Sashe 45
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Please, don’t worry, Your relatives are in good health and we expect them to wake up soon.” da sauri ya tari numfashin ta
“Can you help me go to their room to see them?” A ƙagare yai mata maganar
“Don’t worry I’ll take you to see them but first you need to rest. You’ve traveled for hours, and you must be tired. I’ll turn on the TV so you can relax, and if you need anything, you can use the phone to call me.” ta yi maganar tana nuna mashi wayar dake ajiye saman table na gefen gadonshi
“Ga kuma ƙofar shiga toilet idan kana buƙata” duk abunda ta yi mashi bayani saita nuna mashi da hannu
Bayan ta kammala, Taje gaban plasma tv dake manne jikin bango ta kunna mashi tashar da ake wasan ƙwallon, don tasan mafi akasin maza sunfi sha’awar kallon wasan ƙwallo,
A ƙirji ya rungume pillow yana kallon tv ɗin, fuskar nan ɗauke da annuri banza ta samu an samu ƴanci, Yadda nurse ɗin ke tarairayarshi kamar wani ƙaramin yaro da bai wuci shekara goma ba.
Kafin barinta ɗakin saida ta ɗauki Kayan abincin da ta kawo mashi ta fuce da su robar lemun da bai sha ba kaɗai ta bar mashi, Hannu ya miƙa ya ɗauke ta, Yana sha Yana kallo Hankalin shi kwance gwanin ban sha’awa
*The prisoners Middle step❤*
Wuraren ƙarfe ɗaya na rana agogon birnin san antonio ta buga, adai dai wannan lokacin sambatun muryar Angel ya cika ɗakin da aka kwantar da ita, tana akwance saman haɗaɗɗen gadon, patient’s gown ce a jikinta launin ligh blue, drip ɗin da aka sanya mata tuni ya jima da ƙarewa, zazza6in jikinta ya sauka temperature ɗinta ya dai dai ta.
Muryarta na kakarwa take ambaton sunan danish, Shi ya tsaya mata arai shiyasa take sambatun ambaton sunansa, duk da sanyin A.c na ɗakin hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, zucyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi
“Danish ɗina kura ta cinye min shi, wayyo Allah Danish ɗina na shigo uku munbar Danish Gabriel kura Zata kashe min shi.....” tuntana sambtun a hankali har takaiga ƙware murya da wata irin firgita Ta ware Gray eyes dinta ta zazzare su akan haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakin, Sam bata acikin Hayyacinta, bakomai take gani acikin idanuwanta ba face Fuskar Kurar da ta biyo su A daji tana gurnani, gizo take yi mata, A gigice ta zabura har batasan ta fisge iv line ɗin dake hannunta ba, durowa daga saman gadon tayi Hannayenta bibbiyu daddafe da kanta, Tsantsar tashin hankali ne akan fuskarta, duk tabi ta furgice, doguwar sumar kanta har saitin gwiwarta gaba ɗaya ta hautsine gashin kan tamkar na mahaukaciya, Sam bata acikin hayyacinta batasan A ina take ba? Daji kawai take gani a idonta
Sosai ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, idanuwanta sun makance,,
Da gudun gaske Likitoci suka faɗo ɗakin da take a ciki, Dama jiran farkawarta suke yi, wasu daga cikin Ƴan uwanta sun farka acan inda aka kwantar dasu, Sun rasa gane kan Yaran tsabar tsoro da firgici Jikin su sai kerma ya ke yi sunga mutanan da basu saba gani ba, duk wanda yai yunƙurin tunkararsu ƙara suke fasawa tamkar ana zare ran su, Kalma ɗaya su ke iya ambato abakunansu Sunan Angel wannan yasa Likitocin su ka ƙara da ta farka, don sun fahimci ita kaɗaice zata Iya sarrafa su.
Sam bata ji motsin shigowarsu ba, Sai dai ta ji muryoyinsu akanta, Nan fa hankalin Ta ya ƙara tashi, A firgice ta waiwayo tana binsu da kallo tun daga ƙasa har sama, Waro idanuwanta waje tayi tamkar ƙwayar zata faɗo kasa, jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu, tsantsar tashin hankaline akan fuskarta da ruɗani, sai lokacin ta soma tunanin wai ma A ina take ne? Ya akai ta tsinci kanta a wurin nan? Wanene Ya kawota? ina ƴan uwanta suke? Su wanene waɗannan masu fararen Kayan kamar likitoci ne”? Wahalallan Yawu ta haɗiya, zufa duk ta wanke fuskarta da jikinta, yadda kasan wadda ta yi tozali da aljanu, ganin komai take yi tamkar a mafarki
Cikin kwantar da murya su ke yi mata magana don sun fahimci arikice take babu natsuwa atattare da ita
“Ki kwantar da hankalin ki, Dukanmu nan da kike gani likitoci ne, mune masu kula da lafiyarki, Sannan anan inda kike Asibitine.....” Ras taji gabanta ya faɗi Cikin sarƙewar murya ta soma motsa small lips ɗinta
“Ban...ban..gane ba wanene ya kawo ni nan? Su wanene ku kuma Ina ƴan uwana su ke”? Kallon tuhuma take binsu da shi gani take yi kamar mugaye ne.
“Ƴan uwanki suna nan Cikin ƙoshin Lafiya, idan kika natsu zamu Nuna maki su, wata’ƙil hankalinki ya kwanta” maƙe mashi kafaɗa tayi”wlh bazan yarda daku ba, so kuke ku cutar dani, Ni ku faɗamun Ina danish ɗina yake da sauran ƴan uwana.....” cikin disasshiyar murya tayi maganar hawayen nabin fuskarta, ganin suna matsowa kusa da ita aiko da sauri ta dinga ja da baya tana girgiza masu kai, haɗi da zazzare masu ido don karsu ta6ata
Hakan yasa suka dakata da yin tafiyar, turo ƙofar da akayi ne yasa gaba ɗayansu suka juya don ganin wanene
Nurse rebecca ce Ta shigo ɗakin hannunta ruƙe dana Gabriel, Wani irin farin Cikine Ya lullu6e shi ganin Angel, Ita ko ta runtse ido, Masifa kawai take Ji, da ƙarfi Ya ambaci sunanta”ANGEL!!” Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnanta, Kamar an tsunkuleta Ta buɗe ido Tana faman zazzaresu Akan fuskokinsu, da gudu gabriel Ya ƙarasa gabanta, Gaba ɗaya ya rungumeta Yana dariya, A ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirgita, ƙanƙame shi tayi tamkar zasu koma mutun ɗaya.
Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirkon suna kallonsu, murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, tamkar sun samu tv.
Raba Jikinta Tayi daga na Gabriel Muryarta na rawa take faɗin”Gabriel wanene ya kawo mu nan? Pls ka faɗamin Aruɗe nake bangane komai ba, Ina danish dina da sauran Ƴan uwana?
Ruƙo Hannayenta yai acikin nashi”Angel mun tsira! Mun ku6uta daga kurkukun ƙaddara da Evil forest.......” a tsanake Gabriel Ya kwashe komai Ya sanar da ita, Cikin harshen hausa, hakan yasa Doctors din basuji me yake faɗa mata ba.
Maimakon tayi dariya Sai gani suka yi ta rushe da matsanancin kuka, abunda da ya ɗaure masu kai, tana kuka tana dariya a lokaci ɗaya, slowly ta zube saman gwiwowinta, tare da ɗaura goshinta saman tiles, Sujjada tayi domin nuna godiyarta ga Allah daya nuna mata wannan ranar da suka daɗe suna Jiranta!
*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E15🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
Lokacin da ta ɗago daga sujjadar fuskarta jaga jaga da hawayen, Tafin Hannayenta ta ɗaga sama ta soma ambaton sunan Allah tana Yi mashi kirari, Hakan Ba ƙaramin ruɗar da likitocin yai ba, shi dai Gabriel sai murmushi yake saki yana dubanta, Bayin Allah su kaɗai suka san Wahalar rayuwar da suka fuskanta Dole suji daɗin wannan Ranar, Ta jima tana addu’a,
Sam takasa miƙewa daga zaunan da take, Hawayen fuskarta tamkar zasu ƙare Sai sintiri suke yi saman kuncinta
“Angel pls stop shedding ur tears” Gabriel ne Yai mata maganar, Cikin shessheƙar kuka ta ɗago ta Kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kada jawur da su
“Gabriel dole in yi kukan farin Ciki, kai ka sani irin wahalar da muka sha, munyi rayuwar kulle tamkar dabbobi har ƙwara ni akan sauran ƴan uwana tun suna jarirai, wannan ne karo na farko da zasu ɗanɗani rayuwar ƴanci acikin ƴan uwansu mutane, Iya cuta an cuci rayuwarsu mun tsira amma raunin dake acikin zukatanmu na har abada ne, saboda akwai abubuwan da muka rasa wanda nayi imanin baza su ta6a gogewa a tarihin rayuwarmu ba”
Hankalin likitocin ba ƙaramin tashi yai ba ganin yadda take kuka tana surutu gashi ba su fahimtar abunda take cewa, sai dai sun gane akwai abunda ke damun su wanda yai silar haifar masu da ciwon damuwa da baƙin ciki
Gabriel da ke a tsaye tuni shima ya fara zubar da hawaye.
Gabanta ne Ya ɗan faɗi Jin kukan Jemimah, Nan take shessheƙar kukan da ta ke yi ya dakata, Dr. Laura ce ta shigo Ɗakin hannunta ɗauke da Jemimah Tsabar jaraba ta runtse idanuwanta sun yi suntum saboda kuka, Sunan Genie kaɗai Take furtawa, jikin Angel na rawa Ta yunkura ta miƙe da sauri ta nufi dr. laura Hannu biyu tasa ta kar6eta sosai ta rungumeta a ƙirjinta, hannunta hada cannula da aka sanya mata.
“Angel” Muryar Batul ce ta ratsa kunnuwanta, da sauri ta ɗago tana kallonsu, A jere su ke shigo ɗakin kowan nan su Yasha kuka Idanuwa sunyi luhu luhu, doguwar suman kawu nan su A hargitse kamar waɗanda aka koro daga gidan mahaukata.
Kowan nan su Na sanye da light blue uniform da aka sanya masu, hannayensu sanye da cannula na drip da aka sanya masu.
Batul ce ta farko, Bayanta Parveen ce da hannah, Sai mazan Javed da Naufal, da gudum gaske suka ƙarasa shiga ɗakin gaba ɗaya suka ƙanƙame Angel kamar zasu kada ita ƙasa.
Al’ajabi Ya hana Likitocin cewa komai, Sun saki baki galala suna kallon Ikon Allah, Aransu suna Mamakin ƙaunar da suke yi ma ƙaramar Yarinyar da su ke kira da Suna Angel.
Farin Ciki kamar zai kasheta, Daɗi take ji tarasa ina zata tsoma ranta, Sun lullu6eta suna yi mata kuka, ko numfashi daƙyar take Iya fitarwa