← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 152

Sashe 66

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nurse jessice tace”Kuna burgeni sosai, inaso Inga ƴan uwan masu son junansu, masu haɗin kai, ta hakanne ake cin ribar zaman duniya, idan har kana da ɗan uwa mai share maka hawayenka, mai nuna maka ƙauna wanda baya gajiya dakai tabbas ka gode ma Allah, zai yi wuya ka rasa madafa a duniyar nan, babu wanda zai yi gigin cutar dakai muddin kuna da haɗin kai a tsakaninku, amma idan Ya kasance kuna ƴan uwa baku da haɗin kai, danasani zai biyo baya cos dayawa rashin kulawa keja har damuwa tayi ma ɗan uwanka Illa, ya akaita abunda zakuyi danasani gaba dayanku”

Angel ta natsu Tana sauraron Kalaman Nurse Jessica, Haƙika kalamanta sun ta6a mata zuciya, sai taji ta ƙara ƙaunar ƴan uwanta, ta ɗanyi mamakin yarda nurse ɗin take sakar mata fuska suke Yin fira, saboda ta ta6a Jin ana faɗin turawa sun tsani baƙar fata suna nuna masu wariyar launin fata, sai dai tayi tunanin ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, sannan kuma su basu da banbanci dasu, hasken fata, launin ido da kuma sumar kai, shiyasa suka zama ɗaya.

“Ki tashi muje in raka Ki ɗakunan ƴan uwan naki, Nima Inason ganin su, musamman twins ɗin nan” murmushine Ya bayyana akan fuskar Angel jin abunda nurse ɗin tace, tuntuni ta faɗa mata, ba twins bane Jamimah da azeeza ɗaya ta girma ɗaya amma taƙi yarda, ba ita kaɗai ba hatta sauran nurses ɗin da likitocin kallon twins suke Yi masu acewarsu Basu da banbanci, Komai nasu kala ɗaya.

da zumuɗi Angel ta sauko daga saman gadon, light blue uniform ɗinta ne a jikinta, sai da ta fara zuwa gaban closet ɗin ɗakin ta buɗe ta ɗauko Hijabin da aka bata Nayin sallah ta zura a jikinta.

Hannunsu ruƙe cikin na juna ita da nurse ɗin suka fito daga ɗakin, hasken electric bulbs Ya haskaka Asibitin tamar da rana, a tsanake suke Yin tafiya suna tattaunawa a tsakaninsu, ɗakin Gabriel suka Fara shiga, tayi mamakin ganinshi idon shi biyu Shida nurse rebecca, ta kunna masu kallo sun natsu abunsu.

Jin motsin shigowar Mutun yasa suka kai eyes dinsu ga ƙofar, murmushi ne ya bayyana akan faces dinsu

Mayar masu da martanin murmushin nasu Angel tayi”ɗan uwana, Baka Yi bacci ba? Fadamin meya hana ka Yin bacci”!
Kafin Ya bata amsa nurse rebecca tace”Ni na hana shi, Ko bakisan mun fara soyayya bane, Gabriel baka faɗa mata ba”? Gaba daya suka sanya dariya, jessica tace”har kinyi kamu kenan” ɗaga mata gira tayi”yap, taya zan bari damar nan ta wuce ni”? Firarsu ba ƙaramin nishaɗi take sanyasu ba, Angel tuni ta haye saman gadon gabriel, Ruƙo hannunshi tayi acikin nata,
“My sister, meya hana Ki yin bacci”? Ƙasa ƙasa da murya ta furta”Danish, Hankalina Yaƙi kwanciya da rashin farkawarshi, Yaufa kusan One week kenan a lissafina, Gabriel bansan ya zanyi ba, Ni nafi so Mu koma nigeria....”katse mata maganar yai da cewa”ai kin faɗamin dr laura tace zata taimaka mana mu koma can ko?

Ɗaga mashi kai Tayi”eh, amma har yau shiru, banji daga gareta ba, Kuma kaga sojojin basu ƙara dawowa ba”

Ganin kamar duk ta damu yasa shi kwantar mata da hankali”Wani jinkirin alkhairi ne Angel, wata’ƙil ki ga gobe anzo mana da kyakkyawan labari, don haka Mu ƙara haƙuri kada mu damu kanmu komai zai tafi dai dai My lovely sister” Yai magabar Tare da jan kumatunta da hannunshi, Hakan ba ƙaramin dariya Ya bata ba.

“Masoyiya Angel, zamu Iya tafiya “? Muryar nurse Jessica ce ta katse masu tattaunawar tasu.

Peck tayi mashi saman cheek dinsa”ka kwanta ka huta,” ta ambaci hakan tare da saukowa daga saman gadonshi ta nufi nurse jessice taja hannunta suke fuce bayan sunyi masu sallama.

Room ɗin Batul suka shiga, A kwance suka same ta saman gado, ta ƙudundune da bargo, da alama tayi zurfi abaccinta, Basu shiga ɗakin ba suka wuce ɗakin Jemimah, Itama baccin take Yi, ta wawware ƙafafuwanta ta saki baki da hanci, nurse din dake kula da ita, Tana acikin ɗakin har gaisawa sukayi da ita kafin suka nufi ɗakin Azeeza, Kamar yarda suka samu jemimah haka suka sameta a kwance bacci yai daɗi, murmushi Angel tasaki kafin suka ƙara gaba zuwa ɗakin Parveen, Hallau dai mai hali Baya ta6a canzawa, bata Yi mamakin ganinta a zaune gefen gado ta tasa abinci saici take Yi, An kunna mata tv tana kallon mbc channel Suna Yin cartoon tom and jerry, Sai tiƙar dariya take Yi kamar zata kifa kanta saman table din gaban gadon, babu alamun bacci a idonta, sam bata ji motsin shigowarsu ba, plate ɗaya ne agabanta shaƙe da chicken wings, gefen plate ɗin kuma Apple juice ne, Duniya Ta yi mata daɗi, Gyaran muryar da Angel Tayi mata ne yai silar Jawo Hankalinta ga dubansu, bakinta cunkushe da nama ta furta “Angel”

Nurse ɗin da suka zo atare da ita sai murmushi take saki, Da alama parveen ta burgeta, ba tun Yau ba, duk in tazo dubata sai ta sameta tana Cin abinci, da wuya ka same ta bakinta babu abun taunawa.

Farin Cikine Ya bayyana akan fuskarta, Da sauri ta ƙarasa suka rungume juna ita da Angel.

Shafa sumar kanta Tayi”Parveen kowa Yai bacci banda ke, kina nan kinata cin abinci Ko gajiya bakya yi, so kike ki karya masu jari ko”? Da zolaya tayi maganar, bayan ta raba jikinta daga na Angel, Just 4days Har kumatu ta ƙara.
“Ai nurse ɗinne Yace min duk in ina buƙatar wani abu Inyi mashi magana...” zaro ido Angel Tayi hada ruƙe ha6a tace”Eyehh! Wato saboda yace maki haka shine kuma ko da wani lokaci sai kince mashi zaki ci abinci, Angaya maki nan Restaurant ne? You’re a patient bai kamata aga kina cunkushe cunkushen abinci, kamar me fama da cutar Yunwa” sam Sun manta da nurse din da ke abayansu, Da turancin Angel Keyin maganar, hakan Yasa ta fahimtaci abunda suke tattaunawa, sai faman sakin murmushi take Yi tana binsu da kallo.

“Angel ai su ba ruwansu, komai mutun yake so suna yi mashi, baki ga yarda nurse din Ya ke ji dani ba, Shine ma Ya kunna mun abun nan ba ƙaramin Daɗi naji ba” ta yi magana tana nuna mata plasma tv

Watsa Hannu Angel Tayi”Okey, Koma Ki cigaba da cin abincinki, pls Ki samu ki kwanta ki huta, ki kula mun da kanki” murmushi parveen ta sakar mata

“Thank u sis, Allah yabar mana Angel ɗinmu” Nurse jessica ta tsaresu da ido, gwanin ban sha’awa take kallon su
Sallama sukayi Ma parveen bayan sun fito daga ɗakin suka nufi ɗakin Hannah, Yarinya ƴar madara, hankalinta kwance take sharar baccinta, Rabin jikinta duvet ne.

Bayan sun ƙara gaba ɗakin Naufal su ka shiga da ɗakin Javed, Kowan nan su bacci Yake Yi, daga ɗakin Javed suka nufi ɗakin Haris, Bawan Allah ba laifi Jiki Yai kyau, yana samun kulawa fiye da sauran ƴan uwanshi saboda lalurar shi.

Sunyi tunanin bacci yake yi ganin shi kwance ya rufe idanuwanshi, Har sun Juya zasu fuce muryar shi ta katse masu hanzarinsu

“Angel!” Atare suka Juyo suna kallonshi, Ya buɗe idanuwanshi da suke a lumshe, farin Cikine Ya lullu6e Angel, da sauri ta nufi gadon shi daga gefe ta haye, taimaka mashi tayi ya mike zaune, ta rungume shi a chest ɗinta, hannunta asaman bayanshi tana shafashi

“Haris ɗina Ya jiki naka da sauƙi ko”? Muryar shi, ƙasa ƙasa Ya masa mata”da sauƙi Angel, bana jin ciwo a jikina sai dai har yanzu ina yin mafarki akan Deejana, ina ganinta a prison suna azabtarmin da ita, tana kuka tana roƙona akan in taimaki rayuwarta’ cikin rauni na murya yai maganar

“Ka kwantar da hankalinka haris, Mafarki ba gaskiya bane, sau dayawa mafarki Shaidanne yake assasa shi, wani daga Allah ne wani mafarkin kuma ya danganta daga Yarda ka ƙwallafa abu aranka, shiyasa nace ka dage da yin addu’a, in sha Allah haris in dai Deeja tana araye zaku haɗu ne,”

Nurse ɗin ta zuba masu ido tana kallon su, bata san me suke tattaunawa ba a tsakaninsu, saboda sunyi amfani da harshen hausa.

Still Haris bai ɗago kanshi daga saman chest ɗinta ba ji yake kamar deejanshi ce

“Wlh Angel inason deejana, Kuma inayi mata addu’a, Ko yanzu da kika sameni na rufe idanuwana, addu’a nakeyi mata, Ni bazan ta6a gajiya dayima deeja addu’a ba, Har nunfashina na ƙarshe”

Tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, (Ƙaunar dake a tsakanin haris da Deeja, daga Allah ne, irin son da ake kira true love, Inason ka kana so na badan wani abu ba❤ Allah Ya bamu masu sonmu tsakani da Allah🙏)

Shafa sumar kanshi Angel Ta yi da hannunta, Jin shessheƙar kukan shi Ba ƙaramin Karya mata zuciya yai ba

“Haris pls don’t cry, kasan bana son jin kukan ka, ko ba danni ba, nurse da ke kula dakai bazata Ji daɗi ba, Suna iyakar bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun sanyaka farin ciki duk don ka rabu da ciwon zuciyar dake damunka” a hankali ya ɗago da kanshi Idanuwanshi sun ɗan kumbura.

“Angel, nadaina bazan ƙara ba” tafin hannunta ta ɗaura saman fuskarshi tana share mashi hawayenshi

“Zan tafi Yanzu nurse tana Jirana, Amma kafin nan kayi min murmushi mana” daƙyar ya ƙaƙaro murmushi kan fuskarshi, Hakanan taji gabanta Ya faɗi ƙura ido tayi akan face dinshi kamar tana son gano wani abu sai dai ta kasa gane menene shi.

Ganin yadda take kallonshi yasa yace mata Lafiya Angel’? Girgiza mashi kai Tayi bakomai, ka kula mun dakanka, Sai Allah Yakaimu” daga haka ta sauko daga sama gadon, suka fice daga ɗakin shi ita da nurse jessica.
Last room da suka Nufa ɗakin Garkuwa, tunkafin su ƙarasa take Jin faɗuwar gabanta na ƙaruwa, ji take yi kamar idan ta shiga ɗakin wani abu zai faru, Da bismillah abakinta ta kutsa kai dakin nurse jessica tabi Bayanta, kamar matacce haka suka same shi kamar kullum Sai sharar baccin shi Ya ke yi, Lamarin Danish ba ƙaramin ɗaurewa likitoci kai Yai ba, tsawon kwanaki mutun Yana yin bacci yaƙi tashi? Tun abun na damunsu har sun haƙura sun zubawa sarautar Allah ido.

Saman chair nurse ta zauna idonta akan face din Danish
Chapter 66 · 0% Book details