Sashe 68
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya yi matuƙar Yin mamakin ganin room ɗin da ya ke aciki, a kasalance ya yunƙura Ya miƙe zaune yana ƙarewa ko’ina Kallo, tunani ya shiga yi Ina ne nan? Waye ya kawo su? Fuskarshi da alamun ruɗani ya Tura yatsun hannunshi cikin yalwatacciyar sumar kanshi yaci gaba da cakuɗata tamkar yana sosata, saukowa ya yi da ga saman gadon.
Jikinshi yayi mashi nauyi daƙyar yake taka ƙafarshi, yayin da yake ƙarewa ɗakin Kallo, Angel tana a duƙe tun da tayi sujjada bata ɗago ba, addu’o’i take tayi masu.
Yana ƙoƙarin buɗe baki da niyar ya yi mata magana, Sai ga doctors da nurses sun shigo ɗakin da saurin su, Kusan atare su ka ci uban burki suna kallon kallon a tsakanin su da shi, Mutumin da suka daɗe suna mararin ganin Ya farka, sai yau Allah ya nufa zai tashi, Sun yi matuƙar girgiza da ganin Shi a tsaye kan ƙafafun shi, kyan fasalin shi Ya yi masu ƙwarjini.
Da hannu Yai masu Alamar su wanene su? Sai Ƴan kame kame suke Yi An rasa me Iya buɗe Baki Yayi mashi magana.
Juyawa yai da sauri Yaje gaban Angel da ta yi sujjada, Da hannu ɗaya ya ruƙo damtsen ta, Ya ɗago da ita tsaye kamar wata ƴar baby, nuna mata likitocin Ya yi da hannun shi
“Who are they, and where are we?”
daƙyar ta samu natsuwar Fayyace mashi komai tun daga kan Yadda aka tsunto su a daji aka zo da su asibitin kamar yadda Gabriel Ya sanar da ita.
Bayan ta gama kora mashi jawabi ta kalli fuskokin likitocin tace “ku ta ya ni murna ɗan uwan mu Danish Ya farka”
murmushi kowan nan su Ya saki Nurses din dake a cikinsu kamar sun samu tv haka suke Binshi da mayataccen kallo, ba mazan ba ba matan ba.
“Muna ta ya ki Murna masoyiya Angel, munga brother ɗinki Ya farka cikin koshin Lafiya” nurse jessica ce Tayi maganar
Daƙyar wani dr ya iya buɗe baki yace”Danish Fatan Ka tashi Lafiya, tsawon lokaci muna jiran ranar da zaka buɗe idanuwanka, Sai yau muka samu damar ganin ka, Mun ji daɗi sosai” yai maganar tare da miƙa mashi hannu don su gaisa, Man ɗin fa bai yarda da su ba, dama yana da wuyar sha’ani ga ƙiwuya kamar ƙaramin Yaro.
“Danish Ka miƙa mashi hannu ku gaisa” Angel ce tayi mashi magana, goya hannayenshi yai saman broad chest dinsa, Alamar ba zai miƙa mashi hannun ba”
murmusi yaƙe ta ɗan saki”ku yi haƙuri, Danish baisan ku ba, Har yanzu baccin bai sake shi ba, nasan kafin zuwa gobe zai Warware’
Nurse rebecca tace “badamuwa, Dama mu fatan mu Ya farka da ranshi da lafiyarshi, Hakan ma ya wadatar”
Dr. Anthony Yace”Calm down, Danish. No one will bother you. We are doctors, and we have the right to check your health until you feel better.” still bai tanka masu ba.
Dr harry yace”ni dama tun kafin Ya farfaɗo raina Ya bani zai yi wuyar sha’ani, sai gashi maganata ta tabbata, mutane masu irin Kyanshi bakowa suke kulawa ba” da zolaya yai maganar, Ya ƙara da cewa “mu dai yakamata asaki jiki damu tunda malaman lafiya ne, muna so ka bamu dama mu ƙara bincika Lafiyarka” tun da suka fara Magana bai tanka masu ba sai kallo da yake binsu dashi kamar yaga wasu halittu daba na mutane ba.
“Ko akwai Inda ke yi maka ciwo yanzu”? Dr anthony ne yai mashi maganar, Angel sai ƙoƙarin ingiza hannunshi take Yi don yayi masu magana amma Yaƙiya, Nurse jessica tace”ga dukkam alamu rowar muryarsa yake yi mana, Ni inaga Mu ƙyale shi zuwa gobe nasan zai warware kuma zai saki jiki da mu”
Kamar za su yi hauka wurin yi mashi magiya don yayi masu magana yayi shiru abunshi, har so sukayi su bincika lafiyarshi amma Ya hana, duk wanda yai gigin matsowa kusa dashi, zazzare masu ido yake yi alamar zaiyi fighting dinsu, lamarin ya ɗaure masu kai, ganin sun sanya naci akan sai sun duba shi, Angel ta roƙe su akan su ƙyale shi zuwa gobe, fargabanta kada su hayaƙa shi azo asamu matsala, tunda harya fara zare masu ido yana ɗaure masu fuska. Ba don sun so ba, su ka yi masu sallama da niyar gobe zasu dawo, kusan atare suka fuce waje, aransu suna Ayyana irin kyawun fuskarshi da surarshi, sai santin shi suke Yi musamman nurses din cikin su.
Su Uku Suka rage a ɗakin, Nurse Jessica ta dubi Angel”na lura brother ɗin nan naki, ke kaɗai yake jin maganarki, Inaso ki tambayar min shi ko akwai abunda yake buƙatar ci”? Kallon shi Angel Tayi, idonshi na akan plasma tv ta ɗakin, sai ƴan kalle kalle yake yi.
“My man kana jin Yunwa”? Da budar bakinsa sai cewa yai”Ina haris da su Batul? Inason ganinsu”
Kallon Nurse din Tayi”yace yana son ganin ƴan uwanmu” gyaɗa kai tayi”badamuwa Zamu Iya zuwa”
Ruƙo Hannunshi tayi acikin nata”muje in nuna maka su” nurse jessica tana agaba suna abayanta, tun da suka fito daga ɗakin Yake ƙarewa ko’ina kallo, agogo kaɗai mutun zai kalla ya gane cewa dare ne amma donta hasken light bulbs na asibitin ba za ka ta6a gane dare bane.
Nurses ɗin dake yin zarya da doctors sai satar kallon shi suke yi, hada masu yin tuntu6e.
Ɗakin Haris suka Shiga, tun bayan fitar Angel bacci ya ɗauke shi.
Rabin jikinshi lullu6e da bargo, da sauri Danish ya ƙarasa daga gefen gadonshi Ya zauna Yana kallon shi, nurse da Angel suna a tsaye suna dubanshi.
“Bacci ya ke yi Danish, ko zamu bari sai gobe idan Ya farka mu dawo” ɗaga mata kai Yai alamar eh, dama burinshi ya gansu hankalinshi sai yafi kwanciya, ɗaura hannunshi yai saman sumar kan Haris ya shafata a hankali, tsantsar farin Cikine akan face dinsa’ mintuna Biyar kafin Ya miƙe, suka nufi ɗakin Batul, ko da suka shiga, basu sameta a saman gadonta ba, nan fa hankalin Angel Ya tashi, “ina batul taje” nurse jessica harta buɗe baki zata bata amsa, suka ji motsin fitowarta daga toilet, Kamar a mafarki take kallonsu kafin ta tsayar da idonta kan Danish, da ƙarfi ta ambaci sunanshi, da gudun gaske fa ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi, ɗaura Hannayenshi yai saman bayanta sosai ya yi tighting ɗinta, daɗi kamar zai kasheta, annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake yi, da alama yaji daɗin canjin rayuwar da suka samu.
Ɗagowa tayi da kanta daga saman chest dinsa, ido cikin ido suke kallon juna, tuni hawaye sun cika idonta muryarta na rawa ta soma yin magana
“Ɗan uwana rabin raina, kaga canjin rayuwar da muka samu ko? Nasan Angel ta faɗa maka komai, Danish ba zamu Iya misalta kewarka da mu ka yi ba, wlh naji daɗin farkawarka nayi farin cikin ganinka” a tsanake ya furta mata”nima nayi farin ciki Batul, Ina taya mu murna, ina yi mana fatan wannan ya kasance ƙarshen wahalarmu” Angel da nurse jessica sai murmushi suke saki yayin da suke kallonsu.
“Danish nasan za ka ji wani iri, nan ba kamar prison ba, inda aka ƙuntata rayuwarmu, tun muna Yara wannan ne karo na farko da muka fara tsintar kanmu awajen prison cikin mutanan duniya, Iskar da muke shaƙa a yanzu ta ƴanci ce bata kurkukun ƙaddara ba” kalamai masu daɗi take faɗa mashi
“Muna samun kyakkyawar kulawa awurin mutanan nan” tayi maganar tana nuna mashi nurse jessica”sun bincika Lafiyarmu, kuma sun taimaka mana wurin samun sauƙi, sannan muna samun Cin abinci har sau uku arana, komai muke so sunayi mana, Ina fata kaima zaka saki jikinka da su sannan ka ba su haɗin kai donsu duba lafiyarka, idan akwai wani abu dake damunka zasu taimaka maka wurin samun sauƙi in sha Allah, sannan idan kana Jin yunwa ka yi masu magana zasu baka abinci, ba sai kasha wahalar neman abunda zaka Ci ba...” muryarta na rawa ta ƙarasa maganar, hawaye tuni sun cigaba da wanke face dinta
Ɗaura tafin hannunsa yai saman face nata, share mata hawayen fuskarta ya soma Yi Calmly ya furta”its ok, stop shedding ur tears, ngde da shawararki, zan basu haɗin kai,”
“Danish babu wasu kalmomi da zan Iya yin amfani da su wurin yi maku godiya kai da Angel, Allah ne kaɗai zai Iya biyan ku, haƙiƙa kun taimaki Rayuwarmu kun gatanta mu, kun yi mana silar barin mu kurkukun ƙaddara, duk wani cigaba da zamu samu a duniyar nan kune sila, ba zamu ta6a mantawa da halaccin ku agare mu ba, kun fiye mana iyayenmu sau dubu, matsayin da suka rasa awurinmu kune kuke ruƙe da shi....” sosai ta fashe masu da kuka, Janyota yai zuwa saman chest dinsa ya ƙara yin hugging dinta yana lallashinta.
Daƙyar ya samu Batul ta dakata da yin kukan, bayan ya raba ta da jikinsa, ta rungume Angel sosai suka ƙanƙame juna, tsawon mintuna kafin suka raba jikinsu.
“Allah yabar Mana ke, Our Super star, Allah ya cika maki burikanki dake da Danishi ɗinmu” murmushi kowan nan su ya saki, sun ɗan jima a ɗakin Batul kafin suka Yi mata sallama, Sauran ɗaku nan su Azeeza suka shiga kowan nan su bacci ya ke yi, Ya haƙura sai zuwa gobe zai gaisa da su.
Komawa ɗakinshi su ka Yi, nurse jessica tace da Angel, zata kawo mashi Abinci, kafin ta dawo ta taimaka mashi Ya shiga toilet ya gyara jikin shi, amsa mata tayi da toh, Bayan fitar nurse ɗin, Taja hannun Danish suka shiga toilet, tun da suka shiga yake bin ko’ina da kallo, Karaf Ya ɗaura Idonshi Kan madubin toilet din A firgice taga Ya Juya mashi Baya.
“Danish meya faru”? Hankali atashe tayi mashi Tambayar
“Bana son ganin shi,” ba ta yi mamakin jin abunda yace mata ba, tunawa da ranar da tsohuwa tamira ta basu kyautar madubi, kowa ya duba fuskarshi, amma shi Yaƙi Yarda ya kalle shi.
Dubara tayi wurin Cire Hijabin jikinta, taje gaban mirror ɗin ta lullu6e shi.
“Nayi maganin matsalar Juyo ka gani” a hankali Ya juya yana kallon mirror din nan take ya sauke ajiyar zuciya, ganin ta rufe madubin.