← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 152

Sashe 29

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin girmamawa tayi mata sallama”Assalamu akaikum” on the other hand Hajiya adama ta amsa mata da”Wa’alaikum salam daughter In law, ina kika shiga inata kira ba aɗagawa”? aneelerh tamkar tana agabanta tace”Bana akusa da wayar ne bansan kun kira ba” gaisawa sukayi kafin hajiya adama tace”guest what”? ɗan zaro ido Aneelerh ta ɗanyi tana wurwurga eye balls ɗin ta can tace”kun dawo ƙasar”? Sautin dariyar hajiyar adama ne yasa ta saki murmushin farin ciki.
“Mun dawo, in sha Allah end of this month zamu shigo Abuja, two days kin daina kiran layina Why? Ko dan saboda kada na ƙwace maki Yaro”? Cikin Jin kunyar maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, wlh ina ta zucci zuccin in kira ki Allah ne bai nufa ba” Tai maganar a yayin da take kokarin zama saman stool, Ta gaji da tsayuwar, Zahra ta kasa kunne tana sauraron Firarsu.

“Idan ma don saboda dashi ne to ki kwantar da hankalin ki, babu wanda zai raba ki da ɗanki, Munyi magana da abdallah Ya fahimtar dani game da cutuwar da zakiyi idan muka ce zamu raba ki da shi, Ni kaina bazanso Inyi silar sanya ki baƙin ciki ba....” buɗe ido Aneelerh Tayi Wani irin farin cikine tsantsa akan fuskarta, Zahra da ta tsareta da ido tana kallonta, sai faman yi mata mimi da baki takeyi donta fada mata me Hajiya adama ke fada mata wanda yasa ta farin ciki

“Zan kira mamin naki mu yi magana, Sannan akwai wata gagarumar kyauta dana shirya maki idan mun zo zaki gani” Hawayen farin Ciki ne su ka wanke fuskar Aneelerh, kasa jurewa tayi batasan lokacin da kuka ya kubce mata ba. Muryar Hajiya adama a ɗan ruɗe take fadin Aneelerh why? Kuka kuma? Meya faru? cikin shessheƙar kuka tace mata kukan farin Cikine, taji daɗin ƙaunar da take nuna mata, tana alfahari da su, samun surukai irinsu abune mai wuya, Hajiya adama taji daɗin daɗaɗan kalaman da Aneelerh take faɗa mata, tsawon lokaci suna waya Kafin daga bisani Tayi mata sallama, Idanuwanta acike tab da ƙwalla ta wurga su kan fuskar zahra tambayarta ta shiga me suka tattauna da Hajiya adama? Nan Aneelerh ta sanar da ita komai, Fasa ihu zahra Tayi tare da jefar da wayarta gefenta, ta sauke junaid daga saman jikinta a hankali ta kwantar dashi, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi Aneelerh ta rungumeta kamar zata maidata ciki, Farin Ciki duk Ya cikasu, Miƙewa Aneelerh tayi bayan ta ajiye wayar gaban mirrror, Rawa suka soma takawa ita da zahra, hada ɗebo shoki suna kifawa saman goshinsu, Yayin da suke sakin Dariyar murna.

*EVIL FOREST*

A ƙalla yau satin su ɗaya acikin kogon dutsen ba tare da sun motsa ba, saboda marasa lafiyan cikinsu, jikinsu yai tsauri, duk da haka suna ƙoƙarin basu kulawa ta musamman, Danish Ya haɗa masu garin maganin da su ke sha suna samun warakar raɗaɗin ciwonsu, A cikin gorar ruwansu ya ke jiƙa masu maganin, Bayan haka duk in za su yi tsarki da ruwan zafi su ke yin shi, danish ne yai masu dabarar yin hakan, Alhamdulillam Jikinsu Azeeza yayi kyau sauƙi ya samu, ba su rasa ci da sha ba, kullum ne sai sun ci abinci sau uku, Danish ne ke ƙoƙarin yi masu farautar abunda zasu ci wani sa’in zoman daji yake kaso masu ko tsuntsaye hada kayan marmari ya ke samo masu, saboda su ya ke hana idonshi bacci, A zaune yake kwana shi da Angel dinsa, tana ɗebe mashi kewa, shaƙuwace mai ƙarfi a tsakaninsu.
Burinsu marasa lafiyar cikinsu su ƙarasa wartsakewa ko sun samu su cigaba da tafiya.

Yau tun da sanyin safiya ta soma Jin hayaniya acikin kunnuwanta, ƙasa ƙasa take iya jin maganganunsu, Tsantsar mamaki ne ya kamata Jin muryoyin su Batul, tamkar a mafarki, a harzarce ta buɗe idanuwanta tare da miƙewa zaune tana ƙarewa Kogon dutsen kallo, Haris ne kaɗai ya rage a kwance yana bacci, Ya ƙudundune kanshi cikin bargo, ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya ta soma yi, da wata irin kasala ta miƙe tsaye tare da yin hamma, abu biyu ya ɗaure mata kai da farko tayi tsammanin zata ga su Azeeza sai dai bata kowa ba.
Hankalinta A matuƙar tashe ta fito tana ƙarewa Dajin kallo, Kamar daga sama tajiyo muryar Jemimah tana ambaton Sunan da take kiranta dashi”Genie!’ ras taji gabanta Ya faɗi, A ruɗe ta wurga ƙwayar idonta kansu, Gaba ɗayansu ne banda Haris, Yau wata rana sun fito daga kogon dutse jiki yayi kyau, Sai wasa suke Yi suna tsalle tsalle, Farin Ciki duk ya cikasu, Bakunansu awashe kamar gonar auduga, ba ta san lokacin da hawaye suka soma wanke fuskarta ba, Nan ta ke ta zube saman gwiwowinta tare da kifa kanta ƙasa ta yi sujjada tana godewa Allah da ya nuna mata wannan ranar, Haƙiƙa tayi farin ciki mara misaltuwa, kafin ta ɗago daga sujjadar Jemimah ta watso da gudu ta faɗo saman bayanta, sai tiƙar dariya ta ke yi tana fadin”Genie Daɗi kamar zai kashe mu, Wlh daɗi muke ji, wannan wurin mai kyau bamu ta6a ganin irin shi ba, Genie Yau zamuje gidan daddynki ko”? Kasa ɗagowa Angel tai, wani irin yanayi take jin kanta.
Ƙarasowa Azeeza tayi Hannunta ruƙe cikin na Gabriel, Sauran Ƴan uwansu na abiye da bayansu, agaban inda tayi sujjadar suka tsaitsaya suna kallon ta
“Angel muna son yin magana dake”muryar parveen ce ta ratsa kunnanta, daƙyar ta iya haɗiye kukan da ke shirin kubce mata ta ɗago da kanta, tare da zagayo da hanneyenta biyu ta ruƙe Jemimah gudun kada ta faɗo daga bayanta
Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, tun daga kan fuskar Azeeza dake ta sakin murmushi, fatar jikinta tayi haske sosai dama ita can launin skin ɗinta na farar fata ne, da launin gashinta, ta rame sosai ta ƙara komawa ƙarama. ɗauke idon ta tayi daga fuskar Azeeza ta mayar dasu kan fuskar parveen, itama ta faɗa duk sunyi haske kamar fatalwu, Murmushi ta ɗan saki tare da kallon Batul dake a tsaye tana sakar mata murmushin ƙauna.

“Rabin rai kin tashi lafiya, Nasan kinyi mamakin ganin mu awaje muna shan iskar duniya, Danish ne ya fito da mu waje kuma yace da zarar ya sama mana abinci mun ci zamu kama hanya” lumshe ido Angel ta ɗanyi tare da ware su kan fuskar Hannah.

Muryar Gabriel ce ta janyo hankalinta ga kallon shi”Muna so muyi maki godiyane akan irin ƙoƙarin da kikayi mana, Angel kin cancanci ayaba maki, babu wasu kalmomi da zamu Iya yin amfani da su wurin yi maki godiya ke da Danish, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku” Cikin sanyin murya tace”Allah shine abun godiya Gabriel, Alhamdulillah ala kullu halin, ina taya ku murnar Samun ƴanci arayuwarku, Kuma inayi mana fatan Allah ya bamu sa’a adukkannin abunda muka sa agaba, Ubangiji Allah yasa ƙarshen wahalar mu ce tazo....” addu’o’i ta dinga jera masu suna amsa mata da ameen, Sai da ta kai ƙarshen maganarta, muryar jemimah ta katse ta”Genie ba zamu ƙara komawa kurkuku ba ko?” Batul tace”har abada mu da kurkukun ƙaddara, Daga nan sai Gidan daddyn Genie, ko kina son komawa ne”? Zaro ido tai tare da girgiza kanta”banso, Allah ya tsinema su da tsohuwa zafreen, muguwa idan mu ka yi ƙarfi sai mun kashe su, damu da daddyn Genie, zamu rugurguza kurkukun kowa ya huta, Kuma zamu ƙwato ƴan uwanmu da ke a wurinsu” ranta a6ace ta ke yin magana, kumatunta sunyi jawur da su.
Angel tace”In sha Allah Jemimah mune zamu kawo ƙarshensu, Allah sai ya saka mata cin zalunmu da su ka yi, haƙƙin mu ba zai ta6a barinsu ba, tun agidan duniya zasu fara gir6an abunda suka shuka” tana magana hawaye nabin fuskarta.

“Angel Ba ki faɗa mana ina ne nan ba? Munga wasu abubuwa da su ka ɗaure mana kai waɗanda bamu ta6a ganinsu ba ko a mafarki,” Javed ne yai mata maganar fuskarshi da alamun ruɗu.
“Angel munga kalar ganyan da ake kawo mana muna ci a kurkuku,” still fuskarta da murmushi ta yunƙura ta miƙe hannunta ruƙe da Jemimah, Gabriel ta kalla”meyasa baka yi masu bayani ba”? Ta6e la66ansa yai”sun fi so suji daga bakin ki,” Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa”Okey, Ku jira Danish Ya dawo, idan muka kammala cin abinci, muka kama hanya zanyi maku bayanin komai” amsa mata su ka yi da toh. Kafin wani ya ƙara cewa wani abu, Motsin tafiyar Danish ta janyo hankulansu ga dubanshi.

A tsanake ya ke yin tafiya yana tunkaro su, hannun shi ɗaya a ruƙe da kwandon da ya haɗa masu saboda ajiyar kayan abincin su, tunkan ya ƙaraso Jemimah ta sauko daga bayan Angel, da gudu suka nufe shi ita da Azeeza da parveen, atare suka faɗa mashi tare da ƙanƙame shi suna sakin dariyar farin ciki.

Ganin shi suke yi tamkar mahaifinsu, saboda kyautatawar da ya ke yi masu wurin yin jinyarsu, nufo wurin su Angel tayi tana faɗin”Sannu da dawowa My Man, Na farka ban gan ka, meyasa baka tada ni mun tafi atare ba” ta yi maganar tare da kai hannu ta ruƙo hannun Kwandon da ya ruƙo, sakar mata yai ta kar6a tana leƙa cikinsa Kayan marmari ne ashaƙe cikin kwandon.

Da sauri ta ɗago suka haɗa ido da juna, murmushi ta sakar mashi”sannu da ƙoƙari, duk namu ne wannan,” ɗaga mata gira yai alamar eh, “mun gode Danish, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka,” lumshe mata ido yai kafin ahankali ya ware su akan fuskarta.
Chapter 29 · 0% Book details