Sashe 61
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Junaid, daga yau karka kuskura ka ƙara ɗaga min kira kaji ko”? Ɗaga mata kai Yai alamar eh, tace”yanzu zan sanya number ɗin a black list, hankalina zaifi kwanciya’ ta yi maganar a yayin da take cigaba da daddana wayar hannunta, blocking number din tayi saida ta kammala baby junaid yace
“Mommy namanta ban gaya maki ba yace wai in faɗa maki daddyn um am....” natsuwa ta yi tana kallon shi,
“What”? Shine yace min wai ince maki daddyn ummm...” sam ya kasa tuna sunan duk ta ƙagara da sonjin ƙarashen sunan
“Kai nake sauraro ka fadamin mana”
“Wai ma daddyn.....” girgiza kai ya ɗanyi”mommy kaina ya cunkushe na manta, idan na tuna zan gaya maki”
Murmushine shimfiɗe saman la66anta, Idanuwanta akan face dinsa
“Shikenan My baby boy, yanzu faɗa mun Ina ka 6oye zoben Mahboob? Na duba cikin rigar pillow ban ganshi ba, yakamata mu maida mashi abunsa kada ayi mana kallon 6arayi”
Gatsina mata hanci junaid yai haɗi da murmura idanuwanshi yace”tab ae Allah bani bashi, Na angel ne na 6oye shi wani wuri inda ba wanda ya sani, Allah Angel zan baimawa shi, kuma kada ki fada ma kowa in baki so mu 6ata dake,”
Dariyace ƙumshe abakinta”kai junaid babu kyau fa, da guminsa ya sayi zoben taya zaka ce ba za ka bashi ba? Kana so Angel ɗinka ta sanya abun sata? Kayan haram da ba mallakin ka ba?
Girgiza mata kai yai”a’a mommy, to ai bani da kuɗin da zan siya mata wani”
Shafa sumar kanshi tayi”mommynka tana da kuɗi, zan siya maka wani but pls ka maida ma mahboob zoben shi kaji my boy”
Ɗaga mata kai yai”Toh zan maida mashi badan halinshi ba, kuma Allah idan ya ƙara cinye min chocolate ɗina saina sanya shi kuka” fashewa Aneelerh tayi da dariya, ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.
*DAULAR ALHAJI MUSA*
Ya kasa fita ko da ƙofar ɗakinsa ne, tun jiya da ya zo gidan baƙunta yake yi masu, fitowa yai daga Cikin bathroom jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, ya ɗaure igiyarta a tsakiyar cikinsa daga can ciki akwai short da ya sanya, sumar kansa ta manne ma fatarsa saboda lemar ruwan wankan daya jiƙata, Dr shureim ba dai kyau ba, ta ko’ina sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikinsa, ya ji daɗin dawowarshi gidan uncle ɗinsa baida wata damuwa, musamman tarbar da ya samu awurin Hajiya sarah, ta nuna farin cikin ganinshi kamar ɗan cikinta haka take tarairayarsa.
Walking slowly ya nufi dressing mirror Don Ya kimtsa kanshi
Gyaran muryar da aka yi mashi ne yasa shi yin saurin juyo wa baya don ganin wanene
Lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya yana kallon uncle ɗin nasa
Yana daga tsaye bakin ƙofa, kayan gym ne a jikinsa, short da riga sun ɗame jikinsa, mutumin akwai ƙira kamar ɗan wrestling.
Da fara’a akan fuskar shureim ya furta”My Uncle” yai maganar yayin da yake tunkarar shi, gabanshi sai faɗuwa yake yi ya rasa gane dalilin dayasa a duk lokacin da ya yi tozali da uncle din nashi sai yaji faduwar gaba.
Kyakkyawar fuskar Alhaji musa, mai ɗauke da ƙayataccen saje, ba murmushi sai dai yaɗan sakar mashi fuska.
“Fushi nakeyi da kai shureim baka iya takowa kazo ɗakina ka gaishe ni, ko dama jira kake inzo room ɗinka”? Cike da izza da nuna isa yake yin maganarsa.
Yawu shureim ya haɗiya”ba haka bane uncle, yanzu nake ƙoƙarin zuwa part ɗin naka”
Yamutsa fuska Yai”okey, nima na fadi ne kawai ba don wani abu ba, ko akwai abun da ka ke buƙata”?
Girgiza kai shureim yai”a’a aini ka gama min komai kawuna, nagode sosai da kulawarka agareni, Allah yabarmun kai” matsawa Alhaji musa yai dab dashi, Ya janyoshi a jikinshi yai hugging nashi tightly, in a whisper ya furta”idan akwai abun da kake buƙata ka sanar dani, idan ma baka Iya fadamin ka tura min ta text message, sannan akwai saƙo da za’a kawo maka zuwa anjima, ya ƙarasa maganar tare da raba jikinsu daga na juna.
Still face din Uncle musa ba fara’a, haka Allah ya halicce shi baida sakin fuska.
“Nagode sosai uncle, tun jiya da nazo gidan nan akayi min kyakkyawar tarba naji daɗin Hakan sosai”
“Shureim ba’ayi min godiya, next time kada ka ƙara” fuskarsa a ɗaure yai maganar
Cikin jin shakkar shi shureim ya furta”in sha Allah” ya ƙara da cewa”burina ka canza rayuwarka shureim, banason ganinka acikin damuwa, kaman ta duk wani abun da ya faru a rayuwarka, shiyasa na dawo dakai gidana saboda nasan zaka fi samun kwanciyar hankali, sannan Inaso naji ra’ayinka, bance ka bani amsa yanzu ba, nafi so sai ka natsu kayi nazari tukunna.
Jinjina kai shureim yai, idanuwanshi na kallon ƙasa, saboda ƙwarjinin alhaji musa bai iya jurar kallon fuskarsa.
“Bazan hana Ka Yin duk wani abu da za ka yi don jin daɗin rayuwarka ba, sai dai ban goyi bayan zamanka a cikin gida ba aiki ba, abu na biyu kuma Aure, kasan shi sunnah ce ta manzon Allah SAW, Aure yana ɗaga darajar mutun yazamto mai cikar kamala da natsuwa, rayuwarka zata canza idan ka yi aure, Na gaji da ganinka a matsayin tazuru” Yai maganar yana ɗaga mashi gira, da zolaya akan fuskarshi, kunyace ta hana shureim furta komai, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, Yana jin nauyin uncle din nasa.
“Da ace kayi aure da wuri da yanzu mun samu ƙaruwar babies” da sauri shureim Ya juya mashi ƙeya ya rasa ina zai tsoma ranshi, hakan da yai ba ƙaramin nishaɗi yaba kawun nashi ba
“Zeenatu ta shigo kun gaisa”? Muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mashi da”eh jiya tazo”
“Okey, pls, shureim inaso kana taimaka mata, Kuna fita yawo atare, still ƙanwar taka bata canza ba, sam bata da natsuwa, ni ban ta6a ganin mahaddaciyar ƙur’ani mara natsuwa irinta ba, zaka ga duk min rashin natsuwar mutun indai yana yawan karanta al’ƙur’ani natsuwa na shigarshi amma ita kullum abun nata ƙara gaba yake yi”
A hankali shureim Ya juyo ya kalle sa, mamakine ƙarara akan fuskar Shureim wai yau shine kawu musa keyi ma magana har haka? Mutumin da bai Iya surutu ba.
“In sha Allah uncle, zanyi ƙoƙari wurin ganin na taimaka mata, “ gyaɗa kai yai”haka nakeson Ji, Ni zan shiga Ciki, idan ka yanke shawara game da abunda na faɗa maka, ka same ni a ɗaki ka sanar dani ko kuma ka kirani awaya”
Amsa mashi yai da toh, sallama Uncle musa yai mashi kafin ya fuce daga dakin
Ajiyar zuciya shureim ya sauke, hannun shi ɗaya dafe da ƙirjin sa.
Lokaci ɗaya zuciyarshi ta fara tariyo mashi haukan zeenatu na Jiya, murmushin gefe fuska ya saki, aranshi ya ayyana ko ta na ina yanzu, yasan zai yi wuya ta jure rashin ganinshi.
Ai tun Jiya data bar ɗakinshi Cikin sanɗa ta nufi ɗaki akan hanya suka ci karo da Tani, Abunka game saurin kuka nan take ta ƙware mata baki tana kuka ta faɗa mata abunda ya faru
Lallashinta tani tayi tana fadin to menene aciki, Ki kwantar da hankalinki dr shureim dai ɗan uwanki ne ba wani bare ba, yanzu bari na baki mayafi na ki ɗaura a qugunki, ni kuma zanje ɗakin nashi in ɗauko maki zanin, Ai mantawa nayi ban baki undy kin sanya ba jiya, ke kuma baki tuna min ba,”
Cikin shessheƙar kuka take faɗin Na tsani kaina Tani, bani da hankali, sai yaushe ne zan daina hauka, sam bani da natsuwa, meyasa na kasance haka”? Cikin kwantar da murya tani tace”karna kuskura na ƙara ji kince haka, in banda abunki ma, meye na damuwa?, Haka Allah ke son ganinki, don haka ki share hawayenki, ai ni wlh ba ƙaramin burgeni kikeyi ba saboda kina da hankali, dayawa wasu ƴa’ƴan masu kuɗin basa girmama ƴan aikinsu amma ke kin ɗauke mun tamkar iyayenki, shiyasa nake ƙara ƙaunarki”
“Tani ba zaki gane ba, ni duk ba wannan ba, Yaya shureim bazai ta6a ɗauka na a matsayin mace ba, idan har ban daina wannan haukan ba” tsabar kukan da takeyi make up din fuskarta ya ca6e mata, jan bakin har saman kumatuntu.
Ɗaura mata Mayafi Tani tayi asaman waist dinta, tace”ki koma ɗaki, zan shigo muyi magana” ta amsa mata da toh, ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
A daren ranar daƙyar Tani ta lallasheta, ta kwantar mata da hankalinta akan tadaina cewa ta tsani kanta saboda yarda Allah ya halicce, kowa da irin tashi ƙaddarar, bawa bai ta6a zama 100% batare da an samu naƙasu atare da shi ba. Sannan Idan saboda yayanta shureim ne takeyin kuka waya fada mata rashin natsuwarta zai hana shi sonta? Wata’ƙil ma haukan nata ne zai ƙara mashi ƙaunarta, don shi so babu ruwan shi da yanayin mutun abu ƙalilan ke haifar dashi indai mutun ya kasance ƙaddararka.
Kafin Tani tabar ɗakin sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali tukunna ta fuce, tsakar dare Zeenatu ta farka, ta shige toilet ta ɗauro alwala kamar yarda ta sama tashi yin nafilfilin dare, yawanci addu’arta duk akan Allah ya bata natsuwa take yinta, abun yana damunta.
(Abunda Ya faru a daren Jiya kenan bayan zeenatu ta baro ɗakin Dr shureim)
Tun safe baiwar Allah taƙi fitowa daga ɗaki, tarasa ya zatayi, kunyar duniya ta ishe ta, aƙarshe ta janyo al’ƙur’ani ta cigaba da karantawa, har rana ta fito tukunna Ta ajiye shi ta shiga bathroom tayo wanka, ta fito ta sanya doguwar riga ta zura hijabi maroon har kasa, ko make batayi ba, cikin sanɗa ta fito daga ɗaki tana tafiya tana waige waige kamar wata munafuka, a haka ta ƙaraso part din daddynta.
A lokacin bai jima da fitowa daga wanka ba, tun bayan da ya baro room din shureim, Ya dawo nasa ɗakin, Jallabiyace a jikinsa launin milk mai kyan gaske, Yana daga kishingiɗe saman doguwar sofa ta cikin katafaren ɗakisa, tsayawa zayyana kyawunsa 6ata baki ne hankali ma bazai ɗauka ba.
Ya ɗaura kansa saman pillow, Yayin da apple laptop ɗinsa ke a saman flat tommy ɗinsa.
Idanuwanshi suna a lumshe ya natsu yana kallon wani abu a laptop din nasa, ga dukkan alamu video call ya ke yi, sautin muryarshi baya fita yayi low sosai, yana magana eyes dinshi suna lumshewa.