← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 152

Sashe 120

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin fahimtar kalaman big guy Boss man yace”bazai yiwu ba, Ƴata fa aka kulle aɗaki ɗaya da maciji, Idan ya kashe min itafa” dafa kafaɗarshi Owais Yai da hannu ɗaya”kadaina kiranshi maciji, mutunne, bazan iya yin abunda zai cutar maka da ƴarka ba, Kamar yarda kake jinta nima haka nake jinta, fatan ka fahimce ni” gyada kai Yai still hankalinshi bai kwanta ba.
“A wani daki ka kulle su”?
Atakaice owais Ya furta”A dakin shi” jiki na rawa boss man Ya watsa da gudu ya nufi upstair.
Chief owais Ya maida dubanshi ga Big guy, “Things are starting to get out of control, and I don’t know what to do now. But I want to see his brother, maybe he can control him. kaje ka zo dashi” ya faɗa in a cool voice, amsa mashi yai da toh, da sauri Ya juya ya fuce daga ɗakin, Kallon sauran jami’an yai”ku koma bakin aikin ku, ku tabbatar kun kula sosai” Cikin girmamawa suka amsa mashi da toh, juyawa sukayi da sauri kowa Ya nufi hanyar komawa bakin aikinsa.
Shafa sumar kanshi yai da tafin hannun shi nadama, yanke shawarar komawa gidan obie yayi, yasan suna can hankali duk Ya tashi, ba lallai su iya runtsawa ba.
Cikin takun sauri Ya fita daga part din, Ya nufi ɗaya daga cikin motocinsu, wani jami’i ne Ya nufeshi da sauri Ya buɗe mashi motar ya shiga a mazaunin baya, shi kuma ya zauna a driver’s seat, yai ma motar key ya tashe ta, suka nufi cikin Obie estate......

Unaisa tana akwance idanuwanta sun kumbura suntum, kumatuntu sunyi jawur saboda kukan da tasha, busassun hawayene saman fuskarta, ta lumshe idanuwanta akan giant snake din daya ɗaura kanshi saman kirjinta, karatun qur’ani take raira mashi cikin disasshiyar muryarta daƙyar sautin ke fita, macijin Yayi lamo sai ƙara narke mata yake Yi, ga dukkan alamu yana sauraronta.
Da karfi tajiyo muryar boss man Yana kwaɗa mata kira daga waje Unaisah, Unaisah!!.
A hankali tasoma ƙokarin raba jikinta daga na macijin, ta lalla6a ta sauko daga saman gadon tana cigaba da yin ƙira’ar al’qur’anin, agogon bangon ɗakin ta kalla almost 10 na dare.
A jikin glass door din Boss man Ya jingina yana leƙensu.
Ƙarasowa tayi gaban ƙofa suna fuskantar juna, batasan sa’adda ta fashe mashi da kuka ba, Cikin shessheƙar murya take fadin”kaga irin ƙaddarar da ta sami ɗan uwana ko? Nayi ƙoƙarin na fahintar dasu cewa mutunne amma sunƙi su gane, sai harbinshi suke Yi da bindiga”

Tsananin tausayine ya kamashi ganin yadda ta canza saboda damuwa.
Cikin kwantar da murya yace”Yana ina “?
Matsawa tayi daga bakin ƙofar, karaf idanuwanshi suka sauka akan giant snake din dake nannaɗe saman gadon kamar bacci yake yi.
“Unaisa bai cutar dake ba”? Tambayar daya jefa mata kenan, Girgiza mashi kai tayi”a’a baiyi min komai ba, dan Allah ka taimaka mashi, nasan kai kaɗaine zaka Iya fahimtana,”

Jinjina kanshi yaɗanyi”okey, Ki kwantar da hankalin ki, kidaina kuka bana son ganinki cikin damuwa”
Fuska amarairaice tace”dole in damu boss man, rayuwar ɗan uwana abun tausayice, bazasu ta6a ƙyale shi ba, tun yana jariri suke cutar dashi har izuwa girmanshi sunƙi su ƙyale bawan Allahn nan, mugaye in sha Allah bazasu ta6a yin nasara akanshi ba”
Idanuwanshi tuni sun cicciko tab da ƙwalla
“Dan Allah ka taimaka mashi, akwai ruwan zamzam da ake bashi na addu’a ina da tabbacin idan yasha zai dawo dai dai”
Cikin sanyin murya yace”A ina za’a same shi”?
“Ɗan uwanmune Ya bani address din gidan da zamu ɗauko, namanta takardar acikin aljihun uniform dina, ai kace min kayan suna a hannunku, idan ka duba zaka ga wandona launin baƙi, mu uku keda kalar kayan dani da batul saina danish, pls ka bincika ka dauko ta, Allah yasa bata faɗi ba, nasan ma zaiyi wuya asamu zam zam din koda an samu takardar adreshin”
“In sha Allah za’a nemo zam zam din, ki koma ki zauna amma pls kada ki bari ya cutar min dake” amsa mashi tayi da toh” ajiyar zuciya ya sauke, tamkar karya tafi yabarta haka yake ji, duk da Ya yarda Yaron bazai Iya cutar da ita ba, tunda gashi ya same su asaman gado ɗaya batare daya sare ta ba, shi tausayin yaron ma yake Ji.

Juyawa yai da sauri Ya nufi down stair.
Komawa tayi saman gadon ta haye, ta kwanta daga gefenshi taci gaba da yi mashi karatun qur’ani.

Da matsakaicin gudu motar chief ta ƙaraso bakin entry hall na shiga babban falon gidan baba Obie, dasauri jami’en Ya fito daga motar Ya zagaya other side Ya buɗe mashi murfin car din, Ya zuro kafarshi Ya nufi Cikin gidan da sauri, Kamar yadda yabarsu haka ya same su a tsaitsaye cirko cirko , damuwace ƙarara akan fuskokinsu, hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba idan har ba gawar macijin suka gani ba.

“Owais”! Obie ne ya ambaci sunan shi da mamaki akan fuskarshi.
Dagowa yai da kyawawan idanuwanshi ya daurasu akan faces dinsu, kamar yadda yake kallonsu haka suma suke binshi da kallo, Kamar yaune rana ta farko da suka fara ganin juna”
“Owais Ina macijin”? hateem ne ya jefa mashi tambayar.
Calmly ya furta”mun fitar dashi daga gidan” ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Senate lateef Yace”Wacece yarinyar dake atare dashi? Munji tana kuka tana fadin ɗan uwanta ba maciji bane shin dagaske ne”!
Jinjina kanshi yai alamar eh, ya ƙara da cewa”Ƴar uwarshi ce, ba maciji bane mutunne kamar kowa, ƙaddara ce ta afka mashi”
“Wai kana nufin ɗan mutunne ya rikiɗa ya koma maciji”? His excellency deen ne Ya jefa mashi tambayar, gaba dayansu sun ruɗe da jin maganar,
Abdul razak Yace”bazai yiwu ba, owais kodai ka fara shaye shaye ne? In bahaka ba ta ina mutun zai Iya komawa dabba kamar maciji? Ai sai dai idan ya kasance ba mutun bane shi”
Obie duk Yafi su firgita jikinshi yaƙi daina yin kerma
“Owais bana son ganin macijin nan, ku tabbatar kun fitar dashi daga gidan nan, Idan ba haka ba zai Iya cutar da rayuwar ahalina”
“Baba ka kwantar da hankalinka, zuwa gobe in sha Allah zan shigo muyi magana, nasan yanzu ko nayi maku bayani ba lallaibane ku fahimceni ba, ni kaina hankalina ba a kwance yake ba”
Girgiza kai obie yai”owais idan kaga na kwantar da hankalina to macijin nan baya acikin gidan nan, Ni ban ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, wai yaushema ka dawo kasar? Ita yarinyar dake tare da macijin ƴar wacece? A ina take zaune”?
Shiru yai yana duban face dinshi, sam bayason yawan surutu, abu kadan ke hasala shi, baisan amsar da zai basu ba, don ya fahimci hankulansu ba akwance suke ba.
Gyaran murya mai girma sharafudden Yai, hankalin owais ya dawo kan mahaifinshi”kada ka damu, ka koma bakin aikin ka My son, Ni na fahimce ka, kaje kawai zuwa gobe zamu nemaka donka zo ka warware mana rudanin da muke aciki” lumshe ido owais yai haƙika yaji dadin maganar mahaifinshi, dama yasan shi kadaine zai Iya fahimtar halin da yake aciki
Kafin Ya juya saida ya fara kallon Obie, wanda tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur, tausayin tsohon ne Ya kama shi, yayi matuƙar yin kewar kakanshi.
Matsawa yai kusa dashi Ya rungume shi saman faffadan ƙirjinshi, baba Obie Ya kankame owais tamkar zasu koma mutun ɗaya.
Cikin sigar lallashi yake yi mashi magana”nayi kewarka baba, kana araina, nasan ban kyauta maka ba, amma in sha Allah idan komai Ya lafa zuwa gobe zan shigo gidan” cikin sanyin murya obie Ya amsa mashi da toh, ji yake tamkar karya tafi yabarshi, yana matuƙar ƙaunar jikannan nashi.
Iyayenshi dake kallonsu, murmushi ne saman fuskokinsu.
Raba jikinshi yai daga na baba obie, yakai hannu Ya shafi dogon gemun shi, da zolaya ya furta”kakana nakaina, nifa da jarumta nasanka, kai ɗin Namijin duniya ne, dan Allah kada ka bani kunya, kada ganin macijin nan ya hanaka rintsawa adaren yau, kayi bacci ka huta gobe jikanka zaizo gareka, sabon cake zamu yanka atare”
Farin ciki Ya cika obinna, yayin da yake duban owais, yana dariya yace”ka wahalar dani, bakasan irin kewarka da nayi ba, Na ƙwallafa raina akan son ganinka, ka manta dani owais, gobe idan kazo har tsallan kwaɗi zan sanyaka” dariya Iyayenshi suka sanya, Owais yace”kowani horo zakayi min bazan musa ba, Na cancanci fiye da hakan, Ni zan tafi, ku kulamin da kakana, Make sure he sleeps peacefully tonight.” ya faɗa yana duban iyayenshi, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, owais ba ƙaramin burgesu yake Yi ba, saboda yana son mahaifinsu.
Juyawa yai da sauri ya nufi ƙofar fita daga falon, idanuwan kowan nansu akan bayanshi, Harya ɗaga kafa zai fuce, muryar prime minister ta dakatar dashi
“Owais! ina son yin magana dakai” a hankali Ya juya yana dubanshi, da sauri Hateem Ya nife shi, babu mai Iya jin abunda suke cewa saboda sunyi nesa da sauran mutanan.
Dafa kafadarshi yai da hannu ɗaya, tunkafin hateem yai magana owais ya riga shi furta”uncle sai kunyi hakuri dani, ka zo kasar bansamu lokaci nazo gaishe ka ba” murmushin gefen fuska yasakar mashi”ni wannan ba damuwata bace, nayi maka uziri saboda nasan yanayin aikin ku,’ ya faɗa yana dubanshi kafin yaci gaba da magana.
“Inaso ka faɗamin dagaskene macijin nan mutunne”?

Jinjina kai owais yai”dagaske ne mutunne ya rikida, matashin saurayi”
Shiru hateem yaɗanyi kafin ya kuma cewa”Ya sunanshi”?

“Danish” ataƙaice ya bashi amsa.
Chapter 120 · 0% Book details