Sashe 108
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ya saki har fararen haƙoranshi suka Bayyana, Kalmar ƙarshe ta saƙon Hateem ne Ya bashi dariya daya ce baba tsoho.
Lumshe idanuwanshi yaɗanyi yayin hawaye ke cigaba da wanke fuskarshi, abu ɗaya ne yake fargaba a duniyar nan ranar da zai barta saboda ƴa’ƴanshi, bai sani ba tsakanin shi da su wanene gawar fari, bai fata ma Wani daga cikinsu Ya riga shi tafiya, bazai Iya jurar rashinsu ba, Ya ƙwammace mutuwa tafara Yin awon gaba dashi.
Sumbatar card din Hateem Yai, kafin Ya buɗe na saratu
- On this special day, I want to let you know how much I appreciate everything you’ve done for me, Dad. You’ve always been my biggest fan and supporter, and I can’t thank you enough for that. Wishing you a very happy birthday, with lots of love My Baba, Allah yabarmun kai, madubin dubawata” manna ma card din kiss Yai kafin Ya duba na sauran ƴa’ƴan nashi, waɗanda basu kaiga ƙarasowa Gidan ba, suma sun bada saƙon da aka rubuta masu a cards dinsu.
Farin cikin duniya ya cika Obie, kwanciya yai saman furannin idanuwanshi na fuskantar ceilling.
Ba zato ba tsammani Yajiyo sautin muryoyinsu acikin kunnuwanshi, Suna faɗin”Happy Birthday To You, Happy birthday to You, Happy birthday to our Baba” zumbur Obinna Ya yunƙura ya miƙe daga saman gadon Yana duban ƙofar room dinshi.
Dr. jazz ne Ya fara shigowa hannunshi ruƙe da madaidaicin Cake mai hawa huɗu daga saman shi an jera candle, ga cake knife gefe ɗaya.
Shigowar dr.jazz ke da Wuya, Manyan ƴa’ƴan shi suke shigo ajere kowannansu sanye da hadaddun jallabiyoyi, Mutun Na farko Sir mubarak ne daga bayanshi Senate lafeef ne, wanda ke abiye dashi His excellency Abdul Razak ne Gomnan Jihar lagos, baisan Yaushe Suka shigo garin abuja ba, Yayi mamakin ganinsu, zuwan bazata suka yi mashi, ga kuma His excellency Deen Obinna Na jihar kaduna state, Daga bayanshi mai girma sharafudden Obinna ne, Hannun shi ruƙe dana ɗan uwanshi Prime minister hateem obinna, abun gwanin ban sha’awa, bayansu sai Saratu data shigo itama jallabiyarce a jikinta ta yafa mayafi akanta, Fuskar kowannansu ɗauke da annurin farin ciki, maimakon Ya taso Ya karaso garesu, sai kawai su ka ga ya fashe da kuka, haɗi da sanya tafukan hannayenshi biyu Ya rufe fuskarshi.
Jikinsu duk Yai sanyi, duk da ransu yana basu cewar kukan farin Cikine Ya ke yi, gefe da gefen gadon kowan nan su ya zauna kamar masu neman gafara, Senate lateef Ne Ya fara magana
“Baba meyasa ka yin kuka? Dan Allah kada ka karya mana zuciyoyin mu, munci burin mu faranta maka a wannan ranar mai albarka rana mafi daraja agaremu, ranar da abun alfaharinmu Yazo duniya” ta tsakankanin yatsun hannunshi Yake satar kallonsu, Muryar saratu da shagwa6a tace”baba please kadaina wallahi bamu jin daɗin ganin hawayenka masu tsada suna zuba ƙasa”
“Baba idan baka daina kukan nan ba, muma zamu fara” acewar Sir mubarak
Mr.president sharafudden Yace”Daddy ka bamu dama mu share maka hawayenka da hannayenmu please”
His excellency Deen Ya kar6e da cewa”daddy saboda kai, muka kamo hanya tunda duku duku muka shigo abuja, saboda muhimmancinka agare mu, dan Allah ka buɗe fuskarka ko mun samu damar ganinka, munyi kewar mahaifinmu” kalamansu ba ƙaramin karya mashi zuciya suke Yi ba, sai dai yakasa cire takufan hannayenshi daga saman fuskarshi, Allahu akhbar, wato Iyaye dabanne, duk mun muƙamin mutun shi bakomai bane agaban Iyayenshi, gaba ɗayansu nan manyan mutanene masu ruƙe da manyan muƙaman ƙasa, masu ƙima da daraja a idon duniya, Yau gasu zazzaune gefen gadon mahaifinsu, sun tasa shi agaba suna lallashinshi, abun da yake ƙara haddasa mashi jin ƙaunarsu Biyayyar da suke yi mashi, tun suna ƙanana har zuwa girmansu bai ta6a danasanin kasancewarsu a matsayin ƴa’ƴanshi ba, basu ta6a sanyashi ciwon kai ba, samun ƴa’ƴa nagartattu irinsu abune mai wuya a zamanin nan, damuwarshi tasu ce, suna matuƙar ji dashi suna gatanta shi suna kyautata mashi shiyasa suke damun cigaba arayuwarsu saboda albarkar dayake sanya masu.
Muryar His excellency deen Ce Ta katse mashi tunaninshi
“Baba munji kayi shuru baka ce komai ba, Idan akwai abunda ke damunka please Ka faɗa mana, baka da tamkar mu a duniyar nan, ashirye muke da mu share maka hawayenka”
da zolaya Sir mubarak Ya dubi jazz”faɗamin gaskiya kodai kaine ka 6ata mashi rai”?
Jazz na murmushi yace”wallahi bani bane...” daƙyar ya ƙare maganar ganin irin kallon tsiyar da hajiya saratu take watsa mashi, Muryarta a kausashe tace”tunda ka kawo cake din miƙo min shi ka fuce kabamu wuri,” Jiki asanyaye Jazz Ya nufeta Ya miƙa mata tray din, Tasa hannu ta ƙarba tana faman jifarshi da harara, sam bayason barin Ɗakin, idan Yana atare da su ji yake kamar Yana acikin danginshi mantawa yake yi da shi bakowa bane a family dinsu.
Har Ya juya zai fuce Muryar Hateem ta dakatar dashi”Zonan jazz” dakatawa yai dayin tafiyar da sauri Ya koma gaban gadon, Hateem Ya sanya hannu ya kar6i cake din hannun saratu Ya miƙa mashi”kamar yadda ka kawo shi kai nake so ka fara bashi” ɗaure fuska hajiya saratu tayi badan tana jin shakkar Yaya hateem ba da kuwa babu abunda zaisa ta bashi cake din, bawan Allah Jazz sai faman sakin murmushi yake yi, ya kar6a Yana fadin”nagode daddy hateem,” jinjina mashi kai Yai batare daya ƙara furta komai ba.
Baba, zamu tafi bamusan ko mune ke bakason gani ba, His excellency abdul razak ne Ya furta hakan, Sai lokacin Dattijon arziƙi Ya zame tafukan hannayenshi daga saman fuskarshi, tsufanshi Ya ƙara bayyana sosai, tamoji tamoji duk Ya kame fatarshi, Zaro hanky Sir mubarak Yai daga cikin aljihun shi, Ya soma share mashi hawayenshi, Bayan Ya kammala yasoma dubansu ɗaya bayan ɗaya, bi da bi, gaba ɗaya kamannin fuskarshi suka ɗauko, Musamman sharuffudeen da hateem tamkar yai kakinsu, hatta hasken fatarsu kalar nashi ne, launin idanuwansu ne dai kalar na mahaifiyarsu reddish brown.
Ganin yadda duk suka damu ya sanya shi sakar masu fuska, cikin sanyin murya yace”kai nifa ba wani abu ke damuna ba, Farin Cikin ganinku ne ya sanya ni kuka, don haka ku kwantar da hankulanku, Jazz miƙo min cake din nan” Ya faɗa Yana ƙoƙarin saukowa daga saman gadonshi, mimmiƙewa sukayi tsaitsaye suka kewaye shi, Tuni damuwar fuskarsu ta washe
Miƙa mashi cake din Jazz Yai, sai da suka fara kirga mashi one two three kafin Ya hura Iska Candles din jiki suka mutu, tafa mashi hannu sukai, sai faman sakin murmushi yake Yi,
“Wazai fara bani cake din” ya fada yana dubansu,
Matsa ma jazz hanya sukayi Ya matso kusa dashi, Hajiya saratu ji take kamar ta ingiza ƙeyarshi taji haushin kasancewarshi acikinsu, aganinta bashi ya dace Ya shigo cikinsu ba, Ina laifin su twins suda su ke jikokinshi.
Shikuwa Hannunshi Har kerma yake yi wurin daukar wuƙa, Ya gutsiro cake din Ya miƙa mashi abaki, Ya soma ci atsanake Yana duban Jazz hada ɗaga mashi gira Ya furta”Waye ya haɗa min wannan? Yai min daɗi”
Jazz yace”mommyna ce ta haɗa maka shi” jinjina kai yai”amma ta iya na jinjina mata” daɗi jazz yaji An yabi cake din mahaifiyarshi, saratu kuwa takaicin duniya ya isheta.
Daya bayan ɗaya suka soma bashi cake din Yana ci, Kafin shima Ya kar6a Ya bi kowannansu Ya bashi abaki, Bayan sun kammala ci, Ya daura cake din saman table,
Rungumarsu Ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana bubbuga bayansu da hannayenshi kamar yadda ya saba yi masu tun suna Yara.
Saman gadonshi Ya koma ya zauna yace masu duk su zazzauna yana son yaita kallonsu, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, kamar yadda ya basu umarni haka suka samu wuri saman mattress din suka kewaye shi.
Banda jazz wanda tuni Yajima da komawa ƙofar ɗakin, ganin irin kallon barazanar da hajiya saratu take Yi mashi kamar zata shaƙe shi.
Tun wuraren ƙarfe goma sha biyu na safe, Hamshakan motoci keta kurɗaɗowa cikin gidan tunkafin lokacin da za’a fara gudanar da shagalin Ya gabato, sun Cika gidan, kasancewar Baba Obie mutunne mai tarin jama’a, wasu ma ba a ƙasar suke zaune ba, amma aranar sai gasu sun shigo Nigeria duk don saboda su halacci taron taya murnar ranar haihuwarshi, Masu aikin gidan sai zarya suke Yi wurin Kaima baƙi abinci dana sha, kitchen ya zama Dandalin magulmata, Bakunansu ko gajiya ba su yi da surutu.
“Yau zamu ba idanuwanmu abinci har su ƙoshi” Safa ce tai maganar,
Sophia tace”Hmm, aini yin aiki agidan nan gaba ta kai ni gobarar titi ajos, waiku kunga haɗuwar Prime minister Hateem da matarshi! Wow masha Allah, Allah Yayi halitta”
Marwa tace”shi kaɗai kika gani kenan, baki ga Mai girma sharafudden ba, ai hadashi jiya cikin waɗanda sukaje airport tarbo prime minister, wallahi mutumin ba ƙaramin burgeni yake Yi ba, dashi da ɗan uwanshi hateem, mutanan badai aji ba, komai nasu da dattako suke Yin shi.
Abla tace”yau zamuci uwar sabada, zamu tashe mu watse, Mu raƙarƙashe don nasan dole agayyaci mawaƙa da makaɗa, Ni nama rasa wani kaya zan sanya wallahi”
da zolaya safa tace”kalar dangi, Uban wa kike tunanin zai barki ki shiga hall din taron? Ke kin isama? Sannu isassa mai walkin sa, ai kawai ki tsaya a iya matsayinki, Ta ina zaki nemi haɗa kafaɗa da Manya manyan hamshaƙan attajiran masu kuɗi, ai idan kin ganki a hall din can to amatsayin mai raba abinci zaki je” dariya suka saki.
Abla tace”Nima fa da wasa nake wallahi, Ai ni tsoronma shiga zan ji, jiya izuwa yau bani da kwanciyar hankali saboda jami’an sojojin da suka kewaye estate din ciki da waje, nasan duk zuwan hateem ne yasa aka ƙara tsaro har haka”