← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 152

Sashe 129

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guntun tsoki Zaki Yaja, Ya faɗa katafaren room dinsa, saman gadonshi ya kwanta, haɗi da daura laptop dinshi on his broad chest, hoton fuskarta dake akan wallpaper din laptop nasa ya ƙurawa ido yana kallonta, bazai Iya misalta ƙaunarta da yake ji ba, yana sonta baya jin zai iya son wata ƴa mace aduniyarnan kamar yadda yaso baiwar Allahn nan, sun rayu na tsawon shekaru tamkar ma’aurata rana ɗaya Allah ya ƙaddara rabuwarsu, yana fatan sake haɗuwa da ita, da tunaninta bacci yai awon gaba da shi.

*ANEELERH❤*

Kiran sallar asubar farko, ringing din wayarta ya daki kunnanta, firgigit ta farka daga bacci tana faman sauke ajiyar zuciya, yayin da la66anta ke ambaton sunan baby junaid, mafarkin da tayi da shi ya ɗaga mata hankali, a ruɗe ta mike zaune, rigar baccin jikinta duk ta yamutse, haka zalika sumar kanta a hautsine take.

Daukar wayar tayi dake ajiye gefenta, ta duba me kiranta, missed calls ta gani sun kai biyar na hajiya adama, aranta ta ayyana Allah yasa ba mafarkin da tayi bane ya zama gaske.

Bin kiran tayi nan take kiran ya shiga, bugu uku kafin hajiya adama ta ɗaga.

“Assalamu alaikum, daughter in-law, fatan dai ban katse maki baccin ki ba” da buɗar bakin Aneelerh sai cewa tayi”mommy ina junaid”
Sautin dariyar hajiya adama ne ya fargar da ita, da sauri ta dafe baki tamkar tana agabanta tace”au...namanta ban gaishe ki ba, ina kwana mommy”

“Lafiya lou Aneelerh, lallai yau na shaida kin ƙosa kiga ɗanki, tun da gashi har kin fara ambaton sunan shi tunkafin ki gaishe ni”

Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, daga bacci na tashi bansan Na ambaci sunanshi ba”

Hajiya adama tace”oh am sorry na tada ki daga bacci tun da asubahi, agafarce ni, jikana ne ya takura min akan in kira mashi ke awaya, yaban mamaki da sunanki Ya farka yanata kuka yana fadin wurin mommy zaije shine nace bari na kiraki kuyi magana wata’ƙil hankalinshi zai kwanta, kafin mu shigo gidan zuwa anjima in sha Allah”

Hankalin Aneelerh yaɗan tashi jin abun da mommy adama tace, aranta ta ayyana kodai shima yayi kalar mafarkin da tayi da shi ne?

“Aneelerh kinyi shiru, ga shi ku gaisawa” muryarta adabarbace tace”toh mommy”

Sautin kukan baby junaid ne ya cika mata kunnanta, murmushi tasaki tana fadin”My baby boy, ba hello ba hi sai kuka? So kake hankalina Ya tashi ko”?

Cikin shessheƙar kuka yace”mom..my wallahi kizo ki ɗoke ni, idan ba haka ba bazaki sake gani na ba, mutuwa ma zanyi” rass taji gabanta ya fadi,

“Junaid kadaina ambaton mun mutuwa, banaso, idan wani abu ke damunka ka faɗamin mana!” aɗan tsawace ta furta mashi maganar, tunawa da hajiya adama yasa ta sassauta muryarta,
“My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, Yau in sha Allah mommy adama zata dawo min da kai”

Tsagaitawa yai da yin kukan, Muryarshi da shagwa6a yace”Ai ni tsoro nake ji, bana son zama agidansu....” bai ƙare maganar ba tayi sauri furta”shiru! Agaban mommy adaman kake fadin haka”?

“A’a mommy, ba agabanta bane, ai ta fita daga dakin”

Ajiyar zuciya ta sauke”yanzu fada min me ke baka tsoro? Ko wanine yake bugunka”?

“A’a mommy, idan ina bacci, sai ina ganin wani mutun sanye da baƙaƙen kaya hannun shi ruƙe da ɗan kwano, kalar wannan abun na ɗakin mami, wanda ake zuba fura a cikin shi, hannun shi zaƙo zaƙo da akaifu kalar na Ana mai girka mana abinci, wai yake ce min inzo mu tafi” zaro ido waje aneelerh tayi”Junaid ka natsu kayi min bayani, a mafarki kake ganin shi ko kuwa a zarihi? Kai kaɗai ka ke kwana aɗaki idan dare yayi”

“Ni ba mafarki nake yi ba, dagaske nake ganin shi, kuma a ɗakinsu nake kwana” aneelerh duk tabi ta ruɗe.

“Junaid kaji tsoron Allah, ka faɗamin gaskiya, nasanka da ƙarya, Idan baka fada ba, to bazan baka zoben Angel ba”

“Kin siyane”? Ƙumshe dariya tayi don tundaga kan yadda ya tambayeta ranta ya bata cewar ƙarya ya shirga mata.

“Na siya mana, ai jiya naba mahboob kuɗi Ya siya maka zoben mai kyan gaske”

Tuntsirewa yayi da dariya yana fadin”to mommy wasa nake yi maki, wallahi dama awani cartoon ne da muke kallo a tv, anan naga mutumin” fashewa tayi da dariya sosai har fararen haƙoranta suka bayyana”yanzu naji magana ɗan rainin wayau, duk kabi ka tasar min da hankalina, Yau har mafarkin ka nayi saboda nayi kewarka babyn mommy, ina sonka Yarona”

Yace”nima inasonki mommyn baby” dariya tasaki, idan yana yi mata magana kamar wani babban mutun daya mallaki hankalin shi, sai idan yayi wata kwa6ar ne zaka gane ƙaramin yaro ne.

“Mommy ina mamina? da abie, da uncle mai ƙaton hanci, da mahboob mai son kuɗi, da zahrah mai dogon wuya”

Tsabar yadda take yin dariya hada dafe ciki,
“Junaid baka da mutunci, Uncle dinne mai ƙaton hanci”!
Kaitsaye yace mata”eh mana, baida kyau Allah, mummuna ne uncle dan Iya, ni naji dadi ma bashine daddynki ba, da wallahi bazanyi kyau ba”

Mamaki ne ya kama Aneeleerh, jin yadda yake kushe mata kawunta.

“Junaid dan Allah ka yi shiru kada wani yaji ka, Ni zan ajiye wayar, ka koma bacci zuwa anjima Mommy adama zatayi maka wanka ta shiryaka sannan zata dawo mun dakai gida, fadamin me kake so in tanadar maka”?

Da shagwa6a yace”fura nakesho, asanya kwakwa da yoghurt aciki” bakomai ya tuna mata ba face Angel, tana son furar da aka sanya kwakwa da youghurt, kusan kullun idan tazo gidansu sai ta sanya Aneelerh ta haɗa mata ita, musamman saboda Angel take ajiye damarmar fura cikin robabi ta sanya mata su a frigde don su yi sanyi.

Tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, Muryarta na rawa ta furta”zan ajiye maka my baby boy, ka kwanta ka huta zuwa anjima zamuga juna” daƙyar ta samu baby junaid Ya ƙyaleta, badan ta gaji dashi ba, ta ajiye wayar on pillow, ta sauko daga saman gadon, A hankali take bin bedroom dinta da kallo, har idonta ya sauka akan hotonsu da ta liƙa shi a bango, wanda sukayi tare da aminnanta, su uku abunsu, kowacce ta ca6a uban adon lace, fuskokinsu ɗauke da murmushi.

Ta natsu tana kallon hotunansu, sam ba ta ji takun tafiyar mutun ba, har ta ƙaraso gefenta ta tsaya, Ƙamshin turaren zahra ne yaja hankalinta ga dubanta, tayi mamakin ganinta a ɗakinta, tun ranar da abunnan ya faru na hajiya falmata ko magana bata ƙara haɗa su ba, amma yau sai gashi ta tako ta shigo room dinta, dogon hijabi ne a jikinta daga ƙasa har sama launin maroon hannayenta biyu ta fiddo dasu ta cikin hannun abayar, hada cazbaha ta ruƙe tana ja kamar wata matan limam.

“Aunty Aneelerh Ina kwana, kin tashi lafiya”?

Daƙyar ta iya amsa mata da lafiyalou, ina fata kema haka”
Daga mata kai tayi alamar eh, idanuwanta sam basa akan Aneelerh suna akan hoton da take kallo, wani irin kunyarta take ji, tunawa da rashin mutuncin da tayi mata akan ta bata shawarar ta ba Hajiya falmata haɗin kai, tayi danasani tun jiya da Mahboob Ya fayyace mata komai.

“Nayi mamakin ganinki a ɗakina zahra, ai nayi tunanin mun rabu kenan har abada”

Girgiza kai zahra tayi”Idan kinga mun rabu to mutuwace ta raba”

Aneelerh sam batasan Mahboob ya fada ma zahra ba, bayan ta gargade shi akan karya gaya mata, shi kuma bayason suna gaba atsakaninsu, don ya fahimci zahra ta fusata sosai, Idan har bai fada mata gaskiya ba to kuwa zata cigaba da zabga ma Aneeleeh rashin mutunci abisa rashin sani shiyasa ya yanke shawarar ƙwara ya faɗa mata, don ta yi takatsantsan kada ta wuce gona da iri azo aji kunya.

“Kiyi haƙuri da abunda Ya faru atsakanin mu, nasan na 6ata maki rai, tuntuni nake taso in nemi yafiyarki, sai dai baki bani damar yin hakan ba” Aneelerh ce tayi maganar tana duban zahra.

Cikin sanyin murya zahra tace”ni yakamata nabaki hakuri auntyna bake ba, saboda ni ce mai laifi, ban kyauta maki ba, duk irin shaƙuwarmu da kyautatamin da kike yi amma nagaza fahimtarki, har takai takawo ina zarginki, maimakon na kyautata maki zato, wallahi naji kunya, daren Jiya daƙyar na runtsa tsabar takaici, Ƴan kwanakin da muka samu sa6ani atsakaninmu aunty Aneelerh naji jiki ba kaɗanba, na ƙuntata, na gane mahimmancinki agareni, Ina da abubuwa dayawa da suka faru wadanda nakeso in samu abokin firar da zangayama wa ya tayani farin ciki sai dai kash babu, ke kaɗai ce nake jin dadin tattaunawa dake akan duk wani abu daya shafi rayuwata saboda nasan zaki ƙarfafa min gwiwa ki kuma bani shawarar da zata amfane ni....” zafafan hawayene suka wanke fuskar Zahra, tuni idanuwanta sun kaɗa jawur da su.

“Meyasa banyi dogon nazari ba akan shawarar da kika bani”?

Zuciyar aneelerh ba ƙaramar karaya tayi ba”zarah! Mahboob Ya fada maki ne”?

Jinjina kai tayi”ƙwarai kuwa ya fadamin komai, har gargaɗi na yayi akan kada na nuna na sani, saboda kince mashi kada ya gaya min, shi kuma a ganinshi bai kamata ki zubda mutuncinki a idanuwana ba, saboda ku rufa ma hajiya falmata asiri awurina, don in cigaba da ganin darajarta, hakan kuma bazai ta6a yiwuwa ba, saboda shi mutunci madarane idan ya zube baya kwasuwa, sai dai naji dadi da ke kika yi silar shiriyarta, ke din ta dabance Auntyna”

Rungume Aneelerh tayi, atare suka fashe da kukan farin ciki, yau sun shirya da juna, babu wanda baiji jiki ba acikinsu.
Chapter 129 · 0% Book details