← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 152

Sashe 35

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da su Angel suka tafi nemo masu abinci, Sun yi zazzaune zaman jiran tsammani, Har sun fara lumshe idanuwan su saboda iskar dake kaɗa masu ba ƙaramin kasala take haifar masu ba, kwatsam! Ba zato ba tsammani kunnuwansu suka soma Jiyo masu wani irin sautin gurnani mai matuƙar rikitarwa da razanarwa, A firgice suka ware idanuwansu, Yayin da zuciyarsu ke buguwa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zata 6allo ƙirjin su, tsananin tsorone Ya kamasu sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu suke Yi, a ƙoƙarinsu na su gano ta inda sautin gurnani ke fitowa, sai dai sun kasa sani kuma sun kasa ta6uka komai, Azeeza tuni ta shige ma Batul kamar zata koma Cikinta, Jikin su sai faman yin kakarwa yake yi saboda gurnanin ya cika kunnuwansu, Haris dake azaune gaban shimfiɗar Danish muryar shi adabarbarce ya ke ambaton sunanshi”da..da..nish ka tashi, pls ka tashi danish, Wani abu yana tunkaro mu’ Da rarrafe su batul suka ƙarasa gaban shimfiɗar Danish, Cikin fitar hayyaci suke bugun Jikinshi don ya farka ya ceci rayuwarsu, duk sun bi sun ruɗe tsigar Jikinsu ta tashi haiƙam, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanshi”Danish mun shiga uku, dan Allah ka farka, Wannan wani irin sauti ne haka babu daɗin ji, ga Angel bata nan sun tafi tare da Gabriel, Ni dama nasan zai yi wuya mu bar dajin nan da ran mu’ cikin shessheƙar ku ka suke magana hawaye na bin fuskokinsu, Jemimah da azeeza tuni sun rushe da kuka mai sautin gaske, tunkafin ma suga menene ke tunkarosu, sautin kukansu Jemimah shiya ƙara Janyo hankalin Abunda ke nufo su, basu san sune suke Janyo shi ba, babu wanda yai hankalin Ya tsawatar da su akan su daina Yin kukan suyi shiru, ba su yi tunanin yin hakan ba, lokacin da sautin gurnani ya ƙarfafa hatta ganyayyakin dake a wurin Girgixa suke yi, nan take idanuwansu suka tsaya cak akan wurin da suke zargin zai 6ullo, Kamar An Jeho suka faɗo ƙasan wurin, wasu irin Mugayen Halittun namun dawa, masu gashi gashi a jikinsu babu kyan gani gwanin ban ƙyama, Suffarsu tamkar ta majici sai dai sun gurmi maciji a halitta tsaf zasu Iya haɗiye mutun su nannade shi a cikin bakunansu, Tashin hankalin da ba’a sama shi Date, Wata irin gigitacciyar ƙara suka fasa, Ganin Yadda halittun suke Kurɗaɗowa saƙo da lungu masu Yawan gaske gasu manya manya, Gadan gadan suke tunkarosu Harwani nannaɗe Jikinsu suke yi suna harɗewa, tsabar firgi da tsoro ne yasa suka Watsa da gudun gaske kamar zasu Tashi sama, Gudu su ke yi na fitar hayyaci, gudun ceton rai, su kan su basu son Inda zasu dosa ba, wani ƙarin tashin hankalin Halittun da gudu suke binsu, Ga sauri da Allah yai masu, sun fuskanci matsanancin tashin hankali mara misaltuwa, musamman ƙananun cikinsu Azeeza da jemimah duk sun tarwatse kowa Da inda nufa, dan bala’i, Halittun suna lura da kowace kusurwa suka faɗa, Yadda suka raba kawunansu haka suma halittun su ka karkasa kawunansu wurin binsu, Haris da ba ƙoshin lafiya gare shi ba, tuni Numfashin shi ya soma sarƙewa, bakinshi ya soma fitar da jini, Gashi kowa Ya watse sun barshi, Yana ji yana gani halittar nan Ta ta taɗiye ƙafarshi gaba ɗaya ya kife ƙasa, tana gurnani ta wage bakinta masu haƙora a jere babu kyan gani, ta Zurma ƙafafuwanshi.....Innalillah

A 6angaren Azeeza da ke ruƙe da jemimah suna tiƙar gudu, hada tuntu6e sun rasa ina zasu dosa, Jemimah sai kuka take yi tana ambaton sunan Genie, Cikin rashin sanya Wasu muggan ƙayoyi suka Sargaho ƙafafuwansu kusan atare suka rubza ƙasa kansu ya daku.

A 6angaren Batul da parveen da Hannah da suka nufi Hanya ɗaya, Halittun nan sai binsu suke yi, sun rasa ina zasu dosa, suna gudu Sumar kansu Na rufe Masu idanuwansu, ba zato ba tsammani ƙafafuwansu suka zurma a cikin wani rami da ca6ali ya cika shi, gaba ɗaya su ka nutse cikin shi, Ko numfashi basu Iya fitarwa.

Idan muka Koma 6angaren Angel da Gabriel, lokacin da suka ƙaraso bakin wata bishiyar Mangaro sun tsaya suna tunanin hawa saman bishiyar don su tsigo su, atare suka haye suna aikin tsinkar magaro, sai da suka gama ɗibarshi a cikin kwando, Gabriel na yunƙurin zura ƙafarshi Ya sauko ƙasa kwatsam idanuwanshi suka sauka akan kurar dake ƙasan bishiyar tana cin wani namun dawa data kamo, wahalallan yawu ya haɗiya tare da kallon Angel, ita sam bata lura da abunda ya hango ba,
“Gabriel mu sauko mana, Suna jiran mu” Muryarshi Na kakarwa yace”Angel mun shiga uku, wlh kura ce a ƙasa take cin nama,” Sai lokacin ta wurga Idanuwanta ƙasan bishiyar, Gabanta yai mugun bugu, muryarta da tashin hankali ta furta Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Kafin Gabriel ya furta wani abu daga can cikin Dajin ihun muryar Naufal Ta karaɗe kunnuwan su, Kallon Juna su ka yi nan ta ke su ka fahimci babu lafiya a wurin Ƴan uwan su, zufa tuni ta wanke fuskarsu, ganin tana yunƙurin sauka yasa gabriel damƙo hannunta, muryarshi a hargitse yace”Kada ki sauka angel kashe ki za ta yi” Girgiza mashi kai tayi idanuwanta sun rikiɗa jawur dasu tace”ƙwara ta cinye ni, wlh sai naje wurin ƴan uwana, Baka ji ihun naufal ba, Allah kaɗai yasan meke faruwa dasu” kokawa suka soma yi da Gabriel a saman bishiyar, ya hana ta saukowa sai kiciniyar kwace kanta ta ke yi, aiko Suna cikin Yin kokawar nan Gaba ɗayansu suka ƙundumo ƙasa agaban kurar nan, Bakin ta ca6a ca6a da jini, Kafin ta ɗago da ido ta kallesu, Da iya ƙarfinsu na ƙarshe suka yunƙura suka miƙe a guje suka watsa, da gudu itama kurar tabisu tana gurnani, babu wanda bai fita hayyacin shi ba, lokacin da suka faɗo wurin da suka bar su azeeza hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, gabin babu kowa ga kuma Danish a kwance yana ta sharar baccin shi. Kafin Angel tayi yunƙurin zuwa wuri shi kurar nan ta dako uban tsalle ta faɗo masu, Da ƙarfi gabriel Ya fusgi hannunta tana kuka tana ambaton sunan danish Tana miƙa hannu yaja ta da gudu, wani iko na Allah kurar ta tsalle Danish tabisu da gudu, su kawai ta ke hari, kurɗaɗawa suka yi cikin dajin suna gudun famfalaki Kura ta zamar masu masifa ta hanasu sakat.........”

*Boss Bature✍️*

Tun bayan da dr shureim ya fito daga bedroom ɗinshi ya nufi Palour, A zazzaune ya samu Alhaji ubaid tare da Uncle musa zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Layla tana a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, Idon shi na akan Uncle ɗin nashi, Ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda mai ɗaukar ido, ƙamshin turaren shi Ya cika palourn, idanuwanshi suna a lumshe, hannun shi na dama haɗaɗɗiyar agogon diamond ce wadda a ƙalla price ɗinta ya kai 300m, mutunne mai ji da naira, hutu ya zauna mashi ko Alhaji ubaid ba zai nuna mashi tarin dukiya ba, ko a muƙami bai kai shi matsayi ba, Alhaji musa ƙanine ga Alhaji ubaid uwa ɗaya uba ɗaya, kuma shine former president, akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, A kyawun halitta Musa ya zarce Alhaji ubaid, Yana da hasken fata yayin da Alhaji ubaid yake da duhun fata, Sannan yana da Yalwatacciyar sumar kai tasha gyara ga sajen gefe da gefen fuskarshi baƙi wulik, Kamar matashin saurayi. Ya iya ɗaukar wanka ga aji ga kuma ji da kai.
Daga ƙasan carpet dr Shureim ya zauna cikin girmamawa ya gaishe dasu, Alhaji ubaid ne kaɗai ya amsa mashi, kawun nashi kuwa ko arziƙin kallo bai samu ba, har sai da hajiya layla tace mashi”baka ji shureim yana gashe ka ba”? Ba tare daya buɗe idon shi ba yace”Naji,” sanin halin shi yasa Shureim bai damu ba, Layla dai ce ranta ya 6aci dama ita bata iya 6oye fushin ta, Alhaji ubaid ko murmushi ne akan fuskarshi, Har yau mamakin Halin Ƙanin nashi Yake yi.

“Shureim, kasan shi fa mutumin turaine ba haka yake son ka gaishe shi ba, Ka matsa kusa dashi yaji ɗumin ɗanshi a jikin shi” acewar Alhaji ubaid,

Yatsina fuska layla tayi, aranta kuma ji take kamar ta shaƙe wuyan Alhaji musa, jin kanshi na matuƙar ƙona mata rai, miƙewa shureim yai tare da nufar sofa ɗin da musa ya ke a hakimce, ya zauna daga ƙasa,
“Uncle sannu da zuwa, Ya gajiyar tafiya” sai lokacin ya ɗan ware idanuwanshi tare da kallon shureim na tsawon mintuna, sai da ya mula ya sha iska tukunna ya soma magana
“Babu gajiya atare da ni, kai zanyiwa sannu, ni banzo da niyar in ganka ba, banma yi tunanin kana a ƙasar ba, sai da Ya ya ya ke faɗamin, shureim kafi ƙarfin ka tako kazo gidana ne? Laifin hada ni ya shafa kenan”? Tun da ya soma magana, hajiya layla take jifar shi da harara a fakaice batare da ta bari Alhaji ubaid ya gani ba, ita sam baya burgeta, haushin nuna isar da yake yi take ji,
“Ay min afwa Uncle, bani da kwanciyar hankali ne shiyasa bana samun damar zuwa, amma kuna araina,”
Ta6e baki Alhaji musa yai ba tare da ya furta kalma ba

Hajiya layla tace”To ai kaima ɗin baka damu dashi ba, Ba ka neman shi taya zai yi tunanin kana buƙatar ganin shi a gidan ka......” bata ƙarasa maganar ba, da sauri ta dakata ganin irin kallon da Alhaji ubaid ya ke jefa mata, sam baya son tana shiga tsakanin shureim da ƙanin shi, saboda mugun son shi ya ke yi baya son 6acin ranshi.

“Kare shi za ki yi”? Alhaji musa ne yai maganar sautin muryar shi a kausashe, Shiru tayi bata tanka mashi ba,
“Kada ki shiga tsakanin Uba da ɗansa, Kija baki kiyi shiru” Alhaji ubaid ne yai maganar, Ta6e baki tayi tana faman hura hanci.
“Ae da kabarta yaya ta ƙarasa maganarta,” yai maganar fuskarshi ɗauke da murmushi. Kafin ya kawar da idonshi daga kallonta.
Chapter 35 · 0% Book details