← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 152

Sashe 104

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda yake tariyo rayuwarsu haka itama take tunano daddynta, ji take kamar shine ya rungumeta, shiyasa ta ƙara narke mashi tayi lamo saman wide chest dinshi......

Gaba ɗayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba zato ba tsammani Boss Man yaji dirar wani abu saman bayanshi, da sauri ya ɗago da kanshi idanuwan shi sun canza launi sun kada jawur kamar mai fama da ciwon ido, yayi mamakin ganin pillow da aka jefo mashi ya fadi ƙasa, da sauri ya ɗaga ido sama don ganin wanene ya wurgo mashi pillow saman bayanshi, karaf idanuwan shi suka sauka akan Danish dake tsaye can second floor, hannun shi ruƙe da wani pillown Yana niyar ƙara jeho mashi, fitowar shi kenan daga ɗaki idanuwanshi suka hango mashi Angel ɗinsa rungume da wani ƙato, shine fa yaje ɗaki ya ɗauko fululluka har biyu Ya jeho mashi ɗaya.

Ya haɗe fuska babu annuri, kayan bacci ne ajikinshi riga da wando launin pink sunyi bala’en yi mashi kyau.

Harara ya watsa ma boss man, ganin Angel taki barin ƙirjin mutumin yasa shi ƙara daddagewa ya wurgo mata pillow, da sauri boss man Ya tarbe pillown a hannun shi, Lamarin ya ɗaure mashi kai, sai yanzu ya gane dalilin dayasa yaron yaƙi sakar mashi fuska tun jiya yake daure mashi fuska, ashe kishi ne ke damun shi.

“Unaisah”! Jin boss man ya ambaci sunanta yasa ta ɗago da kanta tana kallon shi, mamaki ne ya kamata ganin pillow a hannun shi, da ido yai mata nuna da bayanta, da sauri ta juya don ganin wanene, a tsaye ta hango shi ya ruƙe qugu yana aiko masu da harara.

Batasan sa’adda ta tuntsire da dariya hada dafe ciki,
da zolaya boss man yace”kishine ya addabe shi shiyasa yake jifar mu da pillow, faɗa min meke a tsakaninki dashi.

Tana dariya tace”babu komai, shaƙuwace a tsakaninmu, baya son yaganni tare da wani idan ba ƴan uwanmu ba, haushi yake ji”

“Kice ƙwara in lalla6a in gudu, tunkan ya sauko don wannan har buguna zai Iyayi, “ ya fada tare da damƙa mata pillow din hannun shi, Ya juya da sauri ya nufi ƙofar fita Yana faman sakin murmushi, bai ta6a ganin namiji mai kishi ba irin Danish.

Zukunnawa tayi ƙasa ta ɗauki ɗayan pillow, ta haɗa dana hannunta, ta nufi upstairs, Har tsoron tunkarar shi take Ji, saboda yadda ya kumbura fuska, soft red lips dinsa sunyi suntum da su”
Koda ta haye up din, taga Ya dunƙule hannu kamar zai nausheta, wurga mashi pillows din tayi saman faffadan kirjinshi, da gudu ta sauko down tana tiƙar dariya, akan idonta ya tattara pillows din ya nufi dakinshi ya shige.

Yau da wuri suka yi breakfast dinsu, saboda gyaran jikin da ummi zatayi masu.

A Katafaren Home beauty station ɗin dake a cikin part dinsu, saboda su aka tadani komai na cikinsa, ɗakin Ya haɗu, bangon dakin beauty shelf ne An jera Kayan gyaran jiki kala kala, dana gyaran gashi acikin kowani shelf, hada foot care product and skin care product, Ga wani faskeken mirror a jikin bango, daga gabanshi wasu hadaddun kujerune kusan guda takwas, A saman kujerun kowa Ya samu wuri Ya zauna su shidda ne matan dake acikinsu, banda mazan tun bayan da suka kammala yin breakfast suka tafi ɗaukar karatu a inda suke Yin sallah. Suma matan acan za’a dinga yi masu karatu.

Kowaccensu tana sanye da bathrobe a jikinta, Ummi ce ta basu rigunan, saboda da taji daɗin gyara masu sumar kansu.

Kujerar farko Unaisah ce zaune asamanta, ta biyu batul ce akusa da ita, sai Parveen itama ta hakimce saman tata kujerar, daga gefenta Jemimah da Azeeza ne saman nasu kujerun bayan su sai Hannah.

sun natsu suna kallon faces dinsu ta cikin madubi sai faman sakar ma juna murmushi suke yi kamar wasu zautattu, daɗi suke ji za’a gyara masu sumar kansu, har sun fara imaginning din kyawun da zasuyi

babu mai magana acikin su, saboda ummi tana acikin dakin ta hanasu surutu

tana a sanye da dogon wando ƴar rigar data sanya daƙyar ta rufe cibinta, babu mayafi akanta.

“Dawa zamu fara” ta faɗa tana dubansu, har suna haɗa baki wurin furta Ni,
“bari in za6a da kaina” ta fada tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a ƙarshe ta tsayar da idonta Kan Unaisah da Batul, daku zan fara, saboda yawan sumar kanku” saukowa su ka yi daga saman kujerun, ta juya ta nufi Corner din da Sink Yake, gefen shi beauty cabinet ne mai ɗauke da jerin shampoo da conditioner da suran mayukan gyaran gashi.

Taci baƙar wahala wurin gyara masu gashi, musamman mutun biyun nan Unaisah da Batul, saboda yawan gashinsu ga tsawo, da ruwan zafi ta jika sumar bayan ta jiƙu ta shafa shampoo ta cuccuɗa ko’ina na gashin, bayan ta wanke shampoo din ta sanya conditioner na tsawon mintuna kafin ta wanketa, tayi masu amfani da Hair dryer ta busar masu da sumar kansu, ta fara shafa masu smoothing serum ta ɗauki comb taci gaba da sharce gashin, tunkafin ta kammala take santin kyawun sumar kansu, bayan ta gama sharce gashin ta kwarara masu hair oils kala daban daban saman sumar taci gaba da cuɗasu da hannuwanta, tuni gashin ya ciza launin shi dark brown sai ƙyalli yake yi da ɗaukar ido, ƙamshin hair oils din data shafa masu Ya cika hancinansu.

Lokacin da suka kalli sumar kansu ta cikin madubi, Ihun farin ciki suka saki suna faman yi mata godiya tace su koma zu zauna, bata gama gyara masu ba, su Azeeza sunyi zuru suna jiran suma ayi masu, sai faman santin su Unaisah da Batul suke Yi har suna fadin suma kalar nasu za’ayi masu.

Ummi tayi ƙoƙari wurin gyara su, Yara kamar ƴa’ƴan wani shege maiji da raina, saida tayi amfani da almakashi ta datse sumar kansu ta rage tsayinta ta dawo dai dai tsakiyar bayansu, hair style din da tayima Batul da Unaisah Triple twist half up ne, Bayan ta gama dasu ta bi sauran ɗaya bayan ɗaya ta wanke masu sumar kansu kamar yadda tayi masu Unaisah haka suma tayi masu banbancin wurin hair style ne, saida ta miƙar masu da gashinsu ta hanyar yin amfani da Straightener, kafin ta ɗaure ma Azeeza da Jemimah gashinsu da ribbom guda biyu gefe da gefe wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗunsu.

Duk wannan gayun da akayi masu, Jemimah bata gode ba, ta sanya rigima akan sai an maida launin gashinta kalar nasu Batul, Ummi taci dariya, bata ta6a tsammanin zata ji ƙaunar yaran ba sai yau, su kansu sunyi mamakin yadda ta dage damtse wurin Yi masu hidima, Abu kamar wasa Jemimah ta fashe masu da kuka, ita damuwarta launin gashinsu Yafi nasu kyau, da ita da azeeza sumar kansu blonde ne kalar na turawa, ita Azeeza bata damu ba sai murna take yi an gyara mata gashi, jemimah daice ta matsa lamba, ummi harta fara tunanin ta canza mata launin gashin da yake suna da Hair dye cikin jerin Kayan gyaran gashin su, Unaisah ce tace abar mata launin gashin kanta, saboda yana dakyau ba lallaima idan aka maida mata kalar nasu yayi kyau ba,” daƙyar suka lallashi Jamimah tadaina yi masu kuka.

Tsawon lokaci kafin Ummi ta kammala Gyara su, hatta skin dinsu da akaifunsu da tafukan ƙafafuwansu duk saida ta gyara masu, ko’ina ka kalla na jikinsu saiya burgeka, kamar basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, tun bayan da aka gama kowannansu Ya koma bedroom dinshi, bacci mai nauyi ya dauke su, duk don saboda gyaran gashin da akayi masu kada Ya 6ace yasa suka kwanta ta rubda ciki.

*OBIE ESTATE*

Danƙara danƙara motocine masu numfashi suke ta kurɗaɗowa ta cikin babban gate din Obie Estate a ƙalla sunkai goma sha wani abu gaba da bayansu motocin fusatattun sojoji ne sun mimmiƙe tsaitsaye hannayensu ruƙe da manyan bindigu, jiniyar motocin jami’an ta karaɗe ko’ina na yankin, da matsakaicin gudu suka haura saman titin da zai sada da su da Airport, Motar farko zungureriya tana ɗauke da dattijon arziƙi tare da Dr.Jaz, mota ta biyu sanate president lateef ne zaune a mazaunin baya shi da Iyalansa Hajiya madina da ya’yan ta biyu Ziyad da zuhra, Mota ta uku Hajiya saratu ce a cikinta tare da twins zayn da zaid, da shi kanshi pravin din, Motar bayansu Sir mubarak ne tare da Hajiya Turai, daga motarsu sai ta sauran ƴan uwa da abokanan arziki da suka hallara domin zuwa tarban babban baƙonsu, kowan nan su yayi shiga ta alfarma, mazan cikinsu shaddojine ajikinsu, matan kuma wankan abaya suka ɗauka, har sun kusa isa Airport din ba zato ba tsammani suka soma hango wasu hamshaƙan motocin daban sun biyo ta titin da zai jagorance ka zuwa Aso Villa, Ƙarshen Haɗuwa ta glass din motocinsu suke hangen su, tunkafin suga su wanene acikin motocin ransu ya basu Mr.president ne tare da muƙarrabansa shima yazo tarban ɗan uwan nashi, abun yayi matuƙar ƙayatar dasu, basu yi tsammani zai halacci zuwa Airport din ba, zuwan bazata yai masu, Motocin shugaban ƙasa na ƙarasowa suka haɗe da nasu motocin Yawan adadin motocin suka ƙaru, hankalin kowannansu akwance yake sun ci burin haɗuwa da babban baƙon nasu, duk sun ƙagara su ƙarasa Airport din.

“Ziyad Ina fata baka faɗa ma Ƴan uwanka ƴan jarida ba ko”? Sanate lateef ne yai maganar a yayin da yake zaune gefen Hajiya madina a back seat na motarsu.

Ziyad na murmushi yace”ai daddy tuni na sanar dasu ku jura zuwansu kawai”
Buɗe baki sanate yai”amma dai wasa kake min ko? Kadai san Kawun naka bai san taron ƴan jarida,”

Ziyad na sakin murmushin shaƙiyanci ya zuge mashi glass din motarsu, har sai da gaban Senate yadan buga ganin motocin ƴan jarida birjik sai faman sharara gudu suke yi har sunfi nasu motocin sauri duk dan su ƙarasa su dauki rahoto.
Dafe kai Senate yai”ziyad kana da matsala, yanzu menene na gayyatar waɗannan mutanan ina amfanin yin hakan”?

Sai lokacin Hajiya madina ta sanya masu baki a maganarsu”ai indai ziyad ne dama ka daina damun kanka, ka riga da kasan halinshi, jikin shi har 6ari yake yi idan ya samu abun daukar rahoto”

Dariya ziyad yai jin abunda mommyn shi tace, shi dai senate lamarin ya ɗaure mashi kai.
Chapter 104 · 0% Book details