← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 152

Sashe 123

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya fargar da ita, tana faman haɗiyar yawu idanuwanta da fargaba take duban zeenatu
Daƙyar ta iya buɗe baki ta yi mata” magana”zeenatu ruwa! Ruwan zan sha”
Tsagaitawa zeenatu tayi da yin kukan jiki na rawa ta sauko daga saman gadon, ta nufi ƙaramin frigde din ɗakin, ta buɗe ta ɗauko mata bottle water me sanyi ta dawo ta haura saman gadon ta miƙe ma benazir, yatsun hannunta na kerma ta kar6i roba ruwan tacire nurfin ta kafa abaki tana sha, maƙoshinta har sauti yake badawa kwat !kwat!. zeenatu ta natsu tana kallonta, gaba ɗayansu sleeping dress ne ajikinsu.
Bayan ta gama shanye ruwan ta daura bottle din saman drawern gefen gadon,
Ajiyar zuciya tadan sauke, kafin ta dubi zeenatu data kwa6e fuska idanuwanta sunyi luhu luhu bacci bai isheta ba an tashe ta daga bacci
“Aunty ki faɗamin meke damunki”
Lumshe ido benazir tadanyi kafin ta waresu akan fuskar Zeenatu
“Babu komai ƙanwata, mummunan mafarkine nayi”
Ajiyar zuciya zeenatu tasauke”amma aunty kin tada min hankalina, nayi tsammanin wani abunne ke damunki ko baki da lafiya, kuma naji kina cunkulina” ta fada tana nuna mata damtsen hannunta, fatar wurin tayi jawur saboda tsunkulin da benazir tayi mata kiris ya rage ta fashe.
Jikin benazir ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin irin illar da tayi mata
“Kiyi haƙuri ƙanwata, bansan nayi ba, cikin magagin baccine na cunkule ki”
Murmushi zeenatu tasakar mata”kada ki damu auntyna, na fahimce ki,” ƙaƙalo murmushi benazir tayi yarinyar ba ƙaramin burgeta take Yi ba, ta damu da ita sosai,
“Ki koma baccinki, kada ki makara a school gobe”
Muryar zeenatu da shagwa6a tace”ae bana zuwa makaranta tunda na kammala secondry school daddy ya hanani cigaba da karatu, yace wai sai idan nayi aure mijin da zan aura ya amince min in cigaba da karatu tukunna zani barni”

Jinjina kai benazir tayi har yanzu bata warware daga fargabar abunda ya faru da ita ba, dauriyace kawai take Yi don kawar mata da damuwar dake atare da ita.

“Idan kina son karatun, meyasa ba zaki fidda miji ba? Duk da ni aganina kinyi ƙaranta da aure, gaskiya uncle bai kyauta maki ba”
Sunnar dakai ƙasa tayi cikin jin kunyar benazir tace”to ai nima inason nayi auran kuma ma ina da mijin da zan aura” da zolaya Benazir ta zaro idanuwanta masu dauke da bacci, da sauri zeenatu ta daura kanta saman pillow tana dariya
Kallon bayanta benazir tayi fuskarta dauke da murmushi,
“Faɗamin sunan saurayin naki inji idan yayi mani”
Muryarta ƙasa ƙasa tace”ki tambayi yaya shureim, yasan shi zai fada maki sunanshi” benazir bata kawo komai aranta ba, tace”to zan tambayeshi idan Allah yakaimu gobe, yanzu dai mu kwanta muyi bacci” amsa mata tayi da toh, atare suka kwanta, hankalin benazir yaƙi kwanciya gani take tamkar abunda ya faru a mafarkinta zai faru gaske, hakan yasa ta rungume Zeenatu ajikinta, gudun kada aƙara shaƙeta, addu’o’i ta karanto ta tottofa masu kafin ta lumshe idanuwanta.

Bakomai take tariyowa ba face fuskar tajuddeen, da fuskar baby din data bari acikin kwamin wanka, tuni hawaye sun wanke fuskarta, taƙosa su dawo ƙasar, fatanta Allah Yasa taj dinta baiyi aure ba, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.

*Ex-prisoners💔*

Tsoro da fargaba ya hanasu runtsawa, sunyi zazzaune saman dining chairs, ummin america bata ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, sam takasa samun natsuwa, jefi jefi takan dago da ido ta dubi su Batul, Har yanzu hanna bata fito daga ƙarƙashin table ba.

Jemimah tana azaune saman laps din Haris Ta ƙankameshi tuni bacci yajima da yin awon gaba da ita, abun duniya ya ishi Parveen, Jikinta sai rawar ɗari yake yi saboda ruwan data watsa ma rigarta, ta jiƙe sharkaf, ga sanyin a.c abu goma da ashirin, azeeza data suma ta farfado tun bayan da sajeed Ya yayyafa mata ruwa, sai faman firgita take Yi, macijin tamkar Yana yi masu gizau, ga bacci a idanuwansu sai dai sun kasa runtsawa, kowa da abunda ke damunshi basu san meke wakana acikin gidan ba.

“Dan Allah Ku bani mayafinku In lullu6e jikina sanyi nake ji” parveen ce tayi maganar, babu musu Batul Ta curo mayafinta ta miƙa mata ta sanya hannu ta kar6a ta lullu6a shi ajikinta.

“Ni nakasa gane meke faruwa! ya akai maciji Ya shigo gidan nan? Ummi ce ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta.

Shiru sukayi babu wanda ya tanka mata, babban abunda suke jima fargaba kada ace mutanan prison ne suka kawo masu hari, shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.

“Ni abunda ke damuna, Danish dinmu da unaisah, bansan awani hali suke aciki ba, Allah yasa babu abunda ya same su” In a cool voice Batul ta furta maganar.

Tamkar ta tsokano Jemimah, cikin bacci ta fashe da kuka tana sambatun”wayyo Allah genie dina, dodo zai cinyeta, kuje ku dauko mun ita” da sauri Haris Ya toshe mata bakinta da tafun hannunshi”kiyi mana shiru, ko so kike dodon Ya jiyo kukanki yazo wurinmu”?

Ba tare data buɗe idanuwanta ba tace”a’a amma genie fa? Tana can ita da Danish dodo zai cutar dasu, Ni dai ku ƙyaleni inje wurinsu” ta faɗa tare da buɗe kumburarrun idanuwanta, da ƙarfin hali tasoma kiciniyar saukowa daga saman laps din haris don ta fita daga dakin
Ummi tace”kada ka bari ta sauko ka ruƙeta, idan ba haka ba zata iya janyo mana macijin nan”
Amsa mata yai da toh, ya rurruƙe jemimah ajikinshi.
“Ki kwantar da hankalinki, babu abunda zai samu Unaisah, ai naga mutanan nan masu baƙaƙen kaya, wata’ƙil ma harsun kashe shi”

Javed ne yayi maganar, jemimah dai taƙi haƙura, tacika masu kunnuwa da shessheƙar kuka.

Ƙwanƙwasa glass din ƙofar da akayine ya firgitar dasu, arazane suka dago duka a tunaninsu macijin ne Ya daki glass ɗin, ganin Boss Man yasa suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa Ummi ta miƙe ta nufi ƙofar, ta bude mashi bai shigo ba daga waje Ya tsaya.

“Ina macijin”? Tambayar data fara jefa mashi kenan”
Yayi mamakin ganin yadda jikinta ke rawa, har saida yadan saki murmushi ta cikin face mask dinshi
“Haba ummi tsoronshi kike ji kema”?
Ta6e baki tadanyi kafin tace”bazaka gane bane, wallahi na firgita macijin yayi girma dayawa”
“Ki kwantar da hankalinki, ba maciji bane mutunne nasan ko nayi maki bayani ba lallai ki fahimce ni ba”

Zaro ido waje tayi”what! Kana nufin mutunne? Tayaya haka zata yiwu”? A rude ta jefa mashi tambayar

“Kodai kana nufin abunda naji unaisa tana faɗi gaskiyane? Na cewa Danish ne ya zama maciji”!

Jinjina mata kai yai”hakane, gaskiya ta faɗi”

Cikin jin faɗuwar gaba ummi tace”ni dama najima ina zargin yaron nan ba mutun bane, saboda kyanshi yayi yawa ashe aljanine”

Boss yace”ba aljani bane, mutunne shi kamar kowa, yanzu bani da isasshen lokaci, zuwa gobe da safe zanyi maki bayani,” tsantsar mamakine Ya kamata.

Muryar Jemimah ce tajanyo hankalinshi ga kallonsu”Boss man ina genie ɗita? Dodon nan ya cinye min ita ko”
Shiga cikin ɗakin yai, sam sun kasa motsawa suna jin muryarshi sai dai tsoro Ya hana su je gare shi
Ɗaya bayan ɗaya yake dubansu,
“Dan Allah ku kashe abunnan bamu son ganinshi duk ya firgitar damu” parveen ce tayi maganar tana dubanshi
Batul tace”boss ina ƴan uwanmu suke ne? Bamusan awani hali suke ciki ba”
Goya hannayensa yai saman ƙirjinshi Yana dubansu
“Basai nayi maku bayani ba, unaisah ce zata faɗa maku komai, abunda nakeso daku Yanzu ku kwantar da hankulanku, Ku tashi muje na raka ku ɗaki ku kwanta kuyi bacci, dare yayi sosai kusan ƙarfe goma sha daya da rabi”

“Nidai bazan kwanta bacci ba, sai naga genie dita” acewar jemimah
Azeeza sarkin tsoro tace”bazan Iya kwana aɗaki ba, wannan abun zai Iya faɗowa ɗakin Ya cutar damu”
Dama yasan da wuya su iya kwantar da hankalinsu.
Kallon Ummi yai”please ki tafi da dasu ɗakinki su kwana kafin zuwa gobe idan komai ya lafa, sai su koma nasu ɗakin”
“Badamuwa, ku tashi mu tafi” acewar ummi.

Miƙewa sukayi daga saman kujerun, matan dake acikinsu, Batul azeeza da jamimah, Boss Yace”Ina ƴar uwarku Hannah”?
“Gatanan ƙarƙashin table,” sajeed ne ya faɗa tare da duƙawa ya janyota da ƙyar, ta ƙudundune kanta kamar kifin gwangwani,.
“Hanna ki tashi ku tafi” daƙyar ta miƙe tsaye zufa duk ta wanke fuskarta,
“Sannu da jiki” boss ne yai mata maganar, sai faman zazzare idanuwanta take Yi.
“Zanje na rakasu ɗaki, Sajeed ka tafi da sauran ƴan uwanku maza” amsa mashi yai da toh,
Tamkar karsu fita daga dining room din, gani suke kamar macijin zai dawo masu, badan boss na atare dasu ba dakuwa babu wanda zai Iya fitar dasu saboda tsoratar da suka Yi, asaman bayanshi Ya goya azeeza, ummi ta dauki jemimah abayanta, Batul ta ruƙo hannun parveen dana Hannah, Ahaka suka jera suna tafiya har suka ƙarasa ga second floor, a ƙofar dakin ummi suka dakata dayin tafiyar, ta buɗe kofar suka shiga daga cikin, bayan boss Ya sauke azeeza daga saman bayanshi yayi masu sallama ya juya ya fuce.

Sai faman baza ido suke Yi, Yau gasu adakin Ummi, Bedroom ɗinta Ya haɗu kamar na amarya, an zuba mata kayan alatu.
Ganin ya fuce daga ɗakin Yasa tayi saurin zuwa tayi locking din ƙofar, tabi windows din dakin ta zugesu, tukunna hankalinta Ya kwanta.
Dubansu tayi sunyi tsaitsaye curko curko suna jiran umarninta
“Parveen ki shiga toilet ki ƙara tsarkake jikinki” amsa mata tayi da toh, a tsorace ta shiga toilet din.
Kallon jamimah da azeeza tayi”akwai wadda takeyi fitsarin kwance acikin ku”? Girgiza mata kai sukayi alamar a’a
“Ke fa”? Ta jefa ma batool tambayar
Itama tace a’a,
Gyaɗa kai tayi”okey, amma gadon bazai ishemu ba, Ni ban saba kwana atakure ba, mutun biyune zasu samu damar hawa gado, Biyu sai su kwana saman carpet” tayi maganar tana nuna masu carpet din dake a shimfiɗe.

“Ga kuma Sofa wazai kwana asama”? Ta fada tana dubansu
Maƙe kafaɗa jemimah tayi”ni wallahi bazan kwana saman carpet ba, tsoro nake ji,”

“Nima bazan Iya kwana ƙasa ba, dan Allah kibari mu kwana saman gadon mu duka” Azeeza ce tayi maganar tana marairaice mata fuska don taji tausayinta.
Chapter 123 · 0% Book details