← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 152

Sashe 121

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Duk da bansan abunda ke damunshi ba, amma idan har mutunne ya rikida hakan na nufin aljanune atare dashi ko”?
Ɗaga mashi kai owais Yai”haka muke tsammani”
Hateem Ya numfasa kafin Yace”Inason ganinshi idan yadawo suffarshi ta ainahi, sannan Yakamata a kira sheikh imam ya duba shi, ina da tabbacin zai Iya taimaka mashi”
Amsa mashi yai da toh, daga haka sukayi sallama owais ya fuce daga falon.
Bayan tafiyar owais, su Hateem suka raka baba obie bedroom dinshi, babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwanta ya runtsa amma Yaƙiya gani yake tamkar macijin zai faɗo ɗakinshi, duk yabi ya firgice, adole mutun biyu suka tayashi kwana, Sharafudden da senate lateef, sauran kowa Ya nufi masaukin shi.
Hankalin Hateem Yaƙi kwanciya, Macijin Ya tsaya mashi aranshi, ya ƙwalla fa rai akan son ganin yaron, ko bayan daya koma Gidanshi dake a estate din, a ɗaki ya tarar da gimbiya mujeedat, tana faman yin zarya, ta kasa kwanciya saboda rashin dawowarshi, babu wanda yasan abunda ya faru a gidan baba obie sai wadanda ke zaune agidan.
Bai sanar da ita komai ba, Saman gadonsu Ya haye ya kwanta yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, tayi mamakin ganin damuwa atattare da mijin nata, har tambayarshi tayi meke damunshi amma sai yace mata babu komai, bacci yake ji, ƙoƙarin faranta mashi tayi har saida ta tabbatar ya fara yin bacci tukunna hankalinta ya kwanta.

*SIR MUBARAK✊*

Babu wanda ya motsa acikinsu, tun da suka ji muryar mutumin daya kira layin jazz, Jikin kowannansu yai sanyi laƙwas tamkar an zare masu laka, har sun fara danasanin jahilin bugun da sir mubarak yaiwa jazz domin kuwa sun tabbatar sune sukayi kuskuren yanke hukunci batare da sun fara bincikarshi ba.
Yarinyar dake a zaune dirshan idanuwanta sun kaɗa jawur yayin da hannuwanta ke asaman fuskar jazz.

kafin Sir mubarak Yai ƙwaƙƙwaran motsi, Muryoyin yaran dake tunkaro ɗakin Ya karaɗe kunnuwan sojojin
Kusan atare suka ɗago suna kallon baƙin ƙofar shigowa ɗakin.

Matasan ƴan mata ne kowaccensu sanye cikin rigunan bacci, babu huluna akansu sai zallar sumar kansu mai tsayi har gadon bayansu, namiji ɗayane acikinsu shima kayan baccin ne ajikinshi, fuskokinsu a yamutse sai hamma suke Yi, ga dukkan alamu kukan ƴar uwarsu ne Ya farkar dasu daga bacci.

“Meya faru da yaya jazz dinmu? Su wanene ku”? Har suna haɗa baki wurin tambayar sojojin.

Cikin shessheƙar kuka Yarinyar dake ruƙe da dr. Jazz ta kware murya tana kallon ƴan uwan nata tace”Sun kashe mana shi, bansan su wanene su ba, kawai sun shigo mana gida sun kama bugunshi”
Fashewa sukayi da kuka kamar gidan mutuwa, da gudu suka nufi inda yarinyar take a zaune, a kewaye da dr jazz suka zuƙunna Suna ambaton sunanshi tamkar ransu zai fita.
Ba zato ba tsammani, sojojin suka jiyo muryar babban mutun Yana fadin”meke faruwane? Su wanene suka shigo gidan”?
Fadowa cikin ɗakin Yayi, daga shi sai short a jikinshi babu riga, yana da faffaɗan kirji ga ƙirar ƙarfi kamar ɗan dambe, kallon ɗaya zaka yi mashi ka shaida farar fatane, fatarshi jawur take daga gani bature ne.
Lokacin da yai arba da su sir mubarak a ɗakin Ras yaji gabanshi yai mugun faɗuwa, adabarbace ya furta”su wanene ku? Meya kawo ku cikin gidan nan”? Kafin wani ya furta kalma, Mutumin ya wurga idanuwanshi akan yaran dake kuka.
Zaro idonshi waje yai ganin yadda suka raunata jazz, da ƙarfi yace”don ubanku ku faɗamin su wanene ku? Uban me yayi maku da kukayi mashi wannan bugun? Waye ya turo ku? Babu alamun tsoro akan idanuwanshi, sai ma dunƙule hannayenshi da yai da niyar yakai masu hari,
An rasa me magana tsakanin Sir mubarak da su tiger.
Gigitacciyar tsawa ya daka masu Yana fadin”bakuji ina magana ba? Idan har baku faɗamin ba, daya bayan ɗaya zan salwantar da rayuwarku”
A harzuƙe tiger da Major suka zaro bindigunsu tare da saita shi, maimakon yaji tsoron bindigar hannunsu sai gani sukayi Ya sanya hannu ya daki ƙirjinshi da ƙarfi Yana fadin”Kunyi kuskuren shigowa gidan nan, abun hannunku bai isa yasa inji tsoronku ba, tunda kuka ta6a jazz sai kunyi danasanin haihuwarku da uwarku tayi acikin duniyarnan, kawai saboda zalunci saiku faɗo gidan mutane kukama bugun mutun baiyi maku laifin komai ba”? Tamkar mayunwacin zaki haka yake yi masu magana yana fitar da huci mai ɗumi
Daƙyar sir mubarak Ya iya sarrafa kanshi, muryarshi a haushine ya furta”dan Allah ka faɗamin wanene kai, Ni da kake gani mahaifin jazz ne, mun shigo gidan nan batare da sanin shi ba, saboda mu atunaninmu wani mugun abun yake aikatawa.....” a tsanake sir mubarak Ya kwashe duk abunda Ya faru dangane da zargin da yake yima jazz ya sanar da matashin saurayi
Lokaci ɗaya sukaga ya sassauta fushin fuskarshi, ga dukkan alamu ya fahimce su.
“Amma baku kyauta mashi ba, shiyasa akace zato zunubi koda ya kasance gaskiya, jazz dai ba mugu bane, mutumin kirkine fiye da tunaninka, waɗanda yaran kuma dakuka gani marayune basu da gata aduniyar nan daya wuce Allah sai kuma waɗannan bayin Allahn da suka taimaki rayuwarsu” yai maganar yana nuna jazz da hannunshi, Yaran dake sauraron su idanuwansu sunyi luhu luhu sunsha kuka kamar ransu zai fita don ba ƙaramin ƙaunar jazz suke Yi ba
Cikin karyayyar murya sir mubarak yace”kana nufin Chief owais shine ke kula daku? ya tambayeshi saboda yaji muryar owais a wayar jazz yana da tabbacin shine Ya kira layinshi

Jinjina kai mutumin yai”ƙwarai kuwa, a ƙarƙashin kulawarshi muke gaba ɗayanmu, shi kuma jazz shine likatan daya dauki nauyinshi don kula da marasa lafiyan cikinsu, Yarinyar nan kuma daka ganshi atare da ita saman gado, bata da koshin lafiya, tana da ta6in hankali, ga magungunanta can saman drawer da alluran da yake yi mata, abunda yasa kuka same shi asaman kanta, ni nasan saboda babu mai iya rike mashi itane, idan dare yayi bayason tashina daga bacci, ni ne nake taimaka mashi wurin ruƙeta ayi mata allura saboda buge bugen da take Yi, idan har ba a ruƙeta ba baza a iya yi mata allura ba, tana da ƙarfine, kunyi zargin jazz yana aikata fasiƙanci da ita bahaka bane abunda na faɗa maku shine gaskiyar zance’
Dafe kai Sir mubarak yai da hannu ɗaya, Wani irin matsanancin ciwon kaine ya farmashi, su tiger sunyi danasanin zargin jazz da sukayi jikin taƙaura yayi la’asar
“Dan Allah ku taimaka mashi kada ya mutu, har yanzu baidaina bleeding ba” ɗaya daga cikin matasan yaran ce tayi maganar, fashewa sir mubarak yai da kuka tamkar ƙaramin yaro, cikin rauni na murya yake fadin”Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’u! Jazz baka kyautamin ba, meyasa baka sanar dani ba, kabar ni inata zarginka gashi har nayi maka illah! Yanzu ya zanyi? Me zan faɗama mahaifiyarshi? Matar da ko bacci bata iyayi idan har bai dawo gidaba saboda ƙaunar da take yi mashi!
Juyawa yai da sauri ya nufi inda yaran suke, bai bi takansu ba, ya sanya hannayenshi biyu ya cuccu6i Jazz Ya ɗaura shi saman kafadarshi, ya dubi su Tiger da rinanun idanuwanshi yace”major muje mu kaishi asibiti, kai kuma Tiger ka tsaya atare da army ku lallashi yaran dan Allah” ya ƙare maganar da sauri ya nufi ƙofar fita, Major yabi bayanshi bayan ya kar6i key din motar a hannun tiger.

Har sun kusa futa daga dakin, matashiyar nan mai fama da ta6in hankali ta fasa ƙara hadi da yunkurawa ta mike aguje tabisu tana fadin”mugaye ku dawo mana da ɗan uwanmu kada ku kashe shi, wayyo Allahna Yaya kana gani zasu gudu dashi “ har takusa fucewa daga ɗakin, Mutumin Ya damƙo damtsen hannunta, Ya rungumeta a chest dinshi yaci gaba da lallashinta.
Tiger ne ya soma lallashin ƴan uwanta dake kuka
“Kuyi haƙuri, kuskure mukayi wurin bugunshi, mu ba mugaye bane kamar yadda kukayi tsammani, mutumin daya dauki jazz mahaifinshine ba wani ba, kuma asibiti zasu kaishi inda za’a duba lafiyarshi, da zarar yaji sauƙi za’a dawo maku dashi” cikin shessheƙar kuka suka amsa mashi da toh, banda mahaukaciyar yarinyar daketa ɗura masu ashar, kamar zata bugesu, mutumin ya ƙankameta ya hana ta kubce mashi.

Kusan rabin awa da tafiyar Sir mubarak, motar Big guy ta shararo da gudu cikin unguwar, tunkafin ya ƙarasa bakin gate din gabanshi ya fara faɗuwa ganin ƙofar gate din abude kusan ƙarfe goma sha ɗaya na dare, nan take ranshi ya bashi cewar wani mummunan abunne ya faru watakil shiyasa lokacin da chief Ya kira wayar jazz yace mashi ya ɗaga baiyi mashi magana ba!!!!😳😳😳

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✊✍️💋🤍*

A tsiyace yai parking din motar, tsabar sauri a buɗe yabarta, da gudun gaske ya nufi cikin gidan batare da jin shakkar komai ba, Shigar shi keda wuya cikin falon ya soma jiyo sautin kukan yarinyar nan mai fama da ta6in hankali, ta dage sai zazzaga masifa take yi tana fadin”wallahi saina tona maku asiri ranar lahira, dukanku sai kun shiga wuta tun da ku ka ta6a min yaya jazz ɗina”. Zuciyarshi ce ta soma dukan uku uku, zaro bindigarshi dake soke a ƙugunshi yai, cikin sanɗa yake tafiya yana tunkarar Upstairs, Ya haura second floor, daga ƙofar ɗakin Ya la6e Yana sauraronsu.

“Ki daina magana mana, bakiji suna bada hakuri ba? Kuskure suka yi wurin bugunshi, bada son ransu ba”

Jin muryar mutuminsu yasa shi yin wuff Ya afka cikin ɗakin, Jin takun tafiyarshi ne Ya janyo hankulansu ga dubanshi, kusan atare suka ɗago suna kallon shi.

Nauyayyar ajiyar zuciya big guy ya sauke haɗi da furta”Ya Allah” kafin Ya daura eyes dinshi akan face din mutumin yace”meke faruwa ne ? Waya ta6a khadeeja take kuka? ya akai naga yaran duk sun farka daga bacci”?

A ruɗe yake jefa mashi tambayoyin, sam bai lura da Sojojin ba, waɗanda tun da ya shigo suke dubanshi da mamaki.

da ido mutumin Yai mashi nuni da sojojin”gasu nan, mahaifin Jazz ne yazo tare dasu, wani abune ya faru na rashin fahimta da yajawo har suka bugi jazz shine take ta kuka”

A hanzarce ya mayar da dubanshi ga Sojojin, Kusan atare suka buga ƙafa tare da Sara mashi.

Jinjina kanshi yaɗanyi da mamaki ya furta”Tiger ! Army Boy! Ya akai kukazo gidan nan?
Chapter 121 · 0% Book details