← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 152

Sashe 34

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Girgiza kai Angel ta yi”A’a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne kaɗai zai Iya shiga dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba,” bubbuga ƙafa jemimah tayi cikin shessheƙar kuka tace”wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki tada shi ki tada shi Kin ƙiya so kike mu mutu ko”?

Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel faɗa, ita kanta Angel kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar fusata.
“Angel ku tada shi mana” Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro kurkuku, baya magana daga Eh sai a’a, su kaɗai ne abunda Yake iya furtawa, amma yau sai gashi yayi masu magana, sun ɗanyi mamaki kuma sunji daɗi ga dukkan alamu sauƙi ya samu
Saboda maganar Haris yasa ta kai hannu ta bubbugi kafadar Danish, Muryar ta ƙasa ƙasa take furta sunanshi”Danish wake up! Ka tashi suna jin yunwa,” shiru bai motsa ba, Kusan sau biyar tana yi mashi magana har acikin kunnanshi takai bakinta

Nan fa gabanta ya fara faɗuwa, Parveen tace”ki buge shi mana wata’ƙil ya farka” Ba tare da ta kalli parveen ba tace”bazan Iya ba” ta ambaci hakan tare da cigaba da kwala mashi kira.

“Angel nauyin bacci ne da shi, Ba haka yakamata Ki tayar dashi ba, let me help u, “ Gabriel ne ya ambaci Hakan, Sai da ya fara janye azeeza daga jikinshi, tukunna Ya matsa gaban shimfiɗar Danish, bubbuga kafadarshi ya yi Da ƙarfi haɗi da ambaton Sunanshi”Danish! Danish!” yadda yake kware murya hatta su kansu sautin Ya cikasu, amma wani iko na Allah Danish ko girgiza Bai yi ba, Zuciyar Angel a jagule ta ɗaura Kunnanta saitin ƙirjinshi Bayan ta yaye mashi bargon, jin heart beat ɗinsa yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya sai dai ta yi mamakin dalilin rashin farkawarshi, Hankalin sauran ƴan uwan Yaƙi kwanciya, Gaba ɗaya suka dawo kewaye da shimfidarshi Kowa Ya zuƙunna
Su Azeeza har sun fara shessheƙar kuka suna faɗin Wayyo Allah Danish ɗinmu meke damunka, dan Allah ka farka ka yi mana magana ko hankalin mu ya kwanta, Mu mun haƙura ma da abinci kai kawai muke so ka tashi.

“Ko dai suma ya yi ne? Ku duba cikin gorar ruwan mu idan akwai sauran ruwa ku ɗauko Mu yayyafa mashi” Gabriel ne yai maganar cikin rashin kwanciyar hankali, Angel tace”a’a kada ku watsa mashi ruwa, Zuciyarshi fa tana bugawa, bacci ya ke yi, kunsan Danish da nauyin bacci, Balle kuma da ya ɗauki tsawon kwanaki bai runtsa ba,’ ɗaya bayan ɗaya suke jogana kunnansu saman kirjinshi don su ji idan zuciyarshi na bugawa, Hankalinsu Ya ɗan kwanta da jin sautin heart beat din nashi.
“Nasan nan bada jimawa ba zai farka, Mu ɗan ƙara haƙuri” Miƙewa Jemimah tayi tare da bubbuga ƙafarta, abunka ga yaro ba haƙuri, Yunwa ce ta addabeta, Juyawa tayi gaba ɗaya suka bi bayanta da kallo, agaban korayen ciyayen dake shimfiɗe a wurin ta tsugunna, ta soma tsigowa tana turawa abaki tana ci, hakan da tayi ne ya tuna masu da Ganyen da ake basu a prison, aiko da sauri batul da Parveen da azeeza suka mimmiƙe agaban jamimah su ka zuƙunna kamar akuyoyi haka suke cizgar ciyawa suna ci, tsawa Angel da daka masu”Meye haka dan Allah? Kunsan wani irin ganye ne ku ke ci? Ku daina” a tsawace ta ƙarasa maganar, ta mike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana kwace ciyawar da suka damƙa a hannun su, Fashe mata da kuka Parveen da jemimah su ka yi Nan take taji zuciyarta ta karya, cikin shessheƙar kuka suke faɗin ba za su iya jurewa ba, yunwa ce ta addabe su, ta taimaka tabar su su ci ganyen, suna jin daɗin shi ahaka.
Idanuwanta acike tab da ƙwalla tace”Is ok, Bari na shiga cikin dajin in nemo mana abincin da zamu ci,” miƙewa Gabriel yai”Zan bi ki Angel” girgiza mashi kai tai”A’a gabriel, Ka zauna ka kula da su Azeeza, Yanzu zan dawo” ba don yaso ba ya amsa mata da toh, Kallon sauran Ƴan uwan nasu tayi”Javed Naufal, Ku kula da su Azeeza, Yanzu zanje na dawo,” Naufal yace”meyasa zaki tafi ke kaɗai, bayan kin faɗa mana mu yi takatsantsan da dajin nan akwai mugayen halittun da zasu Iya cutar damu, why angel? Gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ke kaɗai ba, sai dai mu tafi mu duka,” Yai maganar tare da miƙewa, Javed ma Ya miƙe, haris ne kaɗai Ya rage a zaune yana sauraronsu.
Ita kanta gabanta faɗuwa yake yi gani ta ke yi kamar wani mugun abun zai iya faruwa da ita
Murmushi ta ƙaƙalo akan fuskarta duk don ta kwantar masu da hankulan su yasa tace”Bawani abu fa, da zarar nayi addu’a Allah zai tsare ni har inje in dawo lafiya, ku kwantar da hankalinku” girgiza kai Gabriel yai”bazai yiwu ba Angel, bana so wani abu ya same ki ta silar mu, idan har ba zaki bari mu bi ki ba, To ki bari Danish Ya farka Ya je da kanshi ya samo mana abincin....” tunkan ya ƙarasa maganar Angel tai saurin katse shi da cewa”su Azeeza yunwa su ke Ji, Na yadda Gabriel Ka raka ni mu tafi, ku kuma ku zauna yanzu zamu dawo” Hankalinsu ya ɗan kwanta, Atare da Gabriel Suka nufi Cikin dajin, Hannunta ruƙe da ƙaramin kwandon su, komawa su azeeza su ka yi abakin bishiya suna zaman jiran dawowarsu.

Cikin dajin suka kutsa suna tafiya suna dan tattauna fira a tsakaninsu, ta ko’ina bishiyoyine masu tsayi Da faɗi, Rassansu sun lullu6e wurin da inuwar su.

“Hankalinka ya kwanta ka biyo ni, ni ban san ma ina zamu dosa ba, Ka ta6a shiga daji”? Ta jefa mashi tambaya, girgiza mata kai yai alamar a’a”bazan Iya tunawa ba Angel, na manta da komai na rayuwata, amma inaji araina koda ace ban ta6a shigowa daji ba, zai iya yiwuwa na ta6a kallon shi a waya, Ni yanzu burina mu fita daga Cikin Dajin nan, Ko mun samu mu tona asirin zaluncin da ake yi a cikin kurkukun ƙaddara, Angel na damu da rashin ƴar uwata, ina tsoron kafin mu yi nasara su kashe min ita” yayin da yake yin maganar yanayin fuskarshi ne Ya canza, abun ba ƙaramin ta6a zuciyarshi yake yi ba duk in ya tuna da ƴar uwarshi Gabriellah.
Cikin nuna jin tausayin shi angel tace”ka kwantar da hankalin ka, Idan Allah yasa mai tsawaicin kwanace zamu ganta, in kuma ta riga mu gidan gaskiya, Allah Ya jiƙanta, yana daga cikin ƙaddarar bawa, ba dole ya rayu da abunda ya ke so ba, wata rana ma kowa zai mutu ba wanda za’a bari gadin duniyar.......” fira ta yi daɗi sai nutsawa suke Yi, cikin Dajin ba tare da sunsan inda zasu dosa ba, Ga wata iska mai daɗi da ta ke kaɗawa, wasa wasa Ƙarfin iskar sai ƙaruwa ya ke Yi, ta cika masu idanuwansu daƙyar suke buɗe su.
Chapter 34 · 0% Book details