula da Lafiyarku, Za mu taimaka maku don ganin kun warware daga lalurar dake damunku, Muna so ku ɗauke mu tamkar Ƴan uwanku, idan ku ka yi hakan munyi maku alƙawarin zamu share maku hawayenku, Zamu gatanta ku mu baku kyakkyawan kulawa har izuwa lokacin da zamu miƙa ku ga Iyayen ku.

Tun da tafara Yi masu magana kowannansu Ya natsu yana sauraronta, da alama sun fara fahimtarta

Matsowa Kusa Dr Brown Yai daga gefenta Ya tsaya”duk wani abu da kuke buƙata zamu yi maku shi, ku ɗauka tamkar kuna a gidan Iyayenku ne, burin mu shine ku bamu haɗin kai, Ku daina Jin tsoron mu”
Muryar Dr Jack Ce Ta janyo hankulansu ga dubanshi
“Mun haɗa ku wuri ɗaya ne saboda mun fahimci ba za ku ta6a sakewa damu ba, idan har ba Kuna atare da Ƴar uwarku Angel ba, Muna fata Yanzu hankalinku zai kwanta, ga ku ga Mamanku Angel” Da zolaya yayi masu maganar, murmushi Angel ta saki tana kallonsu, daga gani suna da mutunci.

“Masoyiya Angel faɗa min me ki ke yi wa Yaran nan naki ne? Don na lura ba ƙaramin ƙaunar ki su ke Yi ba” Dr Brown ne yai magana haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, Sunnar da kanta ƙasa Tayi dariya takeso tayi sai da takasa.

“Yaushe kika haife su ne? Sannan Ina Mijin naki”? Kunyace ta rufe Angel da sauri ta ɗaura Kanta saman sumar kan Jemimah dake ruƙe a hannunta.

Dariya Dr. laura ta saki”Wow Kunya take ji, To ko dai Matashin saurayin nan mai bacci ne mijinki? Wannan kyakkyawan don naji kamar kina ambaton sunanshi” gaba ɗaya sun sanyata jin Kunya ji take kamar ta nutse ga farin Ciki da ya lullu6eta.

Da biyu likitocin suke zolayarta, Yana daga cikin aikinsu kwantar da hankalin Mara lafiya musamman su da suke son su saki jiki da su, Ta hakanne zasu samu bayanan da suke so daga gareta.

“Mun fahimci Masoyiya Angel bakinta ya mutu, saboda An sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi, Yanzu faɗa min me kikeson Ci ke da Ƴan uwan naki mu kawo maku” Cikin kulawa Dr. laura ke yi mata magana.

Kallon sauran Ƴan uwan nata tayi

“Ko ba ku jin yunwa ne”? Shiru suka yi ba wanda Ya bata amsa, idonsu akan Angel, Dariya doctors ɗin suka saki
“Oh Baku Iya magana sai da izninta, to ke masoyiya Angel Faɗa mana me kikeso akawo maki keda Ƴa’ƴan naki don bama son barinku da Yunwa”

Cikin Jin kunyarsu Angel ta furta”komai muka samu zamu ci” Jinjina kai Dr Laura Tayi kafin ta juya ta kalli Sister rebecca”A shirya masu lafiyayyan abinci da Kayan sha” amsa mata Tayi da toh da sauri ta juya ta fuce.

Dawo da dubanta tayi akan fuskokinsu
“Yanzu zamu tafi mu baku wuri Pls Idan an kawo maku abincin Ku tabbatar Kun cinye min shi duka kaf, zanji daɗin hakan,’ dr Laura davis Na rufe Maki Dr Mark Yace”Zamu dawo Da Anjima, Kyawawan ƴan mata, dole in za6i ɗaya daga cikin ku, irin wannan Kyau haka”
Dr Bown Yace”ai ba kai kaɗai ba mutumina, Ni ruwan ido ma ya hanani zabar ɗaya, ta ko’ina Kyau nake gani musamman Masoyiya Angel ta tafi da ni” Dariya ce ta kubcewa Angel da Gabriel
Harara Dr Laura davis Ta watsa mashi”bazaiyiwu ba, Duk na riga ku, Nima nayiwa ƴa’ƴana kamun matan aure a Cikin su’ Nishaɗi sosai suka sanya su.
“Zamu tafi Masoyiya Angel, Amma kafin nan Ki kula mana da ƴa’ƴanki, Ki lallashesu su daina mana kuka dake kanki bama so kuna zubda tsadaddun hawayenku” Cikin sanyin murya Angel ta amsa mata da toh, Sallama suka Yi masu atare suka fuce daga ɗakin suna masu santin Kyawun Yaran acikin ransu.
Fitarsu keda Wuya Ange Ta fada saman Gadon rungume da jamimah tana tiƙar dariyar Farin Ciki tana faɗin”ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN”

“Kuyi Farin Ciki mana, Ina Tayamu murna Mun ku6uta daga Kurkukun ƙaddara, Mun zama masu ƴanci” Su Batul sunƙi sakin jiki har yanzu basu fahimci Ta ya ya akai suka tsinci kansu a wannan wurin ba.
Gabriel ne yai ƙoƙarin fahimtar da su abunda Ya faru zuwan Sojoji Dajin.
Wayyo Allah daɗi Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskokinsu, Bakunansu sun kasa rufuwa Fararen haƙoransu tamkar Gonar auduga
“Gabriel kana nufin Yanzu mun bar kurkuku da daji? Muna acikin Mutanan duniya” Fuskar Gabriel da murmushi Ya amsa masu”ƙwarai kuwa, Babu ku babu zubar da hawaye baƙin ciki da kunci sun ƙare” Tsabar Farin Ciki Suna kuka suna dariya, gaba ɗaya suka Haye saman Gadon Angel, suka kwanta a jere da ita sai daɗi suke ji saman ceilling ɗin ɗakin suka ƙurawa ido kowa Yana tariyo abubuwan da suka faru a rayuwarshi jin shessheƙar kukansu ta cika ɗakinne Yasa ta soma yi masu magana cikin lallashi
“Dan Allah ku daina, Yanzu lokacin farin ciki ne, Godiya yakamata Muyiwa Allah, a koda yaushe shi mahaƙurci mawadaci ne, yau gashi dai mun shaida hakan Allah ya kar6i kokenmu yaji ƙanmu ya raba mu da ƙangin rayuwar da muke aciki, A yau mu masu ƴan ci ne zamu shaƙi Iskar duniya son ranmu batare da wani yayi mana Iyaka da ita ba” Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu
Cikin shessheƙar Kuka Azeeza ta soma magana tana fadin”Ni ƴan uwanmu nake tunanawo waɗanda muka rasa acikinmu, tare da Salsabeel da ya taimaki rayuwar mu, nasan dole su kashe shi idan suka kama shi Yana acan kurkuku Suna azabtar dashi”

Naufal ya ɗaura da cewa”babu Deeja! Babu Mubeen Akan idonmu ya yanke jiki Ya faɗi, a lokacin muna aga6ar barin kurkuku.....” Kasa ƙarasa maganar Yayi saboda kukan da ya ciyo shi.

Javed ya dasa daga Inda ya tsaya”Mun rasa tsohuwa tamira! Mun rasa Eve da Yasmin sannan mun rasa Hibba da Rubina, da Sarah! “ tunkan Ya rufe Baki Angel ta ɗaura da cewa”Allah Sarki Unaiza Ƴar gidan daddy, da Majnoon Bayin Allah ban ta6a tunanin zamu tsira ba tare dasu, Muna ƙaunar ƴan uwanmu sosai, Sai dai mutuwa tayi mana Yankan ƙauna, Ta raba mu da su, In sha Allah zamu haɗu da su agidan Aljanna inda babu kurkukun ƙaddara babu duk wani mugu, Allah sarki tsohuwa tamira da Salsabeel waɗannan bayin Allahn Har duniya ta naɗe bazamu ta6a mantawa dasu ba, saboda Sun kafa tarihi acikin zukatanmu In sha Allah a koda yaushe zamu dinga binsu da addu’a, sannan zamu Cika masu burin su na ruguza tarihin KURUKUKUN ƘADDARA.

Abubuwa da dama suke tariyowa na rayuwarsu na baƙin Ciki da farin Ciki
“Angel Danish fa har yanzu bai farfaɗo ba, Haris kuma Bashi da ƙoshin lafiya nurse ta faɗa min abunda ke damun shi ni nasan silar deeja ne, Amma tace Ciwon nashi bazai jima ba, Zaiji sauki”
Jin wannan maganar yasa gabanta faɗuwa, A hanzarce ta miƙe zaune saman mattress ɗin, su Batul ma suka mimmiƙe suna kallonta, sun sha kuka fuskokinsu sunyi jawur dasu abunka ga farare, Ita dai Jemimah tunda ta lafe ma angel hankalinta kwance bata da sauran damuwa.

Ƙasa ƙasa da murya ta ambaci kalmar Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Gabriel Akwai matsala! Wai ni wace ƙasa ce wannan”? A matuƙar ruɗe ta jefa mashi Tambayar, duk budurin da akeyi bata lura da fararen fata bane sai da yayi mata zancen Danish.

“Ni kaina Angel bansani ba” Dafe kai tayi da hannu ɗaya, Yayin da take bin ko’ina na room ɗin da kallo, karaf idonta ya sauka akan wani hoto dake manne jikin bango, a jikin shi an rubuta

SAN ANTONIO TEXAS United states of America

zazzare idanuwanta waje tayi wuƙi wuƙi Muryarta Na kakarwa ta soma maimaita Sunan America, tun da take arayuwarta bata ta6a taka kafadarta a ƙasar waje ba, Iya Nigeria ne, Yau ƙaddara Ta jefo su America a maimakon Nigeria! Hankalinta idan yai dubu toh ya tashi, ta ya ya zasu Koma Nigeria har su samu damar ɗauko ruwan zamzam da zasu ba Danish? Don tana Ji aranta Baccin da yake yi bana lafiya bane zaiyi wuya ya farka batare da giant’s heart ɗinsa ta motsa ba, Muryoyinsu Aruɗe su ke ambaci sunanta”Angel menene? Bamu tsira ba ko? Wani abu zai faru damu”? Girgiza masu kai tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Wlh ba Nigeria bace wannan ba ƙasa ta bace, America ce ƙasar turawa, taya akai haka ta faru!? Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke, don su basu san abunda take gujemawa ba, Lamarin ya girgizata har tafara tunanin dama kurkukun ƙaddarar ba A nigeria ya ke ba? Akwai gagarumar matsala dole su nemi mafita.

“Angel ae zamu Iya zuwa can ko”? Da sauri Gabriel ya amsa masu da cewa”Eh mana ba wani abu, kada ku damu kanku, Sojoji sunce idan muka basu haɗin kai zasu damƙa mu wurin Iyayenmu, Idan suka tambayemu sai mu faɗa masu cewa Mu ƴan nigeria ne”
Chapter 46 · 0% Book details