Sashe 125
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dafa ƙofar room din dakin big guy yai da tafin hannun shi, a hankali ƙofar ta zuge kanta, shi yafara shiga kafin mutumin yabi bayanshi, tunkafin su ƙarasa shiga ya hango abunda ya basu mamaki da al’ajabi, har kallon juna sukayi kafin suka mayar da dubansu garesu, wato abunda yabasu mamaki ƙarfin halin Unaisah, Ta lullu6esu da bargo daga ita har Giant snake din, kana Iya hango ƙafarta da jelarsa.
“Ban ta6a ganin ƙauna irin wannan ba, arayuwar mu ta zahiri, ƙarfin halin unaisah da jarumtakarta ba ƙaramin burgeni suke yi ba” big guy ne ya fada.
Mutumin yace”Ni shaida ne akan ƙaunar dake a tsakaninsu, tamkar anta da jini ....” bai ƙare maganar ba, big guy yai mashi nuni da abun sauraron daya sanya a kunnanshi, da sauri Yaja baki yai shiru don ya fahimci abunda yake nufi wato chief yana sauraronsu ta hanyar earbuds din kunnan big guy.
Abakin gadon suka dakata suna ƙare masu kallo.
Kiran sunanta big guy yai”Unaisah! Muna son yin magana dake” shiru babu alamun zata farka
Ɗaga murya yai da karfi ya ambaci”Unaisah Angel, ki tashi zamuyi magana”
Har cikin dodon kunnanta kiran ya kai mata, firgigit tafarka tana sambatun ambaton sunan Danish, saboda ta kwanta dashi aranta, jin shi ajikinta yasa taji hankalinta Ya kwanta, sai kuma ta fara tunanin wanene ke kiran sunanta, kafin brain dinta ta tariyo mata muryar mai magana ya kuma cewa”Ni ne Big guy, ki fito daga cikin bargon muyi magana” ya fada ne don ya lura tafarka duba da yadda bargon da suka lullu6a yake motsi.
Ta rasa ya zatayi ta raba jikinta daga giant snake din, Ya shige mata sosai, sai faman jan numfashi take Yi da sauri da sauri.
“Kinyi shiru Unaisa!” muryarta da kasalar bacci ta soma magana
“Ƙoƙari nakeyi in fito, ya rurruƙeni ne”
murmushin gefen fuska mutumin ya saki jin muryar daya daɗe yana kewarta.
Kallon big Guy yai”bari na taimaka mata” clapping hands dinsa yai sau uku, wani abun mamaki macijin ya farka, Ya warware jikinshi daga nannaɗetan da yai, ya soma ƙoƙarin yakice bargon don ya fito, hannu mutumin yakai Ya ruƙo ƙarshen bargon ya yaye shi gaba daya ya jefar dashi gefe ɗaya.
Biji biji Unaisah take dubansu, idanuwanta sun kumbura sunyi mata nauyi bata iya ganin su dakyau, a kasalance ta miƙe zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, baiwar Allah gyaran gashin da take ta kaffa kaffa dashi don kada ya tarwatse tuni yafara fita hayyacinshi.
Abun da ya ɗaure ma Big guy kai, ganin yadda macijin duk yabi ya ruɗe, ƙoƙarin saukowa yake Yi daga saman gado, kuma ga dukkan alamu wurin mutumin yake son zuwa, Allah sarki ɗan uwa yaga ɗan uwanshi.
Hawa saman gadon mutumin yayi, agaban giant snake din Ya tsaya, cikin rauni na murya furta”ko baka furta min ba, nasan halin da kake aciki Danish! Saboda ina jin raɗaɗin acikin zuciyata, amma kada ka damu, Allah yana atare dakai muma kuma muna atare dakai, wallahi duk runtsi duk wuya ba za su ta6a cin galaba akanka ba, tunda har su ka yi kuskuren haɗaka da ƙaddararka wadda tayi silar barinka *GIDAN KURKUKUN ƘADDARA!!* Tun da ya fara magana Unaisa ta dabarbar ce, tarasa gane a ina ta ta6a jin muryarnan, sai da yazo ƙarshen maganarshi ya amabaci sunan kurkukun ƙaddara, tamkar ya buga mata guduma a kirjinta, la66anta na rawa ta soma ambaton sunanshi”SAL... SABEEL! SALSABEEL! MAFARKI NAKE YI KO GASKE NE KUNNUWANA SUKE JIYO MUN MURYARKA” amatuƙar ruɗe sai faman ƙoƙarin murza idanuwanta take da yatsun hannunta duk don ta samu damar ganinshi.
Muryarshi ce ta dakatar da ita daga ambaton sunanshi da take Yi
“Angel! Nine ba mafarki kike yi ba, SALSABEEL ƊINKU NE NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA” daƙyar ta iya ware idanuwanta akan fuskarshi, kwamtsa duk ta kakkama idanuwanta saboda kukan da tayi idon ciwo yake mata, sosai ta zazzaresu tana dubanshi tamkar wadda taga abun tsoro, ruɗani ya hana ta yi magana, lamarin yayi mugun ɗaure mata kai, ko amafarki bata ta6a tsammanin hakan zata Iya faruwa ba, kamar yadda take kallonshi haka shima yake kallonta, fuskarshi dauke da murmushi, yayin da idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, macijin kuwa tuni Ya ɗaura kanshi saman laps din salsabeel.
Miƙa mata hannu yai alamar tazo gare shi, ta zabura ta nufeshi, haɗi da faɗawa saman kirjinshi ta ƙanƙameshi, lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya.
Big guy dake atsaye yana kallonsu zuciyarshi tuni ta karaya, duk irin dauriyar shi baisan sa’adda ƙwalla ta cika idonshi ba.
Muryarshi arauna ce ya furta”Sir, are you listening?”
On the other hand, chief owais dake a kwance saman tattausar mattress na gadon shi, Ya amsa mashi da”Yes, I’m listening.”
Ajiyar zuciya big guy ya sauke, ya fahimci sautin kukan Unaisah ba ƙaramin ta6a zuciyar chief yai ba, tun daga kan yanayin muryarshi.
Bubbuga bayanta Salsabeel yai da hannun ɗaya cikin sigar lallashi, yayin da ɗayan hannun nashi yake asaman kan giant snake din”
Tamkar yana ƙara tunzurata, kuka take yi na fitar hayyaci.
Big guy dake amanne da earbuds, muryar Chief ce ta janyo hankalinshi ga sauraronshi”
“Tell her to stop crying, I don’t want to hear it.(Ka faɗa mata ta daina kuka, bana son ji”) amsa mashi yai da toh, kafin ya ɗaga murya yace da salsabeel”ka lallashi ƴar uwarka, tadaina yin Kuka, umarni ne daga chief”
Jinjina mashi kai yai, da karyayyar murya ya ambaci sunanta”Unaisa, Ki daina kuka, danish baya jin dadi, ya fadamin idan baki daina ba shima zai fara kukan saboda kina ƙara tayar mashi da hankali” jin wannan maganar yasa tayi saurin haɗiye kukanta, a hankali ta dago da kanta tana duban fuskar salsabeel, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, kumatunta sunyi jawur, pink lips dinta sunyi suntum dasu, tasha kuka baiwar Allah.
Cikin shessheƙar kuka take fadin”Sal... Sal... Sabeel, ka fadamin ya akai ka tsira daga gidan kurkukun ƙaddara? Ina ƴan uwana suke? Ina deeja take da mubeen? Suma sun rayu ko sun mutu? Inaso nasani, gaba ɗaya na rikice”
Shafa gefen fuskarta yai da hannun shi, Cikin sanyi murya yace”Unaisah, ki kwantar da hankalinki, yanzu bana acikin natsuwar da zan Iya yi maki bayanin komai, nayi maki alƙawarin zan fayyace maki komai idan Danish ya dawo mutun, amma fa sai kin daina yin kuka, kin kuma natsu” jinjina mashi kai tayi alamar zata daina.
“Danish yana yi min magana, yanzu haka” ba ta yi mamakin jin abunda yace ba, tunawa da cewa shima giant ne, abune mai yiwuwa suyi magana ta sirri acikin zuciyoyinsu harma su Iya jin juna, big guy ne kadai al’ajabi ya cika shi, tun yana daga tsaye har yakai ga samun wuri saman sofa din dakin ya zauna yana dubansu
“Ina son jin me yake fada maka” acewar big guy
A lokacin Unaisah ta mayar da kanta saman kirjinshi, ya tallabeta da hannu ɗaya, zazza6i jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi.
Calmly Salsabeel Ya soma faɗa masu tattaunawar da suke Yi da danish.
“Ya faɗamin bayason unaisah tana yin kuka, Zuciyarshi tana karaya, sannan yana roƙona akan in taimaka mashi ya rikiɗa ya koma mutum baya son ganinshi a suffar maciji, yana jin ƙyanƙyamin kanshi, yana acikin mawuyacin hali na ƙunci da raɗaɗi, idan har ya ɗauki tsawon lokaci bai dawo mutum ba Giant’s heart dinshi zata motsa ne, idan kuwa ta motsa gaba ɗayanmu zai Iya cutar damu, saboda awannan matakin babu wanda zai Iya sarrafa shi har ita unaisah” hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba jin abunda salsabeel yake fadi, ita azatonta giant’s heart dinshi ne ya motsa shiyasa har ya iya rikiɗa ashe ba zuciyar bace ta motsa.
Ba ita ba hatta big guy ya ɗan girgiza da jin kalaman salsabeel, har saida ya daura eye balls dinshi akan macijin dake a nannaɗe saman gadon har yanzu bai ɗago da kanshi daya daura saman laps din salsabeel.
Cigaba da yin magana yayi”danish yana acikin damuwa, ina jin shessheƙar kukanshi, roƙona yake yi akan mu taimaka mashi ya canza halittarshi ya gaza rikiɗa baisan ya zaiyi ba, bayason ƴan uwanshi su guje shi, idan kowa ya ƙyamace kamar yadda ya ƙyamaci kanshi hakan zai yi silar motsawar giant’s heart dinshi kuma idan ta motsa zai nesanta kanshi da kowa saboda baya son ya cutar da mu, zai koma inda yasan baza a ƙyamace shi ba, yana nufin tushen shi gidan kurkukun ƙaddara....” tunkan salsabeel Ya ƙare maganar, Unaisah ta tari numfashinshi “A’a danish, ka daina fadin zamu ƙyamace ka, Ni yanzu ma nafara ƙaunarka saboda ina tausayin rayuwarka nasan cewa bayin kanka bane, mugayan mutanan can ne suka assasa faruwar hakan duk don ka koma garesu, sunyi maka hakanne don mutane su guje ka kai kuma kaji ka ƙyamaci kanka saboda sunsan ta wannan hanyarne kadai zakaje gare su, Ni kuma wallahi bazan ta6a bari hakan ta faru ba, Yanzu nafara sonka, Danish ba maciji ba, kowace irin halitta zaka koma a duniyar nan ina atare dakai, har abada har ƙarshen numfashina, kai koda ace zaka dinga cutar danine bazan rabu dakai ba, sai inda ƙarfina ya ƙare, akanka babu gudu babu ja da baya wallahi bazan barka ba.......” kukane yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar.
Macijin yana sauraron duk abunda take cewa, ya ɗago da kanshi daga saman laps din salsabeel, mitsi mitsin idanuwanshi na fuskantarta.
Big guy bazai Iya jurar tausayinsu da yake ji ba, Jikinshi yai sanyi laƙwas kamar wanda aka zare ma laka.
Duk abunda ke faru Chief Owais Yana sauraronsu, yayin da yake a kwance cikin bedroom dinshi saman gadonshi, Muryar unaisah ta cika mashi kunnuwanshi tamkar agabanshi take Yin kukan, A hankali ya dauki wayarsa daya daura saman broad chest dinshi ya dawo da ita saitin kunnanshi, don yaji dadin sauraronta dakyau.
Shafa sumar kanta Salsabeel yai da hannunshi”Ki daina kuka yace min in fada maki bayaso” da sauri ta hadiye kukanta tana fadin”toh na daina, bazan ƙara ba my Man,” ta faɗa tana kallon macijin har girgiza mata kai yake yi, batasa sa’adda tasaki murmushi ba, ta fahimci lallashinta yake yi.