Sashe 69
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“My Man, Ka fara Yin wankan, almost one week jikin ka bai ga ruwa ba, I’ll wait for you outside.” Akan idon shi ta fuce, a bakin ƙofar toilet din ta jingina Bayanta tana jiran fitowarshi, ta kasa kunne tana sauraron motsinshi, daɗi take ji kamar wadda akayiwa albishiri da gidan Aljanna, a ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirga fatanta Allah yasa subar america batare da sun samu wata matsala ba.
Gaba ɗaya hankalinta baya atare da ita, gangar jikin ce kaɗai, ruhin Yana atare da Danish dake acikin toilet, har Nurse jessica ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da food trolley, ta gunguro shi zuwa gaban table, murmushi tasaki tana kallon Angel dake maƙale jikin toilet door, aranta ta ayyana ko dai soyayya ce a tsakaninsu, don wannan shaƙuwar tasu tafi ƙarfin a kirata da abokantaka.
Bayan ta ƙaraso gaban table din, ta soma jera kayan abincin saman shi, har ta gama jera su, ta juya da food trolley din duk Angel bata lura da ita ba, Har ta fuce daga ɗakin.
Jin motsin buɗe ƙofarshi, Yasa tayi saurin komawa gefen gado ta zauna tana faman sakin murmushi kamar wata zautacciya.
Zuro ƙafarshi yai saman carpet dake gaban ƙofar shiga toilet ɗin, Kafin ya ƙarasa fitowa, jikinsa da danshin ruwan wanka da yai, Ya maida uniform dinsa da aka sanya mashi.
Tun ya fito idonshi na akanta, ya lura da tsantsar farin cikin dake akan fuskarta, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba.
Gefenta Ya zauna yana ƙare mata kallo
“Na fito” sai da ya ambaci hakan tukunna ta ɗago suka haɗa ido wani irin asirtaccen kallo suke jefa ma junansu kamar zasu haɗiye kawunansu tsabar ƙauna.
Lokaci ɗaya ta samu kanta da jin kunyar shi, Muryarta adabarbarce ta furta”am..um.. Ga abincinka da nurse ta kawo nasan kana jin yunwa” ta yi maganar haɗi da nuna mashi table din, ɗaura idonshi yai akan kayan abincin kafin ya dawo da dubanshi gareta”baki jin bacci? Naga sauran ƴan uwanmu suna yin bacci, ta hakan na fahimci dare ya nutsa”
Maƙe mashi kafaɗa tayi”bana jin bacci, inaso na zauna a kusa dakai, don na taimaka maka da wasu abubuwan, tun da yau ka farka ba ka san komai dangane da wurin nan ba, bana so in tafi in barka kai kaɗai a room” natsuwa yai yana kallonta, har ta ƙare maganar tukunna ya furta mata”nagode da kulawarki agareni, kuma nagode da nuna damurki akaina” still murmushin fuskarta bai washe ba
“Zamu ci abincin atare? Ko kin ci naki”? Yai tambayar yana duban fuskarta, Yafi son tana kallon Cikin idonshi idan suna magana.
“Bana jin yunwa, amma Zan Iya taimaka maka ka ci naka” amsa mata yai da”okey, “ miƙa hannu tayi tana buɗe plates din, lafiyayyan abinci aka haɗa mashi Grilled chicken with roasted vegetables, and black bean burger with sweet potatoes fries, hada Green tea a mug.
“My Man, komi da ka gani a saman table ɗin nan duka sai ka cinye shi, yadda kasha baccin nan na tsawon kwanaki nasan cikin ka babu komai ko ruwa ma babu, yanzu faɗamin me ka ke son fara ci? Cikin kulawa take yi mashi magana.
“Ki za6a min” murmushi ta sakar mashi, Mug din ta miƙa mashi, Yasa hannu biyu ya kar6a, a tsanake yake kur6anshi da zafi zafinshi, idonshi na akan face dinta, ta ƙurawa adam’s apple dinsa ido.
Batasan Ya janye cup din ba sai dai taji muryarshi acikin kunnanta”me kike kallo”? Yamutsa fuska ta ɗanyi”bakomai, tun da ka gama shan tea din, zaka Sha ruwa? Ko lemu”? Girgiza mata kai yai”a’a, tea din ya ishe ni, sai dai wani abun”
Kamar wani ƙaramin yaro haka take tarairayarshi, da hannu ta dinga bashi grilled chicken din yana ci, Idan ka kallesu a yadda suke zaune sai ka sha mamaki saboda girman da yai ma Angel, Bata wuci Ya lullu6eta da faffaɗan kirjinshi ba, amma saboda sabo da juna, da kuma shaƙuwa da ƙaunar dake a tsakaninsu bata ganin girman shi.
Ɗaya daga cikin abunda ke burgeta, idan ta tura mashi abincin abaki yadda yake motsa tattausan full lips nasa da kuma motsin Adam’s apple dinsa, komai nashi ƙayatar da ita yake yi kamar yarda itama ta ke burge shi, a ƙarshe sai suka koma suna feeding din junansu tana bashi abaki, Shima yana bata abaki.
Abunda basu sani ba, Har safiya tayi gari ya ware babu wanda Ya lura a cikinsu, tuni sun kammala cin abincin, sun shagala suna kallon juna.
*ABUJA NIGERIA A GIDAN ƊAN IYA*
A round ƙarfe 10 na safe agogon Nigeria, tun bayan kammala sallar Asubahi da ta koma bacci bata farkaba ba saboda Jiya sun sha fira da Aneelerh sun kusa raba dare kamar ƴa’ƴan Aljanu, shiyasa yau take ta sharar baccinta kamar matatta, ta wawware ƙafafuwanta saman mattress, ta saki baki da hanci, sai jan minshari ta ke yi kamar ragon sallah, daɗin bacci hada yawu a gefen bakinta, Gajeran wandone a jikinta sai ƴar farar half vest data zura, sumar kanta babu kitso zallar gashinta a hargitse ba gyara.
Tayi zurfi acikin baccinta, Wayarta dake ajiye saman side drawer ta buga uban ringing, Babu alamun zata farka har kiran ya katse, wani ya kuma shigowa, sautin ya cika ko’ina banda kunnan zahra dake yin bacci.
Shigowa cikin ɗakin Aneelerh Tayi, jikinta asanye da doguwar riga, ta yi rolling mayafi akanta, kaitsaye ta nufi drawer din ta miƙa hannu ta ɗauki wayar tana faɗin”Allah ya shirya zahra, wannan bacci haka kamar matatta, ana ta kiran mutun awaya wama ya sani ko arziƙi ne ke kiranta...” Waro ido waje aneeleeh tayi ganin sunan mutumin dake kiran Aneelerh, Ya fito 6aro 6aro saman screen din, bakowa bace face Hajiya Saratu Obinna, Jiki na rawa ta haye saman gadon takai hannu tana bubbuga ƙafar zahra”banza, ki tashi arziƙine ke kiran ki, zahra ki tashi kada muyi asara” yamutsa fuska zahra tayi muryarta kamar ta mashayin giya ta furta”dallah wanene ke takuramin, ni a ƙyaleni inyi bacci na, ba dama mutun ya ɗan kwanta ya runtsa sai an samu wani uban anacin ya tada shi’
cikin magagin bacci take yin sambatun. kiran har yayi rejecting, zuƙunnawa Aneeleeh tayi saitin kunnan ta da karfi ta furta”Shashasha Hajiya saratu obinna ce ke Kira” A haukace Zahra ta zabura Ta miƙe tana faman mutsustsuke ido, A fujajen take fadin”Wai dagaske? Ina wayar? Gaba ɗaya tabi ta ruɗe jin an ambaci sunan Hajiya saratu obinna, sai faman zazzare ido take yi.
Miƙa mata wayar Aneelerh ta yi “yo har yayi rejecting, Tun ɗazu nake ta ƙoƙarin tada ki, Kinƙi ki farka gashi yanzu kin ja mana asara....” bubbuga katifa zahra tayi da hannu tsabar takaici hada hawaye akan fuskarta”Aunty aneelerh, kin karyamin jari, meyasa da kika tada ni naƙi tashi baki shiga toilet kin ciko bokiti da ruwa kin watsa mun ba”?
Babu wasa akan face dinta ta yi maganar, Sakin Baki aneeleeh tayi tana kallonta
Zahra ta ci gaba da yin kuka tana faɗin “Nashiga uku, wayyo Allahna, ni wlh bakiyi min adalci ba, wama ya sani ko kujerar Hajji za’a raba mana,” sosai ta fashe ma Aneelerh da kuka. Lamarin ya ɗaure mata kai, ta rasa ina zahra da mahboob suka gado shegen son kuɗi, sai dai tafi tunanin ta 6angaren mahaifinsu ne.
Lallashinta ta soma yi”Kiyi hakuri sister kukan Ya isa haka, wata’kil ta ƙara Kiran ki,” cikin shessheƙar kuka tace”taya za’ae ta sake kira na, bakisan halin masu kuɗin nan ba, basu ɗaukar raini, za ta yi tsammanin dagangan naƙi ɗaga kiranta, Wayyo Allahna aunty Aneelerh, nayi wa arziki ƙulli, har ƙiyamil laili nayi akan Allah ya bude mun kofofin samu, da kuma miji nagari a sabuwar shekarar da zamu shiga...” dariyace kumshe abakin Aneelerh.
Dafa kafaɗarta tayi”Sorry My lovely sis, Yanzu abunda za’ae, Ki kira Layinta mu gani ko zata ɗaga” kar6ar wayar tayi daga hannun Aneelerh, Yatsun hannunta har kerma sukeyi sam babu natsuwa, kiran layin ta soma Yi, tamkar zata fashe da kuka ta kalli Aneelerh”line busy, dama ni nasani, wlh basa ɗaga kira, idan ba su suka kira mutun ba”
Aneelerh tace”mu ɗan ƙara haƙuri, zuwa anjima sai mu ƙara jaraba kiran layinta, yanzu ki tashi ki shiga toilet ki ki gyara jikin ki, zan Jiraki anan,” cikin shessheƙar kuka ta amsa da toh, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ta shige.
Bayan shigarta da mintuna biyar Aneeleeh tana zaune tsakiyar gadon tana jiran fitowarta, zuciyarta acunkushe take da tunanin baby junaid ɗinta tayi kewarshi, tun shekaran Jiya Uncle abdallah da hajiya adama suka koma gidansu, anyi rabuwar mutunci sun nemi alfarma Junaid ya zauna wurinsu na tsawon 2 weeks, zai dawo gida, sannan duk weekend za’a dinga kai masu shi, yanzu haka yana acan gidan nasu, tsawon kwana uku da yayi acan kullum ne sai ya matsa masu akan su kira mashi Mommyn nasa, wani lokacin tun kafin ta farka daga bacci kiran su ke shigowa wayarta saboda jarabar junaid.
Tayi zurfi cikin tunaninta, Wayar Zahra ta soma yin ringing, Kafin ta wurga idonta kan inda zahra ta ajiye wayar saman drawer, da ƙarfi taji sautin buɗe ƙofar toilet, Ras taji gabanta Ya fadi ganin zahra ta watso aguje, jikinta duk kumfa daga ita sai gajeran towel tayi ɗaurin gaba da shi, hatta fuskarta kumfar sabulu ce, miƙa hannu tayi ta rurumi wayar, tsabar zumuɗin ganin wanene ke kiranta, fatanta Allah yasa hajiya saratu obinna ce, cikin sa’a idonta yai mata nuni da sunanta akan screen, sai ƙoƙarin ɗaga kiran takeyi kumfar hannunta ta hana touching din yin aiki, kamar zata fashe da kuka, sai da aneelerh ta taimaka mata wurin answer mata call din tukunna ta samu natsuwa, a Hands free ta sanya kiran don suji me zata je
Cikin girmamawa zahra tayi mata sallama”Assalamu alaikum” kamar tana agabanta.
On the other hand sautin muryar hajiya saratu ya karaɗe kunnuwansu
“Wa’alaikum salam”
“Ina kwana hajiya, fatan kun tashi Lafiya, wlh bana a kusa da wayar ne, kunata kira bansamu damar ɗagawa ba, da yake na ɗan shiga toilet ne”