← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 152

Sashe 91

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskar zaid a ɗaure ya dube shi”kaga bana son zancen banza, babu ruwanka dani, Kaja baki kayi shiru idan bazaka ci ba”

Ya ƙare maganar tare da maida dubansa ga hajjaty “mun gode Aunty, Idan nagama cin abincin zaki ji feed back dina” jiki asanyaye ta amsa mashi da toh, da sauri ta fuce daga ɗakin tana faman sauke ajiyar zuciya.

Ƙamshin Abincin da Zaid ke ci duk Ya cika mashi hanci da maƙoshi, dauriya ce kawai Yake yi, Yana danna laptop Haɗi da satar kallon Zaid, da gangan yake cuko spoon da abincin Yana turawa abaki, hada sambatun shi”wannan abinci kamar a aljanna aka dafa shi? Kai ka ji wani ɗanɗano mai daɗi, gaskiya duk wanda baici abincin nan ba an barshi a baya” Harara Zayn ya watsa mashi sam bai lura ba, saboda Ya bashi Baya.

Ajiye spoon din ya yi cikin abincin, ya tsiyaya lemu mai sanyi acikin glass, Ya ɗauka Yasha rabi, Ya ajiye.

“bari na ɗan shiga toilet” ya faɗa hadi da miƙewa da sauri Ya nufi toilet door ya shige, shigar shi ke da wuya Zayn ya janye laptop dinsa, cikin sanɗa Ya rarrafa saman mattress din zuwa gaban table din, Yana faman yamutsa fuska Ya ɗauki spoon Ya zura a plate din abincin aranshi yana fadin ba lallai ma abincin yai daɗi ba, mutuminka tun da yayi one spoon abaki, Tsabar daɗi kunnanshi har motsi suke yi, Yana ci yana satar kallon ƙofar toilet gudun kada Zaid Ya riske shi Yana cin abincin Hajjaty, a ƙarshe Ya ajiye spoon din Ya duma hannu ya ɗauko cinyar kaza Yadinga cizga Yana ci, Kusan Rabin abincin plate din ya cinye, ya ɗauki lemu Ya kur6a, Jin motsin za’a buɗe ƙofar toilet Yasa shi yin saurin sauke glass din lemun saman table, ko hannun shi bai goge ba, Da sauri Ya koma can saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard ya ɗauki laptop dinsa Ya cigaba da operating dinta.

Fitowa zaid Yai daga toilet, Yana faman yarfa hannun shi, Satar kallon fuskar zayn yayi, mutumin Ya haɗe rai babu annuri, Sai dai Ya manta bai goge bakinshi ba, yayi dama dama da maiƙon abincin da ya ci.

Ƙayataccen murmushi zaid ya saki aranshi ya ayyana”babyn mommy ai nasan zaka aika, shiyasa na shiga toilet don na baka damar ka ci, ɗan rainin wayau anaso ana kaiwa kasuwa” Ya faɗa Yana zama bakin gadon, da zolaya yace”Zayn ya akai naga abincin dana rage an ci shi”?

Muryar zayn ba wasa yace”ka tambayi wanda kaba ajiya, Ni meye ruwana aciki”? Gumtse dariya Zaid yai”amma dai da kunya wallahi, Ni dai nasan babu 6era agidan nan” rai a6ace zayn yace”ban san iya shege zaid, Uban waye 6eran”?

“Ai ni ban kama suna ba, kawai nayi maganata ne” dogon tsoki Zayn yaja yana faman hura hanci, Aranshi ya ayyana Ina ma zaid Ya rage abincin da kuwa ya cinye shi duka, don ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba.

*SIR MUBARAK🤍*

A Hankali Yake tafiya Yana tunkarar ɗakin Dr. Jazz, Daga shi sai short A jikin shi da singlet, Tura ƙofar Yayi baiga kowa a ɗakin Ba, shiga Ciki Yai Yana bin ko’ina da Kallo zanin gadonshi a hargitse Takalman shi Yashe saman floor, tunani ya shiga yi aranshi ko ina ya shiga? Ko dai yana a toilet ne Ko ya shiga Garden, Yanke shawarar zuwa garden ɗin ya yi don Ya dubo shi, Ahanzar ce Ya juya da niyar ya fuce kwatsam Muryar Jazz ta katse mashi hanzarin shi.

“Oh tsayawa za ka yi Kana kallonta? Babu abun da zaka Iya yi mata? Sai kace ba ka san Hanyar da zaka kashe ta ba idan haukanta Ya motsa”! wani irin bugu zuciyar Sir Mubarak Tayi Jin Kalmar Kisa, A firgice ya juya baya Yana bin toilet door ɗin ɗakin da kallo, don Ya fahimci acikin toilet yake Yin wayar, Cikin tafiyar sanɗa Sir Mubarak Ya nufi ƙofar toilet Ɗin Ya kanga kunnan shi Yana sauraron shi.

“Ai ba dole Saina zo ba, Kaima zaka Iya sarrafata, Idan taƙiya Kawai ka bi Hanyar da nace maka, ka kashe ta kowa Ya huta,” shiru Ya ɗanyi can kuma yaji yaci gaba da cewa”ba yadda za’ai inzo, Ina tsoron asirina Ya toni, hmm bakasan halin da nake aciki ba, ko jiya saida na kamo Hanya zanzo gidan, ganin ana bin motata yasa na karya kwana na nufi asibiti, saboda raina ya bani akwai wanda ke bin diddigina dole Inyi takatsantsan”

Hankalin Sir Mubarak Ba ƙaramin tashi yai ba, sai faman jinjina kanshi yake Yi, Bai ta6a tsammanin Jazz Yana da wayau ba sai Yau, Har yasan Ana bibiyarshi wato shine Ya canza Hanya, Hakan ya ƙara tabbatar mashi da zargin shi akanshi.

“What are you doing here, baby?”

Muryar Turai ce ta ratsa kunnanshi, Hatta dr Jazz dake a toilet, Sai da Ya ji sautin muryar mutun a ɗakin shi, a yayin da yake atsaye gaban sink, wandon crazy jeans ne da shirt a jikin shi, da sauri Yai rejecting call din Ya tura wayar cikin aljihun wandon shi, Jikinshi Ya hau Yin kerma, Tsananin fargabane Ya kama shi, A hankali Yake tafiya yana nufar ƙofar fita, Kafin fitowarshi da sauri Sir Mubarak Yai wuff Ya nufi Turai dake kallonshi da mamaki akan face dinta ganin Yadda ya ke yima Jazz la6e a ɗaki, Harta buɗe baki zata ƙara yin magana ya yi saurin sanya faffaɗan tafin hannunsa Ya toshe mata bakinta, tare da janta zuwa wajen ɗakin.

Lokacin da Jazz ya fito daga toilet din zufa na bin fuskarshi, ya dubi ko’ina baiga mutun ba, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, har wajen ɗakin Ya leƙa bai ga kowa ba, Hakan yasa shi kokwanton wata’ƙil Kunnuwanshi ne suka jiyo mashi ba dai dai ba, hankalinshi ya kwanta, komawa ya yi cikin ɗakin Ya kwanta saman gadonshi, yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, ga dukkan alamu wani abu yake tunanowa wanda yasa shi fitar da ƙwalla a idon shi.

A bedroom Sir mubarak Ya shigar da turai suna tsaye suna kallon juna, kallon tuhuma take bin shi da shi.

“Nayi mamakin ganinka a ɗakin Jazz kana yi mashi la6e, meyasa”?

Fuskarshi a murtuke babu annuri yace”laifi ne don uba ya shiga ɗakin ɗanshi”? Aruɗe tace”ba laifi bane, amma meyasa kake yi mashi la6e”? Shiru ya yi yana duban fuskarta, A yadda suke atsaye suna fuskantar juna, Ko kafaɗarshi bata kai ba, saboda ƙarantarta, doguwar rigace a jikinta ta shan iska, ta tufke blonde hair dinta da ribbom.

“Ka tsare ni da ido kana kallona, Baka bani amsar Tambayata ba”! a ƙagare ta faɗa, Ya rasa ya zaiyi ya kawar da hankalinta daga tambayar da take yi masa.

Dubara ce ta faɗo masa, da sauri Ya sanya Hannu biyu ya ruƙe waist dinta, sama ya ɗaga ta kamar ɗiyar roba Ya kwantar da ita saman gadon shi Rumfa ya yi mata da faffaɗan kirjin shi, tuni tasha jinin jikinta.

“Kin tsareni da tambaya ke ga mai ɗa ko? Ni da ke waye yafi wani iko da shi? Yawu ta haɗiya muryarta na ɗan rawa ta furta”kai”

“Kinsan da hakan shine kike yi min tambayoyi kamar ƴar jarida”? Shiru tayi mashi tana faman zazzare green eyes dinta.
“Jibarki ƴar mitsila dake kamar in matseki nake ji” dariya ce ta kubce mata, natsuwa yai yana kallon fararen haƙoranta.

“Yanzu dai faɗamin me kike shiryawa a birthday din Baba? Ba za kiyi kitso da ƙunshi ba”?

“Idan zaka kai ni inda za’ai min kitson da ƙunshin inaso, sai dai anko din da zasu sanya nasan hajiya saratu bazata barni in shiga cikinsu ba ko da na siya” a marairaice ta ƙare mashi maganar.

Jan hancin ta ya yi da hannun shi”Ina ruwanki da ita? Ai ba dole sai kin shiga cikinsu ba, babban tarone fa za’ayi akwai manyan baƙi da zasu zo, kema zaki samu ƙawaye acikin su”

Da shagwa6e ta furta”baby ba zaka gane ba, hajiya saratu bata son ganina, ita fa haryan zu kallon ƴar aiki take Yi mini, hada faɗa min wai ba ata6a canzawa tuwo suna, ni dai inajin fargabar ta disgani acikin su, ƙwara Inyi zamana acikin gida zai fiye min kwanciyar hankali” daƙyar ta ƙare maganar ganin yadda ya tsare ta da ido, kallon so da ƙauna ya ke yi mata.

“Meyasa kike kira na baby? Ko kunya bakya ji? Nayi maki kama da ƙaramin Yaro ne?” fuskar shi a ɗaure yai mata maganar.
Kashe mashi ido ɗaya tayi”I call you baby because you’re like a baby to me, and I still take care of you kuma ina feeding dinka” ɗan zaro mata ido ya yi da sauri ta rufe baki tana faman zazzare mashi ido.

Da zolaya ya furta”raini ya fara shiga tsakanina dake, saboda ina tu6e kaya agabanki ko”? Runtse mashi ido tayi tana faman tiƙar dariya.

Jinjina kanshi yai”ki saurare dakyau, daga yanzu idan saratu ta faɗa maki magana ki dinga mayar mata da martani, ki daina nuna kina jin tsoronta shiyasa ta rainaki, Kina jina ko”? Tana faman zumbura mashi pink lips dinta tace”ni bazan Iyaba, saboda ta girmeni ko a shekaru kuma ƙanwarka ce,”

“Umarni nake baki ba shawara ba, kada na kuskura na ƙara ganin kin dawo gidan nan kinayi min jan ido akan saratu tayi maki wani abu, idan ba haka ba zaki kar6i horo mai tsanani daga gareni,” muryar shi a kausace yake yi mata maganar
Kama kunnanta ya yi da yatsan hannun shi”Idan kunne Ya tsira”? Da sauri ta ƙarasa mashi karin maganar”Jiki Ya tsira My baby” murmushi yasaki tare da manna mata kiss saman soft lips dinta.

*GIDAN ƊAN IYA*

Zahra ce zaune saman prayer mat, ta zumbula dogon Hijabi, fuskarta sharkaf da hawaye, tun da ta kammala sallar Magrib bata motsa ba, hannunta ruƙe da cazba sai faman janta take Yi, damuwar duniya ta isheta, tun ɗazu data farka daga bacci ta kasa Yin wanka ko abinci bata ci ba, babu kuma wanda yai tunanin ya leƙo ta, tayi trying kiran layin mahboob yaƙi picking call din, har yanzu bai leƙo cikin gidan ba, ga lokaci yana ta tafiya gani take yi kamar ana ƙara gudun agogon ɗakinta, hannayenta biyu ta ɗaga sama tana jera addu’o’i akan Allah Ya kawo mata mafita.
Chapter 91 · 0% Book details