Sashe 139
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
La66an Sajeed na kerma ya furta”kina nufin Danish Giant ne’? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, dafe kai haris yai da hannu ɗaya da wata irin karyayyar murya ya furta”inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un! Mun shiga uku! Wai su waɗannan azzulaman mutanan wani zunubi muka aikata masu ne? Da suke azabtar da rayuwarmu? Meyasa suka cutar da rayuwar Danish? Me bawan Allahn nan yayi masu”? Idanuwanshi tuni sun kaɗa sunyi jawur da su
“Ni dama nasani bazasu ta6a ƙyale mu ba, zasuyi amfani da danish ne donsu maida mu kurkukun ƙaddara”!
Cikin sanyin murya Batool tace”bawan Allah danish, shine abun tausayi, wallahi ina jin baƙin ciki da takaicin azabtar mana da rayuwar ɗan uwanmu da suke Yi, danish tun yana ƙarami suke juya shi, sun hana rayuwarshi sakat, narasa gane dalilin dayasa suke yi mashi haka, Ya Allah ga bawanka nan kai kadai kasan a wani hali yake aciki, Ya Allah Ka fitar dashi, ka kawo mashi ɗauki acikin rayuwarshi’, tuni hawaye sun wanke fuskar Batool.
Cikin shesshekar kuka Azeeza tace”Allah ya isa ba zamu ta6a yafe masu ba, Mugaye azzalumai ƴan wuta, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara danasanin cin zalunmu da su ka yi da kuma ƙuntata rayuwar ɗan uwanmu da suke Yi”
Azeeza na rufe baki, Naufal da takaici ya ishe shi, cikin jin ƙunar rai Ya soma magana”wannan wace irin rayuwace? ya zamuyi da ranmu? Ni yanzu na fahimci KURKUKUN ƘADDARA RAYUWARMU CE!! mune kurkukun ƙaddara saboda duk inda zamu kasance gidan kurkukun ƙaddara yana atare damu, Meyasa!!!”? Ya jefa tambayar idanuwanshi akan fuskar Unaisah, wadda tayi shiru tana sauraronsu, tabbas maganar Naufal abun dubawace, Yanzu ta fara zargin wani abu.
“Naufal, kamar yadda ka faɗi nima haka nake tunani, rayuwarmu itace gidan kurkukun ƙaddara, amma meyasa zai kasance haka? Su wanene suka sadaukar da mu?....” ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta.
Sajeed yace”yakamata mu fallasa asirin komai ke faruwa agidan kurkukun ƙaddara ga mutanan da suka taimaki rayuwarmu ina da tabbacin zasu taimaka mana don ganin an gano su wanene munafukan dake sadaukar damu ta hakanne zamu tabbatar da zarginmu”
Javed yace’nima ina goyan bayanka Sajeed! Mu tona masu asiri kawai, idan da rabon mu rayu zamu rayune duk runtsi duk wuya, kai koda ace zamu mutu ne bayan mun tona masu asiri wallahi munci galaba akansu, tunda har muka yi nasarar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, wanda ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners da suka gudu suka tsira ba sai akanmu”!
A hankali unaisah take binsu da kallo, ta fahimci ransu yakai maƙura wurin 6aci, Jininsu akan akaifarsu yake, kowannansu atsorace yake da abunda ke faruwa da danish.
Fashewa da kuka jemimah tayi haɗi da ɗaura hannayenta biyu saman kanta tana fadin”Wayyo Allahn mu mun shiga uku, Yanzu shikenan danish din mu ya zama dodon kurkuku zai ɗauke mu ya maida mu can mu cigaba da cin ganye” fuskarta sharkaf da hawaye, ruko hannunta Unaisah tayi acikin nata”Ya isa haka, Ki daina kuka, kanki zai Iya yin ciwo,” girgiza kai ta dinga yi tana fadin”genie ba zaki gane ba, wallahi banason komawa kurkukun nan, haushinsu nake ji, Allah zuciyata zata Iya bugawa in mutu kowa ya huta”
Gaba ɗaya idanuwansu na akan fuskar jemimah, ta haƙiƙance tana yin magana shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta.
“Sun kashe mun majnoon dina, sun kashe mana Unaizah, Yanzu kuma mu suke son kashewa fa” ta ƙare maganar tana faman jan majina’
Kwanto da kanta Angel tayi saman cinyoyinta, ta ɗaura hannunta kan sumarta cikin sigar lallashi take yi mata magana”in sha Allah bazamu ta6a komawa gidan kurkukun ƙaddara ba, Har bada, munbarshi kenan bi’iznillahi mune zamu kawo karshen kurkukun da fasiƙan Shuwagabannin su, zamu tarwatsa baƙin tarihin da suka kafa, zamu shafe babinsu a doron duniyar nan, zasu ɗanɗanin kuɗarsu har sai sunji inama ace ba’a halitto su a duniyar nan ba, wannan Alƙawarine!” da ƙwarin gwiwa unaisah ta ƙare maganar.
Shiru jemimah tayi tuni ta haɗiye kukanta, Jikin kowannansu yai sanyi, maganganun da suke yi yai silar fama masu tabon dake acikin zuciyoyinsu.
Daƙyar Hanna ta Iya buɗe baki tace”ni yanzu damuwata a wani hali danish yake aciki”? Tayi tambayar idanuwanta cike tab da ƙwalla
Angel ce ta bata amsa da cewa”har yanzu bai dawo mutun ba, amma ɗazu boss man ya fada min cewa malamin da zai duba jikinshi ya ƙaraso Ina da tabbacin Yana acikin gidan nan, shiyasa Big guy Yace mu zauna a ɗaki bayason ganin gifcinmu, yakamata mu tayashi da addu’a, ita yake buƙata daga gare mu” tunkan ta rufe baki, sukayi saurin daga hannayensu sama, Itama ta ɗaga nata,
“Jemimah ki tashi muyi ma ɗan uwanmu addu’a” Unaisa ce tayi mata magana, daƙyar ta ɗago da kanta haɗi da ɗaga hannayenta sama kamar yadda sukayi
Addu’o’i unaisah ta soma karantowa suna amsa mata da ameen ameen, bayan ta kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, kafin su zame hannayensu, kunnuwansu suka soma jiyo masu motsin buɗe ƙofar dakinsu, A hanzarce suka ɗago suna kallonsu.
Big guy ne ya shigo hannun shi ruƙe da faffaɗan tray Na kayan breakfast dinsu, Daga Bayanshi Ummin america ce, Ta ɗauki wankan turkish gown launin brown anyi mata adon stones launin yellow, mayafin da tayi rolling kala ɗaya ne da stones din rigar, ta sanya high heels a ƙafarta, daga sama rigar ta matseta ta bayyana surar kirjinta, daga bayan rigar tudun mazaunanta ya fito sosai.
Tunda batool taji ƙamshin turaren ummin america hankalinta ya tashi, tasan dole ta hukuntata akan fitowar da tayi daga ɗaki batare da saninta ba.
A tsakiyarsu big guy ya ɗaura tray din kayan abincin kafin Ya soma yin magana.
“Ga auntynku nan Ummi, zata zauna atare daku don ta ɗebe maku kewa, idan kuna buƙatar wani abu, ita zaku faɗa mawa” amsa mashi sukayi da toh.
Big guy ya maida dubanshi ga ummi dake atsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya, Hadaddiyar agogon hannunta sai ƙyalli take yi.
“Ummi, ki kula da su, bana so asamu matsala, malamin ne ya buƙaci a tattara sauran yaran wuri ɗaya sannan aja hankalinsu gudun kada suji sautin abunda zai rikitar da su”
Lumshe mashi ido tayi, alamar taji mai yace, shi kanshi daurewa yake yi, domin kuwa wankan da ummi ta ɗauka yaja hankalinshi, musamman shu’umin ƙamshin humran dake fita a jikinta.
Muryarta da kwarkwasa tace”okey, baka da damuwa”
Bayan fitar big guy daga ɗakin.
Ummi ta kalli su unaisah, atare suka haɗa baki wurin gaishe da ita.
“Ina kwana aunty ummi” yamutsa fuskarta tayi”lafiyalou, Ina batool”? Ta jefa masu tambayar tana kallonsu, kafin su bata amsa idanuwanta suka sauka akan yatsun hannun batul, ta 6oye kanta abayan haris, duk don kada ummi ta ganta.
Babu wanda ya fahimci wani abu, sai ita data san meya haɗasu.
“Kunyarki take ji Aunty ummi, shiyasa ta la6e” acewar Unaisah.
Ta6e baki ummi tayi kafin tace”Ina maganin muran da boss man Ya baki”? Ta fada tana nuna unaisah da hannu.
sai lokacin ta tuna da maganin batasan tun yaushe ta jefar dashi ba.
“Kin yada kenan”? Girgiza kai tayi a’a, Yana a hannuna tun ɗazu, namantane ban kaiga bata ba”
Juyawa baya ummi tayi tana kallon tsakar dakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Blister pack din dake ajiye ƙasa, cikin takun Isa Ta nufi floor din ta zuƙunna ta ɗauki maganin”ajiyar zuciya unaisah ta sauke ganin ta gano shi’
“Ku matsa min anan zan zauna muyi breakfast,” ta faɗa tana nuna tsakankanin Batool da Haris, da sauri Ya matsa mata, taje ta zauna idonta akan batool data ƙanƙame haris, ruƙo hannunta ummi tayi tare da rabata daga jikin haris, duk tabi ta ruɗe, taƙi yadda su haɗa ido.
Bottle water Unaisah ta ɗauka ta buɗe murfin, ta tsiyaya ruwa acikin cup, ta miƙa ma ummi, kar6a tayi tare da fadin”thanks” kafin ta curo maganin ƙwaya biyu ta miƙa ma batul, yatsun hannunta na kerma ta kar6a ta sanya abaki, ta kar6i cup din hannun ummi ta kur6i ruwan ta haɗiye maganin, Bayan ta gama ta ajiye cup.
“Bata da lafiya ne”? Sajeed ne ya tambaya, parveen tace”Mura take Yi,”
“Shiyasa naji muryarta ashaƙe, sis Allah ya baki lafiya” amsa mashi da tayi da ameen, sauran mazan sukayi mata sannu ta amsa masu.
Kafin ummi ta fara serving dinsu, A plates ta zuba ma kowannansu abinci banda batool, ɗaya bayan ɗaya ta miƙa masu, suka kar6a suna ci, kallon Batul tayi”atare zamu ci” ta faɗa tana sakar mata shu’umin murmushi afakaice batare da su Unaisah sun gani ba.
A plate ɗaya ta zuba masu farfesun naman kaza, Yaji kayan kamshi ga uban romo.
Daƙyar batool take iya shan farfesun, saboda Ummi ta hanata sakat, da zarar ta ɗago sai ta haɗa ido da ita, ta rasa gane dalilin dayasa ummi take son takura rayuwarta.
Hankalin Unaisah ba akansu yake ba, saboda damuwar data bijiro mata, ta ƙosa taji me ke wakana da Danish, Malamin Ya fara Yi mashi aiki ko kuwa.......?
Shin meya faru bayan zuwan Sheikh Imam malik!?
Bayan ƙarasowar motarsu akatafaren Gate din shiga gidan Owais Jami’in dake driving dinsu yayi parking a agaban entry hall, Ya fito a hanzarce Ya zagaya ya buɗe masu murfin motar, A hankali Prime minister hateem ya fito daga Ciki, Kafin Sheikh Imam Ya zuro ƙafarshi waje shima Ya fito Yana ƙarema ginin gidan kallo, ya yaba da haɗuwar daular Owais, har saida ya furta masha Allah.
Kafin su ƙarasa falon, Glass door dinsa ta buɗe, Chief Owais Ne Ya bayyana gefe da gefenshi, Boss man ne tare da Big guy, da kuma sauran jami’an isod da suka hallara domin tarbarsu.
Murmushi prime minister hateem yasakar mashi, tare da nufarshi tunkan ya isa gare shi, Chief owais Ya riga shi zuwa Ya haɗa hannayenshi biyu yai hugging din uncle din nasa”
Kafin Ya ɗago Ya nufi Sheikh Imam Ya rungume shi, fuskar kowannansu ɗauke da murmushi.