← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 152

Sashe 137

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ya mu’allim, mu ƙarasa shiga ciki,” ɗaya daga cikin Sojojin ne yai mashi magana haɗi da nuna mashi kofar shiga babban falon, ɗaga kafarshi yai atsanake yake yin tafiya, suna gab da zasu shiga falon, Prime minister ya fito tare da gimbiya majeedat, Murmushin dake kan fuskokinsu ne ya ƙara faɗaɗa, da sauri hateem Ya mika mashi hannu suka gaisa cikin girmamawa”Marhaban bika babana, barka da sauka, ya gajiyar tafiya” ya fada tare da rungumeshi, bayan sun raba jikinsu daga na juna Sheikh imam yace”ai ni babu gajiya atare dani, ni da aka gatantani kamar wani basarake haka aka daukoni a privet jet, hankali akwance naci na koshi na cika tumbina” Ya fada yana nuna tumbinshi da cazbahar hannunshi, gaba daya suka sanya dariya gwanin ban sha’awa, sheikh imam mutunne mai son barkwanci amma fa sai idan yaso.

Prime minister yace”Akara makallah ai kafi karfin basarake awurinmu, ku fa magadan annabawane, kunfi duk wani mai muƙami a karkashin tafin kafarku Yake”

Murmushi Shekh imam Yasaki, Tare da daura idanuwanshi kan fuskar Gimbiya mujeedat, kafin yayi magana tayi saurin gaishe shi cikin harshen larabci.

Da zolaya yace”Hateem dama ana ganin fuskar matarka? Ya akai yau baka rufe lu’u lu’un ka ba”? Koba ita bace matar nan da ake yi mana 6oyanta ba? Kodai Ƴarce”? Kunyace ta rufe gimbiya mujeedat, Ta sanya hannu ɗaya ta kare fuskarta
Hatta jami’an dake a kewaye da Ya shekh Imam saida suka saki murmushi .

Dariya prime minister yasaki a fakaice ya harari Jami’an dake atsaitsaye suna kallonsu, jiki na 6ari suka juya kowa yakama gabanshi, don sun fahimci me yake nufi, wato suna kalle mashi matarshi.

“Ya sheikh Mu ƙarasa cikin falon, mun barka atsaye gashi ka kwaso gajiya” prime minister ya fada tare da ruƙo hannun shi, Suka nufi babban falon Gidan, Gimbiya mujeedat tana abiye da su.

“Hateem Irin wannan daula haka? Anya kuwa kuna tunawa da mutuwa? Ka ajiye lu’u lu’u agidanka ga kuma kayan alatu ta ko’ina, maimakon ku bari sai mun shiga Aljana muji daɗi” Ya faɗa yana Jijjiga cazbahar hannunshi, Dariya suka sanya gaba dayansu, A saman Royal sofa kowan nan su Ya zauna, suna fuskantar juna da sheikh imam, sai faman jinjina kai yake yi yana bin gidan da kallo, duk maganar da sheikh imam zaiyi yanayin amfani da harshen turanci saboda mujeedat yasan bata jin hausa sai dai turanci da larabci.

“Yanzu kai hateem, Har kake iya kwana acikin daular nan? Wannan haɗuwa haka ai sai mutun ya manta da tur6aya aka halicce shi”
Murmushi suka saki suna dubanshi
Sautin takun takalman Yazrin da Nazli ne Ya janyo hankulansu ga dubansu,
Hannunsu ruƙe cikin na juna suke yin tafiya suna tunkarosu, kowaccensu ta yafa mayafi akanta,
Bayan sun ƙaraso, Cikin girmamawa suka gaishe da shekh Imam, Abunda Ya burgeshi da yaran tarbiyarsu, A saman lallausan carpet din dake a atsakankanin Royal sofa din suka zauna kowaccensu ta nade kafafuwanta
“Masha Allah, Matan hurul aini har a duniya, Hateem, wacce zaka bani acikinsu in cike sunnah”? Ya faɗa yana duban faces din Yazrin da Nazli, Yazrin sai famam sakar mashi murmushi take Yi, Nazli kuwa tunda ta gaishe dashi ta sunnar da kanta ƙasa.
“Duk wadda ka za6a malam, zamu baka Ita” acewar mujeedat,
Shekh imam yace”Uwargida maganarnan taki bata kai zuci ba, ni nasan kin faɗine kawai, taya zaku ba yarinya auran dattijo? Mai jan cazba, balle ƴan matan zamani basu son auran malamai”
Murmushi kowannansu yasaki, banda Nazli.
Biyu daga cikin masu aikin gidanne suka nufo falon, hannunsu ruƙe da faɗaɗan farantai daga sama an jera drinks masu sanyi da snacks.
Tunkafin su karaso sheikh imam yace”waɗannan fa? Badai ni zasu kawo mawa ba? Bayan abincin da naci acikin jirgi har wani ƙari za’ayi min? A’a gaskiya Ni a koshe nake, Ko ruwa bana jin zai Iya wucewa ta makoshi na”
Prime minister yace”babana adai daure ko ruwan ne kasha,”
Gyaɗa kai yai toh, naji iya ruwan zansha, Asaman carpet suka daura farantan, mai aikince ta zuba mashi Apple juice mai sanyi a cup ta miƙa mashi, Yasa hannu ya kar6a, Kur6a uku yai ya dawo da dubanshi gasu Nazli”ƴan matan hateem ina fata na same ku lafiya? Ya karatu? Ko da yake nasan kun kammala, to Ya aiki”
Atare suka amsa mashi da cewa”lafiyalou Alhamdulillah,” jinjina kanshi yai”Masha Allah,” bayan ya ajiye cup din alamar ya kammala sha, Prime minister hateem Yace”nasan yanzu ka kwaso gajiya, ko zamu bari zuwa anjima idan ka huta sai mu fara shiga gida ku gaisa da baba kafin mu wuce can gidan Owais din inda Yaron yake”?
Girgiza kai sheikh imam yai”A’a, tun da mahaifin naku baisan da zuwana ba, to ba yanzu zanje gaishe shi ba, nafi buƙatar ganin yaron, don agaskiya ni babu gajiya atare dani, ka tashi mu tafi kawai,”
Kallon mujeedat Hateem yai”zamu tafi, in sha Allah bazamu daɗe ba, a taya mu da addu’a” murmushi tasakar mashi”ubangiji Allah yasa ayi asa’a, Ina yi maku fatan alkhairi” amsa mata yai da ameen, kafin ya maida dubanshi gasu Nazli da Yazrin”daughters ku tayamu da addu’a, ga mommynku nan zatayi maku bayanin komai dangane da zuwa sheikh imam” amsa mashi sukayi datoh, kafin ya ɗago Ya kalli Ya sheik wanda tuni Ya miƙe tsaye, miƙewa hateem yai atare suka nufi kofar fita falon, tunkafin su ƙarasa Jami’en dake atsaye bakin motar data dauko sheikh daga Airport Yai saurin bude masu motar, Bayan sun shiga daga ciki, jami’en Ya zauna a driver’s seat Ya tashi motar, atsanake Yake yin driving dinsu........

*Chief Owais✊❤*

Tun bayan daya dawo daga masallaci, Yin sallar asuba bacci ya addabi idanuwanshi, adaddafe ya shiga bathroom yai wanka, within minutes ya fito waist dinshi ɗaure da white towel, kan mirror chair ya zauna da niyar ya kimtsa kanshi, sai dai yakasa tabuka komai saboda kasalar data kame sassan jikin shi, idan har ba baccin nan yai ba to kuwa bazai ta6a samun sukuni ba, kyawawan idanuwanshi sunyi mashi nauyi daƙyar yake iya buɗe su, miƙewa yai bai nufi ko’ina ba sai saman katafaren gadonshi, Ya haye ya kwanta tare da jan bargo ya lullu6e rabin jikinsa, In a short time bacci yai awon gaba da shi.

Tsawon awanni yanata sharar baccinsa, tun karfe shida har goma da rabi ta buga, Yayin da numfashinshi ke fita cikin natsuwa da kwanciyar hankali, phone dinsa dake ajiye gaban dressing mirror ta soma yin ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, ringin din ya fara takura mashi, mutsu mutsun farkawa daga bacci ya somayi, A hankali Ya ware fararen idanuwanshi dake fuskantar ceillin din dakin nashi
Tsawon minutes, kafin Ya laluba hannunshi Cikin kasala Ya ruƙo wayar ya duba sunan me kiranshi, sunan Uncle Hateem ne Ya bayyana akan screen din wayar,
Kiran harya kusa katsewa yai saurin yin picking, tare da manna wayar akan kunnansa
“My son, Ina fata ban takura maka ba”
Yamutsa fuskarshi yadan kafin ya furta”Barka da safiya uncle, fatan ka tashi lafiya”?
“Lafiyalou, naji muryarka da alamun bacci bai isheka ba”
“Kiran wayarka ne Ya tashi ni daga bacci, Ina fata lafiya”
“Banji dadiba amma kayi hakuri da takura makan da nayi, ni kaina bansan dililin dayasa na damu da yaron ba”
“Ba damuwa uncle”
“Yanzu haka da nakeyi maka magana Muna akan hanyar zuwa Gidan naka tare da sheikh imam”
Lumshe ido owais yai har cikin ranshi yaji dadin jin zuwan Sheikh imam
“Ina yi mashi barka da zuwa, Allah ya kawo ku lafiya” Hateem Ya amsa mashi da amen mun gode son,” daga haka sukayi sallama da juna.
Daura wayar yai saman side drawer ya sauko daga saman gadon Ya nufi dressing room din dakin shi, badajimawa ba ya fito sanye da jallabiya launin sky blue, tayi bala’en yi mashi kyau, Gaban dressing mirror din dakin ya tsaya tare dakai hannu cikin jerin turarurrukansa ɗaya bayan ɗaya yake dauka yana feshe jikinshi, tuni ƙamshinshi ya karaɗe dakin.
Diamond wrist watch din shi dake ajiye gaban mirror ya dauko Ya zura a hannunsa, Kafin Ya miƙa hannu Ya dauki Phone dinsa, A tsanake Yake pressing dinta, Layin Boss Ya danna ma Kira, Bugu Uku Yai picking, gaisawa suka farayi kafin Ya furta”Sheikh Imam Ya ƙaraso, Ina buƙatar ganin kowannanku a main falo, domin mu tarbesa”

Boss Ya amsa mashi da Toh, In sha Allah, Yanzu zan sanar da su” daga haka Yai rejecting kiran.

A dai dai lokacin, Unaisah ta kuma farkawa daga baccin da yayi awon gaba dasu ita da giant snake din, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon gadon, ta kudundune shi da bargo, ta ƙagu da son ganin ƴan uwanta shiyasa zata fita taje gare su, batasan a wani hali suka kwana ba.
Bayan ta fito daga dakin down ta sauko, Moving quickly ta nufi Hanyar da zata hau bene taje dakin ummi, Har ta kusa haurawa saman staircases miryar boss man ta katse ta”Unaisah”! Cak ta tsaya haɗi da waiwayowa tana dubanshi,
“Ina zakije ne”?
Muryarta adisashe ta furta”dakin aunty ummi, Inason ganinsu batul ne, ai ka fadamin acan suka kwana”
“Hakane, Nima dakinta zani je, amma tunda gaki bari in baki sako ki kai mata” ya fada tare da zura hannu cikin aljihu ya curo maganin mura ya miƙa mata.

“Wanene bai da lafiya”? Hankalinta atashe ta fada tana bin maganin da kallo.

“Ummi ce ke bata jin dadi, mura ce ta kamata” Ajiyar zuciya Angel ta sauke tayi tunanin ko cikin ƴan uwanta wani ke bai da lafiya.

Kar6ar maganin tayi, har zata juya muryarshi ta dakatar da ita”Sheikh imam yana akan hanyar zuwa gidan nan, malamin da zai duba ɗan uwanku danish” Waro ido waje tayi lokaci ɗaya ta fashe da dariyar farin ciki, Murmushi yasaki Dama ya fada matane don ya faranta mata rai.
Idanuwanta cike tab da ƙwalla take fadin”Alhamdulillah, wayyo Allah wallahi naji dadi, fatana Allah yasa ayi asa’a danish ɗina yaji sauƙi ya dawo kamar kowa”

Boss yace”in sha Allah zamuyi nasara, yanzu kije ki kai mata maganin, idan kin fito ki same mu a falo,
Amsa mashi tayi da toh, jiki na rawa ta nufi benan ta haye sama, burinta takai mata maganin sannan ta kwantar masu azeeza hankalinsu kafin ta dawo falon don taga sheikh imam”
Chapter 137 · 0% Book details