← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 152

Sashe 93

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adai dai lokacin Zainab mai aikin gidan tana a palour hannunta ruƙe da floor wiper tana goge tiles, ta saba ba tun Yau idan bata son aiki Yayi mata yawa takan fito har tsakar dare Tana aikace aikacen ta don ta rage wasu ayyukan na safe duk idan taji ƙarfi a jikinta.

Tamkar da rana saboda hasken Ƙaton kwan dake a falon Ya gauraye ko’ina, Hankalinta kwance ta duƙufa tana gudanar da aikinta ba zato ba tsammani taji an banko ƙofar falon.

A firgice Zainab ta ɗago tana kallon matar da ta fado cikin falon afujajen, tsabar firgitar da ta yi har batasan sa’adda ta jefar da wiper din hannun ta ba, tun daga ƙasa har sama take kallonta, Hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tsananin tsoro Ya kamata, Jikinta ya hau yin kerma, Muryarta na rawa ta furta”baiwar Allah wacece ke? taya ya akai kika shigo gidan nan? Ƙarfe sha biyu na dare”? Aruɗe take jefa mata tambayar.

Shessheƙar Kukan matar ne Ya ƙara firgitar da ita, ta soma Ja da baya tana ƙoƙarin guduwa cikin gidan don ta faɗo ma Hajiya layla abun da ke faruwa sai dai kafin Ta juya muryar Matar ya ratsa kunnanta cikin harshen larabcin take faɗin.

“AUNTY ZAINAB NI CE BENAZIR!! INA ABBANA! INA UMMI NA! INA MIJINA DA ƳA TA!!! A jere ta jefa mata tambayoyin.

Har abada ba zata ta6a mantawa da muryar nan ba, koda kuwa amafarkine Ta jita tabbas zata shaida mamallakiyarta.

A hargitse Ta juya Tana dubanta, A hankali benazir ta ɗaura ziraran yatsun hannun ta farare tas ta ruƙo ƙasan niƙab ɗin fuskarta ta ɗage shi sama” tsabar kiɗima da ganin fuskar da tayi kimanin shekaru sha shidda ba ta yi tozali da ita bane yasa Jikinta ya hau yin kerma, tsantsar mamaki da al’ajabi ne akan fuskarta, ta zazzare idonta akan kyakkyawar fuskar benazir, sam takasa yarda da abun da idanuwanta ke nuna mana gani take yi tamkar mafarki ne take Yi!!

Tayi wani irin haske Kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Fuskarta sharkaf take da hawaye ta ko’ina, ga zufa dake tsastsafo mata sam babu kwanciyar hankali atattare da ita.

Tsantsar tashi hankaline Akan fuskar zainab, Muryarta adabarbarce ta furta”be..be..nazir! Dagaske ke ce ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba”?

Da ƙarfi ta furta”Ni ce Aunty zainab! Ki amsa min tambayoyin da nayi maki”!

Tana faɗin hakan Nan take Ta yanke jiki Ta faɗi ƙasa a sume, akwatin hannunta ya kife saman floor.

Juyawa Zainab tayi da gudun gaske ta nufi ɗakin hajiya layla, Hada yin tuntu6e tsabar sauri, tunkafin ta ƙarasa ta soma ƙwala mata kira na fitar hayyaci tamkar maƙoshin ta zai 6allo waje.

“Hajiya layla! hajiya layla”

Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnuwan su daga ita har Alhaji ubaid dake kwance saman katafaren gadonsu, A firgice suka farka a lokaci ɗaya suka miƙe zaune suna ambaton Sunan zainab.

Doguwar jallabiya ce a jikin alhaji ubaid wuyan rigar ya karkace, Hajiya layla kuwa Rigar Bacci ce a jikinta, da sauri Alhaji ubaid ya kunna bedside lamp din ɗakin.

Sam babu kwanciyar hankali atattare da su, duk sun ƙura ido suna jiran ganin ta inda zainab zata 6ullo.

Kamar daga sama suka ji ta banko ƙofar ɗakin tana faman Yin haki.
Da mamaki Akan fuskar Layla tace”Zainab baki da hankali ne? Ko kin makance ne? Taya zaki faɗo mana ɗaki a irin wannan lokacin ba tare da kin nemi iznin shigowa ciki ba”!

Kafin zainab ta bata amsa Alhaji ubaid Ya katse mata hanzarinta da cewa”Zainab Lafiya kike ƙwala mana kifa? Kowani abun ne Ya faru”?

Cikin rawar murya ta furta”dan Allah kuyi haƙuri ku yafe ni, bana acikin kwanciyar hankalina ne shiyasa na faɗo maku ɗaki ba sallama nasan bai dace ba” dogon tsoki Layla Taja”Ba dogon bayani na tambaye ki ba, Ki faɗi min uban mi Ya kawo ki ɗakin mu?

Bata kai ga ƙarasa maganar ba, Alhaji ubaid Yai saurin katse ta da cewa”Ya isa haka, Haba kin cikata da faɗa, Kin ƙi bari tayi mana bayani dangane da abunda ke faruwa” tsuke fuska Layla Tayi.

Cikin sanyin murya zainab tace”dama BENAZIR ce ta dawo!”

Kallon juna Alhaji ubaid da layla suka Yi lokaci ɗaya, kafin suka dawo da dubansu ga zainab, Har suna haɗa baki wurin tambayar wacece Benazir!! Tsabar ruɗanin da suka shiga
Zainab tace”benazir ƙanwar dr shureim Ƴar wurinku itace ta dawo, Yanzu haka tana acikin palour ta yanke jiki ta faɗi a sume.

Girgiza kai layla tayi haɗi da cewa”baki da hankali zainab, dama na fara zargin kin fara shan ƙwaya, In ba haka ba, ta ya ya benazir da ta gudu da ƙafafuwanta zata dawo gida! bazai yiwu ba.

Alhaji ubaid Yace”ko dai mafarki ki ka yi ne zainab? Girgiza mashi kai tayi hada hawaye akan fuskarta tace”wallahi dagaske nake yi zaku Iya zuwa palourn ku duba benazir ce da kanta ta dawo”

Kusan atare suka sauko daga saman gadon, da sauri zainab ta basu hanya suka fuce har suna bange juna tsabar sauri.

Tunkafin su ƙarasa falon suka soma hango mutun kwance saman floor da baƙaƙen Kaya ga trolley dinta a gefe ɗaya, kasancewar ta yaye niqab din fuskarta hakan ya basu damar ganin fuskarta, wani irin mahaukacin bugu zuciyarsu tayi A matuƙar gigice suka furta sunanta”BENAZIR” adai dai lokacin gate security officers din gidan suka shigo falon da sallama sam babu kwanciyar hankali akan fuskokinsu ganin Yanayin mutanan gidan yasa suma suka ƙame suna faman zare ido.

Muryar Hajiya layla Na rawa ta furta”wallahi itace Benazir ɗina ce, Yarinya tace data 6ata, itace ta dawo da kanta” ta ƙare maganar jiki na 6ari ta nufi gaban Benazir dake kwance ta zube saman gwiwowinta tare da kai hannu ta ruƙo niƙab din fuskarta ta ƙarasa cire mata shi, Kowa dake a falon saida yai matuƙar Al’ajabin ganin Benazir, yalwataccen gashin kanta har gadon bayanta Ya nannaɗe kamar taliyar indomie, babu alamun wahala atare da ita, sai ma hutun dake kwance saman farar fatarta, wani iko na Allah, gaba ɗaya Jikinta Ya jiƙe da ruwan zufar dake tsastsafo mata, hatta baƙar jallabiyar jikinta ta manne ma fatarta saboda zufar data wanketa, ga wata zufar dake kurɗaɗowa ta cikin sumar kanta ta jiƙe sharkaf duk da sanyin A.c din falon.

Rushewa da kuka Hajiya layla tayi haɗi da ɗaura Hannayenta biyu saman kanta tana fadin”Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un! Dan Allah kuyi wani abu akai mana kun tsaya kuna kallonta, sai kace baku gane ta ba, ɗiyata ce benazir Allah Ya dawo mun da ita da ranta” Sautin kukan ta ya cika ɗakin, Zainab ma tuni ta fashe da kukan farin ciki, security officers dake tsaye Jikinsu ya yi mugun yin sanyi, da farko sunyi tsammanin ba mutun bace amma daga bisani Bayan ta shigo cikin gidan suka dudduba ƙofar donsu tabbatar mutun ce ba aljana ba, ashe Jamlock ɗin ƙofar gate dinne basu kulle shi ba sun manta, shiyasa har ta samu damar sanya ƙarfi ta bangaje ƙofar ta shigo ciki.

Mamaki da al’jabi sun Hana Alhaji ubaid motsawa Ya kafe fuskar Ƴar tashi da ido Yana kallonta, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwanshi haƙiƙa ya yi farin ciki mara misaltuwa kusan shekara goma sha shidda Yau rana ɗaya Allah Ya kaɗo masu da hankalinta ta dawo wurinsu, Allah ne kaɗai Yasan uwa duniyar data shiga.

Cikin shessheƙar kuka zainab tace”yakamata muyi wani abu akai, Benazir tana buƙatar taimakon gaggawa, ga dukkan alamu wani abunne Ya faru da ita wanda Ya haifar mata da fitar da gumi a jikinta”

Da sauri Alhaji Ubaid Ya sanya Hannayenshi biyu, Ya cuccu6eta Ya juya ya nufi sofa mai mazaunin mutun uku Ya kwantar da ita, kallon zainab yai”je ki ɗauko min wayata a ɗaki” ta amsa mashi da toh, da ɗan gudunta ta nufi bedroom dinsu.

Jiki amace layla ta miƙe ta koma saman sofa hand din da benazir ke akwance ta zauna tana duban fuskar ƴartata Kamar Ta haɗiyeta haka take ji.

“Alhaji kun tabbata benazir ɗinmu ce ta dawo”! Mai gemu ne Yai mashi Maganar, Jinjina masu kai Yai”babu shakka itace Allah ya dawo mana da ita” Ajiyar zuciya kowan nan su Ya sauke tsantsar farin ciki Ne Ya kamasu.

“Muna tayaku murna, ita kuma muna yi mata fatan Allah Ya bata lafiya, Ubangiji Allah yasa ƙarshen wahalarta kenan, sannan Alhaji Muna baku shawarar a kira malamin da zai dubata don yanayinta dana gani a matsayina na wanda yake da sani a 6angaren sihiri, Yarinyar ka ba likita take buƙata ba, Malami take buƙata saboda duk wasu alamomi na jikinta sun nuna kamar sihirine daya daɗe a jikinta ya kwance !!! A firgice Alhaji Ubaid Da Hajiya layla suka ɗago suna duban mai gemu da yayi maganar, jinjina masu kai yayi”ba yau na fara ganin irin hakan ba, ina da tabbacin Yarinyar nan kurciya aka yi mata, amma idan kunaso ku gasgata zance na ku kira babban malamin da zai dubata” sam sun kasa magana sai bin shi da kallo da su ke Yi.

Daƙyar Hajiya layla Ta iya buɗe bakinta la66anta na kerma tace”amma benazir da ƙafafuwanta ta gudu tabar gidan tajudden Bayan ta haihu tabar mashi jinjira a cikin kwamin wanka, tayaya hakan zai yiwu? Wanene zai yi mana hakan?

Girgiza kai mai gemu yai”haka zakuyi tunani saboda bakusan dalilin tafiyarta ba, amma abun duba anan tayaya Uwa zata gudu tabar jinjirin ɗan da ta haifa ta hanyar raya sunna!! Duk irin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗanta? Sannan idan har dagaske benazir ta gudu don son ranta tsawon shekara goma sha ɗaya meyasa zata dawo da ƙafafuwanta ba’a cikin Hayyacin ta? Ga zufa duk ta wanke suturar jikinta, Nidai shawarar da zan baku shine a tuntu6i malamin da zai dubata”

Jinjina kai Alhaji ubaid ya yi shi kanshi jikin shi ya yi sanyi da zancen Mai gemu, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalamanshi.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruke da wayar Alhaji ubaid Ta miƙa mashi, Yasa hannu Ya kar6a.
Chapter 93 · 0% Book details