Sashe 141
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowa Major yai daga front seat na motar, Yabi bayan Sir mubarak dake tafiya yana nufar inda nurses din zasu kai Dr jazz, duk inda ya gifta manyan likitocin dake zarya cikin girmamawa suke gaishe da shi, a bakin ƙofar emmergency room din suka dakata da yin tafiyar, damuwar duniya ta isheshi, ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, haƙika yaji takaicin bugun da yayi ma jazz bisa rashin sani.
“Yalla6ai, ka zauna” Major ne yai mashi maganar yana nuna mashi waiting seat dake jingine da bango
Girgiza kai Sir mubarak yai”bazan iya zama ba, Idan har jazz bai farfaɗo ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, Major ka tayani da addu’a Allah yasa yarona ya farka bana so wani abu ya same shi”
Cikin kwantar da murya major yace”Sir in sha Allah babu abunda zai same shi, zai ji sauƙi, ubangiji Allah ya bashi lafiya”
“Ameen” ya amsa mashi.
Tunda aka shiga da jazz cikin emmergency room, likitoci suka taru akanshi, yadda kasan zasu hana shi mutuwa idan tazo daukar shi.
After some minutes, Dr fawan Ya fito daga medical room din, sanye cikin shiga ta likitoci, fuskarshi da face mask, tunkan ya ƙaraso wurin su sir mubarak yai hanzarin nufarshi yana fadin”fawan ya farfado? Ko hanyar yanzu”?
Calmly dr fawan yace”daddy ka kwantar da hankalinka, har yanzu bamuyi nasarar farfaɗo dashi ba, jazz ya bugu sosai, yanzu dai muna ƙoƙarin ganin munyi mashi treatment din raunukan dake akan goshinsa, In sha Allah nan badajimawa ba zai farfaɗo, ina da tabbacin hakan” ya ƙare maganar yana duban fuskar sir mubarak, babu alamun zai kwantar da hankalinsa, fuskarshi duk ta yamutse.
Dr fawan baiyi mamakin ganin hakan ba, yasan da irin shaƙuwar dake atsakaninshi da jazz, dole ya damu.
Duk da yana jin shakkar shi saida yai ƙoƙarin jaraba tambayarshi ya akai jazz yaji mummunan rauni saman goshinsa.
Kasancewar baya acikin natsuwarshi, da kanshi ya labarta ma dr fawan abunda ya faru.
Dafe kai fawan yai da hannu ɗaya tunawa da ranar da sukazo asibitin suka tirkeshi kan ya fada masu abunda jazz yake aikatawa shi kanshi yayi tsammanin wani mugun abun Jazz yake kullawa ashe ba haka bane sun yi mashi mummunan zato.
Ruƙo hannun shi sir mubarak Yai”fawan ka taimaka min, bansan ya zanyi ba, ina jin fargabar jazz ya farfado ya juya min baya saboda bugun da nayi mashi nasan daƙyar zai fahimce ni, nayi kuskure fawan na yanke mashi hukuncin cikin fushi batare dana saurare shi ba” cikin rauni na murya ya ƙare maganar, tsananin tausayinshi ne Ya kama dr fawan, hatta major ya tausaya ma shi.
“Daddy, har abada bana tunanin jazz zai Iya juya maka baya, Saboda ni shaidane akan ƙaunar da yake yi maka, balle kuma baka da laifi, laifin shine dabai sanar dakai ba a matsayinka na mahaifinsa, sannan duk abun da kayi mashi daddy kayi ne saboda ba ka son ya jefa rayuwarshi cikin hatsari, ni aganina kayi abunda ya dace kowani uba na gari yayi, shine ya tsaya tsayin daka don ganin yaronshi bai 6ace hanya ba.....” tunda dr fawan ya fara magana sir mubarak ya natsu yana sauraronshi, major sai faman jinjina kanshi yake yi alamar gamsuwa da bayanin Dr fawan
Sai da ya kai aya a maganarshi kafin major ya daura da cewa”yalla6ai gaskiya ne abun da dr fawan ya ke gaya maka, kuskuren da mukayi bisa rashin sani ne, tun da kake da jazz baka ta6a nuna mashi wariya ko acikin ƴa’ƴanka ba sannan baka ta6a yi mashi koda tsawa bane don yayi maka badai dai ba, don haka bana tunanin jazz zai juya maka baya saboda abunda ya faru, zai fahimce ka kuma zai gane kuskuren shi”
Nauyayyar ajiyar zuciya sir mubarak ya sauke, fatanshi Allah yasa maganar su dr fawan ya tabbata, don bayason jazz ya guje shi saboda ƙaunar da yake yi mashi.
“Major ka kira layin Zaki ka faɗa mashi muna atare da jazz sai zuwa gobe zamu dawo gida”
“Okey Sir” Major ya faɗa tare da zaro wayarshi daga aljihu, Ya danna ma Zaki Kira, Bugu Uku kafin Yai picking, bayan sun gaisa Ya isar mashi da sakon Mahaifinsu kafin daga bisani su ka yi sallama.
“Daddy ku zauna mana, ko zamu shiga daga cikine ka kwanta a resting room dinmu”
Girgiza kai Sir mubarak Yai alamar a’a,
“Bazan Iya runtsawa ba, Nafi buƙatar farfaɗowar Jazz hankalina sai yafi kwanciya”
Gyaɗa kai Dr fawan yai”bari na koma ciki daddy” juyawa yai da sauri ya shiga medical room din, Sir mubarak Yana atsaye ya dan jingina bayanshi da bango, major yana daga gefenshi, idanuwansu sunyi masu nauyi, ga gajiyar hidimar shagalin da akayi ga bacci da damuwar halin da jazz yake aciki.
A ƙalla sun kwashe awanni a tsaye, dare ya nutsa sosai, a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin muryar jazz ya karaɗe kunnuwansu, da ƙarfi yake fadin”daddy zanyi maka bayani ka daina buguna, wayyo Allah kaina zai fashe zafi yake yi min”
A gigice Sir mubarak Ya nufi dakin da aka kwantar da shi da sauri major Ya take mashi baya suna shiga suka tarar da Dr Jazz zaune tsakiyar gadon hannayenshi biyu tallabe da kanshi dake a nannaɗe da bandage, gefen gadon dr fawan ne atsaye Yana lallashinshi, gaba ɗaya ya birkice sai sambatu yake yi masu.
A hanzarce Sir mubarak Ya zauna gefenshi, Muryarshi a raunace ya ambaci sunanshi”Jazz My son”
Har saida ya firgita jin muryar sir mubarak, adabarbarce yake dubanshi da rinannun idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur, abunka ga farar fata fuskarshi tayi ja la66ansa sunyi suntum bawan Allah Ya bugu ba kaɗan ba.
Ido cikin ido suke kallon juna,
“Am sorry jazz, na gane kuskurena na bugunka da nayi ba tare da nayi bincike ba, Dan Allah ka yafe min” a hankali ya ruƙo hannun jazz acikin nashi ya ruƙe shi sosai.
Babu alamun zai furta mashi kalma, sai faman jan numfashi yake yi haɗi da lumshe idanuwanshi har yanzu allurar da dr fawan yai mashi bata sake shi ba.
Daƙyar ya iya buɗe baki ya furta”meyasa ka buge ni daddy? Dama kaine kake bibiyata daddy? Laifin me nayi maka? Kai da kanka ka faɗamin ba zaka iya ta6a lafiyar jikina ba, kuma bazaka bari wani ya cutar dani na, Ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka yi min haka ba, sai gashi yau ka nemi ka raba ni da rayuwata.....” a wahalce ya ƙare maganar yana fitar da huci.
Girgiza kai sir mubarak yai hawaye tuni sun taru cikin idanuwanshi.
Muryarshi asanyaye ya ce”Jazz ba laifina bane abun da ya faru, rashin sani ne, Jazz kaine tun farko baka sanar dani game da aikin sirrin da kake yi ba, a tunanina ka ɗauke ni kamar mahaifinka wanda yai silar zuwanka duniya but why kake 6oye min abunda ya shafe ka? jazz kamanta alƙawarin da muka ɗaukarwa junanmu’? Runtse ido jazz yai hawaye suka soma wanke fuskarshi.
Cikin shessheƙar kuka ya furta”ban manta ba daddy, kayi hakuri, yaya Owais ne Yahana in faɗa maka, shiyasa ban gaya maka ba, nayi ƙoƙarin fahimtar dashi kuskuren yin hakan amma sai yace min kaima kasan da case din Yaran.......” jin wannan maganar yasa hankalin sir mubarak ya ƙara tashi aruɗe yake kallon fuskar jazz tamkar yana karanto wani abu, Major da dr fawan suka kalli juna, da alama sunyi mamakin jin abunda jazz ya furta, dafe kai sir mubarak yayi da hannu ɗaya tunawa da zancen case din yaran da sojojin ƙasar ghana suka nemi hukumar sojin nigeria data kar6i case din daga hannun su, a lokacin basu kar6i case dinba sai suka nemi hukumar Isod da su shiga lamarin yaran, bai ta6a ganinsu ba ko a hoto yadaisan da zancen, sannan baida masaniya akan aikin da owais ya ɗauki Jazz Na kula da lafiyar yaran shiyasa aka samu matsala.
Jinjina kai sir mubarak yayi, cike da danasanin hukuncin daya yanke mashi,
“Jazz ina ƙara baka haƙuri, dan Allah kada ka ruƙeni a zuciyarka, da ace bana sonka wallahi bazan damu da rayuwarka ba, amma saboda ƙaunar da nake yimaka ne yasa harna yi maka shisshigi......” a tsanake sir mubarak ya labarta mashi duk abunda ya faru tundaga rana ta farka daya fara jin shi yana waya a garden kan maganar kaji har zuwa ranar daya yi mashi la6e a toilet yajiyo shi yana fadin akasheta...
“Jazz kasan ba mummunan abu kake aikatawa ba, amma meyasa kake amfani da kalamai masu hatsarin gaske kamar kalmar kisa da naji kana faɗi”?
Numfashi jazz yaja kafin ya bashi amsa da cewa”saboda yaya Owais ya gargaɗeni akan kada na kuskura wani ya san aikin da nake yi, koda kuwa mommyna ne shiyasa nake yin amfani da waɗannan kalaman, lokacin da kaji nace bayasan hanyar da zai kashe ta ba, Ina nufin yasan hanyar da zai magance matsalarta, a lokacin Salsabeel ne ya kirani a waya, ya fada min haukan khadeeja ya motsa, shine nake fada mashi maganganun da kaji inayi”
“Wanene salsabeel”?
“Shine babban cikinsu, atare da yaran yake, ba ƙaramin mutun bane ya girmi yaya owais”
Shiru Sir mubarak yayi, still bai kawar da idanuwanshi daga kan fuskar jazz ba.
“Ya jikin naka? Ina fata babu inda keyi maka ciwo”?
Ɗaga mashi kai jazz yai alamar Eh.
“Yunwa fa”?
“Bana jin yunwa, ina son yin magana da mommyna”
“Ba zamu iya kirantaba a yanzu, tayi bacci, sai zuwa gobe zamu tafi gida”
Don dole jazz ya haƙura da sonyin magana da mommynsa.
A daren ranar major a resting room din dr jazz Ya zauna, shi kuma sir mubarak ya kasa tafiya yabar jazz, kan kafaɗarshi jazz ya ɗaura kanshi, anan bacci yai awon gaba da su manne da juna.
Ataƙaice kenan abunda Ya faru daren Jiya dangane da sir mubarak.
*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*