← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 152

Sashe 49

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ɗaure mata fuska yai”mommy kina goyan bayansa kenan, yaci gaba da kira na mata maza”? Girgiza mashi kai tai”A’a, Ai nafi kowa jin haushin inji ya kiraka da hakan, Yana ta6a min zuciyana, donni nasan namiji na haifa ba maca ba” murmushi Jazz Ya saki”to kice mashi ya daina”
“Zan buga mashi warning, kada ka damuwa” maƙe mata kafadai yai”Allah mommy ni nasani wasa kikeyi, saboda ke kanki shakkarshi kike ji ba zaki Iya buɗe baki ki yi mashi magana akan ya daina ba”
Jan kumatunshi tayi da hannunta In jiwa ya faɗa maka! Ni bana jin tsoronshi awaja ne mutane ke jin shakkarshi, da zarar ya shigo nake juya shi son raina, Har girki yana yi min” Baki asake Jazz ke kallonta
“Uncle mubarak ɗin”! Jinjina masa kai ta yi”ƙwarai kuwa, ae dukkan Namiji bawan matane,
Har ya buɗe baki zai ƙara magana, Wayar Aljihun wandonshi ta soma ruri, miƙewa yai da sauri ya curo wayar, bayan ya duba sunan mai kiran nashi ya ɗago tare da kallon mommynsa, Wanene ya kira”?

Bai amsa mata ba sai dai ya sakar mata murmushi, da sauri Ya fito daga falon gidan, Kamar wani munafuki duk faɗin gidan bai isheshi ba sai da ya shiga garden tukunna ya dakata da yin tafiyar, Yai picking call ɗin jiki na rawa ya kara ta akan kunnansa, Kirari ya soma yiwa wanda ya kira shi wayar tamkar maroƙi,
“Yalla6ai Kajin nan suna nan cikin ƙoshin Lafiya, Suna samun kyakkyawar kulawa yadda ya dace,” dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana sauraron muryar mai magana,
“Ana basu hatsi yalla6ai mai rai da lafiya, Yanzu haka idan nagama magana da mama zan tafi gidan gona domin duba lafiyarsu,” sai faman sakin murmushi yake yi, aladabce yake yin maganar
‘kasan kajin turawa saida hatsi mai kyau, Gaskiya basu da matsala yalla6ai, biyu daga cikinsu ne kaɗai suke neman gazawa, shi zakaran ciwon nashi Ya lafa, sauran Kajin muna nan muna basu kyakkyawar kulawa, in sha Allah zasu samu lafiya harma asamu nayin farfesun sallah”

Tuntsirewa dr Jazz yai da dariya hada dafe ciki.
duk wannan surutun da ya ke yi acikin waya baisan Sir Mubarak na tsaye abayanshi ba, daga shi sai gajeran wando, Da singlet fara, hannunshi ɗaya ruƙe da Cup na coffee

Mamaki ne ƙarara akan fuskarshi Jin dr jazz na Zancan kajin turawa awaya

“Okey toh, Zuwa anjima idan nashiga gidan Gonar zan Kiraka Awaya” Daga haka sukayi sallama, Juyawar da zaiyi karaf suka haɗa ido da sir mubarak, tuni yasha jinin jikinsa, Duƙar da kai ƙasa yai ido ya raina fata
“Jazz! Dawa kake magana a waya? Kajin menene naji ana magana akai? Ni dai A iya sanina likitan mutane ne kai bana dabbobi ba” sosa ƙeya jazz yai, mirya dabarbarce yake faɗin”am...umm..dama “ Ya rasa ta ina zai taro zancen,
Kallon tuhuma Sir mubarak ke jafa mashi hakan yasashi yin saurin fauzewa
“daddy, Ni da abokina ne dr fawan muka buɗe gidan gona, kajin turawa ne muke kiwo, wasu ne babu lafiya shine ya kira muna tattaunawa game da yadda zamu shawo kan matsalar”
Ajiyar zuciya Sir Mubarak Ya sauke”Okey, mu shiga gidan” yai maganar tare da miƙa mashi Cup din hannunsa, da sauri jazz Ya kar6a Yana sha atare suka nufi gidan sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.

*GIDAN ƊAN IYA*

Mahboob ne ke ta faman zuba sauri Yana tunkarar harabar ajiye motocin su, ya ɗauki wankan shadda, tunkan Ya ƙarasa idonshi ya sauka akan motar Uncle abdallah, ƙura ido yai yana kallon bayan motar sunanta Ya karanta, Aranshi Ya ayyana lallai mutanan nan ba ƙananun shaggu bane wannan mota haka mai tsada! saboda almubazzaranci da rashin sanin ciwon kuɗi, Ina laifin ko ƴar ƙaramar honda mutun ya saya ya wadatar, mutane sun ɗaurewa ƙaryar arziƙi wurin zama, Allah dai ya shirya mu, ae ni wlh ko nayi arziƙi ban Iya fidda kuɗina in sayi mota, na ƙwammace duk inda zanje in taka da ƙafata, idan ma da nisa ne ƙwara in biya kuɗi In hau motar Haya, Ita ma wannan motar da nake amfani da ita ba don babansu abokina ne ya bani kyautarta ba kuma ina ganin mutuncin shi saboda ya ji tausayina ya siyamin ganin ina hawa motar haya yasin da tuni na jima da siyar da ita’ Shi kaɗai ya ke yin sambatunsa, Har ya ƙarasa gaban motarshi Ya buɗe front seat Ya shiga Ciki Yana ƴan dube dube, da alama wani abu yake nema, saƙo da lungu na motar yake ta bincikawa, har ƙarkashin seat, tuni ya haɗa uban gumi.

“Ina na ajiye zoben nan Jiya? Ko dai ban shigo da shi mota bane? fuskarshi a hautsine Ya jefawa kanshi tambayar, zurfin tunani ya shiga yi still bai tunano inda ya ajiye shi ba, A ƙarshe Ya soma tunanin kodai Ya shigar da shi ɗaki ne,

Fitowa yai daga cikin motar Ya datse murfin, Jiki na 6ari ya nufi cikin gidan.

Abie da Uncle ɗan Iya ne zaune a saman sofas na palourn tare da Uncle abdallah, Sun nutsa suna tattaunawa dangane da 6acewarsu tajuddeen, Mahboob Ya faɗo falon Ko kallo basu ishe shi ba hankalin shi na akan zoben shi da bai gani ba.

“Wancan ba mahboob bane? Kamar naso na wayi fuskarshi” Uncle abdalla ne yai maganar,

Girgiza kai uncle ɗan Iya yayi Yayin da yake bin bayan mahboob dake ƙoƙarin karya kwana zai nufi sashen ɗakinsa
“Shine, halan bai gaishe ka ba”?

Murmushi ɗauke akan fuskar Uncle Abdalla yace”Tun da muka zo ban yi tozali da shi ba, sai dai naji labarin shi awurin junaid”

Cikin nuna 6acin rai Ɗan Iya yace”baida wayau ne ai ni bansan baizo ya gaishe ka ba, bari ya fito daga ɗakin ɗan rainin wayau, Zahra tafi shi hankali”

Abie yace”Ƙuruciyace ke damunshi, Zahra kuma ae tafi shi shekaru baza a haɗata da shi ba”
Ɗan Iya yace”babu wata ƙuruciya atare da shi, Sarai yasan me yake yi sai girman jiki ba wayau” da alama Ranshi ya 6aci da rashin gaishe da uncle abdallah da baiyi ba.

Kafin wani daga cikinsu ya ƙara yin magana Hajiya adama ta fito daga ɗaki hannunta ɗauke da baby junaid, tun da ya dawo daga school a wurinta ya wuni ya hanata sakat duk inda za ta je ƙafarta kafarshi toilet ne kaɗai yake bari ta shiga, Ta canza Kayan jikinta zuwa atampa riga da skirt, Ta yafa mayafi akanta, kafin ta ƙarasa shiga palourn Mamie ta fito daga ɗakin Ummi su biyu ganinta yasa suka nufi wurinta fuskokin kowannansu da fara’a suka soma gaisawa da junansu

Atare suka ƙarasa shiga palourn, Kowa ya samu wuri ya zauna, Kafin suka fara gaishe da Mazajensu, miƙa ma junaid hannu uncle abdallah yai”zonan kyakkyawan Jikana mu gaisa,” da sauri Junaid ya sauko daga saman laps din Hajiya adama ya nufi sofa ɗin da uncle abdalla yake azaune Ya haye saman jikinshi yana faman sakar mashi murmushi, shafa fuskarshi yai da tafin hannunshi”Masha Allah mutumina, Ka tashi lafiya? Fadamin meyasa baka je school ba yau? Sannan baka bi mu zuwa masallacin Juma’a ba” Zaro ido Junaid yai haɗi da ɗan girgiza kanshi muryarshi da shagwa6e yace”nafa je, ae yau da wuri ake tada mu duk ranar juma’a, kuma ni ai ban isa zuwa masallaci ba inji mommy” maganarshi ba ƙaramin ƙayatar da su take yi ba, musamman In ya haɗa da shagwa6a,

“Junaid kaji tsoron Allah, Aneelerh ce ta faɗa maka haka? Faɗamin gaskiya ka dai san me ƙarya ɗan wuta ne” jin haka yasa shi saurin sanya tafukan hannayenshi biyu ya toshe fuskarshi Yana tiƙar dariya” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta”ba ita bane, ae malaminmu ne yace mu ƙananu ne bamu isa ɗaukar zunubi ba” gaba ɗaya suka saki dariya, bayan sun tsagaita da yin dariyar ne, Uncle ɗan Iya yai masu gyaran murya hakan yasa suka dawo da dubansu gare shi.

“Dama yanzu nake shirin aikawa a kira mun ku, don mu haɗu duka muyi magana, Kafin mu shiga cikin zancen Ina ƙara yiwa baƙinmu barka da zuwa fatan kun wayi gari lafiya” da fara’a Hajiya adama ta amsa mashi a mutunce

Mami tace”tun ɗazu da safe take son yin magana mun fara sai nace ta bari idan kuka dawo daga masallacin juma’a zaifi mu haɗu mu duka mu tattauna tunda abune daya shafi kowannanmu da buƙatar aji shawara daga bakin kowa”

Jinjina kai Abie yai”hakane, Yanzu Ina aneelerhn take”?

“Tana a ɗakin zahra, Bari na shiga na kirata” kafin ta mike muryar junaid ta katse mata hanzarinta.
“Ni zan Kirata” Bai jira amsarta ba, Ya sauko da gudu Ya nufi Ɗakinsu, uncle abdallah ne ya ɗan ɗaga murya yana yi mashi faɗan ya daina gudu kada ya faɗi yaji ciwo, Jin haka yasa shi dakatawa da yin gudun ya soma yin tafiya a tsanake
Chapter 49 · 0% Book details