← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 152

Sashe 140

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Owais fatan na sameka lafiya, tsawon lokaci bamu haɗuba, aiki ya 6oye ka,” Sheikh imam ne yai mashi maganar
Calmly ya furta”Ina lafiya, nayi missing dinka, amma naji dadin ganin ka yau, Ina fata uncle dina bai takura maka ba? Nasan shine Ya matsa maka akan zuwa Nigeria” da zolaya ya fada,
Shekh Imam Yace”kai dai bari, kamar yadda baiyi bacci ba adaren jiya nima haka ya hanani Yin bacci, babu shiri yasa na fara shirye shiryen zuwa Nigeria hada ƙoƙarin turamin jirgin da zai ɗaukoni” Da zolaya yai maganar,
Hateem dake sauraronsu, baice komai ba sai dai murmushin dake akan fuskarsa bai washe ba.
Dubanshi chief yai”uncle, sannu da zuwa, Mu shiga daga ciki, nabarku atsaye”
Atare suka jera zuwa babban falon gidan, saman sofa mai mazaunin mutun uku, prime minister da Sheikh imam suka zauna, Chief Owais Yana daga zaune kan 2 seater, Yayin da Big guy da Boss suke atsaye sun goya hannayensu saman kirjinsu.
Kallonsu chief Yai kafin Ya soma magana”Taj wannan uncle dina ne Prime minister Hateem na ƙasar Canada, Kai kaɗaine bakasan shi ba, wannan kuma Sheikh imam kenan, Aminin kakanmu Obie...”

Cire face mask din fuskarshi Yai, Cikin girmamawa ya soma gaishe da hateem”ina yi maku barka da zuwa, najima ina jin labarin prime minister awurin Owais sai dai ban ta6a ganinsa ba, ashe da rabon zamu haɗu, kuma tunda naga fuskarshi raina ya bani cewar Uncle dinka ne saboda kamanceceniyar dake a tsakaninku”

Ƙayataccen murmushi prime minister yasaki a yayin da yake kallon fuskar taj yace”Nagode da karramawarka agare ni, kuma naji dadin haɗuwa dakai, Ina fata zamu cigaba da yin zumunci a tsakaninmu”
Tajo yace”in sha Allah” har cikin ranshi mutumin ya kwanta mashi, kuma Yayi mamakin haɗuwarshi donshi a hoto yasanshi, kuma yayi mamakin sakar mashi fuska da ya yi a matsayinshi na babban mutun mai ruƙe da babban muƙamin shugaban ƙasar Canada, koda yake yasha ji awurin mutane cewa baida girman kai ko kaɗan, mutunne najama’a kowa nashine mai kudi da talaka awurinshi duk ɗayane.

Chief Owais Ya ɗaura dacewa”Uncle sunan shi Taj, Mahaifin Yarinyar nan, dana ta6a baka labari, ina fata ka gane shi”
Jinjina kai Hateem yai da mamaki akan face dinsa yace”masha Allah, ina ita yarinyar take ne? An gano ta”?

Ɗaga mashi kai yai alamar eh.
“Na tayaka murna my son, Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Ina fata Yaya sharafudden Yasan da maganar mahaifinta da kuma ita kanta yarinyar”!?

Chief owais Yace”Ya sani, na faɗa mashi, sai dai basu ta6a haɗuwa da daddynta ba, amma na yanke shawarar zan haɗasu kwanan nan idan muka shawo kan matsalar yaron nan”
Ga dukkan alamu Hateem yaji dadin ganin tajuddeen, duba da yadda yake kallon shi.
Gyaran murya sheikh Imam yai masu”Idan kun gama magana ina jiranku, Kun ajiyeni kamar buhun masara, Yakamata ku bari in kammala aikina inyaso kunyi firar taku” gaba ɗaya suka sanya dariya banda Chief daya ɗan murmusa.
Prime minister yace”ay mana afwa ya sheikh, nayi kewar yarona, Mun jima bamu haɗu ba” Murmushi sheikh imam yasaki, da zolaya yace”wani yaro kake nufi? Wanda yahanaka runtsawa daren jiya? ko kuwa wanda kuke Yin fira da shi a yanzu”?
Prime minister yace”dukansu biyun nake kewa”
Sheikh imam yace”yanzu naji magana, bismillah owais Muje ka nuna min ɗakin da yaron yake” amsa mashi yai da okey
Atare suka miƙe tsaye tare da nufar Up stairs, tunkafin su ƙarasa ɗakin, suka soma jiyo kururuwar macijin Yana gurnani.
Sheikh Imam yace”Da alama Yasan da zuwana” murmushi kowannansu ya saki, abakin ƙofar ɗakin suka tsaya kafin su shiga sheikh imam Ya dubi Chief owais”naji kace akwai yarinya agidan nan ɗiyar mutumin da naji ka kira da taj ko”? Kafin owais ya bashi amsa Boss man ya riga shi cewa”ba ita kaɗai bace, akwai sauran ƴan uwanta dake rayuwa agidan”

Sheikh imam yace”Toh, ina buƙatar a killace su wuri ɗaya, sannan aja hankalinsu ta yadda baza su iya jin abun da ke faruwa cikin gidan ba, Idan ba haka ba zasu iya firgita arasa gane kansu” boss man ya amsa mashi da toh.
Kafin Ya dubi big guy”please kaje wajensu, ka aiwatar da abunda malam yace” da sauri big guy ya nufi hanyar komawa down stairs, Ya rage saura su uku.

“Bismillah mu shiga daga ciki” dafe ƙofar boss Yai, ta zuge a hankali kafin suka shiga dakin.

Jin motsin shigowarsu dakin Yaja hankalin salsabeel dake atsaye kai idonshi ga dubansu.

Hankalinsu na akan narkeken macijin dake zarya tsakiyar gadon wata irin kururuwa yake fitarwa yana huci.

Gaisawa sukayi da salsabeel, daga bisani, Chief Yai mashi alama da hannu, salsabeel Ya fahimci ƙarin bayani yake nema game da halin da Giant snake din yake aciki”

“Ni kaina bansan meke damun shi ba, Yanzu ya farka daga bacci, Yana huci, zai Iya yiwuwa saboda rashin ganin ƴar uwarshi akusa dashi ne”

Hankalin prime minister hateem ba ƙaramin tashi yai ba, sai yanzu yaga girman macijin Ya wuce misali.

Sheikh Imam Yace”Saboda ni yake wannan hucin, ku dan bamu wuri zan fara aikina” babu musu suka fito daga dakin, anan second floor suka tsaya suna jiran tsammani
Bayan fitarsu ya rage saura sheikh imam da Macijin a ɗakin, Toilet Ya shiga jim kaɗan ya fito da alama alwala ya ɗauro, Bakin gadon Ya tsaya tare dakai hannu Ya damƙi bargon dake a nannaɗe kan mattress, manyan Addu’o’i ya soma karantowa Yana tottofe bargon, kafin ya fara yin karatun alƙur’ani, Yayin da idanuwanshi suke akan macijin dake ta ƙoƙarin saukowa daga saman gadon Hanyar guduwa yake nema sai dai ya kasa yin hakan saboda ɗaurewar da Sheikh imam Yayi mashi da karatun kur’anin da yake yi, Bayan Ya kammala yin ƙira’ar, Ya daddage Ya haye kan gadon, Ya kifa mashi bargon saman jikinshi, Ya daddanne shi da ƙafafuwanshi, da hannayenshi yabi ko’ina ya dafe, wata irin kururuwa macijin yake saki tamkar ana ƙona jikinshi da wuta, hatta waɗanda ke a wajen ɗaki saida suka jiyo sautin, Har saida prime minister ya dafe kunnanshi da tafin hannun shi.
Jami’an dake a kewaye da gidan da gudu suka shigo part din hannayensu ruƙe da bindigu, sunyi tunanin wani mugun abunne ke faruwa, daga saman bene Boss Man Yai masu magana akan su koma bakin aikinsu hakan yasa suka juya da sauri suka bar part din.

Sheikh Imam Ya hada uban gumi, zufa ta wanke fuskarshi duk da sanyin A.c na ɗakin, Yaƙi Sakin bargon daya daddanne Macijin, sai ƙoƙari yakeyi donya kubcema ɗaurin da yayi mashi.
Maƙoshin shekh imam tamkar zai 6allo tsabar yadda yake cigaba da karanta mashi ayoyin ƙur’ani tare da addu’o’in karya sihiri, Yaci gaba da tottofe bargon da yake kudundune.
Ba zato ba tsammani, suka soma jiyo wasu irin muryoyi na baƙaƙen shaiɗanun aljanu suna fadin”kashe ka zamuyi sheikh imam! Dole ka mutu tunda ka shiga sabgarmu, zaka mutu”
Da karfin hali sheikh imam yace”Idan kunga na mutu lokacin mutuwatane yayi don ubanku, Ni da Allah na dogara bada ku ba, Raina a hannunsa yake, Ku bakusa ku cutar dani ba, face da izninsa, Kunsan bana jin tsoronku tun fil azal......” bai ƙare maganarba, sautin dariyarsu Ya karaɗe ɗakin, tamkar ana buga ganga, Hankalinsu boss man ya tashi matuƙa, damuwarsu kada wani abu ya samu sheikh imam.
Cigaba da magana sukayi da kakkausar murya suke fadin”mutuwa zakayi sheikh Imam, ajalinka ne Yazo, kai ka sani ba’a shiga huruminmu a zauna lafiya, mun kashe ire irenka da dama waɗanda suka yi ƙoƙarin yi mana shisshigi, Sheikh Imam kadaina janyo mana ayoyin alkurni bazasu ta6a yin tasiri akanmu ba, Mu ba kalar shaiɗanun da ka saba ƙonawa bane”
Runtse ido sheikh imam yayi, jin numfashinshi na ƙoƙarin ɗaukewa tamkar an shaƙe mashi wuyanshi, idanuwanshi suka kaɗa jawur tamkar garwashin wuta, sautin muryarshi daƙyar yake fita ahaka yake kokarin cigaba da yi mashi karatun kur’anin..........”

“Hankalina bai kwantaba, Inajin fargabar wani abu ya sami malamin nan, Mutanan nan fa ba ƙananun shaidanu bane” salsabeel ne yai maganar.
Boss man yace”ni kaina fargaba nake ji, gaskiya akwai matsala, kada mu jefa rayuwarshi cikin hatsari,”
Duk maganganun da sukeyi akan kunnan Chief owais da prime minister Hateem, jikinsu yai sanyi babu mai magana acikin su.

Lokaci ɗaya bugun zuciyar Prime minister ya ƙaru, arude ya furta”ku buɗe kofar nan” ya fada yana nuna ƙofar dakin danish” da sauri Bossman Ya nufi ƙofar ya sanya hannu ya dafe glass din wani iko na Allah ƙofar taƙi buɗewa, gashi sunji shiru babu motsin sheikh imam da kuma kururuwar macijin.

“Babu lafiya, salsaleel zoka taimaka min mu buɗe ƙofar” matsawa salsabeel yayi gaban kofar, suka haɗa ƙarfi shida boss suka dinga bugun ƙofar taƙi buɗewa.

Da ƙarfi suke ambaton sunan sheikh imam shiru bai amsa masu ba, babu alamun motsinshi.

Hankali atashe Chief Owais Ya ɗago da ido suka kalli juna shida prime minister.

“Bana so wani abu ya sami malamin nan, Ni ne silar kiranshi daga sudan, Idan wani abu ya same shi bazanji dadi ba, zanyi danasani Owais, Yakamata kuyi wani abu akai” damuwace ƙarara akan fuskar Hateem.

“In sha Allah Uncle babu abunda zai faru da shi, ka kwantar da hankalin ka” chief na ƙarasa fadar hakan, Ya nufi ƙofar ɗakin, da sauri salsabeel Ya matsa mashi hanya, Boss man Yaja gefe ɗaya, bismilla ya furta da kyakkyawar niya, kafin ya daki ƙofar da kafaɗarshi, nan take ƙofar ta zuge da gudun gaske, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, salsabeel yayi mamakin ƙarfin owais.
An rasa wazai fara shiga dakin, kowa fargaban ganin abunda zai taras yake yi, hatta shi kanshi chief din....... 😳😳😳

*Something Unexpected*

*WAIWAYE🌹*

*A Obie International Hospital*

Emergency room

Abun da ya faru daren Jiya da Sir mubarak Ya dauki Dr jazz zuwa asibiti, tunkafin su ƙarasa Ya kira Dr fawan awaya ya sanar dashi game da zuwansu, tuni nurses sun fito da stretcher bed din da zasu dauke shi, motarsu nayin parking a harabar ajiye motocin asibitin, Sir mubarak Ya fito jiki na 6ari ya cuccu6i dr jazz ya daura shi kan gadon, A gaggauce nurses suka gungurashi zuwa Emmergency room.
Chapter 140 · 0% Book details