← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 152

Sashe 47

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin wani Ya ƙara magana acikinsu, Nurse rebecca Ta turo ƙofar ɗakin Hannunta ruƙe da faffaɗan tray na kayan abinci da aka jera masu, A saman table ta ɗaura masu, kafin ta ɗago tana dubansu fuskarta ɗauke da murmushi tace”Idan kuna buƙatar wani abu zaku Iya kira awaya ku sanar dani” Ta yi maganar tana nuna masu wayar dake ajiye saman table, al’ajabi ne ya kama su wai yau sune ake tarairaya? har tambayarsu ake yi in suna buƙatar wani abu? Wannan wani irin abun farin ciki ne!

Har ta juya zata fuce, Muryar Angel ta dakatar da ita “Sister, which country are we in?” ? ta tambaye ta ne don ta ƙara tabbatarwa
Juyowa Nurse rebecce tayi fuskarta da fara’a ta furta”San antonio texas” idanuwan angel luhu luhu ta ce”Thank u”
Hankalin Angel Yaƙi kwanciya, sam bata lura Sun fara Cin abincin ba, gaba ɗayansu sun dawo bakin gadon, Su parveen banza ta samu, soyayyar kaza mai maiƙo ta damƙa tana turawa abaki atsiyace take cizgar Naman kazar, Jemimah ta sungumi tsiran nama ita da azeeza, Batul kuwa Soyayyan ƙwai ta ɗauka tana Ci har wani nannaɗe shi take yi kafin ta tura abaki, Hannah ko warmer ta ɗauka shaƙe da Chips tana ci, Ba baka sai kunne, Su naufal an dahi Chicken shawarma, Javed ko Kayan marmari ya damƙa yana sha, kamar kwancen Yunwa Sun zaƙe suna ci suna Korawa da lemu me sanyi kala kala aka kawo masu, basu san akwai cctv ba a ɗakin, Duk wani motsinsu ana kallonsu😂
Ita kanta Angel data dubesu saida gabanta ya faɗi, Ganin yadda suke cunkusa abinci abakunansu Kamar kuraye, Muryarta na rawa take faɗin’pls ku bi a hankali kada ku shaƙe” tamkar kurame babu wanda ya dubeta bama su san akan me take magana ba, a dole ta ƙyalesu ta zura hannu ta ɗauki burger tana ci...........

*BARI MU LEƘA GIDA NIGERIA*

*A DAULAR OBIE ESTATE*

A Zaune take dirshan acikin Katafaren Bedroom ɗin Obinna, wa’iya zubilla kai kace ɗakin matashin saurayine saboda tsabar haɗuwarshi, An kashe dukiya a furniture ɗin ɗakin komai na cikinsa launin Red and golden ne, Ko sarki Albarka, Tanƙamemen gadonsa Royal state bed irin gadon da ko mutun baijin bacci ya hau sai Ya runtsa, Ga wasu matassan kai launin red da golden jere a gaban headboard ɗin, Dogayen labulaye ne a kewaye da ɗakin, ga wasu bedside drawers masu ɗauke da lamp, daga saman ceilling ɗin ɗakin Haɗaɗɗen Chandeliar ne dake bada hasken ɗakin ga wata zungureriyar Sofa Bayan ita akwai arm chairs masu ɗan banzan kyau, Ga wani ƙayataccen table dake ɗauke da Kayan Ado na ɗaki. Daga jikin bangon ɗakin haɗaɗɗiyar wallpaper ce mai zanan flowers masu matuƙar ƙayatarwa da jan hakalin me kallonsu, floor ɗin ɗakin tamkar mirrored tiles ne Kana Iya ganin fuskarka a cikinsa tamkar madubi, ga wani Jigunannan Dressing mirror Tafkekan gaske Jerin tsadaddun turarurrukane ne asaman shi da sauran kayan gyaran jiki, idan nace zan cigaba da zayyana haɗuwar Ɗakin dattijon arziki tabbas zamu ƙare takun tsakiya wurin fasalta Kyawunshi.

Yana daga kishingiɗe saman lallausar mattress ɗin gadon, Apple laptop ce agaban shi, Da alama Video call Ya ke yi da wani, ɗabi’arsa ce yana magana yana shafa gemun shi wani sa’in har Jan shi ya ke yi.

Hajiya saratu tayi zaman cin tuwo saman lallausan carpet ɗin gaban gadon shi, tana jiran Ya kammala Yin wayar, ta tsare shi da ido babu annuri akan fuskarta, Hankalin shi gaba ɗaya yana akan fuskarta, Nazarin yanayinta ya ke yi, kamar daga sama ta tsinkayi muryar shi akanta
“Saratu kin wuni lafiya”? Ƙara tamke fuskarta tayi”lafiyalou baba, fatan na same ku lafiya” murmushin gefen fuska ya sakar mata”Alhamdulillah, in ce ko lafiya? Naga yanayin fuskarki da 6acin rai, Waye ya ta6amin autata ne yanzu in ɗaura ɗamarar yin yaƙi da shi” murmushin Yaƙe ta ƙaƙalo, har ta buɗe baki zatayi magana yai saurin tarar numfashinta”nasan kinzo gaishe da baban nakine kamar yadda kika saba, Naji daɗi sosai mamana, Bari na kira hajjaty A waya ta kawo mana dinner mu ci atare ni da autana” tur6une fuska Hajiya saratu tayi”ba yunwa nake ji ba, Zuwa nayi mu yi magana, kafin barina ɗaki sai da nayi magana da masu aiki nasan sun kai min a ɗakina”
“Ai nasan ba yunwa kike ji ba, Ni nake ra’ayin cin abinci tare da ke, idan mun kammala sai mu yi magana” aruɗe take kallonshi, ƙiri ƙiri Ya hana tayi magana.
Ba tare da ya jira amsarta ba, Ya ɗauki waya dake saman bedside drawer, Ya kira landline na kitchen, bugu uku aka ɗaga kiran, muryar sophia ce ta ratsa kunnansa cikin girmamawa ta gaishe da shi.

“Ina buƙatar Dinner ɗina a shigo min da shi ɗaki yanzu” amsa mashi tayi da toh kafin yai rejecting call ɗin, idanuwanshi akan saratu da ta haɗe rai, kasa jurewa tayi don baƙaramin takura tayi ba hakan yasa ta soma magana ba tare da ta jiran umarninsa ba.

“Baba ni gaskiya ba a kyautamin agidan nan, akan me za’a dinga kushe min ƴa’ƴana ana yabon na wasu, abun yana ƙona min rai bana jin daɗi, haba dan Allah wannan ba adalci bane, kuma ba girman Yaya Lateef bane da yaya mubarak su zauna suna faɗan maganganun marasa daɗi akan ƴa’ƴana, ni kaɗai ke ba’ason ya’ya na a family din nan ko dan saboda ban auri jinsin mu bane” Rai a6ace take yin maganar, tun da ta fara magana bai dakatar da ita ba, ya natsu yana sauraronta idonshi akan fuskarta, dama tun kafin ta fara yin maganar yasan meya kawo ta, Yana mamakin Halin saratu, ko irin alkunyar nan babu, idonta ya rufe akan ƴa’ƴa da miji, abu ɗayane take jin nauyin yi wato idan tana zazzaga masifa bata bari su haɗa ido dashi, murmushine akan tausasan la66ansa
“Kin gama maganar ko akwai saura” bata ɗago ta kalle shi ba idonta na akan carpet ɗin da take a zaune dirshan
“Hateem Faɗa min menene sunan macan da take ɗaukar zigar miji”? ras taji gabanta yai mugun faɗuwa, A ruɗe ta ɗago da ido tana kallon fuskar obinna, ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, Ji take tamkar ta yunƙura ta miƙe ta zuba da gudu don ta fahimci Video call yake yi da Yayanta hateem na ƙasar Canada, Hakan na nufin duk wata magana da ta ke faɗama babansu akan kunnanshi, Hankalinta ya tashi don ba ƙaramin jin shakkar shi ta ke Yi ba, duk acikin yayunta tafi fargabar sharafudden da hateem.

A hankali Obie Ya juya mata Lapton ɗin gabanshi don suyi magana da Yayanta, sunnar dakai ƙasa tayi sam ta kasa ɗagowa ta kalli screen ɗin laptop nasa
Daddaɗar muryar prime minister Hateem ce ta ratsa kunnuwanta
“Ji ra kike in gaishe ki”? Girgiza kai tayi tamkar tana agabanshi, cikin girmamawa ta soma gaishe da shi
“Ina wuni Yayana, Ya aiki Ya iyali”
“Ki ɗago da ido ki kalle ni Saratu”! Da kakkausar Murya ya furta hakan, Yawu ta haɗiya kafin A hankali kamar maijin tsoro ta saci kallon screen ɗin.

Tabarakallahu ahsanun khalikin!! Ni kaina da nake rubutawa sai da alƙalamina ya girgiza da ganin Kyakkyawar surar nan mai cikar kamala, gwarzon namiji jajirtacce, kallon ɗaya zaka Yiwa fuskarshi ka shaida Jinin Obinna ne, Yana ɗaya daga Cikin waɗanda su ke kama da babansu, basu baro komai nashi ba, Kyanshi, ɗabi’unsa da halayansa, Fatarshi kaɗai abun kallo ce, yadda kasan da ruwan madara ake mulketa saboda tsabar kyau, skin colour ɗinshi launin na mahafinshi ne, A zaune yake Cikin Katafaren Office ɗinsa dake a Presidential residence Na ƙasar Canada, tsayawa zayyana kyawun Office ɗin da dukiyar da aka kashe masa wurin zuba kayan cikinsa abune da hankali ba zai ɗauka ba, wata’ƙil zamu ƙare Takun tsakiyane wurin zayyana shi, wasu hadaddun tailored suit ne a jikinsa sunbi shape ɗin jikinsa, mutumin akwai ƙira.

“Bai kamata kiji kunyar haɗa ido dani ba Saratu, tunda har kika iya tako ƙafafuwanki kika zo ɗakin baba don kiyi mashi masifa, Ke ko kunya bakya ji? Ki zauna Miji Yana ziga ki Kan ƴan uwanki? Sara Ba haka nasanki ba, Ni ba haka ƙanwata take ba, jarumar macace mai hankali da tunani, why kike son bani Kunya”? Maganar Hateem tayi matuƙar sanyata jin kunya, duk sai ta ji haushin kanta ya kamata, tayi danasanin zuwa ɗakin obinna, saboda tana matuƙar jin nauyin Hateem, da ace tasan da shi suke yin video call da batayi gigin zuwa kawo ƙorafi ba.
“Kiyiwa kanki faɗa saratu, Ba girmanki bane, Ƴa’ƴanki ai namu ne, babu wani banbanci, nasan abunda Yaya mubarak da Yaya lafeef zasu faɗi bazai wuci akan Cigaban Ƴa’ƴanki bane, maisonka shike faɗa maka gaskiya duk min ɗacin ta, Maƙiyinka kuwa sai dai Ya 6oye maka yakamata Kiyi tunani ƙanwata” Cikin kwantar da murya yake yi mata nasiha, shi kanshi Obinna har lumshe ido yake yi saboda jin daɗin nasihar da Hateem Yake yiwa ƙanwarshi, kuma ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi sosai
Muryarta tamkar zata fashe da kuka ta soma magana”In sha Allah yaya zan kiyaye, bazan ƙara biye mashi ba, zuciya ce ta ɗibe ni, Ni kaina nasani kuna son ƴa’ƴana shiyasa kuke yi masu faɗa don su gyara, duk wanda ya rasa faɗi a duniya yai asara, ina jin daɗin ƙoƙarinku akaina da ƴa’ƴana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku” idanuwanta har sun cicciko da ƙwalla
“Kada ki bari hawayen nan su zuba, Kinsan banaso ko”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh”Okey yi min murmushin nan naki in gani” Dariyace ta kubce mata, da sauri ta ɗaura kanta saman manyan laps ɗinta
“Ya aikin naki? Fatan komai na tafiya lafiya” amsa mashi tayi da”lafiyalou”

Jinjina kai Hateem yai”Allah ya taimaka” sallama sukayi da ita Obie Ya juya laptop ɗin, idon shi akan Hateem
“Shiyasa nake Ƙaunarku, Saboda ku ɗin na dabanne, ƴa’ƴana abun alfaharina, Allah Yabar munku, ubangiji Allah ya tsare mun ku Ya kare munku daga sharrin maƙiya da mahassada......”addu’o’i obinna yadinga jero mashi, Yana masa mashi da ameen ameen hada saratu wurin amsawa daga bisani Suka yi sallama dashi
Rufe laptop ɗin yai tare da miƙe ma saratu, Yunƙurawa tayi tare da matsawa gaban gadon ta kar6i laptop ɗin ta nufi saman desk ɗinta ta ɗaurata.
Chapter 47 · 0% Book details