← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 152

Sashe 151

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

His excellency abdul razak Yace”ai kuwa dai shine, don jiya ko bacci baiyi ba tsabar firgici, yanzu haka ma da kake ganin shi a kwance daƙyar muka samu yayi bacci’
“Abu baiyi daɗi ba” pravin ya faɗa yana ɗan girgiza kanshi”ubangiji Allah ya bashi lafiya” atare suka amsa mashi da Ameen.
Senate lateef ya ɗaura da cewa”ni yanzu so nake naji daga bakin shi Owais, ya faɗa min wanene macijin menene alaƙar shi dashi”
“Bari na kira shi awaya, ai jiya yace zai shigo yai mana bayani amma shiru kake ji wai malam yaci shiru” Deen ne yai maganar tare da curo wayarshi daga aljihu ya danna ma Chif Owais Kira, kusan sau uku tana yin ringing bai yi picking ba.

“Bai ɗaga ba, may be baya akusane da wayar” ya fada yana kokarin maida wayar cikin aljihun, kwatsam kiran owais ya shigo wayar tafara ruri, ajiyar zuciya ya sauke tare da duban su yace”shi ne ke kira,” ya fada tare da yin picking din kiran Ya kara wayar a kunnanshi, bayan sun gaisa deen yace”muna ta tsammanin zuwanka gida shiru baka shigo ba, ga babanku nan kwance ba lafiya saboda abun da ya faru jiya ko runtsawa baiyi ba sai firgita yake yi”.

On the other hand chief Owais ya furta”I will come later, insha’Allah,”

“Okay, we’ll be waiting for you, sannan inason sanin Ina macijin nan yake? Naji kace mutunne”
Muryar chief owais tamkar bai son furta maganar yace”please uncle can i text you” deen yace okey ba damuwa”, rejecting call din yayi, kafin wani ya furta magana ƙarar shigowar saƙo Ya dakatar da su.

Karanta sakon Deen ya soma yi duk sun ƙura mashi ido suna jiran jin me zaice masu, musamman pravin har wani zoƙa kai yake yi yana leƙen wayar Deen.

Ɗagowa yai da alamun mamaki akan fuskarshi yace”tabɗijancan, wallahi dagaske macijin mutunne wai shaidanun aljanune a jikinshi, yanzu haka ya rikiɗa ya koma mutun acan gidanshi yake zaune,........” aruɗe suke kallon shi.

“Wai ko kunsan Prime minister namu shine ya tura da jet din da zai ɗauko sheikh imam daga sudan saboda kawai ya taimaka ma macijin ya dawo halittarsa”?
Jin wannan maganar ba ƙaramin firgita senate lateef yayi ba ranshi a6ace ya furta”what? Bangane me kake nufi ba! Yaushe akayi hakan?batare da sanin mu ba!” a kausashe ya furta maganar,, a sukwane his excellency abdul Razak Ya miƙe Yana fadin”Anya ka karanta saƙon nan dai dai, bani wayar na duba, ya furta hakan tare da kar6ar wayar Deen Yana duba sakon, bayan ya gama yace”ba shakka, kuwa owais dinne ya rubuta da kanshi, magana ta tabbata prime minister namu shi ya tura da jet din daya dauko sheikh imam daga sudan don kawai a duba yaron, muna nan zaune muna jinyar ubanmu shi yana can wajen taimakon yaron da bamusan wanene shi ba, bamu haɗa alaƙar komai da shiba, bansan meke damun prime minister ba, daga shi har owais din shegen son taimakonsu shi zaija su jefa family dinmu cikin matsala ......” kafin Deen Ya ƙare magana senate lateef daya gama fusata yana huci yace”Wallahi basu isa ba, ni bani buƙatarma jin wani ƙarin bayani daga garesu, Yaron nan bazai zauna a estate dinmu ba, tunkafin aje ko’ina harya fara mallake zuciyar ɗan uwanmu hakan na nufin da wata manufa ya shigo family dinmu, zai iya yiyuwa wasu mugayen ne daga maƙiyan jam’iyarmu sukayi amfani da shi don su tarwatsa family dinmu, ku duba kuga fa duk gidajen dake a estate dinmu bai shiga kowanne ba, Ya tsallake nasu Ya faɗo gidan babanmu saboda shine target dinsa.....” a harzuƙe senate lateef Ya ƙare maganar.
Kanwa uban Ƴan Zigi Pravin Ya haɗe girar ƙasa da sama yace”Ni dama tun Jiya hankalina bai kwanta da shigowar macijin nan ba, Ai daga jin yadda abun ya faru zaka shaida makircine aka shiryama baba, so suke kawai su kashe shi, in ba haka ba taya za’ai ace wai mutun ya koma maciji ai sai dai idan sihirine da shi, munafuki kawai wallahi bazamu yarda ba, Yaron nan bazai zauna mana a estate dinmu ba, dole ne owais Ya kore shi daga estate dinmu, sannan A yanke alaƙarshi da kowa na family dinmu idan ba haka ba zaija mana masifar da bazamu Iya shawo kanta ba” Rai a6ace pravin yayi maganar Yana kallon fuskokinsu.

Jinjina kai kowan nan su yayi alamar gamsuwa da bayanin pravin,
His excellency abdul razak Yace”Ai bazamu ta6a yin gangancin nan ba, mu jira owais din ya shigo anjima, shima hateem din Zanyi waya da shi”
Pravin yace “yamakata atara kowa har shi kanshi yaya sharafuddeen din yazo yaji abun da owais ke shirin janyo mana a family, wallahi jiya Saratu batayi bacci ba, saboda fargabar macijin nan, sambatu ta dinga yi min tana kuka tana fadin gashi nan zai sareta, duk tabi ta haukace ta rikice min aɗaki, daƙyar nashawo kanta da ayar Allah”
Aruɗe Senate lateef yace”kunji ko? Tun yanzu ana kokarin ganin bayan ahlinmu”
Damuwa ƙarara akan fuskar Deen yace”Pravin kana nufin saratu batayi bacci ba jiya saboda macijin”? Batare da ɗar ba yace”bata yi ba yaya, yadda taga rana haka taga dare, ni na zauna ina yi mata fifita saboda zufar dake tsastsafo mata gafa ac a daki amma haka ta dinga zubda gumi”
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar pravin
Murya na rawa his excellency abdul razak Yace”Yanzu awani hali take ciki? Tayi bacci da safe?
Girgiza kai pravin yai fuskarshi da alamun jimami yace”batayi ba idonta biyu ko abinci takasa ci,”
“Inason ganinta pravin” acewar abdul razak”
Pravin yace toh, bari naje nazo da ita ya juya jiki na 6ari ya fuce daga ɗakin.

Yana fitowa daga dakin su ka yi kici6us da Hajjaty, ta ɗauki wankan bubu gown ta lace a jikinta, ta ca6a uban ado, ƙamshin turarenta ya buɗe ko’ina, mayafin rigar asaman kafaɗa ta daurashi, doguwar suman kanta ta zubo har gadon bayanta, Hannayenta biyu ruƙe da faffaɗan tray daga saman shi an ɗaura jerin kayan abinci.
Wani mugun kallo da pravin ya watsa mata saida gabanta Ya faɗi, duk tabi tasha jinin jikinta, sarai tasan ya hanata yin kwalliya idan har bashi zatayi mawa ba amma taƙi jin maganarshi.
Sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take yi, tayi mashi kyau sai dai yaji haushin adon data ca6a.
“Kin manta gargaɗin da nayi maki? Baki jin maganata ko”? muryarta na rawa ta furta”am sorry dear, na saba ne” guntun tsoki Yaja “yanzu ahaka zaki shiga dakin obie, bayan kinsan bashi kaɗai bane aɗakin, Balagaggun ƴa’ƴansa duk suna aciki, duk kamun kansu bazasu iya jure shaƙar ƙamshin turaren jikinki ba batare da kin jefa su yanayi ba, ko kallon ki su ka yi sai sun ayyana wani abun aransu....” shiru tayi mashi ba tare da tace komai ba, numfasawa yayi kafin ya ɗaura da cewa”bazan bari ki shiga ɗakin ahaka ba, sai dai ki haƙura da kai masu abincin ki koma ɗaki ni sai in kai masu”

muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”dan Allah dear ka barni in kai masu, Jiya fa bansamu damar gaishe dasu ba”da shagwa6a tayi mashi maganar, nan take kasala tafara kama shi, matsawa yayi dab da ita, ya ruƙo mayafinta data ɗaura kan kafaɗarta, ya janyoshi zuwa saman kanta ya lullu6e mata sumar kanta da kirjinta saboda yana jin kishin agane mashi majiyar dadin shi, ƙoƙarin manna mata kiss yayi saman red lips dinta, kamar daga sama yaji ance”Daddy!” A firgice pravin ya ɗago yana faman zazzare idanuwanshi Jin muryar zayn, su biyune hannayensu ruƙe cikin na juna shida Zaid, fuskokinsu da alamun ruɗani, kafin ƙarasowarsu pravin yayi saurin ɗaukar juice dake acikin jerin drinks din tray din hannun hajjaty ya buɗe murfin ya watsa mata ruwan lemun gefen galenta, baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, mugun tsoron Zayn take yi, tasan muddin ya gane abun da pravin ke ƙoƙarin yi mata sai ta yaba ma aya zaƙinta, ajiya juice din pravin yayi, ya dai daita natsuwarshi, ya nufesu fuskarshi dauke da murmushi ya ware masu hannayensu da niyar yayi hugginsu dinsu,
Sai dai sunƙi bashi haɗin kai, wani irin matsiyacin kallon zayn yake watsama hajjaty data juya masu baya.

Adabarbace pravin yace”kun ganmu atsaye ko? na fito daga ɗakin baba ne na bankaɗeta batare dana ankara ba” kallon tuhuma Zayn yayi mashi kafin yace”daddy mayafinta fa naga ka ruƙe a hannunka akan wani dalili”
“Baka ji mena ce ba, bugeta nayi har tray din hannunta ya girgiza lemu ya 6arar mata jikin gyalenta shine fa na ruko gyalen ina ƙoƙarin goge mata” yayi maganar tare da juyawa ya ruƙo bakin gyalen hajjaty yana nuna masu,
Ajiyar zuciya zayn ya sauke, zaid yace”daddy barka da safiya, ya gajiyar jiya” ya faɗa tare da yin huggin dinsa, pravin yadan bubbuga bayanshi”Alhamdulillah My son, Ina fata kun tashi lafiya, Yau ba zaku shiga office bane” cikin kulawa yayi maganar, hankalinshi na kan zayn, ya lura yafi ɗaukar zafi halinsa ɗaya dana jatumarsa wurin iya masifa.
Chapter 151 · 0% Book details