Sashe 20
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan fitar Layla kaitsaye ta nufi falon gidan, ranta ya 6aci sosai, kalaman Dr shureim sun sosa mata zuciyarta, yau kusan shekara uku da dawowarsu Nigeria tun bayan barin su Dubai, Layla taji takaicin faɗuwar Alhaji ubaid saboda tafi kowa ƙwallafa rai akan hawan shi mulkin shugaban ƙasa don ta ji daɗin yin sharholiyarta a matsayin first lady, sai dai Allah bai basu nasara ba, bugu ɗaya aka ƙundumo shi ƙasa, tun farko sai da ya ji fargabar tsayawa takarar jin wanda za su kara da shi, don kuwa yasan muddin Sharafudden Ya nemi takarar shugaban ƙasa zaiyi wuya ya iya kada shi, sanin farin jinin da Allah ya yi mashi, Mutun ne na jama’a mai kyautatawa al’umma.
“Hajiya..”muryar mai aikin gidan su ce a dabarbarce ta ambaci sunanta ganin yadda ta bi ta da matsiyacin kallo”lafiya”?
Cikin harshen larabci ta ce “Mun yi baƙi ko da ya ke sun wuce baƙi”
“Saboda ƙannan uwata ne”? Ta jefa mata tambayar, Sunnar da kai ƙasa zainab ta ɗan yi”Hajiya Aisha ce matar governor tare da....” bata kai ga ƙarasa maganar ba, layla ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu”ni ban gayyaci uban kowa ba a gidana, Matsiyatan banza gulmace ta kawo su wato an zo aga yadda na ƙare to ta Allah ba ta su ba ƴan kutmar uba, jajen ne har yanzu bai ƙara ba abu an kusa rabin shekara da faruwarshi saboda baƙin hali sunƙi su manta..” tun da ta fara sambatu zainab ta yi kasaƙe tana kallon fuskarta ba ki asake, ta fahimci zallar baƙin ciki ne Azuciyar uwar gidan ta ta, rashin nasarar su ya tsaya mata a zuciya nema ta ke ta zauce, dama ya lafiyar gwiwa mutun mai ƙarancin imani.
Tsawa layla ta daka mata, firgigit! zainab ta ɗan zabura”Ki je ki sanar da su cewa bana nan” muryarta na ɗan rawa tace”Ae an riga an faɗa masu cewa kina a cikin gidan, yanzu haka anyi masu iso suna acikin main palour...” daƙyar zainab ta ƙarasa maganar tana mai haɗiyar yawu ganin irin kallon da layla ta ke jefa mata tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa, guntun tsoki taja”masu aikin gidana sun fara raina ni saboda rashin nasarar mu dole na yi wani abu akai, su kuma waɗancan taron magulmatan zanje gare su, bari na fara zuwa ɗaki in zuba gwalagwalai na don kar su raina ni” acikin zuciyarta ta yi maganar tare da juyawa ta nufi sashen da ɗakinta Ya ke.
Binta da ido zainab ta yi haɗi da ɗan girgiza kanta”Allah ya shirye ki layla” har zata Juya idon ta ya sauka akan Dr shureim da ke shirin fitowa daga ɗakin shi hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, tsananin tausayin shi ne ya kamata ganin yadda ya canza, ta lura da damuwar da ke akan fuskarshi, a hankali yake tafiya yana tunkaro inda take ga dukkan alamu bai lura da ita ba har sai da ɗan yi mashi gyaran murya, tukunna ya ɗaura fararen idanuwanshi akanta, Sam babu walwala akan fuskarshi, darajar da ta ke da shi a idon shi yasa shi nufarta, ya ɗauki zainab taimkar auntynsa, Babbar macace mai hankali da natsuwa.
Yana ƙarasa gabanta ya duƙar da idon shi ƙasa ba tare da ya gaishe da ita ba
“Ko ba ka faɗamin ba dr shureim naga damuwa akan fuskarka, na ɗauke ka tamkar ɗan ciki na, dan Allah shureim ka da ka bari damuwa ta canza ka, inaso ka sani komai ya faru muƙaddari ne daga Allah, rubutacciyar ƙaddara ce wadda ba wanda ya isa ya canza ta” cikin kwantar da murya ta ke lallashinsa, sai faman karkaɗa car key ɗin hannunsa yake yi, tun da ta fara yi mashi nasiha bai tanka mata ba sai da ta kai aya tukunna ya soma magana a tsanake “Aunty zainab na aikata babban zunubin da har abada ni nasan Allah ba zai ta6a yafe min ba, Ni kaina nayi danasin mara amfani....” duk yadda yaso ya jure ya kasa kamar ƙaramin yaro cikin muryar kuka yaci gaba da cewa”Ina sonta aunty zainab sune silar komai, bazan ta6a yafe masu ba na tsane su, Mu kuma tamu jarabtar ta iyaye ce, basu damu da mu ba, buƙatar su itace agabansu, Yan zu haka da nake maki magana Mommy ce ta kore ni saboda na faɗa mata gaskiya, ki yi haƙuri Aunty zainab kada ki ce za ki dakatar dani ƙwara na tafi, zama atare dasu bai da amfani, zanje na nemo ƴar uwata Benazir In ruƙe ta a hannuna waɗannan mutanan ina zargin sune silar tarwatsewar rayuwarta kamar yadda su ka yi silar tarwatsewar tawa rayuwar......” yana magana hawaye na cigaba da wanke fuskarsa, ita kanta zainab ɗin tuni idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, ruƙo hannunshi tai a cikin nata, da sauri ya ɗaura kanshi saman kafaɗarta”Shureim Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wanda ya cuci wani Allah zai saka mashi, ko a tsakanin ƴa’ƴa da iyayen su akwai hisabi, Na yi maka alƙawarin zan taimaka maka akan komai, ashirye ni ke dana zama uwa agareka, Ae ɗa na kowa ne idan su basu so to ni inaso, dama ban ta6a haihuwa ba” jin abinda tace ne yasa shi ɗago da fuskarshi yana kallon ta, murmushi ya ƙaƙaro akan fuskarshi, haƙiƙa kalamanta sun sanyaya masa zuciyar shi.
“Aunty zaina are u serious zaki taimaka min”? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, farin cikine ya bayyana akan fuskarshi’Aunty zainab akwai wani aiki da nake so mu yi atare bana so kowa Ya sani....” bai kai ƙarshen maganar ba, Takun tafiyar Mahaifiyarshi Ya dakatar dashi, muryar zainab na rawa tace mashi
“Ka tafi kawai zan kira ka awaya anjima sai mu yi magana” amsa mata yai da toh, Da sauri Ya fuce ita kuma ta nufi hanyar kitchen.
Cikin takun izza ta ke tafiya, har ta canza kayan jikinta zuwa tsadadden leshi wuyanta da hannyenta Zinari ne, ta buga uban ɗaurin kallabin nan ture kaga tsiya, Takalman ƙafarta high hills ne, ta wanke jikinta da turare, tana tafiya tana hura hanci
Tana dab da zata shiga palourn gidan muryoyin manyan matan da suka kawo mata ziyara ta karaɗe kunnuwanta, da sauri ta la6e tana sauraron abunda su ke tattaunawa
“Ae ban ta6a ganin mutum mai haɗamar tsiya irin Alhaji ubaid ba, nifa tun lokacin da ya sauka mulki yana fama da ciwon ƙafa raina ya bani cewar wani munafuncin suka ƙulla ashe kujerar shugaban ƙasa yake so, yanzu gashi ba wan ba ƙanin duka sun rasa” 6a66akewa su ka yi da dariya
“Ni dama tun da naji Sharafudeen Ya tsaya takarar shugaban ƙasa raina ya bani cewar shi zaiyi nasara, sai gashi ta tabbata, wa zai Iya ja dasu? Ganganci ne ya kai Alhaji ubaid, Ko da ya ke matar shi ce mai haɗamar a yadda na fahimta” hajiyar da ta yi maganar ta ƙarasa tana dariya, wata ta ɗaura da cewa”ai ko sharafudeen bai tsaya takara ba kinsan Allah ba wanda zai za6i ubaid, Mutanan da basu son darajar ƴa’ƴan su ba taya zasu Iya ruƙe ƙasa irin nigeria mai cike da taron Talakawa? Ƴar ta fa benazir tana ƙasar ture, ayadda naji labari karuwanci take yi kuma ana zargin uwarce ta turata, Allah na tuba zato zunubi, duk da ni dai daga majiya mai ƙarfi naji ...”Hankalin layla idan yai duba toh ya tashi, tseguminta da suke yi yayi matuƙar gigitata, bata ta6a tunanin mutane zasu sanya masu ido game da rayuwarsu ba, haƙiƙa ranta ya 6aci, Ta yi niyar ta shiga tayi masu korar kare amma saita lallashi zuciyarta, Ta daidaita natsuwarta tare da yi masu sallama ta kutsa kai cikin katafaren palourn jin motsin shigowar ta ne yasa su ka yi saurin dakatawa da yin firar, ɗaya bayan ɗaya ta ke binsu da kallo, mata kenan abin a Jininsu ya ke.......
*UNCLE ABDALLAH*
A ƙalla yau wata ɗaya da dawowarsu Nigeria, sun fara sauka a adamawa state wurin dangin hajiya adama kafin dawowarsu gidansu da ke anan Jihar jos, zaune ta ke saman sofa mai mazaunin mutun uku, Jikinta na sanye da riga bubu ta material ta yafa mayafi akanta, Yayin da idonta ke asanye da farin glass, hutu yazauna mata ta ƙara ƙiba abunta.
Ta natsu tana kallon portrait artist ɗin dake zuƙunne agaban Drawing board Yana gudanar da aikinsa, daga ƙasa gefenshi Kayan zananshi ne, Hada hoton Angel da hajiya adama ta miƙa mashi don Ya zana mata Ita, tana son ganin yadda zata koma a shekarunta na yanzu don su samu sauƙin gane ta
“Ranki shi daɗe, Yarinyar zata kai shekara nawa Ayanzu”? Me zanan ne yai mata tambayar.
“I think 15 to 16 years,” amsa mata yai da okey, Kafin yaci gaba da aikin zanan shi,
“Mijina ya faɗa min cewa kai ƙwararre ne a 6angaren zana mutane, so please don’t disappoint me” murmushi mutumin ya saki ba tare daya juyo ya kalle ta ba ya furta mata”In sha Allah”
“Assalamu Alaikum”! Muryar Uncle abdallace ta janyo hankulansu ga dubanshi, Shigowarshi kenan Jikinshi na a sanye da shadda launin maroon, idan ka kalli fuskarshi Sak Uzair hatta duhun fatarsu iri ɗayane.
Cikin girmama mai zanan ya gaishe da uncle abdallah, Bayan ya amsa mashi da fara’a ya ɗago ya kalli Hajiya adama”mu shiga ciki ina son magana da ke” amsa mashi tai da toh, Yai gaba ta miƙe tabi bayanshi, A cikin bedroom ɗinsu su ka tsaya suna fuskantar Juna
“Tun ɗazu nake jiran shigowarka, Inataso muyi maganar zuwan mu abuja, almost one month da dawowarmu Nigeria banje naga jikana ba duk irin yadda na ƙwallafa raina akan son ganinshi, “
“Duk yadda kika kaiga ƙagara da son ganinshi ba ki kaini ba,”