← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 152

Sashe 138

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abakin ƙofar dakin Ummi ta dakata tare dakai hannu ta dafi glass door din A hankali kofar ta buɗe, Zura kafarta keda wuya sukayi kicibus da batul, sam hankalinta ba akwance yake ba, ganin ummi ta shiga toilet tsawon lokaci bata fitowa ba shiyasa ta yi dabarar guduwa daga dakin don ba ƙaramin takura tayi ba, baiwar Allah suna haɗa ido da Unaisah, ta faɗa jikinta, Hannu biyu ta ƙanƙameta dasu kamar zata koma cikinta, tun daga kan yadda ta rungumeta ranta ya bata cewar babu lafiya, A hankali itama ta zagayo da hannayenta saman bayan Batul.

“Meke damunki sister? Baki da lafiyane”? Ta fada batare data raba jikinsu daga na juna ba
Muryar batul ashaƙe da mura ta furta”babu komai, Mu tafi dakinmu, Ni kadaice na rage su azeeza sun tafi tun ɗazu, Ni ko sallar asuba banyi ba”
Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba, Jin muryar Batul ashaƙe kamar an ɗaure mata makoshi, A hanzarce ta raba jikinsu, ido cikon ido suke kallon juna, ta ɗanyi mamakin ganin kayan dake ajikinta masu kyan gaske.
Aruɗe ta furta”batul! Dama kece baki da lafiya ba aunty ummi ba? Garin yaya mura tayi maki mugun kamu”?
Shiru batul tayi mata batare data furta komai ba, saboda tana jin tsoron ummi taji ta fada ma wani.
Da sauri ta canza akalar maganar tasu”Meke damunki? Naga fuskarki ta kumbura idanuwanki sun yi ja, ko kema baki lafiya”?
“Ni lafiyata qalou, damuce ta hana ni yin bacci...” bata ƙare maganar ba batul ta kuma cewa
“Ina danish dinmu”?
“Inaso zanyi maku bayanin komai amma sai mun koma ɗaki, Yanzu ki fada min ya akai mura ta kama ki? Ina kuma aunty ummi”?
Murya ƙasa ƙasa Batul tace”nima bansan ya akai ta kamani ba, aunty ummi kuma tana a toilet, itace ma ta kira awaya don akawo min magani, kuma kinga ta bani kaya na sanya” tayi maganar tana nuna mata kayan sanyin jikinta.
Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke” mun haɗu da boss man shine ya bani maganin mura in kawo, ni nama yi tsammanin aunty ummice ba lafiya kamar yadda ya fadamin ashe kece”
Jinjina mata kai batul tayi”Allah ya baki lafiya sisterna, kayan jikinki sunyi maki kyau, a ina aunty ummi ta samu kayan nan dai dai size dinki kamar donke aka dinka su”?

“Nima bansani ba, Mu tafi daki” atakure tayi maganar, tare da ruko hannun Angel, tajata suka nufi down stairs.

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*

Adai dai lokacin Su parveen suna a zazzaune tsakiyar gadonsu Batul, sun kewaye juna, sai faman zazzare idanuwansu suke yi don har yanzu basu daina jin fargabar macijin nan ba.

Motsin buɗe ƙofa ne Yaja hankalinsu ga kallonta, Atare suka shigo hannun su ruƙe cikin na juna, wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da gudun gaske Jemimah da Azeeza suka diro daga saman gadon suka nufi unaisah, tunkafin su ƙaraso ta ware masu hannayenta fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, zubewa tayi saman gwiwowinta yadda tsawonta zaiyi dai dai da nasu, gaba ɗayansu ta haɗasu ta rungume a ƙirjinta, tare da zagaya hannayenta saman bayansu, jemimah tuni ta fashe mata da kuka hada bubbuga bayan Unaisah alamar ranta ya 6aci.

Batul dake a tsaye tana kallonsu sam bata ji takun tafiyar Parveen ba, Sai dai taji muryarta”Batul tun ɗazu muna ta jiran ki shiru baki zo ba, Ina fata babu wani abu daya same ki”?

Kallonta Batul tayi da ido tayi mata alamar tayi shiru bata son Unaisah taji komai daya faru, jinjina kai parveen tayi don ta fahimci me take nufi.

“A ina kika sami kayan jikin ki masu kyau”? Ta fada tana duban Kayan sanyin jikin batul”
Murmushi batool tasaki kafin tace”Aunty ummi ce ta Bani su”
Parveen tace”ko a ina ta same su, ban ta6a ganin kayan da suka yi maki kyau ba kalar waɗannan” kafin batool tayi magana muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta, A lokacin sun ɗago da kansu daga rungumar da Unaisah tayi masu, fuskokinsu sharkaf da hawaye kamar waɗanda suka yi shekara basu ganta ba.

“Meyasa jiya kika tafi kika barmu? Inata kiran sunanki baki amsa ba, tsoron wannan abun ya kamamu”

Shafa fuskarta Unaisah tayi”Am sorry nasan ban kyauta ba, amma kuyi haƙuri, bawani wuri na tafi ba, Ina atare da ɗan uwanmu Danish bashi da lafiya......”

Tunkan ta ƙare maganar, hankalinsu yai mugun tashi jin cewa danish dinsu baida lafiya, damuwace ƙarara akan fuskokinsu

“Unaisah meke damun shi? Meyasa jiya ba kizo kin kaimu mun ganshi ba”? Acewar parveen
Batul tace”ni da ma saida naji araina ɗan uwanmu baida lafiya, Allah sarki danish din mu, Yanzu yana a ina? Ina son ganin shi” ta fada idonta akan unaisa dake ƙoƙarin miƙewa tsaye tana dubansu.

Ruƙo hannunta Azeeza tayi acikin nata”dan Allah ki kaimu wurin shi, muna son ganin shi” idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla tayi maganar.

Numfasawa Unaisah tayi kafin ta soma yin magana”na yanke shawara ƙwara na faɗa maku halin da danish yake aciki, saboda bana son ku guje shi ko ku dinga jin tsoron zuwa wurinshi.......” shiru ta ɗanyi na wani lokaci duk sun ƙura mata ido cike da zumuɗin son jin ƙarashen zancen.

“Amma kafin nan inason ganin sauran ƴan uwanmu, naga babu Hannah! Ina taje ne”? Atare suka hada baki wurin bata amsar cewa suma basu sani ba, tun daren jiya basu ganta ba.

Aruɗe Unaisah take dubansu, Kafin ta furta magana, sallamar Big Guy taja hankalinsu ga duban ƙofar, shigowa cikin ɗakin yai hannun shi ruƙe dana Hannah, daga bayansu Ƴan uwansu ne maza tun daga kan Sajeed, Haris, Javed and Naufal, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Hannah sai faman zare ido take yi kamar wadda aka faɗa ma saƙon mutuwarta, sakin hannunta big guy yai jiki na rawa ta nufi Unaisah ta rungumeta, sunyi farin cikin ganin ƴan uwansu, Sajeed ya nufi azeeza fuskarshi dauke da murmushi yai hugging dinta, Naufal yajanyo parveen ya rungumeta Yana bubbuga bayanta da hannu ɗaya,
Batool da Haris suka rungume junansu, Ran jemimah ya 6aci ganin babu wanda ya rungumeta, harta fara tatta6e la66anta za ta yi masu kuka, javed yai saurin ɗaukarta saman jikin shi, Fashewa tayi da dariya saboda an dauketa.
Big guy dake a tsaye yana kallonsu ya goya hannayensa saman broad chest dinsa, Yaran sun yi matuƙar burgeshi.

Tsawon mintuna suna a manne da juna, kafin daga bisani kowan nan su ya rabu da jikin ɗan uwanshi, gyaran muryar da Big guy yai masu ne yasa suka mayar da hankalinsu gare shi a tsanake Ya soma yin magana.

“Inaso ku natsu ku saurareni, dalilin dayasa na tara ku a ɗakin nan, saboda na fahimci haryanzu baku daina jin fargaban abunda ya faru jiya ba, Ga ƴar uwarku nan Unaisah zatayi maku bayanin komai yadda zaku fahimta, sannan please bama buƙatar ganin gifcin kowan nan ku a falo! Ku tsaya a ɗaki, mai buƙatar shiga toilet ya shiga, wanda zai yi bacci ga gado nan ya kwanta,........” kafin Ya ƙare maganar Parveen tayi ƙasa ƙasa da murya tana fadin”breakfast din mu fa? ni ina jin yunwa, Jiya da dare bamu ƙarasa cinye abincinmu ba” murmushi big guy ya saki ta cikin face mask dinshi
Da zolaya yace”ki kwantar da hankalinki foodie, Indai abincine har sai kin gaji da shi, kamar kina a gidan manomi ne, Yanzu zansa a kawo maku lafiyayyan breakfast” ya faɗa tare da nufar kofar fita yana fadin”Unaisah Ki kula da su” amsa mashi tayi da toh, kamar jira su ke yi ya fita, Har suna haɗa baki wurin tambayarta meke faruwa da Danish.

“Zanyi maku bayani, amma kafin nan ku jira waɗanda basu yi salla ba su yi tukunna, batool tace min ba ta yi sallah ba”
Badan sunso ba suka amince mata

“Kunyi sallah”? Ta jefa masu tambayar
Sajeed yace”munyi a ɗaki”
“Kufa” ta faɗa tana nuna su Azeeza
Girgiza mata kai su kayi alamar a’a, Hannah ma tace nima banyi ba, saboda babu hijabi.

“Okey, yanzu abun da za’ai ku shiga toilet ku yi alwala, kafin ku fito zan dauko maku hijabin” amsa mata sukayi toh.

Ɗaya bayan ɗaya suka shiga toilet, bayan sunyi alwala kowaccensu ta sanya hijabi, asaman carpet din da ta shimfiɗa masu su ka yi sallar, bayan sun kammmala suka cire hijaban suka bata ta ninke ta maida su a wardrobe.

Zama sukayi kan carpet din gefen gado, mazan suna fuskantar matan, sun ƙurama Unaisah ido suna jiran jin me zatace masu.

“Kin yi shiru ba ki ce komai ba sister, ke muke sauraro meke faruwa da ɗan uwan mu”? Acewar Haris
Sajeed yace”tun jiya da abun nan Ya faru mun ganki kina kuka kina fadin danish ya rikiɗa ya koma maciji, abun ya tsaya min araina” da damuwa a fuskarsa yai maganar.

“Akwai abun da na 6oye maku tun muna a prison ban samu damar faɗa maku ba.......” a tsanake Unaisah ta labarta masu dukkan abun da ya faru tun daga kan tattaunawarsu da Salsabeel farkon haɗuwarsu a gidan kurkukun ƙaddara da kuma gwagwarmayar da suka yi wajen shawo kan Danish da ruwan zam zam, Har izuwa kan abunda ya faru jiya daya rikiɗa ya zama maciji, tunda tafara basu labari hankalinsu ya tashi matuƙa, sun girgiza da jin cewa Danish dinsu GIANT ne, Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu, idanuwansu a zazzare, Jikin ta ƙaura yai la’asar, wato an gudu ba atsira ba.
Chapter 138 · 0% Book details