← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 152

Sashe 76

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin Batul ta sanya baki”tun da ya nuna bayaso mu ƙyaleshi, damu da shi duk abu ɗayane, ko da ace baiyi ba mu zamu yi mashi, hakan ma ya wadatar” Angel bata ji daɗi ƙin Yin addu’a da yai ba, addu’oi’ ta soma karanto masu suna amsa mata da ameen ameen, idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, bayan sun Kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, banda Angel maimakon ta shafa addu’ar da tayi saman fuskarta, sai ta shafa ma danish saman sumar kanshi, a hankali ya ɗago da idanuwanshi yana duban fuskarta, harara ta watsa mashi tare da murguɗa mashi baki, hakan da tayi ba ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, muryarshi ƙasa ƙasa ya furta mata”thank u” ta6e mashi baki tayi”kada ka yi tunanin na damu dakai,” ƙayataccen murmushin gefen fuska yasakar mata, Su Batul sun natsu suna kallonsu.

Muryar Dr. laura ce ta katse masu hanzarinsu”Congratulation! My lovely Children Ina tayaku murnar farkawar ɗan uwan ku daga bacci, banjima da shigowa asibitin ba, dr Harry ke faɗamin cewa ɗan uwanku Danish Ya farka, wannan abun farin Ciki ne” ta ƙarasa maganar, a yayin da take ƙarasowa Gaban gadon Danish. Fararen idanuwanta dake asanye cikin farin glass ta ɗaura su kan face dinshi.

“An sanar dani cewa Baya kula kowa sai ƴan uwanshi, dagaske ne masoyiya Angel? Tayi tambayar tare da kallon Angel

Da fara’a akan fuskar Angel ta amsa mata da cewa “Jiya ne amma yau ya saki jiki, zai Iya magana da kowa”

Dr laura tace”Anya kuwa? Naga ko kallona baisan Yi, danish Ya jikin naka? Ko akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka”? Tayi tambayar cikin ƙagara da son jin muryarshi
Cikin raɗa Angel ta furta mashi”danish pls kayi mata magana, sun taimake mu, kuma suna da mutunci” kamar wanda akayi ma dole daƙyar ya iya motsa lips dinsa ya furta”da sauƙi babu inda keyi mini ciwo,”

Dr Laura taji daɗin maganarshi”ina fata kaci abinci babu yunwa atare dakai”? Ɗaga mata kai yai alamar eh
Ta furta”okey, amma meyasa jiya baka ba likitoci damar duba lafiyarka ba”?
A takure yake yi mata magana”saboda lafiyata ƙalau, bana buƙatar a duba ni,” Jinjina kai ta ɗanyi tayi mamakin Halinshi, basu ta6a samun patient irin shi ba.

Muryar Angel ce ta janyo hankalinta ga dubanta”Aunty, mun gode sosai da kulawarku agaremu, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku,” tayi mata maganar ne don ta mantar da ita zancen yi ma Danish maganar duba Lafiyar Jikinshi.

“kada ki damu masoyiya Angel, aikin mun e kula da lafiyarku kuma Alhamdulillah, Naga Jiki yayi kyau Allah ya ƙara Lafiya,” ta ƙare maganar tare da kallon Azeeza da jemimah”My twins, Ya jikin naku” atare suka haɗa baki” da sauƙi” kafin ta ɗaura idonta kan Parveen da sauri ta 6oye Ayabar dake a hannunta, dariya dr laura ta ɗan saki”hmm ai na gani dama kin daina wahalar 6oye mini” duƙar da kai Parveen tayi fuskarta ɗauke da murmushi.

Kallonsu Gabriel Tayi”Ƴan samari, Jiki yayi kyau, badan sister dinku ta matsa akan son komawarku Nigeria ba, da a gidana zan killace ku, In cigaba da rainonku,” murmushi kowan nan su ya saki.

“Zan Koma Office, Ku kula mun da kanku” har ta juya zata fuce Angel tayi saurin cewa”Aunty, har yanzu sojojin basu kira ba naji su shiru basu zo sun duba mu ba”

Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba zato ba tsammani, Suka hango Dr. Mark tare da dr. brown sun nufo ƙofar ɗakin, Kusan a tare suka shigo.

Gaisawa suka Yi da dr laura, Cikin girmamawa su Angel suka gaishe da su, Bayan sun amsa masu, suka tayasu murnar farkawar ɗan uwansu

Kafin daga bisani Dr Mark Ya soma Yin magana”Dr. Ke muke nema, Sojojin nan sun Kira Awaya, idan ba damuwa zamu Iya zuwa office muyi magana”

Amsa mashi tayi da toh, ba tare da 6ata lokaci ba suka fuce daga ɗakin.

Hankalin Angel yaƙi kwanciya burinta taji me zasu tattauna, fatanta Allah yasa su amince da maganar maidasu Nigeria.

Bayan fitarsu ɗakin kaitsaye office din dr Laura suka nufa, kowan nan su ya samu wuri saman kujera Ya zauna suna fuskantar Juna da ita

“Ina sauraronku, me sojojin suke ce ne”? A ƙagare ta tambayesu
Dr mark Ne ya soma kora mata jawabi”Commender dinsu ne Ya kirani awaya, Ya sanar dani cewa Chief na Isod Ya Amince zai kar6i case din Yaran....” tunkan Ya ƙarasa maganar, dr laura tasaki murmushin farin ciki

“Bayan haka, sun ƙulla Yarjejeniya tsakanin ita ummin american da su sojojin, zuwa Anjima zasu zo asibitin domin shirya yaran, zasu ɗauke su zuwa gidanta, sai dai zamuyi kewarsu saboda Commender din ya faɗamin next week chief na isod zai bar ƙasar tare da yaran” ya ƙarasa maganar idonshi Akan dr laura, mood din fuskarta ya canza zuwa damuwa, ba ta yi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, zaman da su ka yi da su na kwana huɗu ba ƙaramin sabo su ka yi da juna ba, sai dai ta wani 6angaren taji daɗi kodan saboda Angel da ta roƙe ta akan ta taimaka masu su koma ƙasarsu.

“Dr lafiya? Naga kamar yanayin fuskarki Ya canza? Ko baki ji daɗin maganar bane”? dr. Mark ne yayi maganar ganin ta haɗe fuska, Murmushin yaƙe tasakar mashi
“No ba haka bane, Na saba da yaran ne, banaso su yi nesa dani, banyi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, inaso zan nemi alfarma abar mana su ko da one month ne su yi anan kafin su tafi”

Dr brown yace”ba zai yiwu ba dr, da ace case dinsu a hannun sojojin yake zamu Iya neman alfarmar abar mana yaran su zauna a wurinmu, sai dai kash sun riga da sun damƙa case din hannun chief na isod, kuma kinsan shi ba ɗan ƙasar nan bane, A ƙasar shi yake zaune Aiki ne mai muhimmanci ya kawoshi america, tun cikin weekend daya wuce yaso barin ƙasar, saboda case din Yaran Ya fasa tafiya, yanzu haka da nakeyi maki magana, yana shirye shiryen barin Washinton zai shigo garin mu saboda ya haɗa kan yaran ya tafi dasu, mutumin babu wasa a aikinsa, Baison 6ata lokaci.

Jikin dr. laura ba ƙaramin sanyi yai ba, tana son su Angel, ganin duk ta damune yasa Dr mark kwantar mata hankali”Tafiyarsu ba yana nufin mun rabu da su ba, Kada Ki manta Sojojin ƙasarmu ne suka tsince su, bayanan su da komai Yana a hannunsu, kuma zasu cigaba da bibiyar rayuwar yaran, wannan dalilinne ma yasa suka haɗasu da Ummin america.

Gyaɗa kai Dr Laura Tayi”Ni damuwata depression din dake damun yaran, da kuma Yaron dake fama da ciwon zuciya, Hankalina bai kwanta da Ummin america ba, Shin zata Iya bamu su kulawar da zata sanya su manta da damuwarsu? nafa santa bata da mutunci macace mai izza kuma ta shahara wurin Iya karuwanci.....” Damuwace ƙarara kan fuskar dr laura, idanuwanta tuni sun ciko tab da kwalla.

“Yaran sunfi buƙatar kulawar mace wadda tasan ciwon haihuwa, bawai karuwa ba! Wadda ta saba ƙwacewa matan aure mazajensu tana fasiƙanci da su! Yakamata Kuyi tunani akan hakan, Ni zanyima Commender din nasu magana, akan su canza masu wadda zata raine su, Yara fa har goma sha ɗaya za’a damka ma karuwa, gaskiya basuyi tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su” ranta amuƙar 6ace take Yin maganar.

Cikin kwantar da murya Dr mark yace”ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba”

Dr brown ya ɗaura da cewa”sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na karuwa ne, su kuma a matsayin ma’aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a damƙa mata amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba”

Gyaɗa kai Dr Laura Tayi”Shikenan na haƙura, bazan yi masu magana ba, amma inaso zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai kai”

“Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da ƙaunarsu, Har na fara jin kewarsu” acewar dr. Mark

Dr brown yace”aini har ƙasarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda damuwa, muna atare da su”

Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin aikinsa.

*DAULAR ALHAJI MUSA*

*Dr Shureim❤*

Ƴan kwanakin da yayi a gidan Uncle ɗin nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr. Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa, kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman ɗaki yakan fito ya zagaye gidan tare da zeenatu, yana matuƙar jin daɗin kulawar da take bashi, sun shaƙu da juna kamar sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta faɗo ɗakin shi yana cikin kallon hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece yake yawon kallo? Don ta fahimci ba ƙaramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba.

A Kishingiɗe yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko’ina ba, ko ƙofar bedroom dinsa bai leƙa ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba ɗaya hankalinsa na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya ɗaura saman pillow,
Chapter 76 · 0% Book details