Sashe 75
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryarta tamkar tame Yin raɗa ta furta “Speechless! Major Ina kuka samun Kyakkyawar matashin nan mai kama da ɗan sarkin aljanu? Anya Cikakken mutunne? Ko dai A cikin Dajin da kuka tsintosu Aljana ta haife shi Ta yada” dariya kowan nan su ya saki jin sambatun ummi dama sai da ransu ya basu zata ruɗe idan taga hoton shi.
Major yace”sai ma kin ganshi a zahiri, ba ƙaramin kyaune da shi ba”
Ko da ta koma ta zauna, sam takasa ɗauke idonta daga kan fuskar Danish, Yayi matuƙar tafiya da imaninta, aranta har ta fara Ayyana koya surar shi zata kasance a zarihi?
Muryar Commender ce ta fargar da ita ga dubanshi”dukansu ne muka nuna maki, shin kin canza ra’ayinka akan kula da su ko kuwa har yanzu kina akan bakanki”
Shiru ta ɗanyi tana yanke shawara da zuciyarta, duk sun ƙagara da son jin amsarta.
“Yanzu haka case din Yaran mun miƙa shi hannun shugaban isod, shine zai cigaba da jan ragamar bincike akansu, jiya muka samu amincewarshi na kar6ar case din nasu, sai dai ya nuna baya buƙatar 6ata lokaci yanason ya tafi tare da yaran can nigeria a jet dinsa, a satin da zamu shiga”
Lokaci ɗaya ummin america ta canza fuskarta zuwa 6acin rai, da farko tayi murnar jin cewa Case din Yana a hannun chief na Isod, daga bisani daya furta komawa Nigeria ne taji komai ya fita aranta.
“Naji kin yi shiru, baki ce komai ba”
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta soma magana ranta a6ace”Idan har kuna so in ruƙe Yaran a hannuna, they should stay in America. I will not follow them to Nigeria,”
Commender yace”amma meyasa? Ke kanki fa ƴar ƙasar Nigeria ce why baki son zuwa ƙasar Ki”
Girgiza kai Tayi still fuskarta da 6acin rai ta furta”Ni ba ƴar nigeria ba ce, asalina ne acan, amma Ni black american ce, tun da nace banaso mubar maganar kawai, Ni zan koma gidan idan ka gama maganar ka”
Yanayin fuskarta Ya canza sosai, 6acin raine tsantsa, sun fahimci kamar akwai wani abu daya ta6a faruwa da ita wanda har yajawo silar barinta ƙasar, kuma batason Anayi mata maganar komawa can”
Ganin yadda ta haɗe rai babu annuri ko miskala zarratin akan fuskarta, Yasa Commender cewa”Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ba zamu takura maki ba, Zaki Iya tafiya” ba don yaso ba ya ambaci hakan, duk basu ji daɗin canzawarta ba, muryarta a disashe ta furta”thank u” ta yunƙura ta miƙe ta nufi ƙofar fita daga office din, Har ta kusa ficewa Muryar Commender ta katse mata hanzarinta”duk da bansan abunda ya faru dake a ƙasarki ba da har yasa kika tsani jin an ambaci sunanta, da akwai wani abu da nike so in faɗa maki ummi” yayi maganar tare da miƙewa hannun shi ruƙe da mug na coffee, Ya kur6a kafin ya ɗaure da cewa”wannan dama ce agare ki, da zaki koma ƙasarki a karo na farko ki nuna ma waɗanda sukayi silar barinki ƙasar cewa Kina araye kuma kinsamu cigaba a rayuwarki ba kamar yadda sukayi tsammani ba, inaso ki basu mamaki ummi, sannan zuwanki Nigeri bana dundun bane na ɗan lokacine zaki dawo nan da zarar Mun samu nasara akan binciken Yaran, zamu dawo dake nan, saboda mu kanmu ba zamu so mu rasa nagartacciyar mace irinki ba, ke kanki kin sani muna ƙaunarki kuma muna daraja ƙimarki a idanuwan mu, ba zamu so abunda zai 6ata maki rai ba ummi, kina da damar da zaki Iya zuwa gida ki zauna ki yi tunani akan maganata kafin ki yanke shawara.
Kalaman shi sun ɗan ta6ata, tuni zuciyarta ta fara sassautowa, ita kanta zataso wannan damar ta zuwa Nigeria ko dan taba waɗanda sukayi silar barinta mamaki.
Numfasawa ta ɗanyi kafin a hankali ta juya tana kallon commender dake tsaye abayanta, kamar bata son furta maganar tace”babu buƙatar yanke shawara, Na amince Zan bi su zuwa Nigeria, Kuma nagode da karramawarku agareni, da zarar na gama aikin, zan dawo ƙasata”
Murmushi major da commender suka saki, Jin abunda tace, har yanzu bata yadda ta kira Nigeria da sunan ƙasarta ba.
Sun ji daɗin amincewarta, ba tare da 6ata lokaci ba, Commender ya dauko mata kundun dake ɗauke da bayanansu Angel, duka takardun akwai Signature dinsu a jiki, saura sanya hannunta suke buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci su ka Ƙulla Yarjejeniya ta (guardianship agreement)atsakanin su da ita, sai da ta natsu ta karanta sharuɗɗansu dalla dalla akan irin rainon da suke so tayima yaran kafin ta sanya hannu a takardun, bayan ta kammala sun bata wasu takaddun yarjejeniyar da zata ruƙe a hannunta.
Bayan tayi masu sallama, Ta fito daga office din, tana tafiya Sojoji Na binta da kallo, Yayin da ita kuma hankalinta na akan takaddun dake a hannunta, Fatanta Allah yasa Ruƙon Yaran da za ta yi da kuma zuwan ta Nigeria Ya zama alkhairi agare ta.
Tun kafin ta ƙarasa gaban motarta da ta bari a harabar ajiye motocinsu, ta hango sojoji dadda6e sun kewaye motar suna jiranta, murmushin gefe fuska tasaki har dimple dinta Ya lotsa, ta fahimci tunda ta shiga office din commender suke ta jiran fitowarta don su yi mata magana, bata tsaya sauraron su ba, daƙyar ta samu suka ƙyaleta ta shiga mota, a tsanake ta tada motar, Ta juya sitiyarin da gudu ta fuce daga head quarter din.
*EX-PRISONERS❤*
Tun ɗazu da safe kowan nan su Ya farka daga bacci, sun wayi gari da jin kyakkyawan labarin farkawar Danish, saboda zumuɗin zuwa ganin shi babu wanda ya nemi breakfast acikinsu, gaba ɗaya sun Hallara a room dinsa, tun daga kan Haris, Javed, Naufal, Gabriel, Batul, Hannah, Jamimah, Azeeza, ƙwansu da kwarkwatarsu sun yi tsaitsaye cirko cirkon suna kallon shi, fuskokinsu ɗauke da Annurin farin Ciki, Ɗaya bayan ɗaya Danish Yabisu ya rungume su a ƙirjinshi, kamar sunyi shekara basu atare da juna, Haris hada kukanshi saboda murnar ganin Danish Ya farka.
Sun tasa shi gaba suna kallonshi kamar zasu lashe shi, Musamman Azeeza da Jemimah, daɗi suke Ji Danish ɗinsu Ya farka.
Muryar jamimah da shagwa6a tace”munyi fushi ma sai yau zaka farka, kullum sai munyi kukan rashin ka, ko bacci bamu Iya yi abincin ma ba mu ci” Harara Azeeza ta watsa mata”wlh ƙarya take yi Danish kullum sai taci abinci sau uku, kuma tana Yin bacci” Murmushi ya saki yana binsu da kallo, Haris dake zaune gefen gadon Danish ya ruƙe hannunshi a Cikin nashi ji yake kamar za a kwace mashi ɗan uwanshi.
“Meyasa Angel Jiya daya farka baki tada mu daga bacci ba? Bayan kinsan irin ƙagarar da muka Yi na son ganin shi” Hanna ce tayi maganar, Gabriel Yace”Ni dai ba abunda zance sai godiya, saboda ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, Yau babbar rana ce agaremu ɗan uwanmu abun alfarinmu Ya farka da ranshi da lafiyarshi” yana daga tsaye yake yin maganar Ya goye hannayenshi saman ƙirjinshi.
“Allah sarki Rayuwa kenan, Har na tuna kokawar da Ku ka yi kaida Danish akan nace zan dire taga” gaba ɗayansu suka sanya dariya.
Batul tace”ai mu bamusan abunda ya haɗa su faɗa ba”
Parveen dake tsaye gefen Naufal hannunta ruƙe da Ayaba sai ci take Yi, Kunnuwanta akansu ta natsu tana sauraransu.
Labari Angel ta basu na abunda ya faru lokacin da zata dire taga, ba ƙaramin nishaɗi su ka yi ba.
Azeeza tace”munyi kuka lokacin sosai, Munyi tsammanin Danish ɗinmu zai rasa idonshi ɗaya, sai gashi Allah ya dawo mana dashi da ranshi da Lafiyarshi, gaskiya munji daɗi” da farin ciki akan fuskarta ta ƙare maganar, idanuwan Danish akan faces dinsu, ita da Jemamah.
Parveen tace”ni banaso muna tuna baya, nafi so inji muna magana akan abunda zai faru agaba”
Jemimah tace”Genie yaushe zamuje gidan daddyn naki? Ni na ƙosa mu koma can, waɗannan mutanan masu jan kumatun, kullum sai sun tsira mana allura a ɗuwawun mu” ta yi maganar tare da nuna ass dinta da indext finger dinta, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Azeeza tace”Kai jamimah ki ji tsoron Allah, Jiya fa ba ayi mana allura ba, nurse ta faɗamin an gama yi mana ita, sai dai magani da zamu dinga sha na tsawon one month” turo mata baki Jemimah tayi
Javed yace”Kufa baku gajiya da abun magana, Kun Cika ɗan uwanmu da surutu, Ko so kuke yi ya koma baccin” atare suka zaro ido haɗi da ɗan buɗe baki”A’a wlh bamu so Ya koma bacci,”
“Alhamdulillah, Tun da yanzu mun haɗu mu dukanmu, Yakamata Muyi wa Allah godiya” Angel Ce tayi maganar, Tare da Ɗaga tafin hannayenta sama, Da sauri suma suka ɗaga nasu zasu yi addu’a, Mutun ɗaya ne bai ɗaga nashi hannun ba, Hatta Gabriel da ya ke Christian sai da ya ɗaga hannunshi don su yi addu’ar atare, Don shi a yanzu baida za6in addini, yafi ƙarfi ta 6angaren musulunci saboda Angel.
Kallon fuskarshi Angel tayi”danish zamuyi addu’a, ba zaka ɗaga hannu ba”
Girgiza mata kai Yayi alamar a’a, ɗaure mashi fuska tayi sai yayi tamkar baisan tana Yi ba
Cikin sanyin murya Haris yace”Danish meyasa har yanzu baka goyan bayan addinin musulunci”?
Shiru danish bai yi magana ba, Kuma babu alamun zaiyi ta.
Damuwace ƙarar akan fuskokinsu
“Pls danish just for today ka ɗaga hannu Muyi addu’a” Muyar Angel tamkar zata fashe mashi da kuka Tayi maganar.
Marairaice mashi fuska Azeeza da jemimah sukayi”Bro pls, let pray together,”
Runtse idanuwanshi Yai, ba tare daya buɗe su ba Ya furta”I can’t, ku daina yi mini magana akan Inyi, bana so”