← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 152

Sashe 6

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ya Allah saida nayi addu’a kafin in fito but why na fara Cin karo da mummunar tsohuwar nan Ina lillahi.....” acikin zuciyarta ta ambaci hakan, Kafin ta yi wani yunƙuri tsohuwa Zafreen ta soma tunkarota sautin takalmanta ƙwas ƙwas har cikin dodon kunnan Angel, Duk ta ku ɗaya idan ta yi sai gaban Angel Ya faɗi, tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba.

Ko da ta ƙaraso gabanta, Bata tanka mata ba, Sai bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo irin na marasa imani, Shuɗayen idanuwanta sun Ciza launinsu.

“Ban yi mamakin Ganin ki ba Unaisah! Ina ji arai na ba yau ba ne rana ta farko da kika fara ƙetare Iyakar Ki, Taurin kan ki da kafiyar ki da kuma rashin tsoron ki su ne suka ƙarfafa maki gwiwar shigowa Cikin prison! Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoner ɗin da ya ta6a ƙetare Iyakar shi ba sai Akan Ki”!

Magana ta ke yi muryarta na fita da sauti mai amo.

yawu Angel ta haɗiya, tuni tasha Jinin jikinta, Ido ya raina fata sam ta kasa magana, Zufa sai tsastsafo mata ta ke yi kan fuskarta har ɗiɗɗiga ta ke a ƙasa.

“Ko za ki Iya faɗa min menene Ya fito da ke? Kuma Ta yaya akai Kika tsaga bangon ɗakin ku kika fito”? Muryar Angel na rawa ta soma magana”Tsautsayi ne da ƙaddara, dan Allah kada ki cutar dani, Zan koma inda na fito, Kawai Inason ganin ɗan uwana Danish ne shiyasa na fito neman shi.....” kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon sautin Dariyar tsohuwa zafreen da ya tari numfashinta.

Tsagaitawa ta yi da yin dariyar, ta soma matsawa tana ƙara kusanta kanta da Angel, A tsananin tsoroce Angel ta ke Ja da baya tana girgiza mata kai

“Tun jiya dana shigo ɗakin ku Raina ya bani cewar Wani abun ku ke shiryawa kuma ke ce jagora a cikin tafiyar, Saboda prisoners basu da wayan da zasu Iya ta6uka wani abu, Unaisah ke ce ƙwarin gwiwar su, Babban kuskuran da ki ka aikata shi ne ƙetare Iyakarki! Hakan Ya sa6awa dokar Kurkuku! Na yi imanin babu mai Iya ƙwatarki daga hannu na! Saina rushe duk wani sashe na Jikin Ki da ke da ƙarfi zuwa mai rauni......” Zazzare ido Angel ta yi tamkar ƙwayar zata faɗo ƙasa Jikinta sai kerma ya ke yi.

“Kin jama kan ki bala’i da masifa! Not only u! Hatta Ƴan uwan ki da Ki ka baro ɗaki, suna cikin masifa, Zanje gare su Bayan na gama da ke, duk saina tarwatsa farin Cikin da ku ke da shi” Muryarta a kausashe ta ke furta maganar.

Hawayen da su ka taru a cikin idonta ne suka soma gangarowa saman kuncinta da wani irin rauni na murya ta furta”duk horon da za ki yi mani kada ki haɗa da ƴan uwana, Ni ce mai laifi don haka Ni za ki hukunta”

Fuskar Tsohuwa Zafreen a murtuke ta jinjina kai tare da cewa “Umarni ki ke Bani? In yi abunda kike so”? A ruɗe Angel ta girgiza kai ba tare da ta iya furta mata komai ba.

“Zan jaraba Ki inga idan zaki Iya ceton Kanki, Nasan baki ta6a shaƙar ƙamshin mutuwa ba amma yau zansa ki shaƙeta sosai, waɗannan Idanuwan naki launin ruwan toka yau zansa su koma launin Ja, Hawayen da ke fito wa ta cikinsu zansa su janza launi zuwa na Jini, La66an ki da su ka saba gaya wa Mutane magana Ayau ɗin nan zan canza masu kamannin.....” Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi tarasa gane inda kalaman tsohuwa Zafreen suka dosa.

Ja da baya tsohuwa zafreen ta soma Yi yayin da ta ke sakin Shu’umin Murmushin nan nata na tantiran Ƴan duniya waɗanda su ka ga jiya su ka ga yau

Juyawa Baya ta yi tare da nuna ma Angel Third floor da sandar hannunta

“Ɗan Uwan ki da ki ke nema Yana a hawa Na Uku, Za ki Iya zuwa gare shi, Fatan Nasara” Kalmar ƙarshe da ta furta mata kafin Ta buga sandar hannunta ƙasa, Nan ta ke hayaki Mai kamar an watsa tiya gas Ya cika idanuwan Angel, bata Iya ganin komai amma taji aranta cewa tsohuwa Zafreen ta 6ace daga wurin da ta ke a tsaye, a hanzarce ta kamo sunan Allah taci gaba da ambaton duk wata addu’a da tazo bakinta, Cikin ƙankanin lokaci ƙurar ta washe Idanuwan ta suka dawo dai dai. A lokacin ta riga ta yanke shawarar komawa ɗakin su gurin ƴan uwanta saboda gudun kada tsohuwa zafreen ta cutar mata dasu kamar yarda ta furta mata cewa zata je gare su, A hautsine Ta juya da niyar tabi hanyar da ta 6ullo don ta koma ɗakin su, Rass gaban yai mugun faɗuwa ganin babu corridor ɗin kwata kwata kamar ba’a ta6a yinta ba, Yawu ta haɗiya zuciyarta na harbawa da sauri da sauri tamkar zata faso ƙirjin ta.

A fujajen ta mayar da dubanta ga dogayen benayen da tsohuwa Zafreen ta faɗa mata cewa ɗan uwanta na anan A hankali ta ke tafiya tana tunkarar benan Yayin da ta ke cigaba da karanta addu’o’in neman tsari a cikin bakinta, firgita ta yi sakamakon Jin sautin shessheƙar kukan Su Azeeza a cikin kunnanta, ta ko’ina sautin kukansu ne kamar zasu zautar da ita, Tunawa da barazanar da aka yi mata acan lokaci na farko data ta6a shigowa prison yasa ta yardarwa kanta cewa ba kukan su bane Anayi ne don a tsoratar da ita, hakan yasa ta samu ƙwarin gwiwa, Watsawa ta yi da gudu ta Haura saman benan Har ta yi tsakiyarshi Taji ya soma motsawa Matakalarshi ta dinga komar da ita baya kamar dai yadda ya faru a jiya, Gudu ta dinga yi tana haurawa, wata uwar zufa ta wanke fuskarta, daƙyar ta samu ta haye saman Second floor.

Numfashi taja tare da fetsar dashi, sai faman yin haki ta ke yi, Tsawon mintuna takwas kafin taci gaba da tafiya tana bin hanyar, wani abu daya ƙara rikitar da ita, Ginin wurin ya dinga canza mata hanyar da take bi, Sai ta yi nisa taga an dawo da ita Baya, hakan ba ƙaramin gigitar da ita yayi ba. Tarasa ina zata dosa, Tamance ma hanyar da zata bi ta isar da ita hawa na Uku, tana Cikin yin tafiyar kamar zautacciya ita kanta batasan inda ta ke jefa ƙafafuwanta ba, Cikin rashin sa’a ta faɗo cikin wani ɗaki.

Idanuwanta basu sauka a ko’ina ba sai akan wasu tsoffin mata da ke agaban manyan tukwanan girki, An ɗaura su saman murhu Wuta sai Ci ta ke, Hannuwansu ruƙe da ludayi Suna Juya naman da ke a cikin Tukunyar girkinsu, Gabanta ne ya faɗi ganin Naman mutun yatsun hannun da ta gani ne cikin romar miyarsu ya tabbata mata da cewa Naman mutunne su ke yi. farfe sun shi.

Basu lura da ita ba sai da ta daddage ta kwatsa ƙara Mai sautin gaske silar hakan Ya janyo hankulansu ga kallonta, zaro ido waje ta yi ganin sun ganta, a kiɗime ta manne ma bango ɗakin, jikinta sae kerma ya ke yi Tamkar a mafar ki ta ke kallon su.

Halittarsu gwanin ban tsoro Munanan gaske, ga Uban tamoji tamojin akan fatar fuskokin su, kamar jijiyoyin jikin bishiya ƴan rigunan da ke sanye a jikin su launin Ja Kamar yar shara ta maza da su ke sanyawa, Ga uban gashi a hammatocinsu sai ɗoyi suke Yi. a ƙalla sun kai su Shida, uban fason da ke a tafin ƙafafuwan su kamar Kwanannar Fura da ta bushe ta tsastsage.

Kamar mahaukata haka suka fashe da dariya mai sautin gaske Muryoyinsu ne suka Cika mata kannuwanta.

“Laah ga Unaiserh Ta kawo mana ziyara, yau zata sha farfesun Ƴan Ci ki, Zonan Unaisah Yarinyar mu, Zo ki sha roman nama”

La66anta na kerma ta furta”Bazanci ba, Ni ba wurin ku nazo ba, Dan Allah Ku ƙyale ni In tafi....” Tun kan ta ƙarasa maganar ɗa ya daga Cikin tsoffin ta ɗebo farfesun a cikin ludayi hada Yatsun hannun mutun, tunkaro Angel ta yi tare da miƙa mata Ludayi” Kar6i nan ƴata ki sha Roman Farfesun Mutun akwai daɗi” Tashin zuciya ne ya farma mata, a matuƙar firgice ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai kash ƙofar ta ƙi buɗuwa.

Fashewa ta yi da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, da hannu ta dinga Bugun ƙofar kamar zata 6alle ta ko motsi ƙofar ba ta yi ba har sai da tsoffin nan suka cimmata, Ta ƙarfi Suka zaunar da ita tare da rurruƙe mata hannayenta da ƙafafuwanta ta yadda ba za ta Iya ƙwatar kanta ba. Tsohuwar da ke a ruƙe da Ludayin ce ta zuƙunna agabanta tare da tsoma hannayenta masu zaƙo zaƙon akaifa ta ɗebo Ƴan hanjin Cikin sai tiri suke Yi, runtse ido Angel ta yi sosai ta guntse bakinta zucuyarta na tashi kamar zata yi hauka, Bata ta6a ganin masifa ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗa ta da tsoffin nan, Duk yadda tazo ta kufce masu abun ya faskara kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, Ta ƙarfi suka 6are bakinta har saida gefe ya dinga fitar da jini, baiwar Allah taji raɗaɗin azaba, duk ta ciccije la66anta da tsiya su ka dunga tura mata ƴan hanjin abakinta, don dole ta dinga haɗiyarshi da zafinshi harshenta duk ya sale haka la66anta ma sun yi suntum.

Kamar zautacciya haka tsoffin nan su ka maida ta, Sai da su ka gama azabartar da ita kafin suka saketa Anan ƙasa ta shiga kwarara amai suna kallonta suna dariya, kaf saida ta amayar da ƴan hanjin da su ka bata, wani azababben ciwon kai ya farmata, Ga jiri da ta ke gani acikin idanuwanta

“Lami ba ta ƙoshi da farfesun ba, A ƙaro mata wani” maganar su taji a cikin kunnanta, a galabai ce ta miƙe jiki ba ƙwari ta dinga bugun ƙofar ɗakin har sai da ta samu daƙyar ta buɗe ta, gudu ta ke yi jini na wanke rigar Jikinta saboda bakinta da suka sanya ƙarfi wurin 6are shi gefe ya tsage bleeding ya ke kamar jinin jikinta zai ƙare.
Chapter 6 · 0% Book details