← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 152

Sashe 43

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ran Hajiya saratu ya 6aci matuƙa, sai faman jinjina kai take yi tana fadin”bari naje wurin baban, yanzu har takai ga ƴa’ƴana aka kushewa agaban sakaran yaron nan jazz? suma waɗanda suka yi maganar zasu fuskanci 6acin raina wlh, zasu san dani suke magana” takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana neman mayafin da zata yafa, Pravin hada saurin rigata ƙarasawa gaban closet ɗin kayansu Ya buɗe ya ɗauko mata mayafi da kanshi ya ɗaura mata shi asaman kanta, A fujajen ta fuce daga cikin ɗakin, fitarta keda wuya pravin ya soma sakin shu’umin murmushi, ba tun yau ba ya saba haɗata faɗa da ƴan uwanta, mugun munafuki ne na bugawa a jarida, A zubin halitta idan ka kalle shi tamkar Namiji.

Bayan fitar Hajiya saratu da ƴan mintuna, ya sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin zame jallabiyar jikin shi da niyar canza kaya, Sallamar Abla ta ratsa kunnuwanshi, Jimm ya ɗanyi kamar bazai amsa mata ba, daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta”shigo daga Ciki” a hankali ta turo ƙofar, Hannunta biyu ruƙe da faffaɗan tray na Kayan breakfast ɗin Hajiya saratu.

Ganin Pravin shi kaɗai a ɗakin Yasa ta ɗanji faɗuwar gaba, miryarta na rawa ta furta”umm..amm dama Kayan breakfast ne na kawoma Aunty saratu” lumshe idon shi Ya ɗanyi, tare da tunkarota Ya ruƙe tray din hannuta”bari na ƙarasa shigar maki da shi ciki,” kar6a yai tare da juyawa ya ɗaura tray ɗin saman table, kafin Ya juya ta yi saurin kai hannu zata tura ƙofar ɗakin saboda sanin halin shi, sai dai kafin ta kaiga ƙarasawa ga ƙofar yai saurin damƙota ya janyota zuwa jikinshi, Hankalin abla Ba ƙaramin tashi yai ba tsananin tsorone da fargaba duk ya cikata, ƙamshin turarensa ya addabi hancinsa, cikin shessheƙar murya take faɗin”pls ka sake ni dan Allah, na roƙe ka kada kaja min bala’e,” kwantar da kanshi yai saman kafaɗarta dogon hancin shi na gogar fatar wuyanta, yayin da hannayensa ke asaman ƙirjinta ahankali yake matsasu, kamar zatayi hauka ƙoƙarin kwace kanta take yi saida ya hanata yin haka saboda ƙarfine dashi kamar doki, fashewa tayi da matsanancin kuka tana yakushin hannunshi da akaifun hannunta kamar zatayi hauka.
“Nashiga uku, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Ya Allah ka kawo min ɗauki,” hankalin shi kwance yake cigaba da ƙoƙarin tura hannayenshi cikin rigarta

“Daddy!” muryar Zayn ce tasa shi saurin sakin Abla, ɗaure mata fuska yai

“Don’t you dare tell anyone what happened. Wipe ur tears off your face right now.” Jinjina mashi kai tayi da sauri ta sanya ƙasan rigarta ta share hawayenta, shu’umin murmushi pravin ya saki’Good zaki Iya tafiya sai mun haɗu wani lokacin” wani irin ɗaci taji acikin zuciyarta, Tana buɗe ƙofar ɗakin taci karo da twins, ko kallonsu batayi ba da sauri tabi ta gefensu ta wuce, awata ƴar corner ta la6e ita kaɗai ta zuƙunna tana cigaba da yin kuka haƙika pravin ba ƙaramin cin zarafinsu yake yi ba, shiyasa suke gudun zuwa su tarar da shi a ɗakin Hajiya saratu musamman idan bata nan, Romancing ɗinsu yake yi tamkar zai kashesu, halinshi ne bunsuranci, har ƙwara Ƴa’ƴan shi twins duk iskancinsu babu ruwansu da masu aikin gidan, amma shi uban nasu baya iya kauda idonshi akansu, Ya maidasu kayan biyan buƙatar shi, Kuma ba su isa su ce zasu hana shi ba, saboda barazanar da yake yi masu, hakan yasa suke mugun jin shakkar fallasa shi awurin masu gidan, kuma hada ƙarin basu son yayi masu silar barinsu aiki gidan, ba don kudin da ake biyansu da dollar ba, sai don sabon da sukayi da mutanan gidan sannan da yawansu Iyayensu masu ƙaramin hali ne, wasu ma babu Iyayen neman na kansu suke yi don su rufawa kansu asiri.

Ex-prisoners Meya hwaru Bayan jirginsu Ya ɗaga daga Cikin Dajin Evil forest shin sun sauka lafiya ko kuwa akasin hakan”?

*SAN ANTONIO-TEXAS🏙*

*UNITED STATES OF AMERICA*

San antonio texas babban birni ne da ke a cikin jihar Texas ta america Yana ɗaya daga cikin jigunannun manyan biranan America Masu matuƙar ƙayatarwa Manya manyan gine gine na tarihi dana zamani, abubuwan more rayuwa masu ban sha’awa na musamman da kuma wadatar arziki, Hadaddiyar daula ce a U.s tsayawa suffanta kyawun birnin 6ata baki ne, balle ni da nake da abunyi.

*San Antonio International Airport🛫*

Katafaren Airport ne na tashi da safkar jirage dake a cikin birnin san antonio, ƙayataccen gaske, sanarwa ce ta soma fitowa daga muryar na’urar computer (PA announcement) Kunnuwan Ma’aitakan Airport ɗin da fasinjojin dake zirga zirga a cikinsa gaba daya sun natsu suna sauraron sanarwar kwamfutar

“Attention, passengers. A UH-60 Black Hawk helicopter is scheduled to land at San Antonio International Airport in approximately 10 minutes. We appreciate your patience and understanding.” (“Amaida hankali, fasinjoji. Jirgin sama mai saukar ungulu na UH-60 Black Hawk yana shirin sauka a filin jirgin saman San Antonio a cikin kusan mintuna 10. Muna godiya da haƙuri da fahimtar ku.”)

Tunkafin ƙarasowar Helicopter ɗin nasu tuni Daga can headquater na sojoji an kira Emmergency Number ta Asibitin University Hospital Domin zuwa ɗaukar Marasa lafiyan da Jami’an su suka ɗauko, Da wata irin jiniya Jibga jibgan Ambulances din suke zuba uban gudu saman titin da dai sadaka da airpot din, jiniyarsu ta karaɗe ko’ina duk inda suka bi darewa akeyi abasu Hanya tunkafin su ƙaraso saboda sanin aikinsu na agaji, kowace ambulance tana ɗauke da tambarin sunan asibitin UHS which means (University Health System) daga gefen rubutun Zanan white cross ne backround dinsa launin Ja,Kusan su uku ne Motocin suka jera, a Airport helipad ambulances ɗin suka Yi parking, helipad yanki ne na musamman da aka tanada domin safka da tashin helicopter.

Mintuna goma na cika cuf cuf A gogon birnin San antonio ya buga ƙarfe 5 na safe, adai dai Wannan lokacin sautin Danƙareran Jirgin Da ke shawagi Saman iska Ya karaɗe kunnuwan kowa dake a yankin airport ɗin ga dukkan alamu Matafiya sun ƙaraso 🛫.

Sannu Ahankali Helicoptern Ya sauke tayoyin shi yayin da ya ke yin ƙasa ƙasa, Slowly yake tafiya har yakai ga inda zai dakata a filin helipad, Sojoji ne Kewaye da Jirgin waɗanɗa suka zo tarbarsu daga headquater, Motocinsu na ajere dana ɗaukar marasa lafiyan.
Buɗe Bayan Ambulances ɗin akayi at same time, Ma’aikan Jinyane waɗanda ake kira EMTs (emergency medical technicians) suka soma diddirowa daga bayan motar, mata da maza turawa cikin shigar fararen kaya masu ɗauke da tambarin Lafiya Hannayensu da ƙafafuwansu duk safunane haka zalika Sun toshe rabin fuskokinsu da face mask.

Saukowa Sojojin helicopter ɗin suka soma Yi daga cikin shi, Biyu daga cikinsu ruƙe da ɗan ta’addan da su ka damƙo a evil forest, Kaitsaye suka nufi motar ƴan uwansu sojoji da suka zo daga headquater, Abayan Kanta suka wurga shi tare da datse ƙofar,
Dawowa su ka yi wurin ƴan uwansu, nan fa aka fara rungume juna, ƴan uwan nasu nayi masu jinjina ta ban girma, akan Nasarar cafke ɗan ta’addan da su ka yi.
Ba tare da 6ata lokaci ba, Emts suka Curo stretcher daga motarsu kusan guda Takwas, agaban Helicopter ɗin suka ƙarasa da shi ɗauke a hannunsu, Da taimakon sojoji suka dinga Jigilar ɗaukar su Angel suna miƙa su cikin motar, da aka zo kan Danish Sai dai sojojin suka kar6i stretcher ɗin suka shigar dashi ambulance ɗin, Bayan sun kammala kwasarsu, Motar sojoji gaba da baya a yayin da motocin Ambulances ɗin ke a tsakiya, da wata irin Jiniya suka haura saman titi da gudun gaske, sauran sojojin dake acikin motar da ɗan ta’addar yake tuni sun raba hanya sun nufi headquater ɗinsu da shi.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E14🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

*Universal Hospital*

Ba sai na tsaya misalta kyawun asibitin ba, tun da akace america zance Ya ƙare just imagining ɗinsa zakuyi, lokacin da motocin suka ƙaraso entry way na shiga asibitin ɗuff suka ɗaukar jiniyar bayan shigarsu A parking space motocin suka dakata da yin tafiyar, Cikin ƙanƙanin lokaci Emts Suka kammala jigilar shigar dasu cikin asibitin duk wani motsinsu akan idon sojojin Bayan kammala Shigar da su asibitin, Likitoci da nurses suka duƙufa domin duba lafiyar jikinsu, tuni sun canza masu kayan jikinsu daga Uniform ɗinsu Jajaye zuwa Patient’s uniform launin Light blue, hatta waɗanda suka 6aci da ta6o sun wanke su tass tamkar basu ta6a faɗawa cikin ca6ali ba.

gaba ɗayan su a Amenity ward aka kwantar dasu, sashe na musamman da ake kwantar da sarakuna da hamshakan masu kuɗi, duk mutun ɗaya ɗaki ɗaya, tsabar haɗuwar ɗakunan tamkar bana jinya ba, anzuba ababen more rayuwa, kama daga haɗaɗɗen gado, ga A’c hada tv da frigde komai na jin daɗi, tuntuni sun farfarɗo daga suman sai dai gaba ɗayansu they were in a state of unconsciousness sakamakon firgici da tsoron da ya rikitar da su, razana suke yi haɗi da yin sambatu hakan yasa likitoci su ka yi masu allurar kashe ƙwarin jiki don su samu damar duba lafiyar jikin su, the first thing da doctors su ka fara yi masu is general checkup wanda ya haɗa da sauraran bugun zuciyar su duba hunhunsu, fatarsu da idanuwansu daga bisani suka fara yi masu gwaje-gwaje da su ka shafi blood test, chest X-ray, da sauran gwaje gwajen hotunan wasu 6angarori na ga6o6in su, domin duba raunukan da suka ji da cututtukan da ke damunsu, Cikin ƙwarewa likitocin su ke gudanar da binciken nasu, ɗaya daga cikin abunda suka gano wanda ya ɗaure masu kai, duka yaran akwai depression atattare da su (ciwon baƙin ciki da damuwa) Mutun ɗaya ne ke fama da Ciwon Zuciya (stress-induced cardiomyopathy, agaggauce su ka fara bashi taimakon gaggawa, Ga ƙarancin Jini da ya ke fama da shi, tuni sun fara yi mashi Blood transfusion.
Chapter 43 · 0% Book details