← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 152

Sashe 95

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr.shureim Tun bayan daya dawo daga sallar asuba Yake ta faman shirye shiryen tafiya jos, tuni Yayi wanka ya kimtsa cikin shigar shi ta larabawa Yabi ko’ina na jikin shi Ya feshe da turare, Hannun shi ɗaya ruke da wayar shi ɗayan hannun Yana ruƙe da car key dinsa, takalmasa Ya zura a ƙafa Jiki Na rawa ya nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ya fito bai nifo ko’ina ba sai part din Alhaji musa don Ya sanar mashi da zancen bayyanar benazir da kuma tafiyar da zaiyi zuwa jos, abakin ƙofar ɗakin ya dai daita natsuwarshi, ya ɗaga murya yayi mashi Sallama, kusan sau uku kafin muryar Alhaji musa ta amsa mashi
“Wa’alaikum salam shureim shigo ciki mana” ajiyar zuciya ya sauke, tare da sanya hannu Ya ture ƙofar ta buɗe, baiyi tsammanin zai ganshi tare da wani ba, ashe bashi kaɗai bane, su biyune shi da Hajiya Sarah suna zaune saman Sofa ɗin ɗakinshi, An jera masu kayan breakfast a saman sofa table din gabansu, mutumin babu annuri akan fuskarshi, Jallabiyace a jikin shi hajiyar tashi kuwa ta ca6a uban adon lace a jikinta, ta kashe ɗaurin kallabinta, wutsiyar gashin kanta ya sauka har saman wuyanta
Fuskarta da fara’a take kallon shureim”barka da safiya My son, fatan ka wayi gari lafiya” shureim na murmushi yace”yawwa mommy, ina kwananku’ ta amsa mashi da Lafiya lou, tare da nuna mashi wuri saman armchair ta ɗakin tace”bismillah ka zauna mana” tun da ya shigo Alhaji musa bai ɗago Ya kalli fuskarshi ba, Hankalin shi na akan abincin da Yake ci, plate ne agabanshi shaƙe da farfesun nama Yaji ƙayan hadi sai ƙamshi Yake Yi, a tsanake Yake cin abun shi.
Kasa zama shureim yayi idanuwanshi akan fuskar Alhaji musa Yace”uncle barka da safiya” kamar bazai amsa mashi ba ya furta”lafiya” da ido Hajiya sarah tayi alamar yayi haƙuri da halin uncle din nashi, murmushi shureim ya sakar mata yaɗan jinjina mata kai
“Ko zaka Bari idan Ya gama cin abinci sai ku yi magana, don bai cika son yana cin abinci ana yi mashi magana ba” hajiya sarah ce ta fada,
Kafin dr shureim ya bata amsa muryar Alhaji musa ta katse mashi hanzarinshi”Shureim ina jin ka, faɗi abunda ya kawo ka”
Ba ƙaramin daɗi Yaji ba, da fara’arshi ya fara magana”uncle bansani ba, ko daddy ya kira ka awaya ya sanar dakai abun farin cikin daya faru a daren Jiya” sai da ya ambacin hakan tukunna alhaji musa Ya ɗago da ido yana dubanshi alamar yana son jin ƙarashen zancen
“Ƴar uwata Benazir ta dawo gida a daren Jiya ƙarfe goma sha biyu na dare!!!”
Tsantsar mamaki da al’ajabi ne Ya bayyana akan fuskar alhaji musa, sai dai babu alamun zai furta magana sai faman jinjina kanshi yake yi.
Hajiya sarah kuwa Tsabar farin ciki mikewa tayi tsaye tare da ɗaga hannyenta sama tana ambaton”ALHAMDULILLAH!! wayyo Allah shureim Allah Yasa ba wasa kake Yi min, dagaske Benazir ta dawo gida da ƙafafuwanta ko kawota akayi”?
Shureim na murmushi yace”da kanta ta dawo gida, kuma abun mamaki tana ta sambatu tana ambaton sunan daddy da mommy da mijinta da ƴarta, kuma muna hasashen kurciya ne akayi mata da har ta gudu tsawon shekaru bata dawo gida ba, shiyasa nake so inje jos din Yanzu.......”
Hawayene suka wanke fuskar Hajiya sarah, Muryarta na rawa ta furta”shureim nima zan bika muje jos din, nasan shima uncle din naka zai je sai mu tafi atare...” kafin ta ƙare maganar Alhaji musa ya dakatar da ita ta hanyar cewa”Ya isa haka? Kinsan bana son shouting” shiru suka yi gaba ɗayansu, duk suka sha jinin jikinsu.
Kallon shureim yayi”ina zaka je da safen nan, naga ka shirya ga key din mota a hannu”?
Cikin sanyin murya yace”jos zan tafi, Inason ganin benazir”

Ta6e baki Alhaji musa yayi, tsawon mintuna ɗakin yai tsita, saida ya mula yasha iska tukunna yace”zanyi waya da yaya ubaid din, basai kaje jos din ba, zansa su zo nan abuja...” har saida gaban shureim Ya faɗi jin abinda Yace, bashi ba hatta Hajiya sarah arude take duban fuskarshi, kallon mara hankali take binshi da shi don wanna Yafi ƙarfin a kira shi da izzah, Tayaya zai nuna ƙarfin iko akan Yayanshi? Waye ya dace yazo gidan wani? Almost 16years yarinya ta 6ace sai Jiya ta dawo ƙarfe sha biyu na dare ko kaɗan bai nuna danuwarshi ba, kuma babu alamun zai je ya taya yayanshi murnar ganin yarsu da suka yi?
Muryarta na rawa ta furta”am..amma hakan bai dace ba, nayi mamaki daka furta wannan maganar, kodai baka ji abunda shureim Yake faɗi bane? Ƴar wurin Yayanka benazir ce data 6ace tsawon shekaru ta dawo gida a daren jiya ƙarfe goma sha biyu na dare Yakama ka tashi ka shirya mu tafi” da buɗar bakinshi sai cewa yai”Umarni kike bani”? Da ƙarfin hali Ta furta”A’a kawai ina ƙoƙarin faɗa maka abunda Ya dace ne” tamkar zaki Haka ya yunƙura ya miƙe Ya dubi fuskar shureim da mamaki Ya gama kamashi
“Nace bazaka je jos ba, ka koma ɗaki ka zauna, zansa Iyayen naka su zo tare da ƴar uwar taka abuja” gyaɗa kai dr shureim yayi jiki amace yace”toh uncle, na hakura, zan jira su zo ɗin” ƙwalla ce ta ciko idanuwanshi da sauri Ya juya ya fuce daga dakin.
Bayan fitarshi Alhaji musa Ya nuna Hajiya sarah da Yatsan hannunshi”koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara shiga tsakanina da shureim idan muna magana, abune da ya shafeni da dangina banaki ba, don haka ki kiyaye” yana gama fadin hakan a fusace yakai hannu ya yago tissue ya goge bakinsa ya nufi cikin dakin.
Jiki asanyaye hajiya sarah ta zauna saman sofa din, lamarin Ya ɗaure mata kai, wannan rashin adalcin har ina? Meyasa zai dinga iko da yayanshi? Ko dan Yana da dukiya ne? girgiza kai tayi ahankali ta furta”wannan ba adalci bane” ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Bawan Allah dr shureim abun duniya ya isheshi, Uncle musa Ya bashi mamaki, bai ta6a jin haushinshi ba sai yau daya nuna ƙarfin iko akan iyayenshi, Ya fahimci ma bai damu da dawowar benazir ba saboda babu annuri akan fuskarshi duk da yasan halin shi ne hakan, amma yaji ɗaci aranshi, don me zai dinga juya mahaifinshi son ranshi bayan shine agaba dashi, ko a shekaru Alhaji ubaid Ya zarce Alhaji musa nesa ba kusa ba saboda shi ba wasu shekaru gare shi ba, shiyasa ko a jam’iyarsu ake kiranshi da ƙaraminsu babbansu. Abun ya ɗaurewa Dr. Shureim kai, har ya fara tunani kodan Yana da dukiyane shiyasa yake sarrafa kowa yadda yake so? In banda rashin ta ido har zai Iya buɗe baki yace zai kira iyayan nashi suzo abuja maimakon shi ya tattara iyalansa suje can jos din su tayasu murnar dawowar ƴar su, Anya kuwa Uncle musa bai fara shan ƙwaya ba”? Saƙe saƙe zuciyar shureim take Yi mashi hakanan ya samu kanshi da kokwanton uncle din nasa.
“Shureim dan Allah ka yi hakuri da abunda uncle dinka Ya faɗa maka, wallahi banji daɗi ba, bai kyauta ba, wannan ai ba adalci bane, bansan meyasa yake yin haka ba”
Muryar Hajiya sarah ce ta katse mashi zancen zucin nashi, har ya kusa shiga ɗakin shi Ya ci burki tare da Juyowa baya yana dubanta
Damuwace ƙarara akan fuskarta, kamar yadda shima tashi fuskar damuwarce
Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi da karyayyar murya ya furta”kada hakan ya dame ki mommy, da ace bansan halin uncle din nawa bane, amma nasani, shiyasa nake yi mashi uziri, bakomai zan jira su zo din kamar yadda ya fada”
Gyaɗa kai hajiya sarah tayi har cikin ranta bataji daɗin abin daya faru ba
“Bari na kira maka zeenatu, nasan zata ɗebe maka kewa, kafin isowarsu” still da murmushi akan fuskarshi Yace toh, zan jirata
Bayan tafiyarta, Ya shiga dakin shi, asaman gado ya jefar da key din hannun shi, Ya tu6e arab tur6an dinsa Ya jefar saman gado, Ya zauna daga gefe hannu bibbiyu ya zabga uban ta gumi takaici Ya ishe shi, mahaifinshi Yafi 6ata mashi rai saboda shine silar komai, da ace tun farko bai bari uncle musa ya raina shi ba da duk hakan bata faru ba.
Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar Zeenatu ta katse shi
“Yaya shureim ɗina” a hanzarce ya ɗago da ido yana dubanta, ta zumbula dogon hajibi har ƙasa Yake ja, ta ruƙo round plate mai ɗauke da mug, sai faman sakar mashi murmushi take yi, kwata kwata babu natsuwa atattare da ita, kafin shigowarta ɗakin mommynta ta faɗa mata xancen ganin benazir shiyasa take ta yin farin ciki, ita fa tun da take bata ta6a ganin benazir ba a hoto kaɗai tasanta saboda kafin guduwar benazir tana ƴar jinjirarta.
Ganin yadda take tafiya babu natsuwa yasa shin saurin motsa la66ansa da niyar ya dakata da ita, sai dai ina kafin yai yunƙurin yin hakan tuni tayi tuntu6e da takalmanshi daya cire a tsakar ɗakin, Mugs din data dauko yai tsalle sama Ya dira daman ƙafarta ruwan coffee mai zafi Ya ɗalli ƙafarta, zafin da tajine yasa ta jefar da plate din hannunta, ta duƙe saman floor tana kuka, da sauri Ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya zuƙunna tare da kai hannu ya damƙi ƙafafuwanta Ya soma tottofe su da addu’o’i, ta dage sai kuka take yi mashi, abunka ga farar fata wurin da ruwan coffeen Ya ta6a yayi jawur kamar zai fashe.
Kukanta duk Ya cika mashi kunnuwanshi, a hankali ya ɗago Yana dubanta, hawaye sun wanke fuskarta, lokaci ɗaya ya soma tariyo sambatun benazir tuni yaji jikinshi yai sanyi, haƙiƙa Yana matuƙar tausayin rayuwar ƴa mace, fuskar benazir ce ta dinga yi mashi gizo akan fuskar zeenatu, har baisan sa’adda Ya rungume ta a kirjinshi Ya zagoya da hannanyeshi saman bayanta, Yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi, ƙanƙameshi zeenatu tayi kamar zata koma cikin cikinsa, daddaɗan ƙamshin turarenshi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba, tuni ta haɗiye kukan da take yi, tayi kwance abunta sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, dr. Shureim sam ya manta dawa ya rungume a jikinshi, kewar benazir duk ta addabe shi, Ya jefa zeenatu cikin yanayi najin shauƙin shi, yayin da shi hankalinshi nacan wani wurin daban...............
Chapter 95 · 0% Book details