← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 152

Sashe 63

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yamutsa fuskarshi Yai, Kafin Yai yunƙurin ƙara furta wata kalma, tayi saurin zame wuyan rigar jikinta, Ba ƙaramin shammatarshi tayi ba, gaba ɗaya ya rasa sukuni, Baisan ya akai ba ya tsinci kanshi asaman gado sun tsunduma suna Korar shaiɗanu, Suturar jikinsu A saman floor na tsince su bansan ina zan kaisu ba, Laundry ko toilet? (🤣 wato duk izzar namiji sai in bai haɗu da mace ba)

Tuni Dr shureim Ya kammala shiryawa, Ya canza suturar jikinshi, still Arab dress ne, kayanshi na gado, Yana daga zaune gefen gadon shi, Hannun shi ruƙe da Wayarshi Yana kallon hoton abar ƙaunarsa da ya buɗo a gallery.

Ba zato ba tsammani Yaji Muryar matashin saurayi Yana Kwaɗa sallama daga bakin ƙofar ɗakinsa, slowly ya ɗago da ido yaɗan Juya yana kallon Saurayin dake sanye cikin black suit, dogo kuma faffaɗa, Hannun shi ruƙe da Ƙatuwar shopping back mai ɗauke da sunan *Obinna tech*

A sukwane Dr shureim ya ɗaura wayarsa saman mattress Ya yunƙura ya miƙe Still idonshi akan mutumin.

“Dr shureim Barka da warhaka”
Muryarshi babu natsuwa ya furta”yawwa barka dai” duk yasha jinin jikinshi saboda mutumin babu fara’a akan fuskarshi kamar wanda aka ɗaurawa aure da mutuwa.

“Saƙo ne daga Uncle ɗinka” nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tunawa da saƙon da uncle musa Yace za’a kawo mashi.

A hanzarce ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, Ya miƙa hannu biyu ya kar6i kayan daga hannun mutumin haɗi da yi mashi godiya.

Fuskar shurem ɗauke da murmushi ya nufo cikin ɗakin, A saman gado Ya ɗaura shopping back ɗin, Bayan yayi bismilla, Ya buɗe ta tare da zura hannu Ya zaro kayan dake aciki, har saida gabanshi Ya ɗan faɗi.

Apple laptop ce, tare da Apple watch, abu na ƙarshe da ya gani Unexpected Danƙareran Key ɗin Mota, Zubewa yai saman gwiwowinsa agaban Kayan Yana duban su, A tsanake Ya ke ƙare masu kallo, haƙiƙa Yayi farin Cikin Kyautar nan da uncle musa yai mashi ya ji daɗi sosai, ɗaga Hannayenshi sama Yai, Ya soma jera addu’o’i Yana yiwa kawunsa bisa irin farin cikin daya Sanya shi ayau, Ya faranta mashi sosai.

Bai gama shan mamakin Kayan ba, Muryar mutumin da ya kawo Kayan ta katse mashi addu’o’in da ya ke yi.

“Dr shureim Zan iya shigowa Ci ki?
Da sauri Ya miƙe tsaye Yana kallon shi.

Manyan Akwatuna ne guda Biyu a hannun shi ya ruƙe handle ɗinsu Yana Jansu irin masu tayoyin nan.

“Bismillah” yai mashi nuni daya shigo Ciki, Bayan ya shiga Cikin ɗakin agaban tafkekiyar Glass wardrobe ɗin ɗakin mai faɗi Ta mamaye bangon da take a jikinsa, Anan mutumin Ya dakata da yin tafiya ya buɗe akwatunan, Farin Ciki Ya hana dr. shureim Rufe bakinsa.

Arab dress ne kala kala Na maza, Kalar waɗanda Yafi so, A ƙalla sunkai kala Hamsin sababbi fitigil dasu shaƙe cikin akwatin, Hada Arab turban ɗin da Yake naɗawa akanshi.

Atare da mutumin suka soma jera kayan acikin wardrobe ɗinsa, Bayan sun kammala jera kayan, Man ɗin Ya buɗe ɗayan akwatin Wa’iya zubilla Uncle musa Ya gwangwaje ɗan nasa da Haɗaɗɗun leather shoes da tsadaddun turarurruka Na Larabawa, Da suran Kayayyakin amfani na gyaran Jiki, a gaban mirror suka jera Kayan, Bayan mutumin Ya kammala, Dr. shureim yai mashi godiya suka Yi sallama da shi.

Yana atsaye idonshi akan sabbin Kayanshi sai binsu ya ke yi da kallo, daɗi kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna.

Muryar Tani ce Ta janyo hankalin shi ga dubanta.

A yayin da ta ke shigowa ɗakin nashi

“Dr shureim barka da rana, Fatan Ka wuni Lafiya? Ya kwanan gidan uncle ɗin naka”

Hannunta biyu ruƙe da Faffaɗan wooden tray, daga saman shi jerin lunch ɗinsa ne.

Da fara’a akan face dinsa Ya soma Amsa mata gaisuwar”Alhamdulillah, Fatan kema Kina Lafiya ya aiki”?

“Lafiyalou, ai Munji daɗin zuwanka gidan nan, Ko ba komai zaka ɗebe ma Zeenatu kewa, Baiwar Allah jiya tayi murnar zuwanka, Tana matuƙar son yayanta” Fuskarta awashe Ta yi maganar, adai dai takai gaban table ta ɗaura mashi tray ɗin.

Murmushin gefen fuska Yasaki tare da faɗin”Allah sarki, Tun Jiya bata ƙara dawowa ɗakina ba, Idan ba damuwa ki kira min ita idan kin fita, nasan saboda Kunyar abunda Ya faru Jiya ne Yasa ta kasa zuwa gaishe ni da safe”

“Wlh kamar ka sani, abunda ya hanata zuwa kenan, ai zeenatu akwai kunya, Yarinyar kuma tana da mutunci ga kamun kai, Ga ilmi, ita dai taji daɗin rayuwarta, Gaskiya ba ƙaramin mai sa’a bane zai mallaki Zeenatu” tun da Tani ta fara Yi mashi sambatun Kyawawan halayar zeenatu Ya natsu Yana sauraranta haɗi da kallonta, Ya fahimci so ta ke Yi, Ta yi mata gyaran hanya awurin shi. Dama tun Jiya da yazo matar take ta yi mashi sambatu akan zeenatu.

“Idan badamuwa, inason Ganinta” washe baki Tani ta yi”Toh, yanzun nan zaka ganta,” Da sauri Ta juya ta fuce daga ɗakin.

Tattara Kayan saman gadonshi yai, acikin Shopping bag ɗin Ya tura su.

Ajiyar zuciya ya sauke Ya koma gefen gadon shi ya zauna yana jiran ƙarasowar Zeenatu.

Akan Hanya Tani taci karo da zeenatu tana tafiya kamar munafuka, sam babu natsuwa atattare da ita, sai ƴan waige waige take Yi, har sai da suka bangaji juna da Tani tukunna ta zabura ta kalleta suka haɗa ido

“Ina kika shiga ne?”

“Ɗakin daddy” ta bata amsa
“Hawayen menene akan fuskarki! Waya ta6amin ke” zumbura mata Baki Ta yi ba tare da ta bata amsa ba.

Ruƙo hannunta Tani tayi”Muje ɗaki ki gyara fuskarki, dr shureim ne yace in kira mashi ke” waro ido waje tayi jin ance Yaya shureim ke kiranta.

Jiki na rawa Tabi Tani suka nufi falo abakin stairs suka hau elevator takai su Second floor, Bayan sun fito da sauri suka nufi ɗakin zeenatu, sai da Tani ta jira tayo wanka tukunna ta taimaka mata wurin canza Kayan jikinta, Pakistan ta sanya riga launin blush pink har gwiwa, Tare da burgujejan wando Fari anyi mashi adon stones, Tani ta ɗaura mata Mayafi akanta, Babu makeup Iya kyawun fuskarta ne.

Flat shoes Ta zura a ƙafarta, Atare da Tani suka baro ɗakin Bayan sun sauko down, sai da Tani taja mata kunne akan ta natsu kada Tayi mashi hauka, ta amsa mata da toh.

A hankali take Yin tafiya tana nufar sashen room ɗinsa, a bakin ƙofar ɗakinshi ta la6e tana leƙensa Yana zaune idonshi akan screen ɗin wayarshi, Ya natsu Yana kallo ko motsi bai yi, Kunyace ta kama ta, muryarta
Ƙasa ƙasa take ambaton sunanshi”yayana rabin raina” shiru dr a
Shureim bai amsa mata ba

“Hubbyna” still shiru, da alama bai ji sautin muryarta ba.

Tunani ta soma yi ko menene ya ke kallon acikin wayarshi wanda yai silar ɗauke hankalinshi! Ras taji gabanta Ya faɗi sakamakon amsar da zuciyarta ta bata na cewa wata’ƙil hoton girl friend dinshi yake kallo.

Cikin sanɗa ta ke yin tafiya cikin ɗakin nashi duk don ta gano abunda Yake kallo, daga 6angare hannun dama na gadonshi ta zagaya tana yi mashi dogon wuya, ƙamshin turarenta ne Ya tona mata asiri, lumshe idonshi yai yana tunanin a ina aka samu fragrance me daɗin shaƙa a ɗakinsa, ɗagowar da zai yi keda wuya idonshi ya sauka akan zeenatu dake leƙan wayarshi, da sauri ya danna power button hasken phone ɗin ya ɗauke screen yai duhu.

Duƙar da kanta ƙasa ta yi, yanayin fuskarta ya canza”yaya shureim ɗina, ka wuni lafiya? Am sorry Jiya ban dawo mun gaisa ba” A hankali Ya miƙe ya zagayo ta Inda take atsaye dab da ita ya tsaya yana ƙare mata kallo.

Baisan ya akai ya tsinci kanshi da kallon wankan pakistan ɗin da ta ɗauka ajikin ta, ta yi bala’en yi mashi kyau, Yarinyar kamar Fure haka take da ɗaukar ido.

Tabbas Idan yaci gaba da kallonta zai shagala ne

Acikin zuciyarsa Ya ambaci

“A’uzubillahi minasshaiɗanirrajim”

A fili kuma Yace”Zeenatu, kada ki damu bakomai, ay nayi maki uziri kece kika takura kanki”

Muryarta da shagwa6a tace “Mommy ne tace inzo muci abinci atare, tun Jiya dana bar ɗakinka banci komai ba” Ya rasa gane wani irin yanayi yake ji atare dashi, tana yin magana blue eye balls ɗinta na jujjuyawa, Yatsun hannunta sai kerma sukeyi saboda rashi natsuwarta.

Abu mafi jan hankali a jikinta ƙirjinta kamar zasu tsonewa mutun ido
“Ki jirani awaje”! Abunda Ya furta mata kenan
“Yaya shureim ba abinci zamuci atare ba”?
“Eh, amma ba’a cikin ɗakina ba, kinsan babu kyau mace da namiji su ke6e a ɗaki ko”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh

“Bari na ɗauko mana kayan abincin sai mu koma dining room” tuna abunda ya faru Jiyane yasa shi yin saurin cewa”No! Ni zan ɗauka,” amsa mashi tayi toh” Ya zagaya other side ya ɗauko tray din Kayan abincin da hannu biyu ya ruƙo shi, yana agaba tana bayanshi, a Haka suka ƙarasa cikin Haɗaɗɗen ɗakin Cin abincin gidan, Dining tables har kala Uku, Kowanne a kewaye da chairs, a saman table Ya ɗaura masu tray ɗin, suka zaune suna fuskantar juna, Hankalin shi ba ƙaramin kwanciya yai ba, A inda suke Masu aiki Na iya hangensu daga main palour.

Sai faman sakar mashi murmushi take Yi

“Yaya shureim, zamu dinga fita yawo atare ko? Kaga kullum ina agida daddy baya barina zuwa yawo, tun da na kammala secondry school kullum Ina agida” ta ƙarasa maganar tare dakai hannu ta ɗauki serving spoon ta buɗe warmer ta Fried rice ta zuba masu a plate Biyu, ta sanya masu spoons aciki.

Suna ci suna Yin fira ga lemunsu me sanyi a glass.

“Kada Ki damu, Munyi magana da daddynki, Yace yanason ina taimaka maki da wasu abubuwan”

Washe baki Tayi”yaya shureim zamu fara fita shan ice cream da zuwa cinema? And shopping ko”? Ɗaga mata gira yai alamar eh, cizon pink lips dinta tayi”Yaya shureim Amma ka ta6a yin soyayya”? Ƙiris ya rage ya shake saboda surutun zeenatu, girgiza mata kai yai”ban ta6a ba ke fa”?
“Maza dayawa suna haukan sona, Ni kuma nafison auran miskilin namiji, mai ilmin addini dana zamani kuma Yana amfani da su, sannan me Koyi da sunnar Annabi Muhammad SAW”
Chapter 63 · 0% Book details