Sashe 85
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fashewa Natasha tayi da dariya fararen haƙoranta a jere kamar gonar auduga, sam firar su bata ɗauke mata hankali ga yin driving din da take Yi ba, har ta zuƙe tabar hannun ta duka.
“Dole kiyi mini dariya ƴar rainin wayau” ta fada tana hararar ta.
Tsagaitawa Natasha tayi da yin dariyar ta dubi fuskar Ummin america”mutuniyata, Kina ta zumuɗin zuwa Nigeria, banji kina maganar mutumin ki ba” cikin rashin fahimtar kalamanta ta furta”Wa? Kashe mata ido ɗaya Natasha tayi”Boss Man, ko kina nufin har kin manta da shi? ta faɗa tana duban hanya.
Yamutsa fuska Ummin america tayi”Allah ya raba ni da alaƙaƙai, bana fata wani abu ya ƙara hada ni dashi, jarababbe kawai”
Natasha na dariya tace”haba ummi, mutumin fa ya mutu akan ƙaunarki, nayi ƙoƙarin ganin na maye gurbinki acikin zuciyarshi sai dai Ya nuna mun cewa ke kaɗai ce za ki Iya sarrafa shi yadda ki ke so, kuma yana nan akan bakansa na cewa ba zai ta6a barinki ba har abada ke tashi ce”
Mood din fuskarta ne ya canza zuwa 6acin rai.
“Natasha, I don’t even want to hear his name, bawai don bana son shi ba, kawai ni bana son mutumin da zai nuna ƙarfin iko akaina, kamar wani ubana, yaushe rabona da shi tun lokacin dana ɗauki cikinsa na zubar ba tare da saninshi ba, muka samu sa6ani dashi ban ƙara ganin ƙeyarsa ba, Kin san fa mutumin akwai zuciya ga girman kai, nasan zai neme ni ne tun da baya gajiya dani”
Natasha tace”kina wasa da damarki ummi, da Ace nice na samu matsayin da kika samu acikin zuciyarshi, bana tunanin zan iya bijire mashi, biyayya zanyi mashi sau da ƙafa””
Ta6e baki ummi tayi”nima ba gudunshi nake yi ba, Ciki ke bana so, saboda zai 6ata min shape din jikina, kuma ni tun kafin mu ƙulla alaƙa dashi sai da na faɗa mashi sharuɗɗana, nace mashi bana ra’ayin yin aure kuma bana son ciki, ban damuwa ba idan zamu shekara munayin sharholiyarmu da shi in dai zaiyi min biyayya”
Murmushin gefe fuska Natasha tasaki”Ummi kenan, Yanzu mu ajiye zacenshi a gefe, ni dai shawarar da zan baki shine idan kika koma ƙasarku, kada ki kuskura ki kula ƙasƙantattun mutanan da su ka yi silar barin ki Nigeria, bana so ki nuna kin san su, inaso ki nuna masu cewa kwandon shara yafi su mahimmanci a awurin ki”
Maganar Natasha ta ta6a zuciyarta ummi, tuni ta ɗaure fuskarta, tunawa da wani abu da ya faru a rayuwarta.
“Please, stop talking about them, i don’t wanna hear it” rai a6ace ta furta hakan, jinjina kai Natasha tayi”shikenan nadaina mutuniyar saboda bana son 6acin ranki” mood din fuskar Ummi Ya canza sosai, abubuwan da suka faru arayuwarta take tariyowa, masu daɗi da marasa daɗi.
“Mutum biyu masu mahimmanci arayuwata, ina fata na sake haɗuwa da su, Yarinyar dana bari inason na ganta duk da bani da tabbacin tana araye ko ta mutu, ba dan bana son ta ba, na tafi na barta, tun tana jaririya, shi kaɗai ne danasanin da zanyi arayuwata”
A cikin zuciyarta ta furta hakan ba tare da sautin muryarta ya fita ba, tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla. Afakaice ta zaro hanky daga hand bag dinta ta share ƙwallar idonta.
Sun jima suna tattaunawa da ƙawarta Natasha, A lokaci ɗaya motar su, da motocin jami’an da suka ɗauko su Angel suka ƙaraso katafaren Airport din, slowly Ummi ta zuge glass din motar don ta samu damar ƙare ma Yaran kallo ita da Natasha, kafin fitowarsu daga mota, suka soma Jin jiniyar motar sojoji, kusan guda uku suka nufi wurin da sukayi parking din nasu motocin, bayan sunyi parking din motocinsu, Commender ya fito daga motarshi, tare da Major da captain da sauran sojojin da su ka zo da su. kowan nan su yana sanye cikin kakinsa, ga dukkan alamu sunzo Yi masu bankwana ne.
Jami’in dake tuƙa motarsu Angel ne ya fito da sauri Ya zagaya Ya buɗe masu kofa, Angel ce ta fito hannunta ruƙe dana Danish, duk da face mask din dake akan fuskokinsu hakan bai 6oye tsantsar kyawun idanuwansu ba, Hankalin Natasha ba ƙaramin tashi yai ba lokacin da idanuwanta su ka yi tozli da kyakkyawar surar Danish, tun kan ummi ta faɗa mata wanene shi tayi saurin cewa”kamar Yaron da kika faɗa min ko”? Ummi na murmushin shaƙiyanci tace”may be shine, ai ni fuskar shi na gani a hoto, naga wannan ya sanya face mask, amma dai ina da tabbacin shi ɗin ne, masha Allah ƙaramin mutum da babbar harka, Ni ma ban ta6a ganin shi ido da ido ba sai yau, Nayi tsammanin jin shi yafi ganinshi, ashe ganin shi yafi jinshi,” lashe baki Natasha tayi da harshenta kamar wata mayya tace”Ya tafi da imanina, Ya za’ai ummi? Anya bazan biyo ku Nigeria ba? Kinga ke sai ki dinga rainon su ni kuma Ina biyan buƙatata da su”
Ummi tace”bismillah zaki Iya bin mu amma ki sani komai ya faru dake kada ki nemi ni, Chief owais sai yayi jajjagen namanki, idan kika ta6a mashi ƴa’ƴanshi”
Har ta ƙarasa maganar, Natasha batasan me take cewa ba, idonta akan Danish, Bayan fitowarshi da Angel, Batul ta fito, Sauran Jami’an suka fito tare da bubbuɗe masu motocin. Gabriel ya fito tare da Haris da hannah, Naufal ya fito da parveen da javeed, dr laura ta fito daga motarta, ta bude masu Azeeza, suka fito suma, Nurses din dake atare da su da dr mark da brown kowan nan su Ya fito waje. Prisoners sun baza ido suna kallon inda suke, tun kafin su shiga cikin Airport din.
Ummi America da natasha sun tsaresu da ido
“Yaran Fa akwai kyau, Yanzu ummi har kina Iya zama wuri ɗaya dasu ba tare da kin rage zafi ba”? Shiru ummi tayi mata ba tare data tanka mata ba, hankalinta na akan prisoners, ta ƙura masu ido, hakanan ta dinga jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, ba tare da sanin dalilin daya haifar mata da hakan ba, jikinta yai wani irin sanyi, ɗaya bayan ɗaya take bin su da kallo, yayin da suke gaisawa da sojojin cikin raha suke amsa masu.
Sai daga bisani Ummin America ta buɗe murfin motarsu, atare suka fito ita da Natasha, Hankalin su Angel Ya dawo kansu, Kallo ɗaya tayi mata sai da gabanta ya faɗi, kuma nan take ta gane wacece ita, tun da taga uban hips dinta da boobs dinta da suka cika ƙirjinta, ranta ya bata cewar tabbas itace matar da aka damƙa ma amanarsu, tun da ta fito hankalin kowa ya dawo kanta, taku ɗaya girgiza goma, wankan suit din jikinta ya tafi da imanin kowa dake awurin.
Kallon kallo suka soma bin juna da shi, tsakanin prisoners da ummin america, da kuma dr. Laura, da jami’an isod, da sojojin da suka halarta, sama sama suka soma gaisawa da ita, Dr laura ta haɗe rai kamar yadda itama ummin american ta ɗaure mata fuska, bayan sun gama gaisawa da juna, jami’an suka buɗe boot na motocin da suka zo da su suka ɗauko suitcases dinsu tare da jakunkunan kayansu, gaba ɗayansu suka ɗunguma zuwa cikin departure gate din Airport, ta inda suka samu sauƙi, Jirgin da zai ɗauke su privet jet ne mallakin Jami’an isod, babu buƙatar jira ko wasu shaidu, An riga An shirya masu komai su kawai ake jira domin tafiya, duk inda suka bi darewa akeyi abasu hanya saboda sojojin dake atare da su, prisoners sai ƴan kalle kalle suke Yi, sunga wuri mai kyan gaske ga mutane launi daban daban suna ta yin zarya acikin wurin, Yankin da jirginsu zai tashi fili ne na musamman aka ware shi domin tashi da safkar jirage masu zaman kansu.
Tanƙamemen Privet jet ne Aka tanadar masu, Mallakin Chief of isod, Aljannar duniyace ƴar ubansu a wurin haɗuwa, tun daga wajen jirgin zaka fara cin karo da sunan ISOD da aka rubuta da manyan haruffa ajikinsa.
Idan ka shiga cikin jirgin kamar ka shiga haɗaɗɗen villa ne saboda haɗuwar kayan alatun dake acikin sa, akwai Falour wanda yaji hadaddun leather seats masu numfashi, tare da ƙayatattun tables, ga fine carpet shimfiɗe saman floor na jirgin, bayan shi akwai large flat-screen TV, ga Conference table domin yin meeting, a kewaye yake da kujeru, ga kitchen da bathroom, and privet bedroom da kuma dining area, Komai fa akwai shi acikin jirgin babu ce kaɗai ke babu, ta ko’ina sanyin A.c ka ratsa cikinsa.
Bayan sun sauka abakin jirgin, Hankalin su Batul Yaƙi kwanciya tun da su ka yi arba da jibgegen jirgin dake agabansu, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da abu kamar wannan ba, duk sun bi sun rude, sai faman zazzare idanuwa suke yi, badan Angel na atare da su ba, da tuni wasu daga cikinsu sun zauce saboda tsabar kiɗima, bankwana suka somayi da sojojin da suka rako su, Dr laura hada hawayenta na rabuwa da su, ɗaya bayan ɗaya saida ta rungume su, tana yi masu fatan alkhairi, Jemimah da Azeeza sunji ɗacin rabuwa da ita, sun sha kuka hawaye duk Ya 6ata fuskokinsu, lallashinsu ta dinga yi tana kwantar masu da hankali, tace kada su damu zata iya zuwa har Nigeria tagan su, babu wanda bai ji kewar rabuwa da su ba, Dr mark da brown suma sun matse ƙwallarsu, hatta nurse jessica da Rebecce sai da su kayi kukan rabuwa da su, musamman masoyiya Angel kowa ya saba da ita, suna sonta sosai, ummin america tuni tayi sallama da ƙawarta Natasha, bayan sun gama ƴan rungume rungume, sojojin da ke atare dasu sunyi masu fatan sauka lafiya, lokacin da zasu hau matakalar jirgin daƙyar suke taka staircases din, har dai suka samu damar shiga ciki, al’ajabi ya kama su ganin haɗuwar jirgin, kowan nan su Ya samu wuri saman tausasan leather seats din suka zazzauna, tun da suka shiga jirgin ummin america bata tanka masu ba, sai dai kallon kallon da suke Yi a tsakanin su, ita dai Angel damuwarta Danish ɗinta, Ya ƙanƙameta, babu alamun lafiya atattare da shi, jikin shi yai zafi rau.