← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 152

Sashe 19

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Allah ya huci zuciyar mai girma jagoran mu, Ni anawa ganin yakamata mu fito da dabarun da za mu bi don ganin mun dawo da ƙarfin ikon da mu ke da shi ada, idan ma ta kama mu bi tsarin da su ka ɗauko wanda yasa jama’a suke rububin tasu jam’iyar, Idan har muna so mu farfaɗo da tamu jam’iyar” bayan Alhaji ubaid yai magana sauran Ƴan jam’iyar kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, Idan ka cire mutun ɗaya wanda tun da ya zauna meeting ɗin idanuwanshi su ke a lumshe daga gani yana da jiji da kai da izza, ɗakin taron ya rikice da zafafan zantuttukan su kowa yana faɗin ta cikinsa, rai amatuƙar amace Ya sanya hannu ya daki table ɗin gabanshi wanda silar hakan ya janyo hankulansu ga dubanshi, Ƙaraminsu babbansu slowly ya buɗe idanuwanshi akan faces ɗin su, sun kasa kunne suna jiran jin me zaice hatta shugaban jam’iyar tasu ya natsu yana jiran jin bayani daga gare shi.

Cikin harshen turanshi Ya soma magana da kakkausar murya”Let’s take a step back and focus on what we need to do right now. We need to come up with a strategy for the next election, We need to come up with a plan to fight back. We need to show the people that we are the party that can make a difference in their lives. We need to show them that we are the party that cares about their needs. We need to show them that we are the party that will fight for them, And We need to let them know that we are the party that is on their side.” tun da Alhaji musa wadata ya soma magana ƴa’ƴan jam’iyar su ke jinjina kansu ga dukkan alamu ya ɗauko magana mai ma’ana a ƙarshe ya daki table din gabanshi ya furta”Sharafudden obinna ba zai haura 4 years a mulki ba! Alƙawarine na ɗaukar wa kaina, duk yadda za’ae sai mun kayar dashi a za6e na gaba, dole jam’iyar mu ce asama babu wani mahaluƙi da ya isa ya durƙusar da jam’iyar mu, abokan hammaya ba za su ta6a cin galaba akan mu ba,” yana kai ƙarshen maganar azafafe ya yunƙura ya miƙe yana gyara malunmalun ɗin jikin shi, Ko sallama baiyi masu ba, Ya haura ƙafa yabar cikin ɗakin taron, yayin da su ke bin bayanshi da ido, har saida ya 6ace ma ganinsu tukunna suka dawo da dubansu kan maiguduma. tattaunarwar tasu ta ɗauki tsawon awa ɗaya kafin suka rufe taron da addu’a da kuma fatan nasara ga jam’iyarsu, Ɗaya bayan ɗaya suke fitowa harabar headquater inda jerin danƙara danƙaran motocinsu suke a killace. Bayan sun ƙara gaisawa da juna kowa Ya nufi motarshi, Musa wadata Yana kishingiɗe a back seat na danƙareriyar motarshi tsadaddar gaske, Ya lumshe idanuwanshi sanyin A.c ta ko’ina, gefen shi P.A dinsa ne, security ɗin da ke jigilar tuƙa su yana zaune a driver seat yana jiran jin umarninsa.

Ƙwanƙwasa glass ɗin motar da akayi ne yasa shi ware manyan idanuwanshi, muryar Alhaji ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi”Ina son magana da kai” Iya abunda ya furta mashi kenan, Muryarshi da izza ya amsa mashi da toh, daga haka yaba drivern nashi iznin ya tada motar su nufi gida” A jere motocin su su ka nufi gate ɗin fita daga cikin headquater ɗin su...

*JOS CITY*

Zaune ya ke saman darduma cikin shigar larabawa farare ƙal, kyakkyawan balarabe daga ganin fuskarshi ba ƙaramin mutun bane ya ɗan fara manyanta, Arab turban ɗin da ke nannaɗe akanshi, ya ƙara mashi kyau ga wani kwantaccen saje baƙi wulik mai matuƙar jan hankali, lallausar sumar kanshi ta sauko har saman wuyanshi dark black.

Daddaɗan ƙamshin turararen jikin shi mai matuƙar sanyaya zuciyar mai shaƙar shi, idanuwan shi suna a lumshe yayin da ya ke yin qira’ar Alqur’ani mai girma, Yatsun hannunshi na dama na a asargafe da cazbaha, Qur’anin da ya ke karantawa yana agabanshi saman wooden qur’anic stand dogayen eye lashes ɗinsa a jiƙe su ke sharkaf da hawaye ga dukkan alamu ayar da ya ke karantawa ce ta sanya shi tsuma.

Sam bai ji takun tafiyar mutun acikin ɗakin shi ba, tafi ƙarfin mintuna talatin da shigowa, idanuwanta akanshi ganin bai da niyar tsagaita karatun ƙur’anin nashi ne yasa ta ambaci sunan shi

*”DR SHUREIM*”Nasan kana jin takun tafiyata don haka idan ka kai ƙarshen Aya ina son magana da kai”! tamkar ta yi magana da bango ko kallo bata ishe shi ba, sai ma ƙara sautin muryashi da ya yi” dogon tsoki taja tare da zuwa gaban dardumar ta shi ta kai hannu ta rufe qur’anin da ya ke karantawa, a tsiyace ta ƙwace cazbagar dake nannaɗe a hannun shi ta ɗaura ta saman qur’anin, don ta fahinci da gayya ya ke yin karatun duk don kada ya saurari maganarta.

Tana huci ta ɗago tana kallon shi still bai buɗe idanuwanshi ba, kuma bai dakata da yin karatun ƙur’anin ba domin kuwa haddace akanshi

“Ka da ka bari raina ya 6aci wlh zan yi maka abunda baka tsammani, na rasa uban me na yi ma ka daka ɗaura mun karan tsana sai ka ce ba uwarka ba! Ko kana da wadda tafi ni ne a duniyar nan”? Ta jefa mashi tambayar, Shiru bai ce uffan ba, gyaɗa kai tayi”ilmin addinin na ka ya tashi abanza tunda ba ka san ka girmama iyayen ka ba, tsawon shekara da shekaru kana nuna wariya tsakanina da mahaifinka laifin me namaka Shureim”? Cikin jin ƙunar rai ta yi maganar, A hankali ya buɗe idanuwanshi farare ƙyal da su ya ɗaura su akan fuskar Mahaifiyar tashi, ba kowa ba ce fa ce Layla mahaifiyar Benazir, Doctor shureim shine babban ɗansu, Ya ya ne awurin Benazir mahaifiyar Angel.

Daddaɗar muryar shi ce ta ratsa kunnuwanta”ba ki min laifin komai ba, har yanzu kina nan a matsayinki na mahaifiyata, kawai bana buƙatar kusancin ki da ni” Zagayawa ta yi zuwa gefen gadon shi ta zauna suna fuskantar Juna”Nasan dalilin dayasa ka ke yin fushi dani, haba shureim tsawon shekaru nawa why za ka ruƙe abu aranka yai ta damun ka? Yakamata mu manta da abunda ya wuce, kuskure ne an riga da an ta6ka, kuma in sha Allahu hakan bazata ƙara faru wa ba” fuskarshi a ɗaure ta ke babu walwala” tayi tsammanin zai tanka mata sai ji ta yi ya yi shiru bai ƙara magana ba.

Ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, zuciyarta na ƙuna tace”na lura sam faɗuwar mahaifinka bata dame ka ba, An ya kuwa shureim kana ƙaunar mu a matsayin mu na iyayenka? Cos na fahimci baka son cigaban mu” murmushin takaici dr shureim ya saki, da ido tabi shi da kallo ganin yana dariya har fararen haƙoran sa su ka bayyana masu kyau da tsari.

“Mahaukaciya ka mai da ni? ina magana kana dariya” fuskarta a ɗaure tayi maganar, Yunƙurawa yai tare da mikewa Ya fuskance ta kafin ya soma magana”Saboda ku ba iyaye bane daya kamata a nuna damuwa akan ku! Daga ke har shi bakusan ciwon kan ku ba, Gaba ɗaya hankalin ku na akan son abun duniya damuwar ku akan cigaban ku ne ba akan mu ba! Ta ya ya zan damu don mahaifina ya faɗi a za6e? Aini abun farin cikine agare ni, don na fahimci siyasarshi tafi komai mahimmanci awurinku! Saboda rashin sanin ciwon ƴa’ƴa Yau tsawon shekara goma sha shidda Benazir bata a tare da ku, hankalin ku a kwance ba ku iya ta6u ka komai ba, duniya kawai kuka sa agaba, Wlh na jima ina danasanin kasancewar ku Iyayen mu! Na yi fatan ace mutun yana iya canza iyaye da tuni na yi hakan, Nifa ba ku da amfani acikin rayuwata! Kun riga da kun yi min abunda har abada zuciyata bazata ta6a mantawa da shi ba, kune silar duk wata masifa dana tsinci kaina aciki.......” daƙyar ya ƙarasa maganar cikin jin ƙunar rai, a bun ka ga farin mutun tuni fuskarshi ta canza launi zuwa ja, numfashi yaja muryarshi adisashe yace”kun manta cewa ƴa ƴa amana ne agare ku? Ranar gobe ƙiyama Allah zai tambaye ku game da amanar da ya ba ku, Rashin nasara yanzu ku ka fara gani, in sha Allah ba zaku ta6a samun abunda ku ke so ba, har tsayuwar dare zanyi maku akan kada Allah ya cika maku burinku na mallakar kujerar.....” bai ƙarasa maganar ba sakamakon zazzafan marin da Layla ta sakar mashi, da sauri ya dafe kuncinsa da tafin hannun shi na dama, Idanuwanshi sun rune zuwa ja.

Tana hu ci ta nuna shi da yatsa”don uban ka ka tattara kayan ka kabar gidan nan tunkafin ranka ya 6aci, shashasha kawai wanda baisan ciwon kanshi ba,” Cikin sanyin murya yace”zan tafi koda ace baki kore ni ba Mommy, dama ita gaskiya ɗaci gare ta, kuma in sha Allah zanje na nemo ƴar uwata benazir aduk inda take, idan ku bakusan ciwon kanta ba ni na sani....” tunkan ya kai ƙarshen maganar layla ta nufi ƙofar fita ɗaki kamar zata tashi sama tsabar 6acin rai.

Zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa idanuwansa jawur hawaye na cigaba da gangarowa saman kuncinsa, haƙiƙa mahaifiyarshi ta fama mashi mikin dake acikin zuciyarshi, matsawa yai gaban gadon shi ya miƙa hannu ya ɗauki wayarshi yana duban hoton da ke a kan wallpaper na wayarshi, lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su sosai akan hoton da yake kallo, baya gajiya da kallon fuskarta A hankali ya furta

_ke ce silar tarwatsewar farin cikina kuma kece silar shiriyata! Ki yafe min nayi kuskuren da bazan ta6a gyara shi ba, ina son ki sosai ina jin ki har cikin raina, nasan haƙƙin ki ne ya ke bibiyar rayuwata_

kifa kansa yai saman mattress sosai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro.
Chapter 19 · 0% Book details