← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 152

Sashe 112

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aneelerh da ƙarfin Hali tace”idan kinga na fita gidan nan to nagama faɗin ta cikina ne, Kuma wallahi koda gigin wasa kika ce zaki ta6a lafiyar jikina saina naƙasa ki bakisan wacece Ni ba” ta faɗa tana jefa mata harara, lamarin Ya ɗaurewa Hajiya falmata kai, ganin karfin hali na Yarinyar nan data zo gidanta tana Yi mata rashin Kunya.
Goya hannayenta tayi saman ƙirjinta”ina sauraronki, Me ya kawo ki gidana!”
Gyaɗa Kai Aneelerh Tayi”zuwa nayi don Inyi maki nasiha, don na fahimci Wadda iyayenki suka yi maki tuni shaiɗan Ya hure maki kunne, dan Allah Jibarki cikin shiga ta mutunci kamar wata mutuniyar arziƙi, al’halin nan kuwa fuska biyuce ke, A fili musa a zuciya fir’auna, Haba baiwar Allah, Da hankalinki da tunaninki da shekarunki kika za6i ki sa6awa Allah don kawai ki ji daɗin duniya? Kin manta da Allah yana ganinki kuma zaki mutu ki koma gareshi, a ko’wani yanayi mutuwa tana iya riskarki, idan taƙamarki kuɗine ki tuna Allah ne Ya baki Arziƙin bake kikayi ma kanki ba, Idan yaso zai Iya ƙwace wa, kuɗi da kike gani wallahi masifane Idan baka tafiyar dasu ta hanyar da ta dace ba, Ita kuma rayuwar duniya jin daɗinta ƙalilan nan bata da tabbas, bakisan yaushe zaki mutu ba, kin sanya mugunta aranki saboda Allah Ya azurtaki, Kina cutar matasan Ƴan mata, waɗanda Iyayen su suka sha wahalar basu tarbiya ke kuma kina gur6ata masu rayuwarsu, Allah kaɗai yasan adadin Ƴan matan da kika 6ata, kin goga masu jarabar da bazasu Iya gogeta ba, Kin cutar da rayuwarsu mutane suna kuka da su saboda sun addabi rayuwar al’umma kuma ire-iren ku ne ku ka yi silar lalacewarsu, wallahi kiji tsoron Allah kamar yarda ba zaki so ayi da ƴar ki ba to kema kada Kiyi da ɗan wani, duk da naji irinku Harda ƴa’ƴan naku kuke Yi, saboda shafewar basira da neman duniya kun makance bakwaji bakwa gani ku ala dole saikun siyama kanku tikitin shiga wuta”? Tun da Aneelerh ta soma Yi mata magana da faɗa haɗi da tsiwa take ta faman zare ido tana binta da kallo, tun da take arayuwarta wani ɗan adam bai ta6a gigin tunkararta Ya faɗa mata magana game da abunda Take aikatawa ba sai Yau da Allah Ya haɗa ta da Auntyn Zahra mai dimple, Ayoyin kur’ani aneelerh ta soma karanto mata tana fassara mata, kamar an rufe mata baki takasa dakatar da ita duk irin masifar da take da ita yau an kashe mata bakinta
“Allah Yana son bayinshi waɗanda suka aikata 6arna suka tu6a saboda tsoronshi suka koma gareshi, dan Haka ina baki shawarar tunkafin lokaci Ya qure maki Hajiya falmata ki Gyara Halayanki, Ni bance zan sanyaki ki shiryu ba don nasan irinku taurin kaine daku kamar kwakwa, ko malamai sunyi maku nasiha bakwaji bakwa gani sai ranar da Allah Ya damƙe ku tukunna zaku gane kurenku, Ni in banda ma shafewar basira, wai ku bakwa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari ne? Baku tuna duk abunda kuka mallaka zai ƙare, daga kai sai halinka za’a binne ka a ƙabarin ka fa? Ke yanzu kin za6i ki mutu kina aikata mummunan zunubi na bin Ƴan uwanki mata? Ga hakkin Iyayen da kika sanyasu zubar da hawayensu ta silar lalata masu rayuwar ƴa’ƴa da ki ka yi ga kuma Matasan ƴan matan da kika gur6ata ma rayuwa, wannan fa zunubine mai cigaba da yaɗuwa ko bayan kin mutu zaki cigaba da samun kamasho acikin shi, saboda kinbar tarin ƴan matan da kika gur6ata agari suna aikata fasadi, wallahi kiji tsoron Allah tunkafin lokaci Ya qure maki, Ina ƙara jan hankalinki ki tuba ki koma ga Allah tunkan mutuwa ta risƙe ki don ita bata kwankwasama mutun ƙofa balle Yace zai shirya mata”

Wata irin zuface ta soma wanke goshin Hajiya falmata, Haƙiƙa kalaman Aneelerh sun fara karya mata zuciya, sai faman zare ido take Yi, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin maganar Aneeleerh ba, Yarinyar tayi matuƙar burgeta kuma ta bata mamaki da har ta iya yi mata nasiha batare da jin shakkarta ba, saboda mutane dayawa basa Iya yin magana agabanta, amma Ita wannan ido cikin ido take furta mata magana .

“hajiya falmata, duk runtsi duk wuya kada ki Karya zuciyar wanda Ya aminta dake! Ina magana akan zahra da ta dauke ki tamkar mahaifiyarta saboda ƙaunar dake a tsakaninta da ƴarki fatima, Kin karya mata zuciya, naji daci lokacin da na sameta ta kulle kanta acikin toilet tana Yin kuka babu ci babu sha ita kaɗai batare da kowa ya sani ba, Kin hanata runtsawa saboda taƙi baki haɗin kai ku aikata sa6on Allah, haba baiwar Allah, idan kece akayima yarki haka zakiji daɗi! Don kawai mutun Na buƙatar agazawarka sai kayi anfani da dukiyarka donka cutar dashi? Babu wanda yafi ƙarfin ya nemi taimako a duniyar nan, koda ba a wurin mutun ɗan uwansa ba, zai nema awurin Allah Idan har baka agazama bawansa ba tayaya kake tunanin zai agaza maka?

Jinjina kai Aneelerh tayi, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskarta cikin muryar kuka taci gaba da cewa”Kin ƙona mata rai, zahra ta yarda dake fiye da tsammaninki, tana kuka tana fadamin yadda ta aminta dake amma kika karya mata zuciya, Zahra da kike gani tafi ki Hankali, Yarinyar tana da tawakkali, tana jin tsoron Allah, Na jarabata don inga ko tana da wayon jure ƙaddara idan ta sameta, Ni dakaina nabata shawarar ta baki haɗin kai, da buɗar bakinta sai ce mun tayi ita ko duniya za’a mallaka mata bazata ta6a amincewa ta sa6ama Allah ba, saboda tana jin tsoron shi kuma tana jin tsoron ranar da zata koma gare shi, Hajiya falmata kin ta6a tunanin hakan? A matsayinki na babbar mace wadda ta haura shekara arba’in da ɗuriya a duniya? Shekaru sunja amma baki tsoron mahaliccin ki? Kina amfani da dukiyarki wurin Gur6ata duniyarki da lahirarki, maimakon kiyi amfani da su wurin taimakon bayin Allah marasa ƙarfi wadanda zasuyi alfahari dake ko bayan ba ranki kuma ki samu lada awurin Allah, Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar da kika daukarwa kanki”!?

Ƙafafuwanta ne suka gaza ruƙeta, Jiri Ta soma gani a cikin idanuwanta, adaddafe ta nufi sofa ta zauna tana faman fitar da numfashi.

Hankaɗe Kafaɗa Aneeleerh Tayi”Alhamdulillah nagama faɗar ta cikina, duk wanda yayi da kyau don kanshi, akwai mutuwa akwai hisabi, maganar kuɗi Kuma nazo maki da su miliyan Uku Cuf, Idan ma kina son ƙari zan ƙara maki, saboda inaso kisan muba jinin faƙirai bane idan arziƙine muma mun gaje shi gaba da Baya”

Ɗaga murya Aneelerh Tayi da ƙarfi ta furta sunan Mahboob, shigowa ɗakin Yayi hannun shi ruƙe da jaka baƙa, tunkan ya ƙarasa yake bin ko’ina da kallo, ganin haɗuwar falon gidan aranshi Ya ayyana Lallai hajiyar nan ta tara shiyasa take tsula tsiyarta son ranta saboda tana da arziƙi.

“Zoka ajiye mata tsiyarta,” Aneelerh ta faɗa tana nuna mashi gaban Hajiya falmata, Ta zabga uban tagumi da hannu biyu, da alamun nadama atattare da ita.

Koda mahboob Yayi arba da fuskarta saida yasha jinin jikin shi ganin yadda ta haɗe rai, ga gumi na fita a goshinta.

Kamar mai jin tsoronta Haka Ya ajiye mata jakar agabanta.

Aneelerh ta ruƙo hannun shi acikin nata, har sun ɗaga ƙafa zasu bar falon muryar Hajiya falmata ta dakatar da su
“Dan Allah Ku tsaya”!! Kusan atare zuciyarsu ta buga, a sukwane suka waiwayo suna dubanta, Gabansu ba ƙaramin faɗuwa yayi ba ganin ta fashe da kuka, miƙewa tayi daga saman sofa din ta nufe su tana fadin”wallahi nayi nadama, dan Allah kuyi haƙuri da abun kunyar dana aikata, Nima ba halina bane ƙawayene suka tunzurani har na faɗa harkar” zubewa tayi saman gwiwowinta agaban aneelerh tana kuka tace”Tun da nake a rayuwata wani ɗan adam bai ta6a yi mini nasihar data ratsa zuciyata ba sai akanki, bansan wacece ke ba, amma nayi sha’awar In yi koyi da kyawawan halayanki, duk naji na tsani kaina, na zubda mutuncina da girmana a idon zahra, wallahi naji kunyar da ban ta6a jin taba, Naji ƙuncin Halin dana jefa zahra, saboda ni tagaza runtsawa Na hana baiwar Allah yin bacci na hanata cin abinci, na jefa rayuwarta cikin ƙunci batare da nayi tunanin raɗaɗin da zataji acikin Zuciyarta ba, wallahi nayi nadama koda ace bazaku yarda dani ba, Na tuba kuma in sha Allah bazan ƙara aikata zunubin nan ba, angama bi’iznilillahi, saboda inaso Inyi kyakkyawan ƙarshe kuma inaso in tsira ranar gobe ƙiyama, In sha Allah daga yanzu nagama yin amfani da dukiyata don in sa6awa Allah, da kuma gur6ata tarbiyar ya’yan mutane.....”daƙyar ta ƙare maganar tana faman jan magina.

Ba Aneelerh ba hatta Mahboob Yayi mamakin wannan Ikon Allahn, sun yi sototo suna kallonta kamar sakarkaru duk ta zama abun tausayi tsoron Allah ya shigeta, wata’ƙil dama itace silar shiriyarta shiyasa Allah Ya haɗasu da ita.

Muryar Hajiya falmata na rawa tace”Ku taimaka mun dan Allah, inason in wanke kaina awurin zahra, saboda inason taci gaba da kallona kamar yarda tasanni ada, Nayi alƙawarin zan taimakamata, kuɗin da ku ka zo dasu na yafe mata ku ɗauka ku maida mata su, Sannan inaso taci gaba da yin aiki a company dina, Kayan da suke son ayi masu order A dubai gobe in sha Allah zasu iso Nigeria”

Kallon juna mahboob da Aneelerh suka ƙara Yi, Atare suka furta Alhamdulillah, Aneelerh tace”nagode ma Allah daya bani baiwar Iya tsara kalamin da har suka ja hankalinki, Naji daɗi dana zama silar shiriyarki, Ina fata zaki canza rayuwarki daga Yau ki koma ta gari, wadda kowa zaiyi alfahari da ita”

Jinjina kai Hajiya falmata tayi Cikin sanyin murya tace”in sha Allah,” ruƙo hannayenta aneelerh tayi acikin nata, miƙewa tayi tsaye suna fuskantar juna
“Ki godema Allah, saboda Yana son ki da shiriya shiyasa Ya baki damar gyara rayuwarki tun da sauran numfashinki,”

Jinina Kai Hajiya falmata tayi.
Aneeleerh ta ƙara da cewa”sai dai kiyi haƙuri, ba zamu maida kuɗinba, nariga dana kawo maki dasu, Ki ruƙe su a hannunki, zahra kuma bazata ƙara Yin aiki a companynku ba, zan nema mata aiki awani wurin”!!
Chapter 112 · 0% Book details