Sashe 16
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Agogon bangon da ke a ɗakin ta kalla ƙarfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga ƙwayar idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta ɗanyi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tace”Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje” da zolaya ta yi maganar a yayin da take ƙarasa shigewa Cikin bedroom ɗin, Cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, ɗaukar shi ta yi saboda mugunta ta ƙure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke ƙara nannaɗe kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yunƙurin buɗe ido da sauri Zahra ta rage sanyin a.c ta ajiye remove ɗin saman drawer, ta ruƙe qugu tana binta da kallo.
Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse, Tunkan ta buɗe ido ta soma surfa masifa tana faɗin”junaid bana hana ka ƙara min sanyin a.c ba? Saboda ka raina min wayau ko?wlh idan ka bari na damƙi hannun ka sai ka gane ba ka da wayau, Sullu6iyo kawai......” Bata ƙarasa maganar ba ta soma Jin sautin dariyar Zahra, hakan yasa ta yi saurin ware idanuwanta tare da wurga su kan fuskarta.
Gwalo ta yi mata tare da ɗaga mata gira tace”Ba junaid bane yayar shi ce mai irin halin shi, “ Harara Aneelerh ta shiga watsa mata kamar ƙwayar idon zata faɗo kasa.
Zahra tana dariya tace”Iya hararar ne kawai idan mutun ya isa ya sanya hannu ya dake ni, kai da ka zo baƙunta gidan mutane ka ishe su da baccin lalaci.....” bata samu damar ƙarasa maganarta ba, Aneelerh ta rarumi pillow a zafafe da duro daga saman gadonta, zaro ido zahra ta yi kafin ta juya da gudu ta nufi ƙofa cikin rashin sa’a ƙafarta ta jirkice ta fasa ƙara zata kife ƙasa da sauri Aneelerh ta janyota zuwa jikinta, sosai ta ƙanƙameta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi ta firgita sosai.
“Rasa kunya 6eran tanka, Yanzu ga ki a hannuna, mai ƙwatarki yau sai Allah” Kokoyi su ka soma Yi kamar ƙananun yara, Zahra sai ƙwalawa Umminta kira ta ke yi tana faɗin tazo ta cece ta daga hannun Aunty aneelerh zata kashe mata ƴarta, Aneeleh na dariya tace”Nima ai ina da uwar sai in kirata tazo taga idon mara kunya” ta ambaci hakan tare da ƙwalawa Maminta kira.
Sun shaƙe junansu sai nishi su ke yi gyalen Zahta tuni ya jima da zamewa saman tiles, gashin kanta baƙi wulik anyi mata kitson kalaba ya sauko har kafaɗarta.
“Aunty Aneelerh Am sorry wlh na miƙa wuya, zan maki biyayya na tufa bazan ƙara ba” Azabar zafin da taji ne yasa ta furta mata hakan donta ƙyale ta.
Sakinta Aneelerh ta yi don itama ta gaji da kokawar Sai haki ta ke yi, A nan ƙasa suka zauna saman floor suna kallon juna.
“Ɗauko mun ruwa mai sanyi in sha” harara zahra ta ɗan jefa mata”Baki da hannu ne”? Zaro ido Aneelerh ta yi tare da cewa”bugun da nayi maki bai ishe ki ba” Jin haka yasa zahra yin saurin miƙewa hannunta ɗaya dafe da qugunta, Binta da kallo Aneelerh tayi fuskarta ɗauke da murmushi fucewa tayi daga Cikin ɗakin, after some minutes ta dawo hannunta ɗauke da glass ɗin ruwa me sanyi, ta miƙa ma Aneelerh hannu tasa ta kar6a tare da kafa ruwan abakinta Kur6a uku tayi mashi ya ƙare, Janye shi tayi daga bakinta tadan kalli zahra da ke tsaye tana gatsina mata hanci.
“Ki gama yi mini rashin kunyar ina nan ina jiran ki, in dai ni ce za ki zo roƙona in faɗa maki ƙiyamil lailin da za ki yi don ki mallaki Zuciyar matashin saurayin nan da ki ka ƙwallafa rai akan shi, meye ma sunan shi? tai tambayar tana kallon Zahra, Dariya ta saki tare da kai hannu ta kar6i glass cup din hannun aneelerh, Cikin kwarkwasa ta Juya ta nufi ƙofar fita daga ɗakin tana faɗin”Heart beat of Obinna” Murmushi Aneelerh tasaki tare da cewa”Ehem shi nake nufi, zakiyi bayani ne” bayan fitar zahra miƙewa Aneelerh ta yi tare da juyawa har ta kusa shiga toilet Muryar zahra ta katse ta”Bafa tafiya nayi ba, taimakon nan dai da aka saba aunty Aneelerh, “ Juyawa aneelerh ta yi tare da kallonta, Fuskarta ɗauke da murmushi.
Harara ta jefa mata”ƴar wahala wanka zan shiga idan na fito zamu tattauna” Zahra tace”idan ma shekara za ki yi zan zauna in jira ki” ta6e mata baki Aneelerh ta yi a yayin da ta ke shigewa cikin toilet taja ƙofa ta datse.
Daga gefen gadonta Zahra ta zauna tana jiran fitowarta, almost 15 mins Aneelerh ta buɗe ƙofar toilet ta fito jikinta sanye da rigar wanka fara ƙyal, ganin yadda zahra ta tsare ta da ido yasa ta murguɗa mata baki “Tubarkallah” Dariya Zahra ta sa ki kafin ta tsagaita da yin dariyar tace”Masha Allah Iyayen mu sun Iya haihuwa” girgiza kai Aneelerh ta ɗanyi”Allah ya shiryeki Zahra, Yanzu dai ta shi ki fuce zan sanya sutura, Ki jira Ni a palour “ maƙe mata kafaɗa zarah tayi”Nifa ba ƙaramar yarinya bace da zaki kore ni, Menene aciki don kin sanya kaya agabana, sai kace wani gardin ƙato Nima fa macace kamar ke komai ki ke dashi ina da.....” Kafin ta ƙarasa maganar Aneelerh ta nufeta da gudu Zarah ta bar Cikin ɗakin tana dariya.
Kaitsaye ta nufi Cikin Hadadden palourn gidan mai girman gaske. Tun kan ta ƙarasa ta hango mami da ummi zaune saman sofa suna fira, kowaccen su na sanye da atampha riga da zane ba ƙaramin kyau su ka yi ba.
“Gani nan tafe” kamar daga sama suka ji miryarta.
Atare suka ɗago suna kallonta, mami tace”yaushe kika dawo gidan”?
“Ban jima da shigowa ba, Na shiga ɗakin Aunty Aneelerh ne, Na same ta kwance Tana bacci,” Tai maganar a yayin da ta ke zama saman sofa mai mazaunin mutun ɗaya.
“Nasan kin kwaso gajiya, Tun asuba sai yanzu aka kammala aikin decoration ɗin, Kin ci abinci kuwa”? cikin Kulawa mami ta yi mata maganar, Fuskarta ɗauke da murmushi tace”mun aikatu Mami, Uban aiki kamar zamu shekara muna Yi, kinsan hidima idan akace maki ta Hamshaƙan attajiran masu kuɗine komai dagaske ake yin shi basu ƙaramar harka, Mami zanso Kije Gidan nan zaki sha mamaki wlh, Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce....” tun kan Zahra ta rufe baki Ummi tace”Ae Obie estate Aljannar Duniya ce Mai zaman kanta, Idan fa ki ka shiga gidan Sai ki rasa gane Awace ƙasa kike, tsabar kayan alatun da ke a cikinsa, Yasin in mutun mai ƙaramin Imani na rayuwa acikin tuni zai daina Sallah.....” Dariya mami ta saki Yayin da take sauraron su, daga uwar har ɗiyar gwanaye ne wurin Iya bada Labari.
“Aunty duk yadda zan kwatanta maki Haɗuwar Kayan alatun dake acikin Estate ɗinsu Ba zaki Fahimta ba, Gani da ido yafi abaka Labari, Obinna family duniyace mai zaman Kanta, Ranar dana ta6a zura ƙafa ta cikin gidan wlh Sai da gabana ya faɗi, nace Anya ko Mutane suna tunanin duniya? Yo abu kamar baza a mutu ba, wannan ae sai mutun ya manta cewa da tur6aya aka halicce shi” Dariya sosai Mami ta ke yi tana kallon Aunty Ummi da ke kora mata jawabi, Zahra ta ɗaura da cewa”Ni wlh Naso Daddy ya sama mun Ko aikatau ne agidan su, tun ranar da naji Salary din masu aikin gidan da dollar ake biyan su, Ci da sha da suturarsu duka A kyauta ake yi masu, ai duk wanda Ya haɗa alaƙa Da ɗan familyn Obinna kakar shi ta yanke saƙa, Shi da talauci sun raba Jaha....” in serious matter za’a ta ke magana, Ummi taci gaba da cewa”Shiyasa naso mahaifin ki ya kutsa ki cikin danginsu tun da dama ɗan bangar siyasa ne, Ni ko wannan Yaron ne *DR JAZZ* kisamu ki aure shi, ko mun samu muma mu dangawali arziƙi” ta ƙarasa maganar tana dariya, tur6une fuska zahra tayi Jin abunda Ummi tace”haba ummi, dr Jazz fa meye haka, Ni da na ke harin bugun zuciyar Family ɗin gaba ɗaya, Taya zaki haɗa ni da yaron da har yau ba’asan waye ubanshi ba acikin family ɗin” da mamaki akan fuskar Mami tace”kamar ya ba’asan Ubanshi ba”? Zahra tace”ɗaya daga Cikin ma’aikatan gidan su ce tazo dashi aikatau, Matar ma farar fata ce, ba ki ga yaron ba kyakkyawa ga son mutane, ni bazan Iya auran mara asali ba, Ta ya Ummi zatai min fatan auranshi? Ga gwarazan samari a family din kyawawan gaske masu kama da kakansu Obinna....” tana magana tana turo baki.
Ummi tace”Saboda nasan baza ki Iya samun wanda kike so ba, Haukan banza ki ke yi a kan shi, ke kin sani Ruwa ba sa’an kwando bane, Babban Goro sai magogin ƙarfe, Wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, In banda haɗama irin ta zahra taya zaki nace wa mutumin da yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba? Shiyasa nace ƙwara Dr Jazz ɗin shine dai dai da ke,” ɗaure fuska Zahra tayi jin abunda Umminta take faɗi, ta haɗe rai sosai, Muryarta a ƙule tace”Mami kinga ni ko? Ita fa mahaifiyata ce amma bata min fatan naci ka burina, Kullum sai dai tayi discouraging ɗina, meyasa ta ke yi min haka ne”? a bun ka ga me saurin kuka tuni idonta sun ciko tab da ƙwalla.