← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 152

Sashe 103

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ya Allah ka jiƙan ƴan uwanmu da suka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah kakai rahama ƙabarinsu, Ya Allah kabamu ikon cinye jarabawarka, Ya Allah ka bamu haƙuri da juriyar rungumar duk wata ƙaddara da zata riske mu mai kyau ko mara kyau, Ya Allah ka tsare min sauran ƴan uwana da nake atare dasu da sauran al’ummar musulmai, ya Allah ka bamu nasara akan burinmu da muke son cimmawa na ganin mun kawo ƙarshen azzaluman mutanan da suka ƙasƙantar da rayuwarmu suka cutar damu Allah kada ka basu nasarar cigaba da aiwatar da zalunci..........” cikin shessheƙar kuka ta ƙare maganar, hawaye tuni sun wanke fuskarta tunawa da rayuwar sauran ƴan uwansu ƙananun yara da ake cutarwa a cikin kurkukun ƙaddara, tasan ba zasu fasa cin zarafinsu ba suna lalata rayuwarsu kamar yadda su ka yi silar mutuwar ƴar uwar su Unaiza ƴar gidan daddy da Majnoon yaran da ba suji ba basu gani ba.

Sautin kukan Unaisah ya karaɗe cikin ɗakin, batul ko motsi batayi ba, tunda ta kifa kanta saman darduma bacci mai dadine yai awon gaba da ita ko addu’a bata samu damar yi ba.

“Bazan ta6a mantawa da wasiƙar da kika bani ba, kuma bazan manta sunan mugun mahaifinki ba, In sha Allah zan ɗaukar maki fansa koda kuwa zan jefa rayuwata ne cikin haɗarin da zaiyi silar mutuwata ne.....” cikin karyayyar murya take furta kalaman masu ta6a zuciya, idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur, hawaye sun kwanta saman fatar fuskarta har zuwa gaban hijabin dake a jikinta.

“Ya Allah ka bayyana min daddyna idan yana araye, Inason nasake ganinshi shi kaɗaine nake da burin haɗuwa dashi a duniyar nan”

Tunda ta fara karanta addu’o’i, yana la6e bakin ƙofar dakinsu Yana sauraronta, basu jima da dawowa daga sallar asuba ba, ya rakosu Sajeed ne tuni sun nufi bedroom dinsu.

Zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta, abubuwa dayawa sun so su rikitar dashi, kamar yarda take zubar hawaye haka shima yake zubar da su saman fuskarshi, farar jallabiyace a jikin shi ya sanya mask akan fuskarshi, Ji yake kamar ya faɗa ɗakin Ya rungumota a jikinshi, duk a tunaninshi Unaisah ta manta dashi ashe ba haka bane yana aranta har addu’a tana yi mashi, haƙiƙa yayi farin ciki mara misaltuwa, cikin sanɗa Ya juya zaibar ƙofar ɗakinsu kwatsam muryar Jemimah ta tona mashi asiri da ƙarfi ta furta”BOSS MAN!!!” cak Ya dakata da tafiya, hatta Unaisah dake a ɗaki saida taji sautin sunanshi da jemaimah ta ambata, aiko da sauri ta miƙe ta nufi kofar fitowa daga ɗakin.

A hankali Ya waiwaya baya yana duban jemimah, tasha dogon hijabi ajikinta kamar zatayi tuntube da gudu ta nufo shi, Azeeza ma ta fito tabiyo bayanta itama hijabin ne a jikinta.

Kallon da yake binsu dashi tamkar kallon da uba yake yiwa ƴa’ƴanshi ne, saboda yana matuƙar ƙaunar yaran ya dauke su kamar jininsa, musamman yadda suka fara nuna mashi yarda, Jiya izuwa yau sun saki jiki dashi, duk in zai gifta sai sun ambaci sunanshi kamar su suka raɗa mashi.

Jemimah na ƙarasowa ya sanya hannu biyu ya ɗagata sama, ta kama tiƙar dariya tana fadin”dan Allah kada ka sauke ni ƙasa”

Fuskarshi dauke da murmushi yace”raini ya fara shiga tsakanina dake ko? Tun jiya badama kiga na gifta sai kin ƙwala min kira kamar wani tsaran wasanki, bakisan ni baba ba ne”?

Tace”to aini daɗin sunan nake ji, Boss man shiyasa nake kira,” tana magana yana kallon jajayen kumatunta bakomai yake tunawa ba face Angel ɗinsa, lokacin ƙuruciyarta yaci wuyarta yakuma ji dadin shiriritarta.

“Jemimah Ina fata yau kinyi sallah ta hankali, don jiya Azeeza ta faɗa min abun kunyar da kika yi” ya faɗa yana sauketa ƙasa, duban Azeeza yai har ya miƙa hannu zai ɗauke ta ganin ta tsare shi da ido yayi tunani ko itama so takeyi ya daga ta sama, da sauri ta maƙe mashi kafaɗa tana fadin”ai ni ba ƙarama bace, Na girmeta da shekaru” dariyace ta kubce ma Boss man.

“Oh saboda kin girmeta shine bakyaso in ɗauke ki? To aini a wurina jinjira nake kallonki” ya faɗa tare da ɗaukarta ya ruƙeta a hannunshi, Kunyar duniya ta cika Azeeza sai faman noƙe mashi kai take Yi.

“Kasan Allah Boss man itama Azeeza bata Iya sallaba, ko karatun sallah ma bata iyaba, idan nayi ƙarya kace ta maimaita maka Rabbighfir li” tuntsirewa yai da dariya.

Ran Azeeza ya 6aci tace”wallahi ƙarya take yi min, ai acikin zuciya nake yin karatun sallah tayaya har tasan abunda nake faɗi acikin zuciyata” gwalo jemimah tayi mata”oho dai, ni dai duk rashin Iya sallana nasan yadda ake karatun sallah”

Idanuwan Azeeza tuni sun cicciko da ƙwalla, boss man yace”badai kuka zakiyi min ba”? Cikin shessheƙar kuka tace”wallahi ƙarya take yi min na iya karatun sallah, kaji na rantse maka, idan ma kanaso sai in faɗa maka kaji, itace fa bata Iya komai ba, jiya muna sallar isha’i tana buga min dundu abayana, kuma ban rama ba”

Kwantar da kanta yai saman kafaɗar shi haɗi da daura hannun shi saman kanta Yana lallashinta.

Idanuwanshi akan jemimah dake ta dariya, dama tun jiya da yayi tozali da fuskarta ranshi ya bashi daƙyar in bata iya rashin ji ba, kamar dai Angel dinsa da tana ƙarama .

Lallashinta yai”yi hakuri my daughter, kuruciya ke damunta dama kince min kin girmeta don haka inaso ki ruƙe girmanki kada ki biye mata, idan tayi ba dai dai ba kiyi mata nasiha a matsayinki na babba mai hankali da tunani, in sha Allah wata rana zata daina ne” tunda ya fara magana Azeeza take amsa mashi da toh, jemimah kuwa sai faman ta6e mashi baki take yi hada ruƙe qugu, tana fadin”tab ita ɗin zata min nasiha, Allah ya kiyaye, ai ni bana jin maganar kowa idan bata Unaisa ba”

Mamaki jemimah take bashi gata ƴar ƙarama idan tana magana sai kayi tsammanin ta ɗare shekarunta.

Sauke Azeeza yai saman floor, yace da ita”ki ruke hannun ƴar uwarki ku tafi ɗaki, da anjima idan nashigo zamuyi magana” ta amsa mashi da toh nagode, kafin ta ruƙo hannun jemimah tuni ta watsa da gudu ta nufi hanyar komawa ɗakinsu duk don kada azeeza ta ruƙe hannunta.

Murmushi ya saki yayin da yake bin bayansu da kallo, Har ya ɗaga ƙafa zai nufi hanyar fita ɗakin, Muryar Unaisah ta dakatar dashi”Boss” A hankali ya juya baya yana dubanta tun ɗazu tana tsaye tana kallon su, sai da ta bari su Azeeza sun tafi tukunna ta yanke shawarar yi mashi magana.

Ta wanke hawayen fuskarta, tana tafiya hijabinta na ja da ƙasa, har gabanshi ta ƙarasa ta tsaya, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, ji yake kamar ya rungumeta koya rage radadin da yake ji acikin zuciyarshi, sai dai ba halin yin hakan yasan yadda take da masifa idan Ya kuskura yai hugging dinta tsaf zata mare shi tunda batasan wanene shi ba.

Ido cikin ido suke kallon juna, tsawon mintuna kafin ta numfasa tace”ina kwana? Ka tashi lafiya? ya fama da mu”
Cikin sanyin murya yace”lafiyalou Unaisah, ya akai naga idanuwanki sun canza launi, ko baki da lafiya ne”?

Girgiza mashi kai tai, cikin disasshiyar murya ta furta”lafiyata qalou, kasalar bacci ce,”

Jinjina kanshi ya ɗanyi, ji take kamar tace mashi ya cire face mask dinshi sai dai bata son ta takura mashi don ta fuskanci bayason su san wanene shi.

“Kin tsare ni da ido kina kallona ko akwai wani abu da kike son fada min ne”?

Murmushin gefen fuska ta saki, Har dimples dinta suka lotsa,

“Dan Allah taimako nakeso kayi min sai dai bani da ko sisi a hannuna”
“Kada kiji komai ki faɗi koma menene zanyi maki shi in sha Allah”

Tana faman noƙe kai tace”um dama waya ce da Aunty laura ta bani kyauta ɗaya daga cikin likitocin da suka kula da lafiyarmu a america, to wayar babu sim aciki gashi inason in fara amfani da ita”

ta faɗa tana duban fuskarshi, ya natsu yana sauraronta idan tana magana kuruciyarta yake tunawa, yarinyar data sanya shi ciwon kai da zazza6i, cikin ikon Allah yanzu ta ƙara girma ta zama kamilar mace ta mallakin hankalinta.

“Sim kaɗai kike buƙata”? Girgiza mashi kai tayi”a’a, da Allah kada kace na takura maka, “ aranshi ya ayyana takura kuma ta nawa My Angel, nida nayi jinya gadon asibiti saboda ke”

“Cikin Kayan da aka tsunto mu da su a daji, akwai backpack ɗina inason jakar, gadonmu ce bansani ba ko sojoji sun haɗo mana da su” ta tambaya tana dubanshi.

“Duk wani abu naku yana atare damu, saboda muna buƙatar abubuwan da zasu taimaka mana wurin yin bincike tamkar shaidune agare mu, amma kada ki damu zan ɗauko maki backpack din, da anjima zan shigo maki da ita tare da sim din da zaki sama wayar” wani irin farin cikine Ya lullu6e Unaisah, godiya tadinga yi mashi, yace mata yaji daɗin ganin farin cikinta, juyawa tayi da niyar ta koma ɗaki, hijab din jikinta dake jan ƙasa ta harɗe ƙasan takalmin ƙafarta, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da zafin nama Boss man Ya ruƙo damtse hannunta Ya janyota ta faɗa saman kirjinsa, har saida taji gabanta ya fadi, ƙanƙameta yayi da hannayensa biyu daya zagayo dasu ta bayanta, Jikinta yai wani irin sanyi kamar wadda aka zare ma laka, bawan Allah tunda ya rungumeta yai tighting dinta kamar karya saketa, ita kanta takasa raba jikinta daga nashi, saima hannayenta data zagayo dasu saman bayanshi, ta ƙankameshi, Jini ɗaya ba wasa ba, sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi at same time, batasan ya akai ba ta tsinci kanta da jin hawaye sun cicciko idonta, shi kuwa tuni sun wanke face mask dinshi.A hankali yake ɗan bubbuga bayanta kamar yana lallashinta, tsawon shekaru rabon daya ji ɗumin jikinta anashi, bazai ta6a manta ƙaddarar data afka masu ba, wadda tayi silar rabuwarsu, bazai ta6a manta sautin shesshekar kukanta da muryarta a lokacin da yake gudu dasu cikin mota tana daddy hancina jini, haka zalika bazai ta6a manta lokacin da ya jefar da ita cikin ruwa ba duk don ya ceci rayuwarta Sai gashi cikin ikon Allah ta rayu Allah ya tsare mashi ita, Allah kaɗai yasan irin wahalhalun rayuwan data fuskanta da ƙananun shekarunta.....
Chapter 103 · 0% Book details