← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 152

Sashe 118

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kaga Bana son surutu, Yanzu na dawo cikin gidan nagaji ina buƙatar in huta,” yaƙi bari ta ƙwace kanta daga ruƙon da yai mata.

“Bansan meyasa kike Yi min haka ba! Sam baki darajani a matsayina na mijinki, bakya jin shakkar fadamin kin fita ba tare da iznina ba” a faɗace ta fusge kanta daga jikinshi ta juya tana dubanshi.

“Oh gidan Yaya hateem din ne saina nemi izinin ka zan shiga? Sai kace na tafi wata uwa duniya, ko kamanta ne? Acikin estate din nan gidanshi yake, na shiga wurin matarshi ne don mu ƙara gaisawa, shi kenan komai zanyi dole saina faɗa maka”? Ta faɗa tana jifarshi da harara, bawan Allah Ya tsare ta da ido yana kallonta, Idan tana yi mashi magana tamkar zata rufe shi da bugu

Guntun tsoki taja”ka daina kallona, ka wani tsareni da ido kamar zaka lasheni, ni bansan meyasa kake son zama ɗaki ba kamar wani munafuki, gasu baba can a falo ka shiga wurinsu ka zauna ayi fira dakai”

Shiru yai bai tanka mata ba, babu alamun zai daina kallon nata.
Ta6e baki tayi”Idan baka da abunyi ni inada shi, don haka bani wuri In wuce”

ta faɗa tana ƙoƙarin bi ta gefenshi da niyar ta tafi, ba zato ba tsammani taji ya damƙi damtsen hannunta, ruƙo bana wasa ba, har saida ta ɗago idanuwanta azare take dubanshi.

“Kidaina yi min faɗa, bafa tsoronki nake ji ba, Ina raga miki ne saboda ƙaunar da ke atsakanina dake” har saida taɗanji gabanta ya faɗi rass, ganin yadda ya haɗe fuskarshi, kwata kwata babu annuri tamkar bai ta6a dariya ba.

“Ke komai baki Iya ba dangane da zamantakewar aure? Sai kace ba mace ba? Baki Iya soyayya ba sannan baki da lokacina sai idan kinga dama zaki bani hakki na? Abu kaɗan saiki rufeni da faɗa kamar ɗan cikinki? Ko kin manta matsayina awajenki? Idan kin manta bari na tuna maki, Ni mijinki ne a ƙarƙashin ikona kike, Nafi kowa Iko dake hatta mahaifinki, Aljannarki tana a ƙarƙashin ƙafata idan har bakiyi min biyayya ba tayaya kike tunanin zaki sameta”? cikin jin ƙunar rai Ya furta hakan, maimaikon yaga nadama akan fuskarta sai gani yai ta tuntsire da dariya har fararen hakoranta suka bayyana, fisge hannunta tayi daga ruƙon da yai mata.

Ta ruƙe qugu ta matsa dab dashi kafin ta soma magana”Naji abunda kace babyn baby, sai dai akwai gyara a kalamanka, bani ce nake a ƙarƙashin ikonka ba, Kaine kake a ƙarƙashin ikona, ko kamantane, agidanmu kake zaune, cin ka shan ka suturarka dama komai nice nake kula dasu, baka da wata power pravin, babu yadda za’ai nayi maka biyayya sai dai kai kayi min saboda nina cancanci hakan, Nice hula kaine ɗan kwalin, aljanna kuma ta mai rabo ce” da wulaƙanci take furta maganar, lamarin ya ɗaure mashi kai, a iya saninshi saratu tana da ilimin addini amma idan tayi wasu kalaman ba ƙaramin mamaki take bashi ba, Ƙululun bakin ciki Ya hana ya furta mata magana, idanuwanshi sun kaɗa jawur dasu, Ranshi Ya 6aci sosai a fusace Ya juya ya fuce daga ɗakin, ta6e baki tayi aranta ta ayyana”matsalarka ce koda yake laifina ne dana auri dangin kirishna, masu bautawa soyayya” ta faɗa tana dariya.

❤🤍❤

A Zazzaune suke saman tattausan carpet, ɗan ubansu zubin kafi mage Laushi dake A cikin katafaren falon gidan baba obie, daga tsakiyar Royal sofa set din falon carpet din Yake a shimfiɗe hadadden gaske, tamkar shimfiɗar sarakuna, an kewaye bakin carpet din da tuntun, asaman su dattijon arziƙi Ya ɗaura kanshi, Prime minister Hateem Yana a kishingiɗe shima ya ɗaura kan nashi saman tuntun, Basu kaɗai bane saman carpet din akwai senate lateef tare da his excellency deen da kuma His excellency abdul Razak duk sun kishingiɗa kansu saman tuntun, kowan nan su jabbiyace a jikinshi, ta obie data hateem launi ɗayane ruwan toka, hateem ya manna farin glass a idanuwanshi hannunshi na dama hadaddiyar Agogon azurface mai kyan gaske, zobenta ne a yatsun hannun shi.
Jallabiyar sharafuddeen data his excellency deen launin brown ce, yayin data Senate lateef ta kasance milk colour, hankalinsu kwance suke shan firarsu, sun baro iyalansu a makwancinsu, yayin da su kuma suka haɗa majalissarsu afalo.

Babban tray ne aka ajiye masu kan carpet din, Saman shi Tea pot ce mai ɗauke da green tea, ga jerin kofuna, suna fira suna shan abunsu
“Baba mun cika ka da surutu ko”? Senate lateef ne Yai maganar yana duban fuskarshi.

Ɗaura hannu yai saman gemunshi tamkar yana kitsa shi Yace”Ni ai banƙi kuyita surutu ba daga yau har gobe, wallahi bana gajiya da sauraronku, Ina jin daɗin ganin ku atare dani, nayi kewarku sosai”

Murmushi kowan nan su Ya saki, In ka cire hateem daya lumshe idanuwanshi ga dukkan alamu bacci yake ji.
“Kamar yadda baka gajiya da sauraronmu muma haka bama gajiya da faranta maka,” acewar his excellency deen
lumshe idanuwanshi yadanyi hadi da jinjina kanshi
His excellency abdul razak Yace”baba, akwai wata magana mai mahimmanci da nakeson Yi dakai, tunda yanzu duk mun haɗu agaban ka, Inaga Yakamata muyi anan idan ka bani dama”!

Mayar da hankali obie Yai akan abdul razak”ina sauraronka”

“Dangane da matasan family dinmu, bai kamata mu zuba masu ido muna kallonsu ba, yakamata kowan nan su ya fidda matar da zai aura”

His excellency Deen Yace”Ni kaina abun yana damuna, wani abin ɗaure kanma Yaran tamkar basu da ra’ayin ajiye Iyali, kaga Justice namu da dr nawaz sam basu son Inyi masu zancen aure”

Murmushi obie Yasaki yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Senate yace”har ƙwara Ziyad, idan nayi mashi maganar aure sai kaji yace inada wannan burin baba in sha Allah nan bada jimawa ba zan fidda matar da zan aura ka tayani da addu’a Allah ya bani mace ta gari”

Mai girma sharafuddeen dake sauraron yayyan nashi, hannun shi ruƙe da mug na tea da yake kur6a, da alama yana jin dadin tattaunawarsu.

Deen yace”su kuwa waɗannan ba’a maganar ƴa’ƴansu, dama ance magaji mafiyi, akansu na fara shaidar hakan” yai maganar Yana nuna Sharafuddeen da Hateem.
Gyaran murya sharafudden yai kafin ya soma magana atsanake”lamarin Owais namu sai addu’a, Ni bana gane kanshi, mace bata agabanshi, na ta6a yi mashi zancen aure sau ɗaya sai ce min yai baya son ya ɗaurawa kanshi nauyin da bazai Iya sauke shi ba”

Murmushi kowan nan su ya saki, Obie yace”kada ku takura kanku akansu, lokacin yin auran nasu ne baiyi ba, da zarar time yayi babu wanda zan saurara acikinsu sai dai kawai suji sanarwar ɗaurin auransu a masallaci”

Jinjina kai sanate Yai”baba ka kawo shawara mai kyau, mu haɗa kowan nan su da abokiyar rayuwarshi, tunda muna da ƴan mata a family namu”
His Excellency abdul razak Yace”wai Ina ɗan uwa mubarak Yaje ne”?
Senate lateef Ya bashi amsa da cewa”ɗazu dai muna zaune naji wayar shi na ruri har nace mashi ya dubata ana kiranshi, tun da ya fita har yanzu shiru bai dawo ba, wataƙil ya wuce gidanshi”
“Mu ma yakamata muje mu kwanta, mu huta” acewar deen.
Daura ido obie yai akan fuskar Hateem babu alamun Yana sauraronsu.
Gyaran murya yai mashi haɗi da zungurin kafaɗarshi da hannu, firgigit Ya ware idanuwanshi Yana faman yamutsa fuska”Idan bacci kake Ji yakamata kaje ka kwanta” girgiza kai yai”a’a ba bacci nake ji ba, Ina sauraronku”

da zolaya senate lateef yace”Oh, mu ka maida shashashu mun saki baki munata surutu ka kasa kunne kana sauraronmu, Wato kafi ƙarfin ka tanka mana”

Mai girma sharafudeen Yace”bacci yake ji fa, ba sauraronmu yake yi ba, tun ɗazu na lura dashi, baba ne Ya farkar da shi,” ya faɗa yana duban hateem”malam ka tashi kaje wurin Iyalinka ka kwanta ka huta”
Yamutsa fuska Hateem yai”Na faɗa maka ba bacci nake ji ba, idona biyu” ya faɗa yana zare mashi manyan idanuwanshi, dariya suka saki gaba ɗayansu.

Kafin wani Ya kuma furta kalma, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka Jiyo masu sautin fashewar glass, Baba obie Yace”kuna jin abunda nake ji kuwa? Ko dai kunnuwana ne suka jiyo mun badai dai ba”

Senate yace”kamar fashewar glass, bari in duba” ya faɗa yana mikewa tsaye, karaf idanuwanshi suka sauka akan Giant snake din dake ƙoƙarin faɗowa ta ƙofar glass din wani ɗaki dake acan upstair hawa na Uku, ras yaji gabanshi Yai mugun faɗuwa, Muryarshi na rawa ya furta”inna lillahi wa’inna ilaihirraji’in!” Jin ya zabga salati yasa Sauran ƴan uwan nashi sukayi saurin miƙewa, tare da daura idanuwansu saitin inda senate Yake kallo, tashin hankalin da ba’a sanya mashi date, sunyi matuƙar firgita da ganin danƙareran macijin dake bin jikin bene Yana ƙoƙarin saukowa down, jikin baba obie Ya hau yin kerma abunka ga tsoho, Ido Ya raina fata, lamarin ya ɗaure masu kai, Deen yace”maciji kuma? Tayaya akai ya shigo gidan nan? ina jami’an dake tsaronshi? Wannan wani irin ganganci ne”?

Kafin wani ya bashi amsa, kwatsam suka jiyo takun tafiyar jami’an isod, da gudun gaske suke shigowa cikin falon, hannayensu ruƙe da bindigu, atare suka hada baki wurin furta”yalla6ai ku kwantar da hankalinku, zamu kawar maku dashi,” A matuƙar ruɗe baba obie yace”baku da hankali, taya akai kuka bari maciji Ya shigo gidana? A haka kuke fadin mu kwantar da hankalinmu? Kun makance ne baku ganin girman shi? tayaya zaku Iya kamashi”! Da sauri Senate ya tari nunfashinshi”baba kayi haƙuri, zasu fitar dashi, mubarsu suyi aikinsu”

Daya daga cikin jami’an yace”kayi hakuri yalla6ai ba laifinmu bane, mu kanmu bamusan tayaya akai Ya faɗo cikin estate din nan ba, babu wanda yasan daga ina Yake”

da hannu deen Ya nuna masu hanya”ku shiga kuyi aikinku” da sauri suka nufi benan.

Adaidai lokacin Unaisah dake ta faman gudu ta shigo cikin falon tana haki, duk ta fita hayyacinta, kusan atare suka ɗaura idanuwansu akanta, da mamaki akan fuskokinsu suke dubanta, kafin wani yai yunkurin yi mata magana, Chief owais Ya faɗo falon tare da big guy, sunyi mamakin ganinshi babu wanda yasan yana a ƙasar, tsabar firgici da tsoro Ya hana Obie furta sunanshi sai faman binshi Yake Yi da kallo.
Chapter 118 · 0% Book details