← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 152

Sashe 74

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaitsaye ta nufi hanyar da zata sada ta da office din commender domin amsa kiran da yayi mata, tasan ko’ina na headquarter din, don ba baƙuwarta bace, Ba yau bane rana tafarko da ta fara shigarta.

Tun kafin ƙarasowar ta, tuni Anyi mata iso wurinshi, jiranta kawai Yake yi, yana daga zaune saman chair, acikin katafaren office dinsa, komai na cikinsa army green ne, hatta desk din gabanshi, dake dauke da computer dinsa, da wayar hannunsa tare da flag and map, daga jikin bangon office din akwai book shelf, da jerin hotunansa da awards dinsa, bashi kaɗai bane a office din hada Major.

Shigowarta office din, Tuni sanyin Iskar A.c ɗin cikinsa ta gauraya da ƙamshin shu’umin turarenta.

Har saida suka shaƙe shi sosai a hancinansu.

Da kwarkwarsa ta ƙarasa gaban desk dinsa, kamar yadda ta saba yi mashi duk in tazo office dinsa haka yau ma tayi mashi, Ta buga ƙafa tare da sara mashi, hakan ba ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, har sai da suka saki murmushi, tun kafin Ya bata iznin zama, ta zauna saman chair din dake facing dinsa, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, murmushi ta sakar mashi haɗi da ɗaga mashi gira ɗaya ta kashe mashi ido.

A wayance ta soma yin magana cikin harshen turanci”fatan na same ku lafiya” lumshe ido commender yai tare da kai hannu ya gyara zaman wuyan rigar kakinsa.

“Lafiyalou ummi, I’m glad to see u, Ina fata kiran da mukayi maki bai taƙura maki ba”?

Ɗaga mashi gira tayi alamar eh ba tare da ta furta ba, a mutunce suka gaisa da junansu. Bayan kowan nan su ya natsu, Major Ya miƙe ya bi ta ƙofa ya fuce waje jim kaɗan ya dawo hannayen shi ruƙe da mugs na coffee guda biyu ya ɗaura su saman desk, ya ɗago da ido Ya kalli Ummi”zaki Iya sha” ta furta okey, kafin takai hannu ta dauki mug din ta soma kur6an coffee din, da alama ya yi mata dadi kusan sau uku tasha kafin ta ajiye mug din, ta dawo da dubanta ga commender”am all eyes”

“Dalilin da yasa na kira ki ummi, Magana ce mai muhimmanci muke san yi da ke, Ina fata za ki bamu haɗin kai kamar yadda kika saba taimakon mu” cikin harshen turanci commender yayi maganar a tsanake.

Hankalin major na akan ƙirjinta har wani ƙara leƙensu yake yi kamar zai zura kanshi cikin rigarta.

Kallon da Commender ya watsa mashine yasa shi saurin kawar da idonshi ya kame mutuncin kansa

“Babu takura, ko da yaushe ina maraba da ku, zaka Iya faɗin komai ka ke so kai tsaye”

ta ƙare maganar tana shafa saman boobs dinta da yatsun hannunta.

Yawu commender Ya haɗiya Kutt throat dinsa Ya bada sauti, shi kanshi daurewa yake yi, surar ummin America na neman kwance mashi masarrafinsa.

“Ina so ki natsu ki fahimce ni kafin ki bani amsa” amsa mashi tayi da toh
Bayani ya soma yi mata dalla dalla tun daga farkon tsintarsu Angel da su ka yi a Daji, har izuwa kawosu asibiti, da kuma abun da su ke buƙata daga gare ta, tunda commender ya fara labarta mata, ta natsu tana sauraronshi.

“Muna so ki bamu haɗin kai wurin Kula da yaran ki ruƙe su tamkar ƴa’ƴanki, munsan zaki Iyane shiyasa muka za6e ki, tun da ba yau kika fara yi mana aiki ba, mun yarda dake ummi, burinmu ki tarairayesu ta yadda yaran zasu yarda dake har su Iya faɗamaki ainihin abun da ya faru arayuwarsu’ ya ƙarasa maganar idonshi akan fuskarta.
Lumshe ido ta ɗanyi kafin ta waresu akan fuskarshi

“ta ya ya zaku yi tunanin damƙa amanar yara har goma sha ɗaya a hannuna? Bayan kunsan wacece ni, Ban ta6a haihuwa ba, kuma ni banason Rainon ƴa’ƴa, ban ta6a sha’awar haihuwarsu ba, balle har in iya kula da yaran wasu, Ina mai baka haƙurin Cewa Ni bazan Iya wannan aikin ba! zaifi ku samu macen da tasan zafin haihuwa mai kamun kai ku bata rainon su” tana magana jikinta na jijjiga, major duk yabi ya susuce ya rasa natsuwarshi, ba dan commender na akusa ba da ba abun da zai hana ya damƙeta ko da zai sha mari ne.

“Ummi, Ki sassauta kalamanki, Kina yi min magana da tsiwa, Ko kin manta a ina kike ne? Ki duba da kyau ki gani, nan ba club ba ne, ba kuma gidan karuwai bane, sannan ba ga6ar taku bane, Head quarter din sojoji ce” Ya yi maganar tare da zaro bindiga daga cikin drawer chest na desk din gabanshi Ya daurata saman desk din.

Tuntsirewa Tayi da dariyar rainin wayau

“Kai ma ka sani, Ummin america bata tsoron bingida, ni da ni ke yin mu’amala da masu ruƙeta, yanzu haka da nake yi maka magana shigowa ta head quarter din nan gaba ɗaya na tada masu jarabarsu, suna can waje, wandunan su sunyi masu nauyi’ cike da shaƙiyanci tayi maganar, ta riga ta gama raina su bata jin tsoron su ko kaɗan.

Cikin kwantar da murya commender yace”is ok, kibar yi min wasa, Muyi magana ta hankali, ki taimaka ki kar6i buƙatarmu, kome kikeso zamuyi maki, sannan ɗawainiyar yaran da komai nasu mune zamu bada tallafin da za’a cigaba da kula da rayuwarsu, tun daga cinsu shansu, suturarsu, da karatunsu, Iya taimakon da muke so kiyi mana kija su a jiki ki zama tamkar mahafiyarsu” yamutsa fuska tayi tana faman wurwurga eye balls dinta tace”Kana nufin wai a gidana zasu zauna? Ka san gidana gidan mazane, a koda wani lokaci Ina busy wurin biya masu buƙatarsu, how ka ke tunanin zasu Iya samun kulawar data dace? Kuma naji kace yaran suna fama da depression hada me ciwon ciwo, gaskiga ba ƙaramar ɗawainiya bace kula da su, bazan Iya ba commender, kada ka tursasamin, kasan ina girmamaka saboda halaccinka agareni”

Kallon major commender yayi, hakan ya bashi damar Yi mata magana

“Ba zamu takura maki ba, amma kafin ki tafi Inaso zan nuna maki hotunan Yaran Ki gansu”

Miƙewa Major yai daga saman kujerar da yake a zaune Ya zagaya ta 6angaren Commender Ya juyo mata da laptop din saitin fuskarta.

Operating ɗinta Ya soma Yi, hotunansu Angel Ya buɗo, daga kan hotonta Ya fara Nuna ma Ummin america
“Sunanta Angel” Ya ambaci hakan yana kallonta, da alamun mamaki akan fuskarta ta furta “wow she’s beautiful sai dai daga ganin bakinta za ta yi tsiwa, ni kuma bana sha’awar Yara masu masifa” ta faɗa haɗi da yamutsa fuska, still murmushi ne akan fuskar major da commender.

Hoton Batul ya nuna mata, sai da ta ta6e la66anta kafin tace “tana da kyau, sai dai daga ganin fuskarta bata da masifa, wannan ko yatsa aka sanya mata abaki bazata Iya cizon shi ba” ta kare maganar tana hura hanci.

Hoto na gaba fuskar Hanna ce, Ummin america tace”har ƙwara Yarinyar daka wuce akan wannan, taci ka sanyi daga gani babu kuzari a jikinta” yadda take fayyace ɗabi’unsu kamar ta ta6a ganinsu.

Ko da akazo kan Hoton Parveen Ya cika screen din laptop din.

Da buɗar bakin Ummi sai cewa tayi”yarinyar nan daga ganin kumatuntu mayyar abinci ce, zai yi wuya idan ba asame ta da shegen ci ba, Ni bana so mutun mai ciye ciye” murmushin fuskar Major da commender sai ƙara faɗada yake yi, don ba ƙaramin nishaɗi take basu ba.

Hoton Jamimah Ya nuno mata, waro ido waje tayi hada sanya Hannu ta dafe saman ƙirjinta.

“Major, ruƙon wannan Yarinyar ai sai likitan mahauka, shi kaɗai ne zai Iya sarrafa ta, ba dai ni ba, Ni ina zan Iya kula da ita, daga ganin bakinta zatayi tsiwa” Major yayi dariya tare da nuno hoton Azeeza, shiru tayi tana ƙare mata kallo, kafin ta ɗago da ido ta kalli Major”sai naga kamar ƴan biyu ne ita da Yarinyar da ka nuna min kafin ita, sunyi kama” Major yace”haka muke tsammani, sai dai muna hasashen azeeza tafi Jemimah shekaru kamar yadda ɗan uwansu ya faɗa mana”

Yamutsa fuska Ummin america tayi”tana da kyau sai dai daga ganinta matsoraciya ce, wannan ko tsawa na daka mata zata Iya sakin fitsari a wando, gani da tsiwa bansan ya zamu ƙare da ita ba” ta fada tana ta6a baki tace”wai Iya matane Yaran”? Ta yi tambayar tana kallon Fuskar Major

“akwai maza” ya bata amsa, a dai dai kan hoton Haris Ya buɗe mata shi.

“Sunan shi Haris, shine yaron da commender Ya faɗa maki cewa Yana fama da ciwon zuciya”

Ta6e baki tayi”nifa banason namiji mai raunin zuciya, daga gani baya da hayaniya ba laifi yana da kyan fata” ta faɗi hakanne saboda kasancewarta baƙar fata, tana son mutun me duhun fata.

Wuce hoton Haris yai adai dai kan hoton Javed ya dakata Yana dubanta

“Amma dai wannan Yaron ɗan south korea ne ko?

Major yace”bamu da tabbacin ɗan Ina ne, duka yaran bamu san wani jinsi bane, sai dai sun faɗa mana cewa Ƴan Nigeria ne” da sauri ummin america ta girga kai tana fadin”Impossible, babu kalan waɗannan a nigeria, may be sun yi loosing memory ɗin su ne shiyasa su ka faɗi hakan”

Hoton Naufal Ya budo mata, lumshe ido ta ɗanyi tare da waresu akan kyakkyawan fuskarshi
“Wow, kaga Namiji, sumar kanshi ta burge ni, Yayi min kyau” ta yi maganar tana hura mashi kiss.

“Yaro ne” Commender ne yace haka,
Ummi tace”Ai shi namiji baya kaɗan, especially idan abunsa ya ruƙa, a wurina wannan ba yaro bane Namiji ne” murmushi suka saki, basu damu da abun da tace ba saboda sun san halinta, bata mu’amala da matasan samari, Sai mazan da su ke da aure waɗanda tasan idan ta bibiyesu za’ayi bala’i idan matansu suka kamata.

Bayan Ya wuce hoton Naufal Ya buɗe mata hoton Gabriel, tunda ta kafe shi da ido bata ƙyaftaba sai faman jinjina kanta take Yi alamar mamaki

Can dai ta numfasa tare da cewa”Allah Ya yayi halitta, gaskiya idan aka bani rainon yaran nan tamkar kun ba kura ajiyar nama ne, major idan akwai wani hoton nuna mini na ƙosa na ƙarasa ganinsu”

Lokacin da Major Ya hasko mata hoton Danish daga zaune ta zabura ta miƙe tsaye tana duban fuskarsa data cika screen na laptop din, duk suna akwance akayi masu hotunan idanuwansu arufe.
Chapter 74 · 0% Book details