Sashe 102
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tunda tayi wanka ta canza kayan jikinta zuwa rigar shan iska bata ƙara saukowa daga saman gado ba, ta tsare hajiya layla da tambayoyi
“Mommy shifa yaya shureim ko baya kasar ne”?
“Yana agidan uncle dinki”
“Baku faɗa mashi na dawo ba ne?
“Mun faɗa masa tun jiya da daddare shima yayi farin ciki hada kukanshi, yace ma yau zaizo saboda ke’ murmushi tasaki”naji dadi Allah ya kawo shi lafiya, nayi missing din yayana”
Hajiya layla ta amsa mata da ameen.
Kafin benazir ta ƙara furta wani abu, Alhaji ubaid ya shigo da sallama abakinshi, atare suka ɗago suna kallon shi, da sauri benazir ta miƙe zaune tana ambaton sunanshi
Murmushin yasakar mata kafin ya zauna daga gefen gadon yana dubansu yace”Bansan meya faru ba, Ina ta kiran layin shureim dana musa babu wanda ya ɗaga acikinsu, Har laurat na jaraba kira itama bata ɗaga ba” kafin wani ya furta magana acikin su ba zato ba tsammani, sautin ringing din wayarshi ya daki kunnuwansu, hajiya layla tace”wata’ƙil wani daga cikin su ne yake kiranki” da sauri ya ciro wayar daga aljihun shi ya duba sunan me kira, murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi
“Wanene”? Layla ce ta tambaya ganin yadda ya saki fuska
“Musa ne Ke kira” ya faɗa tare da picking call din Ya kara a kunnan shi
Saboda ji da kai na Alhaji musa sai da Ubaid Ya fara yi mashi sallama tukunna ya amsa mashi da cewa”wa’alaikum salam, ina kwana yayana fatan kun wayi gari lafiya”
Alhaji ubaid na faman washe baki yace”lafiyalou, ya iyalin naka”?
“Suna lafiya” atakaice ya amsa mashi, tun da ubaid ya fara waya, layla da benazir suka zuba mashi ido suna kallon shi duk da basa Iya jin me alhaji musa yake fadi
“Shureim bai faɗa maka zancen dawowar benazir ba”? Ya tambaya ne don yaji baya da niyar yi mashi maganar
Da gadara Ya furta”ya faɗa min, tun ɗazu da safe, na tayamu murna, Ina fata tana lafiya”
Alhaji ubaid yace ai gatanan ma zaune kusa dani, Ko in bata wayar kuyi magana ne”?
Da sauri yace”No need, basai munyi magana da ita a waya ba, dama dalilin da yasa na kira naga missed call dinka ne, ɗazu da safe shureim ya shirya zai taho nan jos, Ni na hana shi, nace mashi ya bari zanyi maka magana kuzo nan abujan gidana” da mamaki Alhaji ubaid yace”amma dai wasa kake yi min ko? Tayaya zakace min in kwaso iyalina inzo gidan ka? Ni dakai waye ya dace yazo gidan wani? ai nayi tunanin idan na fada maka dawowar benazir jiki na rawa zaka kwaso iyalinka kuzo nan domin tayani murna sai kuma naji akasin hakan”
Alhaji musa yace”bazan Iya zuwa jos din bane, saboda Ina da ayyuka dayawa da zanyi, shiyasa nace kuzo nan ɗin,”
Mamaki da al’ajabi ne akan fuskar hajiya layla, don taji martanin da alhaji ubaid Ya bashi.
“Baikamata kace min haka ba, yanzu ayyukanka har sunfi ganin ƴata da za ka yi muhimmanci?
Babu alamun damuwa a muryarshi yace”yaya kasan banason jan magana, meye aciki don nace kazo gida na? Laifine? Alfarma nake nema bawani abuba, idan ba zaka yi min ba zan aje waya”
Gyaɗa kai alhaji ubaid yai”shikenan, zamu fidda lokaci mu shigo abujan”
Ya amsa da yawwa, sannan bana buƙatar ku zo a mota, Ni zan shirya maku komai na tafiyarku” amsa mashi yai da toh, daga haka Alhaji ubaid yayi rejecting call din, yana mai mamakin Halin Alhaji musa.
“Me ku ka tattauna ne”? Layla ce ta jefa mashi tambaya
Muryarshi a raunace ya furta”yace bazai samu damar zuwa nan ba, shine ma ya hana shureim zuwa saboda yafi son muje can gidan shi”
Ta6e baki hajiya layla tayi”shine kai kuma sai ka ce mashi zamu samu lokaci muje can din ko?
Jinjina mata kai yai alamar eh, masifa ta soma zazzaga mashi”kasan Allah babu inda zamuje sai dai kai daya gama asirce ka kama hanya ka tafi,Ni ban ta6a ganin mutun mara kunya irin shi ba, yarinyar ta 6ace tsawon shakaru sai jiya tsakar dare ƙarfe shabiyu tadawo bata ahayyacinta shine zaice mu kwasa mu tafi gidansa saboda muke son yaganta? Kwata kwata bashi da tunani kuma baida hankali, kaida kakeyi mashi biyayya gayanan shi bai damu da ƴarka ba,
...” tun da tafara faɗa, jikin benazir yai sanyi duk sai taji ba daɗi, Cikin sanyin murya tace”mommy dan Allah ki yi haƙuri, kada hakan ya dame ki, Ni banga laifin shi ba saboda ai ni na gudu da kaina ba korata akayi ba, wata’kil Yana jin haushin abunda na aikata shiyasa yace muje can....”
Katseta hajiya layla tayi”benazir ba abunda kike tunani bane, mutumin nan baya ƙaunarki, saboda bai damu dake ba, tun lokacin da kika 6ace bai ta6a magana akanki ba, Mune kaɗai muka damu dake munyi nemanki har mungaji mun fidda rai da kina araye, amma musa bai ta6a sanya baki akan maganar 6atanki balle har ya taimaka wurin bada gudummuwar mu nemo ki.....” Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mata maganarta”kidaina faɗa mata wannan maganar, bai dace ba, taya zakice kawunta ƙanin mahaifinta bai sonta? Akan wani dalili? Shiya furta maki da bakin shi”
Harara layla ta watsa mashi”alama nagani shiyasa nace haka”
Idanuwan benazir ne suka cicciko tab da ƙwalla, cikin sanyin murya tace”Ni ban damu ba, koda ace baya sona, tun da Iyayena suna sona Alhamdulillah, soyayyarku kaɗai ta ishe ni sai kuma ta mijina da ƴata, da kuma Yayana, sannan Ni na amince zanje abujan bawai don saboda shi ba, saboda inason ganin Aneelerh”
Girgiza kai layla tayi”bafa zan ta6a bari ki je gidan mutumin nan ba, Saboda Ni ban yarda da shi ba, Idan kuma kika takura akan kinason zuwan bazan hanaki ba sai dai ki sani bazan biku ba” babu alamun wasa akan fuskarta tayi maganar.
Magiya benazir ta dinga yi mata akan ta amince suje da ita, don ita batason suyi nesa da juna, daƙyar layla ta amince zata bisu abujan, da wata manufa a ƙasan zuciyarta don taci alwashin idan sukaje gidan Alhaji musa saita fada mashi baƙaƙen maganganun da zasu hana shi sukuni, yanzu dai sun tsaida magana zuwa jibi zasu yi tafiyar.
Aranar shureim ya samu damar kiran Alhaji ubaid ya fada mashi uzirin daya hana shi ɗaga kiran shi, bayan sun gama magana, har benazir yace abata waya su gaisa, sun jima suna waya da ita kusan awanni suka kwashe, kafin daga bisani yayi masu sallama.
Idan muka koma 6angaren zahra tun bayan da ta koma gida, babu mutunci a tsakaninta da Aneelerh ko gaisuwar arziki bata haɗa su, ta canza mata bata sakar mata fuska ba kamar yarda suke ada ba, aranar mahboob yai mata maganar motar ta da wayarta yace dama jingina yabada su, idan tana so zata bada kuɗin adawo mata dasu, farin ciki kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha dama bada Son ranta ta bada su ba, ta haɗa mashi kudin ta bashi, a daren ranar ya dawo mata da su, tuni ta fara amfani da wayarta bayan ta mayar da sim dinta.
A washe garin ranar laraba suka fara shirye shiryen fara aiki a Obie estate tare da sauran Interior designers dake aiki a ƙarƙashin company dinsu, tuni kaya sun iso daga dubai, Hankalin zahra ya kwanta bata da sauran damuwa yanzu, ta ƙagara gobe tayi don suje su fara gudanar da aikinsu saboda gagarumin taro ne zasuyi idan obie zai yi birthday kamar shagalin biki saboda dukiyar da suke kashewa wurin ƙawata gidan, shiyasa zasu fara yi masu aiki tun alhamis kafin Juma’a da za’a gudanar da shagalin
❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤
❤ANEELERH❤
A zaune take saman mirror chair, bata jima da fitowa daga wanka ba, ta zauna ne domin gyara jikinta, ƴar rigar wanka ce a jikinta, ta kasa ta6uka komai hannunta na a ruƙe da wayarta layin hajiya adama take dannawa kira, phone din na fara ringing taji sanyi ya ratsa zuciyarta, bayan hajiya adama tai picking call din Aneelerh ta yi mata sallama, on the other hand muryar Hajiya adama ta bayyana da alamun kasalar bacci”wa’alaikum salam daugher in-low, ya ki ke ya gidan yasu mami da ummi”
Da fara akan fuskar Aneelerh tace”Lafiya lou mommy, yasu daddy fatan duk kuna lafiya”
“Alhamdulillah Aneelerh, halan kin ji ni shiru yau ban neme ki ba shiyasa kika kira”
Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace”haka ne dama nakira ne don mu gaisa” da zolaya Hajiya adama tace”kodai kin kira ne don ki faɗa min jibi zaki zo ɗaukar baby junaid tun da time ya cika”
Ƙumshe dariya Aneelerh tayi kamar tana agabanta sai faman noƙe kai take yi, jin tayi shiru yasa Hajiya adama cewa”dama nasan ba zaki faɗamin ba, to ki kwantar da hankalinki, in sha Allah friday zanzo dashi gidan naku”
Abeelerh taji dadin maganarta”nagode mommy, Allah yakaimu lafiya.
“Nima ngde ki kulamin da kanki, ki kuma gaishe min da su mami, junaid din bacci yake yi zuwa anjima idan ya farka zan kira ki video call ku gaisa, dama yanata sambatu yana ambon shi wurin mommy zaije”
Murmushi Aneelerh tadan saki kamar tana agabanta”zasuji nima agaishe da daddy, “ daga nan suka yi sallama da juna.
❤A washe garin ranar Alhamis❤
Wuraren sallar Asuba Unaisah tana zaune saman darduma ta zumbula hijabi, Batul tana akwance agefenta saman dardumar, tun jiya da suka fara sallah da zarar sun gama sai ta kwanta wahala take ji idan tana yin sallah hada ƙarin rashin sabo har ƙwara ita akan su azeeza masu yin kalle kalle in suna yin sallah, mazan cikinsu sunfi natsuwa shi kanshi Boss man yayi mamakin yadda suka Iya sallah da karatunta ya ƙara jinjinama Unaisah akan ƙoƙarinta, yanzu karatun addinine zasu ƙara koya masu dana boko kafin asanyasu makaranta bayan kammala bincike akansu.
Tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tanayin addu’a muryarta abuɗe take fadin