Sashe 13
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
“Salsabeel ko bayan ba raina inason yaran nan su ku6uta daga KURKUKUN ƘADDARA! Ka yi min alƙawarin nan, ka taimaka masu ko dan su isar da saƙon mu zuwa ga mutanan duniya, Bana so acigaba da aikata zalunci agidan kurkukun nan Ina mai jin takaici da baƙin Cikin ganin yadda ake tauye wa ƙananun yara haƙƙinsu na rayuwa, basu ji ba basu gani ba, An hana su more rayuwar su ta duniya, Ana kashe masu rayuwa a lalatasu A ƙasƙantar dasu kamar dabbo bi, sannan a kashe su, kuma su mutu a wulaƙance! Ka faɗa min Laifin me suka aikata da su ka cancanci Yin irin wannan rayuwar? Idan har kana so In yi alfahari da kai a matsayin ka na Jini na to ka cika min burina, Bana so Ganin mutuwa ta yasa zuciyarka ta raunata nafi so a lokacin da ka yi tozali da gawata ka ƙara Jin ƙwarin gwiwar aiwatar da umarnin da na baka, idan mutuwa ta risƙe ni a gidan kurkukun nan bana so kabar gangar jikina a gidan kurkukun ƙaddara Ka yi nesa dani kafin ka binne ni.........” lokacin da tsohuwa Tamira ta yi mashi maganar sosai ya fashe mata da kuka yana faɗin zai yi duk abunda take so amma tadaina maganar zata mutu, ya ta ke so ya yi da rayuwar shi? Bashi da kowa a duniyar nan bayan ita, murmushi ta yi tare da ce mashi Kana da Allah sannan bayan shi ga ƴan uwanka nan suma basu da gatan daya wuce Allah da kuma kai, Don haka ka daina tunanin cewa sai da ni zaka Iya aiwatar da komai. Ni dai fatana Ku tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, Azzaluman shuwagabannin da suka ƙirƙire shi ku tabbatar tun agidan duniya sun ɗanɗani kuɗarsu kafin su koma ga mahaliccin su bana so kubar hukuma ta hukunta su saboda duniyar nan acike take da marasa gaskiya idan kunga ba zasu baku goyan baya ba ku yi amfani da ƙarfin ikon da ku ke dashi wurin yi masu mummunan kisan da sai sun yi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan, Kafin su mutu ku Azabtar dasu ta yadda zasu manta da duk wani jin daɗi da su ka yi a duniya, Idan har ku ka yi min hakan to zan jin daɗi, zan yi kuma alfahari da ku, Bayan ta yi mashi wannan maganar salsabeel yana kuka ya roƙe ta alfarma ɗaya kafin faruwar duk waɗannan abubuwan yace mata yana so ta kar6i musulunci akaro na biyu ta yi imani da Allah, Numfasawa tayi tare da ce mashi”Ba zai yiwu ba saboda Allah ba zai ta6a kar6ar tubanta ba ko da ta musulunci saboda ɗumbin zunubban da ta aikata sun yi muni sosai, Salsabeel ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita ta hanyar Yi mata nasiha ya nuna mata cewa shi Allah gafurirrahim ne yana son bayinsa waɗanda su ka aikata zunubi suka gane kuskuran su kuma su ka tuba zuwa gare shi, daƙyar ya samu tsohuwa Tamira ta sake kar6ar shahada maganarsu ta ƙarshe data furta mashi”Zan je wurin Yaran can inaji araina wani abu yana faru a ɗakin su, Kafin na isa wurin su inaso ka yi gaggawar zuwa Ɗakin Madubin sihiri Ka canza ganin su ta yadda ba zasu fahimci abunda ke faruwa ba......wannan itace magana ta ƙarshe da tsohuwa tamira ta furta mashi kafin tabar wurin shi, akan hanyar shi ta zuwa ɗakin madubin sihiri Ya ga duk wani abu da ya faru da Angel kun ji yadda akai har yaje gare ta.
Cakumar Batul ya yi da hannun shi tare da janyota ta dawo saman faffaɗan ƙirjin shi, Rungumeta yayi da hannayenshi tamkar zai mayar da ita cikinshi, Hakan da yayi mata ne yasa ta sassauta kukan nata......
Tsoro da fargaban abunda idanuwansu zasu nuna masu ya hana su shiga Cikin ɗakin, Bayin Allah suna atsaitsaye Bakin ƙofar suna sauraron gunjin kukan da Batul ta ke yi.
Idan mu ka koma 6angaren Angel kuwa tun bayan tafiyar Salsabeel tana zaune cikin matsanancin tashin hankali, Da fargaban farfaɗowar Danish, Ba zato ba tsammani ta ga yatsun ƙafarshi na motsi, A gigice ta yunkura da niyar ta miƙe Sai dai kash ƙafarta ta ƙi bata haɗin kai, Wani irin tsami ta yi mata, a tsananin tsoroce take ja da baya tana kallon shi jikinta nata 6ari
A hankali Ya ware kyawawan idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin na tsawon daƙiƙa talatin kafin Ya yunƙura ya miƙe zaune.... Ta wutsiyar idon shi ya ke hango kamar mutun na motsi, hakan yasa shi yin saurin kai idon shi gare ta, unexpected idanuwan shi su ka sauka acikin nata, da wani irin kallo ya ke bin ta da shi, gani ta ke yi kamar bai dawo hayyacin shi ba.
Ya kasa tantance wacece ita? Saboda daskararren jinin da ke a jikinta, ta koma mashi kamar aljanna, ranta ne ya bata cewar ko dai ya dawo hayyacin shi? Wata’ƙil saboda munin da ta yi ne yasa bai gane ta ba, Cikin jin shakkar shi muryarta na kerma ta ambaci sunan shi”Da..nish..its me ur Angel” Ware fareren idanuwan shi yai sosai akan fuskarta, jin muryar da ya daɗe yana mararinta, ba zai ta6a mantawa da muryarta ba, A ruɗe ya motsa la66ansa tare da furta sunanta”Angel? Is that you”? Ita kanta batasan ya akai ta iya miƙewa ba, Tsabar farin Ciki da gudu ta nufe shi tana ƙarasawa gaban shi slowly ta zube saman gwiwowinta tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi sosai ta rungume shi tana ku ka, Bai damu da ƙarnin jinin da ke a jikinta ba, sai dai zuciyar shi ta rikice ya shiga ruɗanin ganin canzawar da ta yi, Jikinta duk raunuka ta yi muni kamar ba Angel ɗinsa ba, Tunawa da Ƴan uwanta da kuma ƙurarren lokacin da ke gare su yasa tace mashi”Ka tashi mu tafi Danish ka kaini ɗaki, na bar su Azeeza suna jiran mu” shiru bai motsawa ba saboda ya rasa tunanin shi.
Bugun bayan shi ta dinga yi da hannunta Cikin shessheƙar ku ka ta ke faɗa mashi Ya tashi ya ɗauke ta suje ɗaki ƴan uwan su na acikin haɗari, “ daƙyar ta samu Danish Ya miƙe ɗauke da ita saman faffaɗar kafaɗar shi, daga ina ya ke a tsaye Ya 6ace bai dura a ko’ina ba sai A cikin ɗakin su, Tunkan ya sauke ta ta riga zame jikinta, Su Haris da ke a tsaye bakin ƙofar ɗakin tsohuwa, a ruɗe su ke kallon shi Musamman Gabriel yasha ruwan mamakin ganin Danish da idon shi Garas.